Skip to content
Part 26 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Kaso arba’in da biyar cikin ɗari na baƙin cikin da suka ƙunsa mata ya ragu sanadiyyar wannan matakin da ta ɗauka a kansu. Ko banza ta rama ma Shahid ninkin ba ninkin marin da Fatima tayi masa.

Shi kuwa Mukhtar! Ƙaƙƙarfan ƙwafa ta sake tana jijjiga kai, alamun da ke nuna basu gamu ba tukun! Za dai su gamu.

Ƙofar ɗakin da suka shige ta gallawa wata matsiyaciyar harara, sannan ta fice da sassarfa zuwa ɓangarenta. Ko da ta leƙa ƴaƴan har lokacin barci suke yi, har ta juya za ta shiga banɗaki sai kuma ta juyo da sauri ta sake kallonsu.

Barci suke yi, amma suna ta ɗan rawar ɗari alamun suna jin sanyi. A gaggauce ta ƙarasa ta taɓa jikinsu sai taji zafin ya ninninka na ɗazu. Hankalinta ne ya ƙara tashi.

Idanunta suka cicciko da hawaye. Bargo ta janyo ta rufa musu sannan ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwalar sallar la’asar. Jikinta a sanyaye ƙwarai, akai-akai take sharar ƙwallah har ta kusa idar da sallar.

Tana sujuda a raka’ar ƙarshe tana fara addu’a hawaye ya ɓalle mata. Cikin kuka take faɗa ma Allah ga halin da take ciki ya dubeta ya kawo mata mafita da gaggawa.

Bayan ta idar ta daɗe zaune kan sallaya, babu abinda take yi sai istigfari, tasbihi, hailala. Gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi, lokaci bayan lokaci take ɗaga idanu ta kalli ƴaƴan da suke barci da zazzaɓi a jikinsu.

****

“Hello! Hajiya kina ji na?”

Ta tambaya bayan ta ji ntwk ɗin wayar kamar ya fara rawa. Ba sosai take jin muryar Hajiyar na fita ba.

Tsinkewa kiran yayi, kafin ta sake kira sai ga kiran Hajiyarmu ya shigo cikin wayarta. Sabon gaisuwa ta sake yi ma Hajiyar a ladabce, da muryarta a sanyaye ƙwarai, har sai da Hajiyarmu ta ce.

“Ina jin ki Fareeda. Me ya samu muryarki? Kina mura ne?

“A’a! Lafiyata ƙalau Hajiya.”

Sai kuma ta ɗanyi shiru, kafin ta cigaba da cewa

“Hajiya ga su Sayyid kwance babu lafiya. Don Allah, idan babu damuwa ki aiko direba ya kwashe su zuwa gurinki.”

Sai muryarta ta fara rawa, alamun ko wane lokaci za ta iya fashewa da kuka.

“Zafin jikinsu ƙara hauhawa yake yi tun da rana. Tsoro nake ji, don Allah ki aiko…”

Ƙit wayar ya sake katsewa a karo na biyu.

Ajiye wayar tayi a gefe ɗaya ta kifa kanta hannun kujera, hawaye wasu na korar wasu a idanunta. Yanzu gurin awa huɗu da rabi kenan suna kwance, tun suna barci da rawar sanyi da zafin zazzaɓi sama-sama, yanzu jikin nasu ya sake ɗumewa sosai da zazzaɓi. Sun farka, sai suka fara wani irin nishi sama-sama suna kuka suna surutan da sam ba ta gane me suke cewa.

Ko da tayi yunƙurin ɗaga su zuwa jikinta sai suka zame suka ƙara kwanciya kan gado. Shahid da ya fi Sayyid zafin zuciya har wannan lokacin bai daina sauke ajiyar zuciya ba. Farar fuskarsa ta ƙara wani irin jaaaa, shatin yatsun Fatima sun sake fitowa ruɗu-ruɗu a ƴar ƙaramar fuskarsa.

Da da ne da bata shiga cikin hankalinta kan fita ba da izinin mijinta ba a fujajan za ta kwashe su zuwa asibiti. Amma a yanzu baza ta iya ba, ko kusa baza ta iya sake maimaita makamancin kuskuren da ta dinga aikatawa a baya har ya janyo mata faɗawa cikin ƙaƙanikayi a yanzu ba.

Wani irin fushi ne ta ɗauka da Mukhtar, ko da zazzaɓin yaran zai ninka haka ya sake ninkawa ba ta jin za ta iya ɗaga wayarta ta kira shi balle har ta sanar da shi halin da suke ciki. Kuma ba ta son kiran ƴan’uwanta ta ɗaga musu hankali.

Tsoron kar yaran su mace mata ita kaɗai a cikin ɗaki yasa ta yanke shawarar kiran Hajiyar, ta sanar da ita halin da yaran suke ciki.

Wai aka ce abin cikin ƙwai ya fi ƙwan daɗi, jika wahal da kaka. Fareeda da take ta saka idon ganin direba ya zo kwasan yaran sai ga Hajiyar da kanta, wani abu da Hajiya ta kwana biyu bata yi ba shi ne tuƙa mota da kanta zuwa unguwa. Amma yau saboda zaƙuwa da son ganin halin da ƴan biyun jikokinta ke ciki ta kasa jiran ƙarasowar direba, tun da ta kira shi ya ce mata yana hanya taga an shafe mintuna goma bai zo ba kawai sai ta tuƙo motar da kanta, ga dare ya fara shiga, lokacin ƙarfe bakwai da rabi na yamma.

Ƙarfe takwas da minti ashirin sai ga sallamar Hajiya a ƙofar falon Fareeda, sai kuma ta ƙara da ƙwanƙwasa ƙofar da ɗan ƙarfi ta yadda duk inda mai ɗakin take za ta ji.

Ta fito daga kicin kenan ta haɗo musu tea ɗan kaɗan ko za su sha ta tsinkayi ƙwanƙwasa ƙofar. Da gaggawa ta ƙarasa ta buɗe, suna haɗa idanu da Hajiyar ta kasa riƙe kanta, sai kawai ta faɗa jikinta ta fashe da kuka mai ƙarfi.

Da walakin goro a miya. Tun daga yadda Hajiyarmu ta ji muryarta a waya ta san ba damuwar ciwon ƴaƴan bane ya ɗaga hankalin Fareeda haka. Tana riƙe da ita a jikinta taja ta zuwa kan kujera suka zauna, tsawon lokaci tanz sharɓen hawaye kanta na kwance kan kafaɗar Hajiya. Kafin ta fara ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi.

“Ya isa haka. Ummm?”

Daƙyar ta samu ta tsayar da kukan da take yi, ta zame ƙasa ta gaishe da Hajiya, idanunta sun kaɗa sunyi jajur, har wani ɗan kumbura suka yi.

“Me yake faruwa? ina yaran?”

Hajiyar ta tambayeta.

“Suna cikin ɗaki.”

Ta amsa tambaya ta biyu kanta a ƙasa.

Bata sake cewa komai ba ta miƙe ta nufi cikin ɗakin, Fareeda na biye da ita a bayanta. Ganin wani irin kwanciya da yaran suka yi yasa hankali tashe Hajiyar ta zauna gefen gadon haɗe da janyosu zuwa jikinta.

“Subhanallahi, Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un! Wani irin zazzaɓi ne haka ya rufe su lokaci ɗaya? Ko sun daɗe suna ciwon ne?”

Ta jero tambayoyin a ruɗe tana kallon Fareeda. Sai kuma ta mayar da hankali kan yaran, ta taɓa jikin wannan ta taɓa na wancan, hankalinta a tashe. Karaf idanunta ya faɗa kan fuskar Shahid, idanu warwaje ta shafa gurin shatin yatsun a tsorace.

“Miye nake gani haka? Wannan ai kamar shatin yatsun hannu ne. Dukansa kika yi? Fareeda wannan ɗan ƙaramin yaron kika mara haka? Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un… Fareeda kin haukace ne…?”

“Hajiya ba fa ni na mare shi ba.”

Ta faɗa cikin rawar murya.

“Amaryar Mukhtar ce ta mammareshi.”

Ta ƙara da faɗin haka don wanke kanta.

Tsuru Hajiyar ta ƙura ma Fareeda idanu, kamar wacce ta warke makanta, bakinta a buɗe, don tsananin mamaki.

“Ta mam-mare shi?”

Ta figo maganar daƙyar daga maƙogwaronta.

“Marin ma ba ɗaya ba? To me yayi mata?”

“A kan idanuna tayi mishi mari biyu. Ni ma bazan ce ga takaimaimai abinda yayi mata ba. Fita suka yi suna buga ƙwallo ina kwance kan kujera na jiyo ihunsu.”

Wani irin matsanancin ɓacin rai ne ya mamaye mamakin da ke kwance male-male kan fuskar Hajiya. Ta yunƙura ta miƙe tsaye da Shahid rungume a jikinta.

“Ɗauko Sayyid ki fito min da shi.”

Ta umarci Fareeda. Sannan ta fice daga cikin ɗakin.

Ko da suka fita falo ita Fareeda ta zaci Hajiya za ta fita da yaran zuwa gurin motarta ne sai taga Hajiyar ta zauna kan kujera. Ta ɗauko wayarta a cikin jaka ta danna ma Mukhtar kira.

A can tsakar gidan shi kuma Mukhtar ya dawo sallar isha’i kenan ya ci karo da motar Hajiya. Mamaki ne ya kama shi, da sassarfa ya nufi ɓangaren Fareeda, fuskarsa a ɗaure tamau. Zuciyarsa cike da tunanin irin zazzafan matakin da zai ɗauka kan Fareeda. Duk a tunaninshi ko Fareeda ta kai ƙararshi ne gurin Hajiyarsu, wato ita ne mai bakin kai ƙara bayan duk irin haukan da ta zuba musu ɗazu ko? Lallai zai nuna mata ita ƙaramar mara kunya ce.

Fatima tana zaune a gefen gado, hannunta riƙe da ɗan ƙaramin madubi tana kallon kumatunta da suka tasa saboda marukan da ta sha a hannun Fareeda. Man zafi ne ajiye a gefenta, idan ta dangwalo man zafin sai ta shafa a kumatun, zuciyarta a ƙuntace da ɓacin rai. A zamanta gefen gadon ta tsine ma Fareeda ya fi baki ɗari.

Kwatsam kira ya shigo wayar Mukhtar da ke ajiye a gaban madubi. Kamar baza ta ɗauka ba, sai kuma ta miƙe a hankali ta ƙarasa gurin tana kallon fuskar wayar.

Gabanta ne ya ɗan faɗi ganin sunan wacce take kiranshi. Ta san mahaifiyarsa ce, don ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ta sha raka Fareeda gidansu Mukhtar ɗin. Ta san ƴaƴanta gaba ɗaya har Fareeda da Hajiyarmu suke kiranta. Kamar baza ta ɗaga ba, sai kuma wata zuciyar ta ingiza ta ta ɗaga kiran, ta lanƙwashe murya sosai cikin firirita ta fara gaishe da Hajiyar.

“Keh! Wacece ke da har za ki ɗaga kiran da nayi ma mamallakin wayar?”

Aka faɗa mata cikin tsawa daga can ɓangaren ba tare da an amsa gaisuwarta ba.

“Kiyi haƙuri Hajiyarmu. Baya nan ne ya tafi masallaci. Amaryarsa ce, Fatima, ina yini?”

A daidai wannan lokacin Mukhtar ya murɗa hannun ƙofar falon Fareeda ya shiga ciki, bakinsa ɗauke da sallama.

Tsakanin Hajiya da Fareeda babu wacce ta amsa sallamarsa a fili. Hajiya ta kalle shi da wani irin fusataccen kallo ba tare da ta katse wayar ba ta ce

“Wace ƴar iska ce ka ba damar ɗaga min waya idan na kira?”

Tsuru yayi cikin dambarwa yana kallon Hajiyar, ya rasa ta cewa. Abinda ya sani kawai shi ne ya bar wayarsa a ɗakin Fatima, amma shi bai bata umarnin idan an kira shi ta ɗaga ba.

A can ɓangaren Fatima cikin sauri da tsoro ta katse wayar. Tayi saurin ajiye wayar a inda ta ɗauka. Jikinta a saɓule ta koma gefen gado ta zauna. Ta buga tagumi da hannu bibiyu. Sai kuma ta miƙe zumbur ta nufi falonta, labule ta yaye ta leƙa tsakar gidan. Ganin baƙuwar mota a fake yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfi.

“Hajiyarmu na cikin gidannan ke nan? ko dai Fareeda ne ta kira ta?”

Ta tambayi kanta.

“Na shiga uku!!”

Ta faɗa a fili, idanunta a warwaje ta ɗora hannu akai.

Nan take ta fara safa da marwa a tsakiyar falon cikin ruɗu da tashin hankali. Cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa zufa tayi kashirɓin. Sai tufka da warwarar maganganun da za ta faɗa don kare kanta a gaban Hajiya take yi. Ruwa ba ya tsami banza, zuwan sarkuwar nasu bagatatan a wannan dare dole akwau dalili.

Tana wannan zurga zurgar sai ga Mukhtar ya buɗe ƙofar falon ya shigo babu ko sallama. Fuskarnan a ɗaure tamau. Ya kalleta ya aika mata da wani mugun kallo.

“Me yasa kika ɗaga min waya?”

Ya tambayeta a fusace.

Ƙwalƙwal tayi da idanunta, ta lanƙwasa kanta a hankali ta ce

“Kayi haƙuri. Na ga Hajiyarmu ce…”

“Hajiyarki ko tawa?”

Ya daka mata tsawa da wannan tambayar.

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa, jikinta sai kyarma yake yi a tsorace.

Yayi ƙwafa, ya juya ya nufi hanyar fita yana cewa

“Ki biyo ni zuwa falon Fareeda. Hajiya tana son ganinki, saura kuma ki tsaya ɓata mata lokaci ki ga yadda za mu kwashe da ke a darennan”

Ko da ya koma can falon ya sanar ma Hajiya ga Fatima nan zuwa kamar yadda ta buƙata juya mishi da fuskar Sayyid tayi yaga abinda ke kwance a kumatunsa.

Don ɗazu da ya shigo hankalinsa na kan Hajiyar, duk a tsammaninsa ƴaƴan barci suke yi, Shahid a jikin Hajiya Sayyid a jikin Fareeda.

Ckin fushi da fusatar da ya daɗe bai gani a fuskar Hajiyarmu ba ta ce

“Ka ga fuskar Shahid ko? To ba shatin komai bane wannan sai shatin yatsun amaryarka. Idan ita shafaffiya da man taka ta shigo, ka tambaya min ita me wannan ɗan ƙanƙanin yaron yayi mata da zafi da har za ta yi mishi irin wannan marin na tsantsar zalunci da rashin tausayi. Ina so ka sani, ko tana da ƙwaƙƙwaran hujja sai na rama ma wannan ɗan tatsitsin yaron marin da tayi mishi. Idan kuwa ba ta da ƙwaƙƙwaran hujja hukuma ce za ta raba ni da ita.”

A daidai lokacin Fatima ta sanyo kanta cikin falon, karaf maganar Hajiya ya sauka a kunnuwanta. A kiɗime ta zube ƙasa tun daga kan kafet ɗin bakin ƙofa.

“Na tuba Hajiya. Na bi Allah na bi ki. Don girman Allah kiyi haƙuri ki yafe min.”

Ta faɗa a tsorace da saurin baki, hankalinta a tashe.

A cikin su ukun babu wanda ya tanka mata. Fareeda kawar da kanta tayi gefe ɗaya tana jin yadda sabon ɓacin rai ya lulluɓeta da ganin Fatima.

Hajiya kuwa ƙura ma Fatima idanu tayi, zuciyarta cike da mamakin yadda a mafiyawancin lokuta soyayya ke kauce hanya. Lallai so hana ganin muni ko rashin dacewa.  Saboda Allah mai dirarriyar mace kamar Fareeda me idanunsa za su hango a jikin Fatima?

Mukhtar dai tun da yaga fuskar yaron yayi suman tsaye na tsawon wasu daƙiƙu, idanunshi a warwaje baki a buɗe. Kamar wanda aka sheƙa ma ruwan sanyi haka ya dawo hayyacinsa a firgice ya juya gurin Fatim. Bakinshi na rawa kamar mai taunan ƙanƙara a lokacin sanyi.

“Fffffffffatima…? Me yayi miki kika mmmmmmare shi?”

Ya ƙarasa da wani irin in-ina a muryarsa.

Sai kuma ya juya jikinsa na rawa ya ƙarasa kusa da Hajiya ya karɓi yaron da jikinsa yake ligif, kamar wanda ya suma.

“Na shiga uku! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Hajiya, ai kamar ma baya motsi. Na shiga uku!! Shi kenan ta kashe min ɗa saboda zalunci da son zuciya…”

A bazata wani jiri ya taho zai kifar da shi da saurin gaske Hajiya ta karɓe yaron hannunsa, ta galla mishi harara ta ce

“Idan za ka faɗi, ka kifa kai kaɗai. Kowa ya ɗeɓo da zafi bakinsa.”

Ta mayar da hankalinta kan Fatima ta ce

“Keh! Ban kira ki nan domin ki min magiya ko daɗin baki ba. Kin ga waɗannan”

Ta nuna ƴan’biyu, sai ta cigaba da cewa

“A yanzu na fi ƙaunarsu akan mijinki. Don haka maza faɗa min abinda yasa kika yi mishi irin wannan ɗanyen hukunci.”

Ta ƙarashe da tsawa sosai a muryarta.

Hannu bibiyu Fatima ta ɗora akai ta cigaba da sharɓan kuka. Ko da tayi katarin kai idanunta cikin na Mukhtar da yanayin neman agaji wani irin mahaukacin kallo da ya aika mata kamar zai cinya ta ɗanye ba shiri ta janye idanunta daga cikin nashi.

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi, sai kuma ta ɗago ta kalli Hajiyar. Kwarjini da haibar da ke fuskar Hajiya yasa duk ƙarerayin da ta shiryo daga ɗakinta suka ɓace ɓat a ƙwaƙwalwarta.

Ba ta da yadda zata yi dole ta faɗi gaskiyar abinda ya faru. Ashe suna buga ƙwallo ne sai Shahid ya ɗauki ƙwallo ya ruga da gudu ɗan’uwan na bin bayansa suna dariya. Yana wannan gudun har ya ƙarasa ƙofar ɗakinta, ita kuma a daidai lokacin ta buɗe ƙofa sai ya faɗa jikinta.

“Shi ne na ɗan mare shi…”

“Kika mare shi?”

Mukhtar da Hajiya suka haɗa baki gurin tambayarta a mamakance.

Saboda tsananin kunya da muzanta ta kasa amsawa. Sai ƙarfin gudun hawayenta da ya ƙaru.

“Mari nawa kika yi mishi?”

Hajiya ta tambayeta.

Shi kuma Mukhtar a zafafe ya ce

“Amma ni mai kika faɗa min ta waya? Ƙarya kika yi min kenan?”

“Hajiya don Allah kiyi haƙuri, ki yafe min. Mari uku kacal nayi masa, nayi mishi ɗaya kafin fitowar Fareeda nayi mishi biyu kuma a gabanta, ki tambayeta…”

Tsakanin Hajiya da Fareeda babu wanda ya lura da miƙewar Mukhtar da ƙarasawarshi kusa da Fatima kamar wani walƙiya, kawai dai sun ji kakarinta ne saboda wani irin muguwar shaƙa da yayi mata daga tsugune. Idanunsa sun kaɗa sunyi jajur yake cewa

“Ɗan ƙaramin yaron nawa za ki yi ma mari har uku saboda ke ɗin azzaluma ce muguwa mare imani? Ɗana za ki kashe Fatima? Ɗan nawa za ki kashe? To bari ni in fara kashe ki tun kafin watarana ki kashe min ɗaya daga cikinsu.”

Daƙyar Hajiya ta samu nasarar ɓamɓare hannun Mukhtar a wuyan Fatima. A lokacin ta galabaita iya galabaita, gwanin ban tausayi. Ta ma kasa miƙewa tsaye, tana kwance wanwar a tsakar ɗakin tana jan numfarfashi a wahalce.

Fareeda dai tana zaune kakim kamar dutse, ko kallonsu bata yi ba. Ita fa Allah ya sani gaba ɗaya lamarin Mukhtar da Fatima sun ƙarasa fice mata arai.

Daman tuntuni ta aje lamarin Fatima a gefe ɗaya ne. A yanzu ta yanke shawarar ƙarasa ajiyeta gefe ɗaya, babu wani abu da zai zo ya gitta a tsakaninsu in Allah ya yarda. Idan kuwa ita Fatiman tayi kuskuren sake shiga harkokinta za ta daka ta ne, tsakaninsu yanzu ba sanyi ba sanyayawa.

Shi kuwa Mukhtar, wani irin zama ne ta ƙudura a ranta za su juya yi ita da shi. Zama shigen na mace mai sayar da ruwa da mijinta mai faskare, idan ya ɗauke mata gammo ta ɗauke mishi gatari.

Tana kallon yadda Mukhtar yaja Fatima kiiiii a wulaƙance kamar kayan wanki ya fice da ita daga falon Fareeda. Duk yadda Hajiyar ke mishi faɗan ya tallafeta a hankali bai saurara ba sai da ya kaita waje ya yasar.

Hankali tashe ya sunkuci Sayyid a jikin Fareeda Hajiya ta riƙe Shahid suka fice da nufin kai yaran asibiti.

“Ki taho mu kaisu asibiti.”

Ya faɗa ma Fareeda a tausashe.

Wani irin kallo da tayi mishi kamar na ƙyama da sauri gaske ya kawar da fuskarsa daga gare ta.

“Kuje kawai. Ko kuma ka tafi da Fatima ita mai tarbiyya wacce ta iya bayar da tarbiyyah”

Ta faɗa mishi cikin gatse da gatsali.

<< Rabon A Yi 25Rabon A Yi 27 >>

2 thoughts on “Rabon A Yi 26”

  1. Ma sha Allah
    Sannu da aiki ya mai jiki
    Allah ya qara sauki.
    Allah ya qaro fasaha
    Muna jin dadin wannan littafi
    Da Kuma frequent update
    Jazakillahu khair

  2. Na ji dadin wannan chapter sosai
    Allah ya bawa mara sa lafiya isasshen lafiya Allah ya kuma sa a gama bikin lafiya. Mun gode

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×