Da wata irin gajiya ya dawo gida daga makaranta. Da sallama ya murza handle ɗin ƙofar yana taka kafarshi cikin falon.
Tura ƙofar yayi ya rufeta, kafin ya juyo ya ji Khateeb ya maƙale da ƙafafuwanshi. Baisan lokacin da murmushi ya ƙwace mishi ba. Hannu ya zagaya ya kamo shi.
"Don."
Ɗago Khateeb yayi.
"Khateeb..."
Dariya kawai Khateeb yake yi. Duk ciwon da Dawud yake ji a zuciyarshi in dai Khateeb na dariya haka yakan ji kamar yaron na raba farin cikin ne tare da shi.
"Mamiiii......"
Dawud ke kira don bai ji motsinta ba, ya cire takalmanshi yana. . .