Skip to content
Part 39 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

Dakika
Mintina
Awanni
Kwanaki
Satittika
Watanni
Shekara daya
Shekara biyu…

Gani yake kamar idanuwan shi ya rufe ranar da Mero ta tako cikin gidan shi a matsayin mata, ya bude su ya ganta rike da rabon da suka samu, ya ganta rike da dansu Haidar. Ba akan shi aka fara masa haihuwa ba, tun da ga Salim, ga kuma Fadila, ga kuma wani cikin a jikin Saratu, dan haihuwar gab da gab takeyi. Abubuwa da yawa sun faru daga ran daren aurensu zuwa yanzun. A cikin wannan abubuwan akwai batan Yelwa da har yanzun suke cikin duban hanya don ganin ta inda zata bullo.

Mutum, ba dabba ba, a wayi gari ace an nema sama ko kasa an rasa? Kwanaki bakwai bayan bacewarta, bai san abinda Dije take ji ba, hakama Datti, ya shiga gidan ya same su zaune duka suna kuka, babu wanda yake yunkurin bawa wani hakuri a cikinsu, sai ya juya kawai batare da yace musu komai ba, shima idan ya fita da safe hanyoyi kawai ya kebi, inda duk kafarshi ta dauke shi sai duhu ya farayi tukunna ya dawo. Yayi tunanin duniya ko a cikin hirarrakinsu Yelwa tayi wata magana da zata saka shi fahimtar inda take, amman ya rasa. Rabi da kwatar hankalin shi yana kan dokin ganin Mero ta zama mallakin shine, gata a cikin gidan shi, su kwana su tashi daki daya, amman bashida nutsuwar nuna mata tarin kaunar da yakeyi mata.

“Akwai abinda zan maka ka kasa yafe mun Hamma?”

Ta tambaye shi kwanaki biyu kafin daurin auren su, cike da mamakin tambayar ya girgiza mata kai.

“Abinda nayi maka wanda ka sani da wanda baka sani ba, da ma wanda zanyi maka a gaba duk ka yafe mun?”

Murmushi yayi, yasan bata son Modibbo, amman a cikin idanuwanta yake ganin wani yanayi na mika kai, da kuma sallamawa da cewar bata da wani zabin daya wuce hakuri da auren.

“Auren nan bashi bane karshen duniyar ki Yelwa, ki kwantar da hankalin ki, nima nayi nawa binciken, Modibbo bashida wani hali marar kyau.”

Murmushin da ta mayar masa ya karya wani bangare na zuciyar shi, saboda ta saka shi hasaso ace masa ya hakura da auren Mero, ko kuma a musanya masa auren nata da wata duk kyawunta da kyawun halayenta. Sai yaji ko Marake zata hade abune da ba zai taba yarda dashi ba.

“Kiyi hakuri…”

Ya furta da sanyin murya wannan karin, sai tayi dariya, dariyar da yake juyowa har yanzun, saboda ta zama kamar itace dariyarta ta karshe da yaji.

“Kaunar da nake maka mai yawa ce Hamma, kai dai ka yafe mun kawai…sai yaushe zanga Meron ka?”

Ta karasa tana canza akalar zancen. Da yasan ba za’a ganta kafin Mero ta shigo gidan shi ba, da yaja hannunta ya kaita sun gaisa, sai dai da yasan zasu nemeta su rasa din a washegari da idan ya jata ya kaita taga Mero ba zai taba bari ta bacewa ganin shi ba balle har suzo inda suke yanzun. Kanwar shi, tilon kanwar shi da yanzun yake kara fahimtar tarin kaunar da yakeyi mata.

“Ba’a ganta ba ko?”

Saratu ta tambaye shi, idanuwanta cike taf da hawaye, kai ya girgiza mata, a karon farko tun da aka fara nemanta yanajin idanuwan shi sun ciko da hawaye, hakan Saratu ta gani ta riko hannun shi, fisgewa yayi yana sake girgiza mata kai, ta kara rikowa, wannan karin tana kamo duka hannuwan nashi.

“Ina Yelwa zataje Saratu? Ina zataje haka bata fadamun ba? Auren Mero ya dauke hankalina har haka ne? Ta nuna alamun da idona ya rufe bangani ba?”

Kai Saratu take girgiza masa, ita kanta batan Yelwa ya maye mata gurbin duk wani tashin hankali da auren nashi ya haifar mata. Mutanen da take so a rayuwarta basu da yawa, zata iya kirgasu da yatsun hannunta, Yelwa na daya daga cikin mutanen nan. Ko ranar da ta kwanta, tunaninta bai kai na yanda Julde baya tare da ita akan gadon nasu ba, bai kai ga yana wajen Mero ba, balle tayi tunanin yanda ranar ne karon farko da zata rabashi a matsayin miji da wata. Gajiyar ranar da taji ta saukar mata gabaki daya bayan ta kwanta, laushin katifar na saka jikinta amsawa da wani yanayi mai dadi duk kuwa da zuciyarta da take a cunkushe. Sai tunanin Yelwa ya sake danneta, ina take? A wanne hali? Ta samu inda zata kwanta? A wanne irin yanayi?

Sai hawaye suka cigaba da saukar mata, wani na bin wani. Me yasa ba tayi magana da Datti akan auren Modibbo da Yelwar ba taga ko ita zata iya sauya ra’ayin shi? Ko ita zai saurareta tunda yaki sauraren Yelwa. Babu kalar tunanin da baizo mata ba, kafin gajiyar dake nukurkusar jiki da ruhinta suyi galaba akanta bacci ya dauketa.

“Da na saka ido akanta…”

Muryar Julde ta sake kutsawa cikin tunaninta, kai ta girgiza masa, tana hade tazarar dake tsakanin su, duk da cikin jikinta ya sake saka musu wata tazarar, yana hana mata riko shi jikinta yanda zuciyarta take sonyi.

“Ka daina, dan Allah karka dora laifin nan akanka…”

Hannuwan shi ya zame ya tsugunna, yanajin duka gwiwoyin shi sunyi masa sanyi, dakyar ta samu itama takai kasa tana zama. Tana kallon yanda yake kokawa da numfashin shi kafin ya mike. Batayi yunkurin masa magana ba balle ta hana shi, shiya shigo dakin da kanshi. Yana fita wajen dakin Mero ya nufa, ya sameta a kwance, tana shirin mikewa ya bita kan gadon ya kwanta a gefenta.

“Nagaji sosai.”

Ya furta cikin karamar murya, saita kai hannunta tana dorawa akan fuskar shi, lallashin shi take so tayi, wani nata bai taba bacewa ba, ba zatayi karyar hasaso yanda yakeji ba. Kamar jira yake ta tabashi, wasu siraran hawaye suka zubo masa, kirjin shi yayi nauyi fiye da yanda ya tabayi lokacin rasuwar Hammadi. Akwai bambanci a wancen rashin da wannan, tunda dashi aka zuba ma Hammadi kasa har aka rufe shi ruf, yasan inda yake, ko yanzun yaso zaije makabartar, har gaban kabarin yayi masa addu’a. Amman Yelwa fa? Ba zai ce ga halin da take ciki ba ko inda take balle ya fara nemanta.

“Idan ba’a ganta ba fa?”

Ya tambaya

“Za’a ganta, zata dawo…”

Mero tace masa, bai yarda ba, amman kalamanta sun dan nutsar dashi. Kamar yanda ya nemi samun nutsuwa a tare da ita. Sai ya waye garin, kamar sauran dararen da ya raya tare da ita. Wata irin nutsuwa ce da bai taba tunanin ana samu tare da mace ba. Da farko ya dauka mantar dashi tashin hankalin da yake cikine na kankanin lokaci da yayi. Sai dai kamar komai, batan Yelwa ba ciwo ya daina musu ba, sabawa sukayi da ciwon. Meron ce daban, ita din da kanta ce yake jin ta bambanta da duka sauran matan da ya taba mu’alama da su. Sai dai me, ya dauka ta ishe shi, a zuciyar shi Mero ta ishe shi, bashida wani waje da zai sake saka wata mace kuma da sunan aure.

Inda ba’a hada shi da Saratu ba, Mero ta ishe shi a matsayin mata, kawai wata murya ce a cikin kanshi take saka masa alamar tambayar ko akwai mata kamar Mero? Ko akwai wanda suka fita? Duk idan zaiga wata macen ta wuce sai tambayoyin su cigaba da yi masa yawo. Kuma su suka sake janshi ya koma bin mata watanni shidda bayan auren su da Mero. Bai san tana da kishi ba sai daren daya dawo taga sawun labba da jambaki a bayan wuyan shi.

“Saika nuna mun abinda kowa yake gujemun da aurenka Julde? Saika shigomun da tambarinta cikin daki? Ba zaka iya wanke jikinka daga daudar daka kwaso ba zaka hawomun gado kana neman hada jikina da naka?”

Ta karasa tana hankado shi daga kan gadon cikin karfin da bai taba sanin tana dashi ba, kokarin tambayarta yakeyi abinda tagani a jikin shi tunda baisan da jambakin ba, kamar ya tunzurata, ta cigaba da hauka kamar wadda jinnu suka shafa, dakyar ya iya riketa ganin kamar tana neman abinda zata illata shi dashi, saida yasa karfi sosai tukunna ya iya riketa, saita fara wani irin kuka daya rikita masa lissafi.

“Na daina, kiyi hakuri dan Allah, ba zan sake ba Mero, ki kalle ni…ba za sake ba”

Yake fadi yana rike fuskarta da tasa hannuwanta akan nashi tana kokarin kwacewa.

“Ba zan sake ba…”

Yake fadi yana maimaitawa, yana so ya yarda da kalaman shi fiye da yanda yake so ta yarda dashi. Tana son Julde, tana masa wani irin so da kafin ta shigo gidan shi taga wanda Saratu takeyi masa ta dauka ba zai misaltu ba. Sai yanzun da take hadiyar abinda tasan Saratun ta shanye a shekarun zamanta dashi takejin ba zata iya ba, mutuwa zatayi, zuciyarta fashewa zatayi ta mutu. Saratu bata shiga harkarta, idan ita ta gaishe da ita zata amsa, amman idan batayi mata magana ba, ko inda take bata taba kallo. Idan kuma tace bata kishin Saratu zatayi karya, ga yaranta masu kyau, tana gidan ta haifi Fadila. Ranar farko tana tsakar gida a bakin kofar dakinta, Saratu takai ruwan wanka, amman Fadila ta ki barinta ta shiga wanka saboda kukan da takeyi.

“Ko ki kawo in rike miki ita?”

Ta fadi, yanda Saratu ta kalleta sai taji tsoro, sai dai ga mamakinta, kwanto Fadila tayi daga bayanta tana karasawa ta mika mata ita, ta juya abinta. Ta dauka Salim da baya zuwa wajenta ko ta masa magana, Saratu ce ta hana shi, abinda bata sani ba shine, Saratu bata sonta don so, inda za’a bata zabi zata zabi tabar mata gidanta da mijinta. Amman bata da wannan zabin, yara ne kona rana daya bata saka a ranta Mero zata cutar mata dasu ba. Abu ta wanke mata wannan shakkun daga ranta. Labarai takeji akan kishiyar uwa, inda za’a bawa wani labarin yanda Abu ta riketa zai iya karyatawa, yace ba gaskiya bane ba, shisa itama ta zabi ta shure duk wani mugun labari.

Tun daga ranar kuma in dai zata bukaci daukar Fadila, Saratu bata hanata, saita je har kitso tabar mata Fadilan, ba dai ta shiga harkarta ko kadan.

“Yar uwata ce Mero, ko ban auri Saratu ba ‘yar uwata ce…zan rokeki, ki zauna lafiya da ita gwargwadon yanda zaki iya…”

Shine rokon da Julde yayi mata. Koshi yayi mamakin da a cikinsu babu wanda ya taba kai masa karar dan uwan shi, Saratu ta bashi mamaki. Sai wata kimarta da bai taba tunanin zai gani ba ta ginu a zuciyar shi duk da soyayyarta har lokacin ta kasa samun waje.

“Na daina, ba zan sake ba.”

Sune kalaman shi, ta haddace su, amman ta dade da daina yarda dasu. Da ta auri Julde ta aure shi da halin shi, amman a kasan zuciyarta ta aure shi da nufin soyayyar da taga yana mata ta canza shi, ita zata canza shi, zatayi abinda matar shi ta gida ta kasa. Sai yanzun ta gane babu yanda zaka canza wanda baya so ya canza, babu wata soyayya da ta isa ta canza halayya in har babu niyya, idan da niyya soyayyar ko yanayin saiya zama tsani na canjin, taimako kawai zaiyi bashi bane jigo. Jigon canji na kowanne irin hali shine niyya, niyyar nan itace komai.

Idan ta kalle shi taji wani ciwo da yake taso mata tun daga dan yatsan kafanta har kasan zuciyarta sai ta dinga hasaso barin shi, ko ta tafiyarta ta huta, tabarshi da matan da ya zaba akanta, akan su iyalin shi. Amman abubuwa da yawa sai su riketa, kalaman shi, nadamar shi kowanne lokaci ta sake kamashi kamar ba zai kara ba, soyayyar da take masa da take sakata jin kamar ta yafe mishi, kamar zata cigaba da yafe mishi a kullum. Musamman da ta samu ciki, sai kulawa da soyayyar da yake nuna mata suka karu, kamar bashi da wasu yaran, kamar a tare da ita zai fara samu.

Tana son abinda yake cikinta tun kafin tasan jinsin shi, amman kalar soyayyar da Julde yake nuna ma abinda ke cikin sai ya sake ninka mata kaunar da takeyi masa. Gajeriyar nakuda tayi, kuma mai sauki, cikin kasa da awa biyu har tayi ta gama. Da taimakon Dije da kuma matan Baabuga guda biyu da suka zo, da aka saka mata yaronta a hannu sai da ta faki idon mutane ta share kwallar farin cikin da ta silalo mata don kar ace tayi rashin kunya. Amman murmushin dake fuskarta yaki bacewa, ta kuma kasa daina kallon shi.

Addu’arta ta amsu akan yaron da yaci suna Aliyu, take kuma kiran shi da Haidar. Yayi kama da Julde, yayi kama da sauran yan uwan shi Salim da Fadila. Ta kuma ci albarkacin Haidar, Salim na zuwa wajenta saboda yaron, duk da sai tayi masa magana hamsin sai taci sa’a zai amsata sau biyu, zai daga kai ya kalleta sai ya dakuna fuska, a yan shekarun shi yana nuna alamar kamar bayason hayaniya, kamar sautinta yayi masa yawa a cikin kunne, tunda wani lokacin zata ga idan baki tayi, yan uwanta daga gidan Baabuga, yana zaune a dakin, zai takai dan yatsa kunnen shi kamar mai son toshe hayaniyar su, karshe zai riko gefen zaninta yana nuna mata Haidar, in ta dauke shi zai tashi ya fice daga dakin.

Tana son yaron, yanda yake komai nashi kamar ya girmi shekarun shi, komai ma a tare dashi, tsayin shi, nutsuwar da zaka gani a fuskar shi da rashin son hayaniyar shi. Har ranta taji dadin yanda Saratu batayi mata katanga da yaran nata ba, bata kuma yi musu katanga da nata yaron ba. Zata so zumuncin su ya dore.

Sam bata hango inda lokaci ya saka ma alakar su aya ba.
Kamar yanda batayi tunanin zamanta da Julde ba mai dorewa bane ba.

Shisa ta kara mike kafafuwanta, ta sake bude zuciyarta tana karbar sabuwar soyayyar da Julde yake nuna mata sanadin Haidar, kulawar shi kamar ba zai kara bata mata rai ba, kamar sabani ba zai sake shiga tsakanin su ba. A dan lokacin, idan ma ya koma halin shi, to yana iya bakin kokarin shi wajen boye mata. Hakan yayi mata, kar taji, karta gani kuma. Bata son duk wani abu da zaizo ya birkita mata kwanciyar hankali da ta samu. Larabarta a nutse tazo mata, shisa bata hango juma’arta zata zo da wani abu akasin abinda larabar ta wanzar mata ba. Tana zaune a kofar dakinta tana kallon Haidar da take jin kamar a cikin zuciyarta yake rarrafen da yakeyi, kaunar shi na cika mata zuciya.

“Kiyi mun addu’a, akwai abinda nake shiryawa, idan harya tabbata zamu bar Marake, Mero zamu koma Kano ko don su Haidar, ina so su samu ilimin da ban samu ba, ina jin kamar ba zasu mori tarin dukiyar da nake da ita a kauyen nan ba…”

Saita tsinci kanta da hasaso mafarkin shi, itama ko basu bar Marake ba, tayi ma kanta alkawarin Haidar saiya samu ilimin addini dana boko, saiya cika mata burinta data watsar saboda soyayyar Julde.

“Assalamu alaikum…”

Taji muryar da ta roka mata aminci amman babu amincin a tare da ita kwata-kwata. Zuciyarta ta dunkule tana gangarawa ta tsaya a dai-dai kafafuwan Talatu, kafin ta daga kai ta kalleta, ta cogalo daurin dankwalinta gaban goshi, mayafinta akan kafada, fuskarta tasha kwalliyar da ko cikin dare ka farka saika ganta a furkar Talatu. Da cingam abakinta da take taunawa cike da duniyanci. Talatu, itace Autar su Musa da rikonta ya koma hannun shi tun farkon auren shi, shekaru takwas ta baiwa Mero, lalacewar da Musa yaga zatayi yasa shi yi mata auren da ta kaso a watanni hudu kacal da yin shi, bayan nan aurenta hudu, harda na farkon biyar. Na karshen ne Mero tana da cikin Haidar taji labarin Talatu ta kaso shi shima.

Ko da tana gidan Musa, idan Talatu ta kaso aurenta tafi kowa shan wahala, haka kawai ta dauki karan tsana ta dora mata, kamar kishi takeyi da ita, duk wani abu da zata gani a wajenta in bata rabata dasho ba sai ta samo irin shi sak, ko dinki Mero tayi sai Talatu tayi irin shi. Sai daya suka hadu tunda Meron tayi aure, tunda sau daya taje ganin gida da tayi arba’in din Haidar.

“Ke kuma duk bokon sai kikaci baya? Kika bar binni kika tafi kauye aure?”

Yanda Talatu tayi maganar zaka rantse ba kauye bane asalinta, Mero murmushi kawai tayi bata tanka ba, ta dai kula da yanda Talatu take ta kallon Haidar, tunda kayane masu kyau da tsada, irin na binni Julde yake bayarwa a siyo musu, daga ita har shi da suke a kauye sunfi Talatun kyawun gani.

“Yau dai gani a gidan ki.”

Cewar Talatu, tana tsugunnawa ta dauki Haidar, sai Mero ta kasa amsa mata sallamar da tayi mata, ta kasa ko da yi mata murmushi, saboda zuciyarta na gaya mata zuwan Talatu ba alkhairi bane a wajenta, saboda Talatu bata da wani dalili da zata kawo mata ziyara tun daga Kano har Marake.

Hasashenta gaskiya ne
Hasashenta baiyi mata karya ba
Zuwan Talatu dai-dai yake da hargitsewar gidan aurenta…

*****

Comments da likes din karku gaji, na fada zan kara tuni ne kawai, da su zan samu a biyani. Nagode da tarin goyon bayanku.

#SonSo

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.4 / 5. Rating: 12

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rai Da Kaddara 38Rai Da Kaddara 40 >>

1 thought on “Rai Da Kaddara 39”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×