DakikaMintinaAwanniKwanakiSatittikaWatanniShekara dayaShekara biyu...Gani yake kamar idanuwan shi ya rufe ranar da Mero ta tako cikin gidan shi a matsayin mata, ya bude su ya ganta rike da rabon da suka samu, ya ganta rike da dansu Haidar. Ba akan shi aka fara masa haihuwa ba, tun da ga Salim, ga kuma Fadila, ga kuma wani cikin a jikin Saratu, dan haihuwar gab da gab takeyi. Abubuwa da yawa sun faru daga ran daren aurensu zuwa yanzun. A cikin wannan abubuwan akwai batan Yelwa da har yanzun suke cikin duban hanya don ganin ta inda zata bullo.Mutum, ba dabba. . .
Julde Bai kyauta na rayuwarshi ba