Tunda yake bai taba tunanin shan wani abu ba sai a sati dayan nan, idan yana cikin yanayi irin wannan Madina ce kawai yake gani yaji komai ya dan lafa masa, to yanzun abinda yake ji yana da alaka da ita. Ashe da yayi tunanin ya san girman son da yakeyi mata karya yayiwa kanshi, ko da yaga ya kusan rasata bai shiga rudani irin na kwanakin nan ba, idanuwanta ne abu na karshe da yake gani cikin kanshi kafin ya samu bacci, haka daya bude ido dasu yake fara sallama, ba dan bai taba ganinsu cike da abubuwa da yawa ba, tunda tana da idanuwan da zasu iya baka labarai kala-kala akanta idan ka natsu cikin kallon su, ba tare data bude bakinta ba, amman ranar ta dago ta kalle shi, tayi masa kallon da bata taba yi masa irin shi ba, ta kalle shi da wani kyalli da shine karo na farko daya fara ganinshi cikin idanuwan nata.
Ta kalle shi kamar duka fatanta yana karkashin kafafuwan shi, sai yaji wani abu daya girmi ace tsikar jikinshi ce tana tashi, ko yayi musu sallama ba zai tuna ba, ya dai bar dakin, ya saka takalman shi yaja kafafuwanshi zuwa motar shi, inda yana zama ruwane abinda ya fara nema ya jika makoshin da yakejin ya bushe masa.
“Yarinya ce Salim, ko shekaru sha takwas bata karasa ba, yarinya ce, get a grip.”
Yake fada yana sake maimaitawa kanshi, a lokaci daya kuma yana so ya tuna ma kanshi bai kamata ace yarinya kamarta bace take neman susuta shi haka. Shisa ya dauke kafarshi, ya bata tazara ta gama karbar dawowar itayenta, tayi musu duk wata tambaya data jima tana adanawa a cikin zuciyarta. Yanda ta kalle shi kamar babu wani abu da zai tambayeta da zata kasa yi masa ya bashi tsoro, ya girgiza wajajen da baisan da zaman su ba a cikin zuciyar shi. Ko zata karbi soyayyar shi daya mika mata bayaso tazo ta haka, bayaso ta karbeshi saboda ya zama sanadin dawowar iyayenta, idan zata karbeshi yana so ta karbeshi saboda shine zabinta.
Amman sai tazarar take taba shi fiye da yanda yayi zato. Sai ya zamana kamar komai na rayuwarshi ya yanke shawarar tuna masa ita, ko a asibiti duk wasu marassa lafiya da suke karkashin kulawar shi a satin, suna dauke ne da cututttukan da suka tattauna akai shi da Madina, yana duba su komai na hirarrakin na dawo masa, kewarta da son ganinta na kara nukurkusar shi. Kwanan shi na hudu kenan a asibiti, anan yake wuni kuma. Abinci ma sai dai yayi order a kawo masa har cikin asibitin, turawa yakanyi saboda, abincin kanshi yana kara tuna masa da cewar alkawarin da yayi mata na ba zai dinga zama da yunwa ba, ko da bayaji ma idan har yasan jikinshi na bukatar abinci ko kadanne zaiyi kokarin ganin yaci.
Sai gashi ta fara kutsowa har cikin baccin shi tana sakashi farkawa babu adadi a duk wani bacci da zaiyi na dare ko na rana. Ranar kwana na takwas dinne kiran Nawfal ya shigo wayarshi ya daga batare da yace komai ba
“Zaka dawo gida da kanka ko in kwaso kowa muzo asibitin su tayani dauko ka?”
Hannu yakai yana murza goshin shi, ta inda yakejin alamun ciwon kan dake neman wajen zama
“Bajjo”
Ya kira, muryarshi na fitowa da gajiyar da baiso ba
“Mu taho din kenan”
Halayenshi basu taba hana duka kannen shi tsokanar shi ba, amman a cikinsu babu wanda yake iya sakashi yin abinda bai niyya ba kamar Nawfal, saboda ko me zaiyi ma Nawfal din sai dai ya yi, amman abinda yace zai yi ba zai fasa ba. Kowa din ba zai wuce Khalid ba, in kuma za’a hada Nawfal da irin Khalid biyar ba zasu iya daukar shi ba. Sai dai bayason kure Nawfal din, baya son yaga shi da Khalid dinne kawai zasu zo ko kuwa harda wasu zai gayyato suyi masa hayaniyar da bashida wajen daukarta.
“Ba zaka iya numfashi a hankali bane?”
Salim ya fadi yana janye wayar daga kunnen shi, shisa yake amsa waya a speaker, saboda ya tsani yanajin wannan numfarfashin cikin kunnen shi
“Ya zanyi numfashi a hankali Hamma?”
Kara hade girarshi Salim yayi kamar Nawfal din yana ganin shi sannan yace
“Ban sani ba, karar numfashin yana shigarmun kunne”
Ya karasa yana saka kiran a speaker ya ajiye wayar kan teburin da yake gabanshi
“Karar numfashi? Kasan me? Ba kira nayi muyi maganar nan ba, mu zo?”
Wannan karin numfashi Salim ya sauke
“Zan dawo gida anjima.”
Ko da baya ganin Nawfal yasan kai yake jinjinawa
“Idan baka dawo ba zamu zo”
Bai amsa ba ya kashe wayar. Bai fita daga asibitin ba sai bayan la’asar, daya fito daga masallacin saiya nufi motar shi, duk da hargitsin da yake ciki akwai wata natsuwa ta daban da koya taba saninta toya manta haka take, duk lokacin da zai shiga masallaci ayi sallah dashi a jam’i akan lokacinta sai yaji kamar an diga masa haske a duhun da bai taba sanin yana tare da zuciyarshi ba. Ba kamar lokacin da inya hada salloli ya idar zaiji wani irin nauyi ya danne masa zuciyar ba, yanzun sakat yake jinta ta wannan fannin, sai tarin zunuban da yake rokon yafiyar Allah akansu cike da wata kunya marar misaltuwa.
Kunya hadi da tsoro saboda yaga maikon da zina take dashi, yaga yanda take da karfin ruguza abubuwa da yawa, a duniya kenan, ko anan din bashida kafafuwan tsayawa a gaban makusantan shi idan daudar zunuban shi ta bayyana, sai yanzun tsoro ko yace firgici yake shigarshi, nauyin zunubanshi nayi masa rumfa.
“Astagfirullah…”
Ya furta a kasan numfashin shi yana murza mukullin motar ya tasheta, a kasan duk wannan firgicin baya manta Allah Mai yawan Gafara ne, Mai yawan Rahma. Yana fita titi wayarshi nayin kara alamar shigowar kira, harya shirya zagin da zai watsawa Nawfal idan ya daga sai zuciyarshi tayo wani zullo kamar tana son fitowa ta daga kiran da kanta ganin Madina ce, yana karawa a kunnen shi kafin yace wani abu ta rigashi da fadin.
“Hamma…”
Kuma baisan ko zuciyarshi bace take kitsa mishi abinda su duka suke sonji, kamar akwai kewarshi a muryarta, a yanayin yanda ta kirashin.
“Kina ina?”
Ya tambaya saboda ba zai iya sake kwana bai sakata a idanuwan shi ba.
“Ina gida”
Ta amsa a takaice, kai ya jinjina kamar tana ganin shi ya sauke wayar daga kunnenshi yana katse kiran daga bangarenshi, kafin ya mike yana shan U-turn ya koma hanyar da zata hadashi da gidan Daada. Yana parking din motar shi yana jinta tana kwankwasa gilashin motar kamar tana kofar gida tana jiranshi, daga inda yake ya fara kallonta. Rigace mai hula a jikinta, ta saka hannunta daya a cikin aljihun rigar, dayan tana kwankwasa masa kofa, akwai wata hular ta sanyi fara kal a saman kanta, sai kuma taja ta rigar da take baka tana dorawa a sama, fuskarta fayau inka cire ta gilashin da yake manne a jiki, tayi masa kyau har baisan ajiyar zuciya ta kubce masa ba. Da kasala ya mika hannu ya bude mata murfin motar ta shigo tana zama.
Ta jingina jikinta da kujerar motar sosai bayan ta rufe kofar, sannan ta dan juyo da kanta tana kallon shi, farar rigar da take jikinshi ta kara haska fatarshi, wannan kyawun nashi da yafi na kowa a gidan yana fitowa. Kallon shi takeyi kamar tayi wata bakwai bata ganshi ba maimakon kwanaki, idanuwanshi sunyi zuru-zuru kamar wanda yayi jinya, sai taga kamar yayi duhu bayan ramar da yayi mata, ga gajiya fal idanuwan shi. Ta raba idanuwanta daga fuskar Yelwa, ta kalli inda yake don ta samu saukin hargitsin da takeji sai taga baya dakin, hakan ya tilasta mata maida kallonta kan Kabir daya samarwa kanshi wajen zama kan daya daga cikin kujeru masu zaman mutum daya dake dakin.
Sai take ganin fuskarta a cikin tashi, bambancin na gashin da yake a tashine da kuma gilashin da yake tata fuskar. Shima ita yake kallo, saita dauke idanuwanta tana tashi tabar falon gabaki daya zuwa dakinta, a karo na farko tana kullewa daga ciki dan batason kowa ya shigo mata, ta hau gado taja bargo tana rufe jikinta gabaki daya duk da ba sanyi akeyi ba. A litattafai ba haka haduwa da iyaye bayan wasu shekaru yake kasancewa ba, wasu za’ace suna sauke idanuwansu akan mahaifiyarsu ko da basu santa ba zasuji a jikinsu cewar sun hada jini da ita, zasu ji wannan hadin da yake tsakaninsu tun suna kwance a cikinta, kafin wata irin kauna da basu tabaji akan wani ba ta dirar musu.
Sai rungume rungumen juna ya biyo baya, cike da hawaye, sannan tarin tambayoyi, ina kika shiga? Me ya faru dake? Bayan amsa wannan tambayoyin, uzuri, uzuri saboda kauna da murnar ganinta ta cika zuciyarka. Ita akasin hakane ya faru da ita, ta kalli Yelwa, babu komai a zuciyarta sai mamaki, duk wasu tambayoyi sai suka bace mata suna barin guda daya tal, tana da rai bata nemesu ba duk tsayin lokacin nan? Sai wani kunci ya ziyarceta yana danne mata komai. Data kalli Kabir sai taji babu abinda yayi mata bayan tambarin kasancewar shi mahaifinta da jininshi da yake da karfin fisgar da yawa daga cikin kamanninta, sai kuma tabon da take tunanin shi da Yelwa sun hadu wajen ganin ta kasance dashi har karshen rayuwarta.
Da ta kwanta din a daki, tayi juyi sai muryar Salim ta dawo mata
“Ina son ki”
Ko da kaddara ta zabar masa ita a matsayin yar uwa yana da zabin sonta ko akasin haka. Saiya zabi ya sota a matsayin ‘yar uwa. A hankali sai lokaci ya juye hakan ya kalleta a matsayin mace batare daya duba cewar nata iyayen ma sun nisanta kansu da ita ba ya sota. Kafin nan Salim na tabbatar da bataji kadaici ba, yana kula da duk wani abu daya danganceta, karami ko babba, mai muhimmanci da marar muhimmanci duka a wajen shi basu da wani bambamci. Shisa bai zauna ba sai da ya gano mata iyayen da yanzun take jin kamar bata shiryawa ganinsu ba.
Duk wani abu da zai sama mata sauki shi Salim yakeyi, me take jira da ba zata amsa soyayyar da yake miko mata duk da bata cancanceta ba? Da ta sake juyawa kwanciya sai wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Suka cigaba da fitowa tun tana goge su harta daina. Taji dadi da babu wanda yazo ya kwankwasa mata saida ta tashi da kanta dan tasan ya kamata ace ta dora musu girki duk da batajin yunwa. Idan bata fita ba Daada zatace ta dora. Sai dai tana samu ta sauko daga gadon ta bude kofar ta fita falon sai taci karo da abinda batayi tsammani ba, ta kuma yi mamakin nisan da hankalinta yayi da jikinta har bata juyo hayaniyar dake faruwa ba haka.
Julde ne ya kama Kabiru ya shake shi, yanda yake jjijjigashi zai sanar dakai Kabirun baya wani yunkuri na ganin ya kwace kanshi ko ya hana Julden abinda yakeyi, tana hango kyallin hawayen da yake cikin idanuwan Kabirun. Saratu ma tana nan ta tsaya a gefe tana saka mayafin jikinta tana share kwallar da take zubar mata, Yelwa ce ta riko Julde tana fada masa abinda baya karasawa kunnuwan Madinar saboda wani yanayi daya lullubeta, wani yanayi na son bama Kabiru kariyar da bata samu daga wajen shi ba. Ko da Julde ya sake shi yanda ya koma cikin kujerar batasan kafafuwanta suna takawa ba sai da ta ganta tsaye a gabanshi, sai dai bakinta yayi mata nauyi da tambayar da take mata yawo a cikin kai
“Baka ji ciwo ba? Babu abinda ya sameka?”
Sune abinda take son tambayar shi, sai hawaye ne suka taho mata a maimakon maganar
“Hamma….Hamma dan Allah…”
Ta tsinto muryar Yelwa data durkushe a kasa tare da Julde daya hade fuskar shi cikin hannayen shi yana kuka kamar karamin yaro, itama kukan takeyi, su duka kuka sukeyi banda Yelwa da take kokarin lallashin Julde babu wanda yake wani yunkuri wajen ganin ya ba wani hakuri, Julde ne ya bude fuskarshi yana kallon Yelwa
“Sai kika bishi? Sai kika zabe shi akanmu? Farin cikin shi kika auna da tashin hankalin da zamu shiga kikaga farin cikin nashi yafi muhimmanci…idan kina tunanin su Daada ba zasu fahimce ki ba Yelwa nifa?”
Kai take girgiza masa, soyayyar Kabir ce ta fada mata zata iya hakura dasu, zata iya nisa dasu, dashi, zata iya tsallake kowa a ciki hardashi, amman ko nisa motarsu batayi ba wani abu ya danne zuciyarta. Shine abu na karshe data yi duk wani kokari na ganin ta binne can kasan zuciyarta, ko kewar kowa na nukurkusarta bata bari tashi ta taso mata
“Hamma…”
Ta furta cikin kuka tana sake rikoshi, kwacewa yakeyi tana sake kai hannu ta rikoshi ya sake tureta, sunyi hakan fiye da a kirga kafin ta dago rinannun idanuwanshi ya kalleta, saiya kamo hannuwanta yanajin gazawar da yayi a cikin kulawa da ita da ganin wani abu makamancin hakan bai faru da ita ba, yana jin kuskuren daya kusa aikata mata da yanzun bai samu karfin gwiwar tsayawa a gabanta yana fadin ta barsu ba
“Hamma dan Allah…”
Yelwa ta sake fadi a wahalce, kai ya jinjina mata kamar ya amshi yafiyar da take rokonshi duk da bata furta ba, yana saka wani gunjin kuka kwace mata, kukan da Madina taji ya ratsa zuciyarta yana sakata son rike Yelwar ko zata sama mata sauki. Saita sake barin wajen tana komawa daki kawai, waye yake da nutsuwar jin yunwa harya iya cin wani abinci a halin nan da suke ciki? Sai dai da daddare Daada ta kwankwasa mata daki ta miko mata abinci a robar da ta tabbatar mata da siyowa akayi, ganin tambarin restaurant din manne da robar tasan Julde ne, dan yana son abincin wajen, yana yawan yi musu siye-siye a gurin. Ta ci kadan da fatan Salim bai zauna da yunwa ba manne a zuciyarta. Taso ta kirashi amman jikinta kamar anyi mata duka haka take jinshi, da ta samu tayi isha’i saita kwanta.
Wannan karin bata kulle kofa ba, kuma fitilar da take karatu da ita a kunne take, shisa taga shigowar Yelwa, ta kuma bita da idanuwa data ga tahau gadon, sai taja jikinta ta matsa can karshe, kwanciya Yelwar tayi batare da tace mata komai ba. Saita tashi zaune ta mika hannu ta kashe fitilar, duhu ya mamaye dakin, ta koma ta kwanta tana sauraren bugun zuciyarta da yayi kasa. Haka kawai taji hawaye na taruwa a idanuwanta, saita cire gilashin ta lankwashe shi tana ajiyewa can gefe. Hakan kuma yaba hawayenta damar saukowa, kuka takeyi batasan yayi karfin ba sai da taji hannuwan Yelwa sun rikota, sai wani abu ya sake saukar mata yana sa kukan kwace mata sosai, kuka tayi a jikin mahaifiyar da bata hango sakata a idanuwanta ba, kuka tayi irin wanda bata tabayi ba a yan shekarun da take dasu. Kuka tayi har bacci ta dauketa.
Kuma a kwanakin nan duka basa wata magana da Yelwa, banda gaisuwa, batasan me zatace mata ba, Kabiru ma yazo sau biyu, duka zuwan sun gaisa, duk da Daada da Yelwa sun basu waje, zama kawai sukayi batare da sun cewa juna komai ba, da alama basu san ta inda ya kamata su fara ba, bai sake dawowa ba, inya dawo dinma har yanzun bata san me zatace masa ba. Wuni takeyi a dakinta, daga gidan Julde ake kawo musu abinci yanzun, abinda ko da sallah bata taba ganin anayi ba. Duk dare kuma Yelwa zata zo dakinta ta kwanta, ko da bataje jikinta a lokacin ba idan tayi bacci to inta farka tana manne da ita kamar mai son komawa cikinta dan karta sake tafiya ta barta. Yau kuma da ta tashi wasa take tayi da wayarta, kamar tana jiran kiran Salim da take da yakinin ya bata wajene dan ta samu lokaci dasu Yelwa.
Amman kamar kwanakin sunyi yawa, tun bayan data sanshi basu taba daukar lokaci mai tsayi basu ga juna ba haka, kasa hakuri tayi da yamma shisa ta kirashi, yanzun kuma da ta ganshi a gabanta sai wata sabuwar kewarshi ta kara danneta, da taga ramar dake fuskarshi sai zuciyarta tayi mata nauyi
“Me ya sameka”
Ta tsinci kanta da tambayar shi, kafadu kawai ya dan daga mata, me zaice? Ita ta same shi? Tunaninta ne ya hana masa sukuni? Ko kewarta? Duk inda aka zagaya, duk wata kwaskwarima da zaiyiwa kalaman karshe dai ita dince damuwar shi
“Karatuna fa?”
Muryarta ta fito can kasan makoshi, da ba shi bane zai wahala aji me tace, kallonta yayi cike da rashin fahimtar inda tambayar ta dosa
“Idan na aureka, Hamma karatu na fa?”
Ta furta wannan karin tana saka idanuwanta cikin nashi kafin ta sauke kamar abinda take gani a cikin nashi ya girmi daukarta, kallonta yakeyi tambayarta nayi masa yawo
“Mug…”
Ya kira, bata dago ta kalle shi ba
“Saboda abinda nayi ne zaki aureni?”
Abinda yayi na gano mata su Yelwa, tasan shi yake nufi, kai ta girgiza a hankali, ba saboda shi bane ba, saboda kafin ta shigo motar babu wannan tunanin a tare da ita, batasan zatayi masa tambayar da tayi masa ba. Kamar yanda ya fado rayuwarta babu shiri, ta fito daga dakine ta ganshi tsaye a cikin kitchen din Daada a ranar, haka kuma ta fito daga makaranta ne ta hange shi a tsaye a jikin motar shi kamar ya saba jiranta. Kamar yanda duk wani abu daya shafe shi yake faruwa da ita babu wani shiri haka wannan ma, kamar yanda ya fada mata yana sonta a karo na farko bata fahimci kalar son da yake nufi ba, haka a karon karshe data fahimci inda ya dosa duk da batayi tsammani ba haka taji bata da wani daya kamata ta raba sauran kwanakin rayuwarta dashi da zai wuce mata shi.
Da safen nan da ta tashi ta janyo durowar kusa da gadonta da nufin saka wasu cikin litattafanta, sai taga agogon da Nawfal ya bata ranar da zai tafi. Da ta kalli agogon sai ta hango shi da Murjanatu a ciki, zata rantse da Allah taji muryar shi ya kira
“Jaan…”
Ta kuma hangi idanuwan shi da baka ganin komai a cikinsu idan Murjanatu na gabanshi sai son da yakeyi mata, kamar yanda a cikin nata idanuwan zakaga yanda duniyarta take tsaye tare da Nawfal din. Ko abinci ta zubo musu, tana ajiyewa Nawfal din nashi Murjanatu take dauka, zata ajiye nata a gefe saita tabbatar na shi ya huce, ta fara ci, ko ruwa Nawfal zai sha idan tana kusa saita fara sha take mika masa, kamar tana son tabbatar da abinda zaici yayi dai-dai yanda ba zai cutar dashi ba. Da ta saka litattafan ta danne agogon dasu ta mayar ta rufe, a karon farko taji tana son samun wannan kusancin da yake tsakaninsu, tana son ta kwanta ta tashi da sanin akwai wani a kusa da ita da ba zai taba barinta ba duk rintsi.
“Bayan Daada, kaine abu mafi tabbaci a rayuwata Hamma, duk idan na juya ina ganinka…sanda nake bukatar dama sanda bansan ina bukatar ka ba sai naganka, duka kana nan…”
Wani irin numfashi yaja ya sauke
“Aurena ba zai shiga tsakanin ki da karatu ba…”
Kai ta jinjina tana sake gyara zamanta a cikin kujerar
“Hakan na nufin zaki aure ni?”
Kai ta sake daga masa
“Idan nace bana so ya dauki lokaci fa?”
Kallon shi tayi tana jin inda rayuwarta a hannunta take zata iya bashi ajiya saboda zai kula da ita fiye da yanda zatayi, kai ta sake jinjina masa
“Mug…”
Ya iya furtawa yana hango nesan da tazo masa kusa, murmushi na kwace masa, yana kallon murmushin da tayi itama, sai dai bai iya hango akwai tazara a tsakanin wannan murmushin nata da sake yin wani ba.
*****
Comments da likes din karku gaji, idan kunyi like ku daure da comment din, sai mu koma whatsapp mu sha hirar acan, na fada zan kara tuni ne kawai, da su zan samu a biyani. Nagode da tarin goyon bayanku.
Nice