Skip to content
Part 14 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Da wata irin gajiya ya dawo gida daga makaranta. Da sallama ya murza handle ɗin ƙofar yana taka kafarshi cikin falon.

Tura ƙofar yayi ya rufeta, kafin ya juyo ya ji Khateeb ya maƙale da ƙafafuwanshi. Baisan lokacin da murmushi ya ƙwace mishi ba. Hannu ya zagaya ya kamo shi.

“Don.”

Ɗago Khateeb yayi.

“Khateeb…”

Dariya kawai Khateeb yake yi. Duk ciwon da Dawud yake ji a zuciyarshi in dai Khateeb na dariya haka yakan ji kamar yaron na raba farin cikin ne tare da shi.

“Mamiiii……”

Dawud ke kira don bai ji motsinta ba, ya cire takalmanshi yana takawa, kitchen ya nufa ya ɗauko ruwa ya fito yana sake kiranta.

“Ka ganni a ɗaki Dawud, har ka dawo”

Mami ta faɗi daga can ciki.

“Na dawo mami.”

Ya ƙarasa maganar yana sauke Khateeb akan kujera tare da zama kusa da shi yana fitar da numfashi, kanshi ya jingina da bango yana sauke numfashi cike da gajiya.

Mami ce ta fito daga ɗaki ta kalle shi.

“Sajda ke ta ciwon ciki, yanzun……”

Bata ƙarasa maganar ba Dawud yai wata irin miƙewa yana wuceta ya nufi ɗakin da ta fito. Sajda ya gani kwance kan gado, zuciyarshi na dokawa ya ƙarasa kan gadon ya zauna a gefenta.

“Sajda…. Sajda…..”

Yake faɗi ya saka hannuwanshi duka biyun ya tallabo ta. Da ƙyar ta buɗe idanuwanta ta kalle shi.
“Yaya cikina ciwo.”

Ta faɗi tana yamutsa fuska, ji yake kamar ya karɓi ciwon da take ji ya maida shi jikinshi. Bai damu da duk abinda zai same shi ba in dai su suna nan lafiya.

Mami ce ta shigo ta ƙaraso inda yake.

“Mu tafi asibiti.”

Kai kawai ya ɗaga mata ya ɗago Sajda ya miƙe da ita kamar wata ‘yar tsana.
“Yaya zan iya tafiya.”

Sajda ta faɗi, ko kulata Dawud bai yi ba ya karɓi hijabin da Mami ta miƙo mishi na Sajda, kan ɗayar kafaɗarshi ya rataya hijabin, bai jira Mami ba da ke saka hijabinta.

Ya fito da Sajda yana kama hannun Khateeb.

“Ina za mu je? Ice cream?”

Khateeb yake tambaya. Dawud bai kula shi ba, kawai hannunshi ya ja ya fita da su. Mota ya buɗe ya saka Sajda, dai dai fitowar Mami ta kulle gidan.

Hijabin Sajda ya miƙa mata ya buɗe motar Khateeb ya shiga sannan ya zagaya ta ɗayan ɓangaren shima ya shiga, ya kunna motar yana janta suka nufi asibitin Dialogue.

*
Sa’adda suka ƙarasa ana ta kiran sallar Magariba, inda Allah ya taimaka suna da file a wajen. Nan ya bar su a waiting area ya ja Khateeb suka fita suka yi sallar Magariba suka dawo.

Nan ya bar Khateeb da Mami ya shiga wajen ganin likita da Sajda. Akwai abubuwa da yawa da Mami ke barin Dawud yayi don tasan ba barinta zai yi ba.

Wannan na ɗaya daga cikinsu, ba wai dan bata da muhimmancin hakan a wajen shi ba. Iya zaman su ta fuskanci Dawud, da zai iya ko yana da lokacin girki ma in dai ƙannenshi ne za su ci da wahala ya barta ta dafa.

Don ta kula komai da kanshi yake so yai musu, baya son raba hakan da kowa. Ƙaunar da ke tsakanin shi da ƙannenshi mai girma ce.

Sosai aka dudduba Sajda ɗin. Ga tambayoyi da ta sha, likitan ya tabbatar ma da Dawud food poisoning ta samu.

“Da me dame kika ci duk yau?”

Shiru Sajda ta yi tana sadda kanta ƙasa.

“Sajda me kika ci?”

Dawud ya tambaya muryarshi ƙasa-ƙasa.

“Awara…..”

Ta faɗi a hankali, da ɓacin rai Dawud ya kalle ta, bata da lafiya, ba zai iya mata faɗa ba. Amma ya kawo iya wuya. Wannan ne karo na biyu da awarar nan ke saka ta ciwon ciki.

Magunguna ya rubuta mata ya ba wa dawud tare da yi mishi gargaɗi kan hanata cin awarar tunda ɓata mata ciki take yi.

Godiya Dawud yai mishi ya miƙe tare da kama hannun Sajda. Ta san ta ɓata mishi rai. Idanuwanta cike da hawaye ta ce,

“Yaya kayi haƙuri.”

Shiru yayi ya ƙyaleta ya buɗe ƙofar office ɗin suka fice, magana ta sake mishi. Bai ce komai ba, yana janta dai har suka ƙarasa Pharmacy ɗin asibitin ya siya magungunan.

“Yaya….. Allah ba awara bane, ni da Khateeb fa muka ci, kuma ka ga ba abinda…..”

Sakin hannunta Dawud yayi, ya juya yana fuskantarta idanuwanshi sun sake kala saboda yadda ranshi ya ɓaci.

Shiru Sajda tayi.

“Go on…….”

Da sauri ta girgiza kai. Duk da Dawud baya dukansu su duka suna shakkarshi. Da wahala ya maka faɗa, za ka daina ganin fara’ar shi ne kawai har sai ka gane kuskurenka.

“Sajda yaushe kika daina jin magana? Ya muka yi da ke last time da kika ci awara? Me kika ce min?”
Kanta a ƙasa ta ce,

“Cewa na yi na daina.”

“Yayi miki kyau.”

Ya faɗi yana kama hannunta suka ci gaba da tafiya.

“Don Allah yaya ka yi haƙuri, bazan sake ba, na daina.”

Magiya sajda ta ci gaba da yi jin ya ƙi kulata. Har suka ƙarasa inda Mami take bai ce komai ba,

annunta ya ja yana miƙa wa Mami ita tare da ledar magungunan.

Kafin ya riƙo hannun Khateeb ba tare da ya kalli Sajda ba yai gaba.

“Me kika mishi?”

Mami ta buƙata, rau-rau da idanuwa Sajda ta yi tana kwantar da kanta a kafaɗar Mami daga tsayen da suke. Tana jin yadda ɓacin ran da ta saka Dawud ke ci mata rai yana ƙoƙarin danne ciwon cikin da take ji.

“Likita yace awarar da na ci ne.”

Sai lokacin Mami ta tuna an ma hana Sajda cin awara, kuma a gabanta suka ɗauko plate suka ci ita da Khateeb bayan ta dawo Islamiyya.

Don hutun sati ɗaya kawai suka yi bayan saukarsu. Da yawa ƙawayen Sajda basu koma ba. Ita dai tana ganin ko kaso goma cikin ɗari bata yi ba a ilimin addini.

Sauka baya nufin ƙarshen karatunka na Islama, yana nufin ka dai samu ci gaba ne babba a hanyarka ta neman ilimi, don kogi ne, yana da faɗi, sai dai kayi iya yinka.

“An hana ki cin awarar nan Sajda ba kya jin magana.”

Langaɓe kai tayi.

“Na sani Mami, wallahi ina son awara sosai. Kuma da baya min haka.”

Kama hannunta Mami ta yi suka soma takawa suna fita daga asibitin.

“Tunda yana miki haka yanzun sai ki haƙura. Kin ga yayanki ba shi da kwanciyar hankali in baku da lafiya.”

Shiru Sajda tayi tanajin duk bata kyauta ba. Ta fi kowa ɓata wa Dawud rai a gidan, Zulfa bata  cika zama ba balle ta yi wani laifi.

Rabin rayuwarta a gidan su Labeeb take yinta. Don Sajda zata iya rantsewa sai dai ta ji Dawud na ma Zulfa faɗa amma ba zata ce ga abinda tayi ba.

A mota suka samu su Dawud, buɗe bayan motar Mami tayi ta sa Sajda ta fara shiga sannan ta bita. Ba tare da Dawud ya ce musu kanzil ba. Yanayin tuƙin da yake yi kawai zai faɗa maka ranshi a ɓace yake.

****

A buɗe suka samu gidan, yasan Tayyab ne ya dawo, saboda irin haka yasa da wuya su fita babu key a jikinsu su duka.

Su Mami suka shige ciki, Dawud kuma sai da ya tsaya ya ɗauko Khateeb da yai bacci ya kulle motar tukunna ya shiga ciki.

Kanshi tsaye ɗakin Ummi da ya zama nashi ya wuce da Khateeb. Ya kwantar da shi ya cire mishi takalma ya gyara mishi kwanciya.

Sannan ya fito, karo ya ci da Tayyab.

“Ina kuka je haka? Ina ta kiran wayarka a kashe.”

Ɗan dafe kai Dawud yayi.

“Na manta ma, tun da na shiga class na kashe, tana mota ma, mun je asibiti ne, Sajda ke ciwon ciki”
Ware idanuwa Tayyab yayi.

“Subahanallah…….”

Ya faɗi yana juyawa da sauri. Bayanshi Dawud ya bi, Tayyab yai ɗakin Mami shi kuma ya koma falo ya zauna.

Gaba ɗaya gajiyar da yake ji baisan lokacin da ta bar jikinshi ba. Kiran sallar Isha’i ya ji. Yana da alwala don haka ya fice masallaci abinshi.

Sa’adda ya dawo a falo ya samu su Mami da Sajda. Idanuwanshi kan Mami ya ce,
“Ya jikin nata? Ta sha magani? Amma ta ci abinci ko kaɗan ne.”

“Ta ɗan ci abinci, yanzun ta sha magani.”

Kai ya ɗan ɗaga.

“Allah ya bata lafiya.”

Mami ta amsa da amin. Sajda kam kallonshi ta yi, muryarta a shagwaɓe ta ce,

“Yaya ina wajen fa….”

Bai ko kalleta ba ya zauna kan kujera.

“Kai ba za ka ci abincin bane?”

Mami ta buƙata.

“Zan zuba idan na tashi, ba yanzun ba Mami, ina da ayyuka sosai.”

Tayyab ya shigowa gidan daga masallaci da sallamar shi ya kalli Sajda

“Sajda cikin da sauƙi dai ko?”

Kai ta ɗaga mishi tare da faɗin,

“Yayi sauƙi Yaya Tayyab . In ɗauko system ɗinka in ƙarasa kallon Shrek ɗin?”

Kai Tayyab ya ɗaga mata yana wucewa kitchen. Sakwara Mami tai musu da miyar alayyahu.

Murmushi ya ƙwace ma Tayyab.

Abincin da Ummi ta fi so kenan. Addu’a yai mata a cikin zuciyarshi, yana zubowa ya fito. Don in ya tsaya fadin yadda yai kewarta a zuciyarshi zai kwana a tsaye a kitchen ɗin bai gama ba.

Tun kafin ya zauna ya fara ci.

“Haba Tayyab, ka zauna mana.”

Bakinshi a cike ya ce,

“Ka ji yadda abincin nan yayi daɗi kuwa.”

Yamutsa fuska Dawud yayi.

“Gross…..”

Dariya Tayyab yayi yana zama. Ya sake ɗibowa ya cika bakinshi.

“Mami kinsan jiya da na biyo kasuwa sai da na ga wajen da kike cefane.”

“Halan ka biyo ta layin ‘yan doya.”

Dawud ya faɗi yana kallonshi. Sai da ya haɗiye abincin da ke bakinshi ya ƙara wani sannan ya juya ya ɗan kalli Dawud ɗin.

“Wallahi kamar ka sani, ta nan na biyo da zan dawo…..”

Mami da Sajda da ke zaune suka bushe da dariya.

“Yaya Tayyab ka jingina da kujera sosai.”

Sajda ta ƙarasa da dariya tana buɗe system ɗin Tayyab ɗin da ta ɗauko, murmushi yayi.

“Na san za ku ce santi nake y. Abun ya faɗo min ne yanzun…. Kai abincin nan yayi daɗi.”

Miƙewa Dawud yayi.

“Mami saida safenku.”

“Allah ya tashe mu lafiya.”

Mami ta amsa shi.

“Yaya saida safe.”

Sajda ta faɗi, bai ko nuna ya ji ta ba ya wuce. Dariya Tayyab yayi.

“You are getting the silent treatment…. Me kika yi?”

Daƙuna fuska Sajda tayi.

“Allah gara ya zane ni an wuce wajen da abun nan.”

Jim Tayyab yayi kafin ya ce,

“Ba ke kaɗai ba fa, sai yayi kamar ba ka wajen.”

Nan Mami ta barsu, ta wuce ciki abinta, tasan Tayyab zai koro Sajda in ya ga goma ta yi. Shi yasa ma bata damu ba.

****

Makaranta ta fara mishi zafi saboda watan exams ɗinsu na semester ɗinshi ta farko a ajin shi na ƙarshe ya kama.

Ga rashin bacci da yake fama da shi da dare, tun Labeeb na damunshi kan ya je asibiti har ya gaji ya ƙyale shi. Abin ya zame mishi jiki. Bacci na mai wuyar yi da dare.

Zai iya cewa ta ɓangaren karatunshi hakan abu ne mai kyau, saboda yana samun damar yin nazari sosai da sosai da gama ayyukan shi akan kari. Ta ɓangaren lafiyarshi kuwa abu ne da baya son taɓowa.

Yau da wuri ya dawo daga makaranta, din a hanya yai sallar Asr. Kasancewar malamin da zai shigo musu da yammacin ya ce ba zai samu zuwa ba.

Da yunwa ya shiga gida, Mami kaɗai ya tarar da ke zaune ya gaishe da ita ya nufi kitchen ya zubo abinci. Shinkafa da miya ce Mami ta yi musu da soyayyen dankali.

Ruwa ya ɗauko ya haɗo da shi ya fito ya zauna kan kafet cikin falon ya soma cin abincin.
“Sajda har sun tafi ne?”

“Eh sun tafi, ta ce ma ga sunan wani littafi in ka dawo ka siyo mata shi. Da kamar ba zata ba, ta ce za ai duka wanda bai siya ba.”

Karɓar takardar yayi daga hannun Mami.

“Da baki bari taje ba Mami, tunda duka za a yi.”

Dawud ya faɗi yana jin yadda ranshi ya soma ɓaci da tunanin wani ya taɓa lafiyar Sajda.
“Kasan sajda da makaranta dai.”

Kai ya ɗaga yana cin abincin da sauri-sauri.

“Bari in gama sai in siya in kai mata.”

Kai Mami ta ɗaga mishi. Tana jin maganar da take son mishi tun jiya na tsaya mata a maƙoshi.
Tasan in dai zaman amana suke yi ya kamata ta faɗa mishi. Balle yadda duka suka ɗauketa, musamman Sajda, Zulfa da Khateeb da ta shigo rayuwar su da ƙuruciya a tare da su.
Kafin ta ƙara kasawa ta ce ma Dawud,

“Ina son magana da kai Dawud, sai bansan ya zaka ɗauke ta ba “

Sosai ya kalleta.

“Ki faɗa min kawai Mami, zaman da muke ya girmi wannan tunanin ya dinga zuwa zuciyar ki.”

Kai ta rausayar. A zuciyarta tana hango yadda ta ga Zulfa da Labeeb zaune a bayan motarshi jiya. Don ta ji jirin mota a ƙofar gida. Hakan yasa ta leƙa ta window don ta ga ko waye da ta ji ba a shigo ba.

Zaune suke bayan motar, glass ɗin a sauke suke, ice cream ne suke sha suna hira da dariya, gaba ɗaya rabin jikin Zulfa akan Labeeb ɗin yake.

Kuma hankalinsu kwance suke hirarsu ba tare da tunanin yanayin da suke haramtacce bane. Tunda da aure a tsakanin su da Labeeb.

Wannan ba shi bane karo na farko da ta ga hakan. Inda da yarinta a tattare da Zulfa yanzun babu ita. Ganin yadda Dawud ya tattara hankalinshi kanta ya sa cikin sanyin murya ta ce,

“Ba ka ganin kusancin Zulfa da Labeeb yayi yawa? Yadda suke haɗa jiki akwai haramci a cikin ha…….”
Kafin Mami ta ƙarasa Dawud ya miƙe tsaye tare da katse ta da faɗin,

“Mami Labeeb ba zai taɓa cutar da Zulfa ba, shaƙuwar da ke tsakaninsu ta wuce yadda kike tunani…..don Allah ki bar irin tunanin nan.”

Ya ƙarasa yana barin yadda bai ji daɗin maganarta ba na fitowa a muryarshi. Kimar Labeeb da yake gani a idanuwanshi yasa duk wani abu mai muni irin wannan da za ai mishi zato yake ɓata mishi rai.
Mami bata ce komai ba, tana kallo ya fice, ita dai zuciyarta bata son wannan kalar shaƙuwar. Saboda babu dacewa ko kaɗan a cikinta.

Ita zuciya bata da ƙashi, Shaiɗan na iya tasiri a zuciyar kowa. Allah ya kyauta kawai ta faɗi a zuciyarta.

*****

Khateeb ta ajiye makarantarsu don ita ce farko kafin ta wuce ta su, awara ta ga har an fara soyawa yau da wuri. Gashi ta yi kyau sosai,yaushe rabon da ta ci, an fi wata biyu.

Gani tai dan ta siya ko ta naira hamsin babu abinda zai faru in sha Allah. Da sauri ta tsallaka wajen. Ga mamakinta yau ba ma Abida bace. Duk da ta taɓa ganin wannan ɗin tana suyar.

Kuma lokuta da dama tana ganinta tare da abidar, sai ta ɗauka ko regular customer ce. Koma dai menene tasan ba damuwarta bace ba.

Sallama Sajda tai mata ta amsa, da mutane ma a wajen.
“Bani ta hamsin…”

“Aikam akwai ɗan jira, amma yanzun zan soya miki.”

Ta faɗi tana karɓar kuɗin. Ɗan ɓata rai Sajda tayi.

“Don Allah a ɗan bani da wuri, sauri nake yi.”

Kallon ta Sajda ta ga tayi kamar ba zata amince ba. Ƙila uniform ɗin da ta gani a jikinta ne yasa ta cewa,

“Barin in kwashe wannan in sa wata sai in baki.”

“Yauwa nagode.”

Sajda ta faɗi, tana gyara jakar makarantarta da ke rataye kan kafaɗarta.

*****

Ranshi a ɓace ya fito daga gida, ko mota bai ɗauka ba, don babu wani nisan kirki, kuma ya ga akwai bookshop ƙarami a kusa da makarantar su sajda da ake siyar da litattafan Musulunci.

Aikam yayi sa’a ya samu a nan ɗin. Sauri yake don ya kai mata ba sai sun shiga aji ba an zo karatu a ga bata siya ba a doketa. Kamar an ce ya kalli gefenshi.

Sajda yake hangowa jikinta sanye da uniform tsaye gaban mai awara. Da hanzari ya ƙarasa ranshi a ɓace. Yarinyar nan bata da hankali.

Kullum ta ci awarar nan sai cikinta ya ɓaci. Ya hanata ashe bata ji ba. Siya take ta tafi Islamiyya. Sajda da ke tsaye kamar ance ta ɗago ta ko sauke idanuwanta kan fuskar Dawud.

Gabanta ta ji ya faɗi ganin yanayin da ke fuskarshi. Yana ƙarasowa ƙafa yasa yai harbi da bokitin awarar tare da fatali da shi cikin ƙasa.

Matsawa Sajda tai idanuwanta na cikowa da hawaye.

“Me nace miki? Kin rainani ko? Ban isa in hanaki ki hanu ba!”

Girgiza mishi kai take alamar A’a don ta kasa magana. Ji yai ana taɓa mishi kafaɗa. Yasa hannunshi ya ture hannun koma waye ba tare da ya juya ba.

Idanuwanshi na kafe kan sajda. Zagayowa mai awarar tayi. Cike da masifa ta ce,
“Wallahi sai ka biyani awarata. Taɓɗi!”

Ba tare da ya kalle ta ba ya zaro wallet ɗinshi daga cikin aljihu. Dubu biyu ya zaro ya watsa mata tare da faɗin,

“Abinda ya fi wannan zai faru idan kika sake siyar mata da wannan banzar awarar.”

“Ƙanwarka za ka ja wa kunne ko budurwarka ce oho. Ba ni zaka buɗe ma idanuwa ba.”

A fusace ya juya yana sauke idanuwanshi kan yarinyar da take jin zata iya faɗa mishi duk abinda ya fito daga bakinta.

“Uban……”

Kasa ƙarasawa yai. Ya nemi inda kalamanshi suka maƙale ya rasa. Abu ɗaya ne yake da tabbaci akai. Abinda ke cikin idanuwanta ya taɓa shi.

Ya taɓa shi ta inda bai taɓa zato ba, sadness ne da ya sha ganin kalar shi a idanuwan Ummi duk da yadda ta so ta ɓoye mishi.

Abu ne da ya sha gani a tashi fuskar in ya kalli mudubi. Ba kowa zai fahimci yanayin ba sai wanda rayuwa ta taɓa ta fanni fiye da ɗaya.

Lokaci ɗaya ya tsinci kanshi da son jin labarinta, da son kareta daga koma menene wannan da ya bayyana wannan yanayin a fuskarta.

Ganin kallon da Dawud ke mata ya sa muryar Sajda na rawa ta ce

“Yaya…..”

Girgiza kanshi Dawud yayi yana son ko me yake ji yabar jikinshi kafin ya juya ya kama hannun sajda. Janta kawai yake tana ƙoƙarin ƙwace hannunta.

Tsallakawa yai da su ɗayan ɓangaren tukunna ya saki hannunta. Littafin da ke ɗayan hannunshi ya miƙa mata yana ɗan dafe goshin shi.

“Yaya am…….”

Jajayen idanuwanshi ya sauke mata.

“I will loose my mind in kikai magana Sajda.

Kibarni kawai,  kin girma, ban isa in faɗi magana ba ki ji. Baki damu da lafiyarki ba, baki damu da me zanji ba in baki da lafiya…… Sajda…. Kije kawai.”

Ya ƙarasa maganar yana sauke muryarshi ƙasa. Emotions sun mishi yawa. Wucewa Sajda ta yi batare da ta ce mishi komai ba duk da hakan shi ne ƙarshen abinda take son faɗa.

****

Zazzaɓi-zazzaɓi yake ji tun jiya, ya kuma rasa dalili, ga zuciyarshi tayi nauyi. Rabon shi da yanayi irin wannan yanayin tun satin rasuwar Ummi.

Haka yakan yi in yana cikin damuwa ko tunani ya mishi yawa. Zaune yake a ɗakinshi yana assignment. Ya ji an ƙwanƙwasa.

“Shigo……”

Ya faɗi a hankali. Turo ƙofar ya ga anyi. Sajda ce jikinta sanye da uniform na makarantar boko.

Agogon da ke jikin system ɗin ya duba ya ga bakwai da mintina takwas.

Maida hankalinshi yai kan abinda yake yi.

“Ina kwana Yaya.”

Kai ya ɗan ɗaga mata, zama ta yi a gefen gadon. Tai shiru na ‘yan mintina, baka jin sautin komai a ɗakin sai na keypads ɗin da Dawud ke punching kamar yana son huce abinda yake ji a jikinsu.

“Na san nayi laifi Yaya, it’s stupid, duk abinda kake don lafiyata ne, na kasa ganin hakan. Ba zai sake faruwa ba yaya. I mean it this time. Zan iya ɗaukar komai banda wannan fushin Yaya. You are my mum, my dad, my brother, my friend, in baka min magana ba bani da duk wannan abubuwan.”

Sauke numfashi Dawud yayi, yana kallon sajda.
“You have a way with words kinsan wannan ko?”

Dariya ta yi.

“Zama da Yaya Don.”

Murmushi kawai yayi.

“Ya wuce Sajda.”

Miƙewa ta yi da faɗin,

“Thank you Yaya, mun tafi school.”

Miƙewa yayi.

“Muje in sauke ku, sai tara zan fita yau.”

Wucewa ta yi gaba, yana bin bayanta, a falo suka haɗe da Mami ta shiryo Khateeb. Sake gaisawa suka yi da Dawud duk da sun gaisa da Asuba.

Sannan suka yi addu’a suka fice.

****

Tun yana hanya yake ganin kiran Labeeb, ɗagawa yai da sallama.

“Kana gida?”

“Yanzun dai zan dawo, na kai su Khateeb school ne, lafiya dai ko?”

Jim yaji Labeeb yayi kafin ya amsa shi da,

“Lafiya, bari in taho kawai mu yi magana don yau zamu wuce Kano wajen ƙarfe goma.”

“Alright saika shigo.”

Dawud ya faɗi yana sauke wayar daga kunnenshi. Baya son ya kira waya a kashe mishi ko da ya gama magana, ya fi son ya kashe daga ɓangaren shi.

Shi ya sa bai kashe kiran Labeeb ɗin ba, yasan zai kashe daga nashi ɓangaren.

Yana zuwa gida kuwa ya samu motar Labeeb ɗin a ƙofar gida, tashi yai parking a gefe ya shiga da sallama. Yana zaune daga ɗaya kujerar suna hira da Mami, Zulfa na kusa da Mami ɗin.

Kallo ɗaya Dawud yai mata duk da ya kwana biyu bai ganta ba, yasan fuskarta ta kumbura, kamar ta yi bacci ya mata yawa ko kuma ta yi kuka.

Waje ya samu ya zauna a kujerar dake gefen labeeb, suka gaisa.

“Aure zan yi Don, wannan satin mai kamawa.”

Da mamaki Dawud yake kallonshi. Kafin yai ‘yar dariya.

“You are kidding right?”

Idanuwan Labeeb kafe kan Zulfa ya ce,

“Nope, da gaske nake, pressure na mutane akan in yi settling yayi yawa, idan nayi ɗin sai hankalin su ya kwanta.”

Ya ƙarasa maganar yana dawo da kallon shi kan Dawud.

“Ka bar abinda mutane suke so El, ka yi abinda kake so.”

Wani tight murmushi yayi.

“Ban taɓa yin abinda nake so ba Dawud, meye zai canza yanzun? Ku shirya ku dai ranar asabar in sha Allah.”

Tunda dawud yake bai taɓa jin aure daga sama haka ba. Amma in Labeeb ya ga ya shirya, meye nashi na ɗora ayar tambaya akai.

“Nan da kwana uku kenan?”

Kai labeeb ya ɗaga.

“Ba wani taro za a yi ba. Family kawai, close family.”

“Allah ya kaimu.”

Ya amsa da amin yana miƙewa, Mami yai ma sallama da Dawud ɗin. Bai sake kallon inda Zulfa take ba kamar yadda ta kauda kanta gefe itama.
Yana fita ta miƙe ta bar falon, Dawud ya bita da kallo, baisan matsalar ta ba, koma menene ya tsaya mishi a rai.

****

Kamar yadda sauran ranakun suke gudu, haka kwanakin uku suka shuɗe musu ba tare da wani abu ya canza na daga cikin hidimar su ba.

Banda zulfa da rashin maganarta da kowa ya ƙara yawaita, wuni take ɗaki a kwance, abinci ma sai Dawud ya sa baki take ci.

Yai tambayar duniya meke damunta ta ƙi faɗa mishi, ta ce babu komai, kawai hayaniyar ce bata so. Shiryawa ya gama yi tsaf cikin shadda fara, sai dai maɓallai ne kawai a jiki babu aiki.

Komai fari ne har hular kanshi da takalmi da agogo, Tayyab ya kalle shi.

“Wannan kamar kai ne angon”
Hararar shi dawud yayi.

“Kaga ai maka aiki jikin shaddar nan ka ƙi, shi kaɗai ya kashe ɗinkin.”

“Ɓata lokaci ne, haka ya fi kyau, da an saka mata color za’a lalata ta.”

Girgiza kai Tayyab yayi.

“Ai idan aurenka ne rainbow za’ayi a jikin shaddar auren sai muga rashin son colors.”

Dube-dube tayyab ya ga yanayi, ya kwashi kayanshi dake kan gado da gudu ya bar ɗakin yana dariya.

Turaren shi na Oud ya fesa sannan ya fito falon, Sajda da ke zaune cikin shigar doguwar riga na material less ruwan ƙwai ta kalle shi.

“Yaya wallahi ka yi kyau, kawo wayarka in ɗauke ka hoto please. Yaya Tayyab yai mana tare.”
Girgiza kai yayi.

“Sajda kin cika shiririta, ku yi hotunan ku dai ga wayar….”

Ya ƙarasa yana zaro wayar daga aljihunshi ya miƙa mata. Ɓata rai tayi.

“Ni dai har da kai….. Pleaseeee…. One shot kawai.”

Bakinshi ya cika da iska yana fitar da ita.
“Fine….”

“Yeeeee…..”

Sajda ta faɗi tana rugawa da ƙwala ma Tayyab kira ya fito yai musu hoto, da sauri ya fito jikinshi sanye da wandon shaddarshi fara, sai singlet, rigar shi a hannu.

“Lafiya?”

Ya tambaya yana ware idanuwa, kwashewa da dariya Sajda tayi.

“Hoto za ka yi mana.”

Wani dogon tsaki ya ja, yadda ta dinga ƙwala mishi kira ya ɗauka wani abu ne ya same ta.

“Wata rana in na fito kwaɗa miki mari zan yi, ban hanaki min wannan kiran ba?”

Turo baki tayi.

“Yi haƙuri, don Allah zo kai mana.”

Hararar ta yayi, ta sake taɓare fuska.

“Pleaseeeee, pretty pleaseeee.”

Karɓar wayar yayi, da sauri ta zagaya ta gefen Dawud ta riƙe shi gam.

“Sai kin min squeezing ɗin kaya ne wai? Sake ni mana.”

Dariya tayi tana ƙara ruƙunƙume mishi hannu, juya idanuwanshi kawai yayi, babu yadda zai yi da Sajda kam. Hotuna Tayyab yai musu. Sai ga Mami ma ta fito ta gama shiryawa cikin atamfar da akai ta family. Har gida Labeeb ya kawo mata tata, ta kuwa ji daɗin karamcin.

“Oh my goodness, ku kalla Khateeb….”

Dawud ke faɗi yana kasa ɗauke idanuwanshi daga kan ɗan ƙanin nashi, farar shadda ce shima aka saka mishi da babbar riga, anyi aikin blue a jiki irin na su Tayyab, sai hula blue a kanshi.

Tahowa Khateeb yayi.

“Nima hoto, Anty nimaa…”

Yake ce ma Sajda,ɗaukar shi hotuna Tayyab yayi, sannan suka haɗu su duka suka yi.

“Ina Zulfa?”

Dawud ya tambaya. Sauke ajiyar zuciya Mami tayi.

“Ba zata je ba wai, kanta ke ciwo.”

Mukullin mota Dawud ya miƙa ma Tayyab, ka sauke su Sajda gidan Mummy. Ka wuce wajen ɗaurin auren, zan taho.

Babu musu Tayyab ya karɓa, suna wucewa da su Sajda. Dawud kam ɗakin Mami ya wuce inda ya samu Zulfa kwance tana danne-danne da wayarta.

Shi ne gift ɗin da Labeeb ya bata da ta yi candy. Jin shigowarshi yasa ta ɗago kai ta kalle shi kafin ta maida kanta kan wayar.

Takalmanshi ya cire duk da sabbi ne babu inda ya taka da su. Ya ƙarasa cikin ɗakin ya zauna gefen gadon.

“Saboda me ba za ki je ba?”

Ba tare da ta kalle shi ba, muryata ƙasa-ƙasa ta ce,

“Kaina yake min ciwo, bana son hayaniya.”
Kallonta yake yi sosai.

“Zulfa me yake damunki ne? Meye matsalarki da bakya son faɗa min?”

“Ba…..”

Ta fara ya katse da.

“Karki sake ki ce min bakomai, yeah rabin rayuwarki ko ince fiye sa rabi gidan su El kike yinta, but hakan baya nufin ban sanki ba.

Baya nufin bana lura da yanayin walwalarki ko akasin hakan, bazan ce dole sai kin faɗa min ba.

Amma baki da wanda ya fi ni.”

Hawaye ne suka zubo mata, ta sa hannu ta goge su, har lokacin idanuwan Dawud na kanta.
“Kawai na yi kewar Ummi ne.”

“Da kuma me?”

Girgiza mishi kai ta yi hawaye na ci gaba da zubo mata, alamar babu saura.

“Ko auren El ne?”

Wannan karon da sauri ta girgiza mishi kai.

Abinda zai faɗa gaba tun kafin ya fito yake mishi zafi a ƙirjinshi.

“Abba?”

Ya furta kalmar a wahalce, ɗagowa tayi tana sake ɓata rai.

“I hate him….”

Sauke numfashi Dawud yayi, saboda bai san me zaiyi da ta ce har da kewar Abba ba. Hannuwanta ya kamo yana dumtsewa cikin nashi.

“I am here in kin shirya magana, zan fahimta in bakya son faɗa min, but karki sake min ƙaryar bakomai. Kin ji ni?”

Kai ta ɗaga tana matse hannuwanshi dake cikin nata.

“Good. Tashi ki shirya, saboda bazan barki ke kaɗai ba a gida, in kin je akwai inda za ki zauna babu hayaniya abinki. “

Muryar dayai amfani da ita yasa ta sanin babu wajen musu, don haka ta ɗaga mishi kai. Tashi yai ya fita don ta shirya.

Yana shirin ƙwala mata kira don ta jima ya ga fitowarta. English wears ne a jikinta, wandon blue daya kama har ƙwaurinta, sai riga daga ciki fara ta sauko har cinyarta, sama ta dora wata jacket pink colour, mayafin ta ma pink ne tai rolling ɗinshi, haka ma sneakers ɗin da ke jikinta.

Sai wayarta da earpiece a hannunta. Fuskar nan tasha kwalliya. Sai ƙamshin turarukan da Dawud ba zai ce ga su ba take yi.

“Muje Yaya.”

“A haka za ki je? Ba kin dinka irin kayan sajda ba?”
Ɗan daga mishi kafaɗa tayi.

“Ba wani fitowa zan yi ba, don ka hanani zama a gida ne. Beside material ɗin Bai min ba.”

Girgiza kai kawai yayi. Bai ce komai ba har suka fita, takawa suka yi har titi suka shiga Napep.

****

Duk da ba biki Dawud ke zuwa ba, bai taɓa ganin wanda ya burge shi kamar na Labeeb ba. Babu wasu mutane banda family ɗinsu da na amaryar shi Zafira.

Ranar da aka ɗaura aure ƙarfe biyu aka kai mishi amaryarshi a gidanshi da ke barnawa. Sai washegari da suka yi walima a gidansu Labeeb ɗin daga ƙarfe huɗu zuwa Magrib.

Ranar Labeeb ke faɗa mishi Daddy ya gaya mishi za su tashi daga nan gidan za su koma Unguwar Dosa, har da su kawu da Abba. Gida yai musu guda uku a waje ɗaya.

Dawud baiga ta inda hakan ya dame shi ba, in akwai abinda maganar Labeeb ta canza shi ne ya gama zuwa gidansu Labeeb ɗin in ba dole ta kama ba.

Din ƙarshen abinda yake so bai wuce ganin fuskar mutumin nan ba. Baya son ko hanya ta haɗa su. Saboda haka Allah ya sanya alkhairi kawai ya furta.

Sa’adda suka dawo gida ma abin ya fita daga ranshi don har ya manta an yi wani abu irin wannan. Akwai abinda yake ranshi sai dai ba zai ce ga shi ba.

Bayan sati daya

Zaune suke shi da Mami a falo suna kallon labarai. Zulfa da Sajda suna ɗaki abinsu, Khateeb da Tayyab kuma sun fita.

Suka ji ana ƙwanƙwasa ƙofa.

“Waye?”

Dawud ya buƙata. Ƙwanƙwasa ƙofar aka ci gaba da yi ba tare da anyi magana ba.

“Ka tashi ka duba mana.”

Mami ta ce mishi, miƙewa yayi. Baisan me yasa duk takun da zai yi zuwa ƙofar ba sai zuciyarshi ta doka da ƙarfi. Yana buɗe ƙofar ya ga dalili.

Hannu ya kai wuyanshi yana taɓa maƙoshin shi cikin ƙoƙarin haɗiye abinda ya taso daga ƙirjinshi ya tsaya a wajen. Duk shekarun nan, idan akwai abinda ganinshi yayi bai wuce tsanarshi da ta dawo ma Dawud sabuwa ba.

Numfashi yake mayarwa da sauri-sauri, kafin ya maida ƙofar ya rufeta a fuskar Abba. Ya dawo ya zauna jikinshi ko ina ɓari yake.

“Waye?”

“Bakowa.”

Ya faɗi da sauri, ƙwanƙwasa ƙofar aka sake yi.

“Babu kowa mami, just….. Bakowa.”

Da mamaki take kallon Dawud, ci gaba da aka yi da ƙwanƙwasa ƙofar kamar za a karyata yasa Mami miƙewa.

“Karki buɗe.”

Dawud ya faɗi muryarshi a karye, Mami bata ce mishi komai ba ta ƙarasa ta bude ƙofar. Ba sai an faɗa mata ba, kamar da suke da Sajda kawai yasa ta gane ko wanene.

Ita kanta sai da ta ji zuciyarta na dokawa, bai ce mata komai ba, niyyar shigowa ciki ta ga yanayi, da sauri ta raɓe gefe ɗaya ta bashi hanya.

Wucewa yayi ciki, da sauri Dawud ya miƙe.

“You have no right, ka fitar mana daga gida! Ba ma buƙatar ka!”

Dawud ya faɗi cike da hargowa, abin ƙarin takaici murmushi kawai Abba yayi.

“Zan fita Dawud, kuma haka, zuwa na yi in tafi da ku…..!!!”

Tun kafin ya ƙarasa Dawud ke girgiza kanshi yana faɗin,

“No…. No… This can’t be….. No and No….. “

A fili yake faɗa cikin kanshi da zuciyarshi babu komai sai muryar ummi.

“Ka yi min alƙawari Dawud, duk ranar da Abbanku ya buƙaci ku koma wajen shi za ku koma!”

Hannuwanshi Dawud yasa yana toshe kunnuwanshi kamar yana son toshe muryar ummi. Da ƙarfi ya ce,

“No!!! A’a!!!”

Ihun Dawud shi ya fito da Zulfa da Sajda daga ɗaki da sauri. Wani irin firgici ne ya mamaye fuskar Zulfa da ganin Abbansu a tsaye.

Runtsa idanuwanta ta yi, babu abinda ke mata yawo cikin kanta banda ranar da Abbansu ke watso musu kaya waje, ranar da ya sa hannu ya hankaɗe Ummi harta fadi.

Ranar da yake faɗin baya son ganinsu, kafin ta buɗe idanuwanta ta sauke su akan shi, yana nan yadda tasan shi, bata ga ya canza mata ba, sai dai akwai wani abu tattare da shi da ta kasa fahimta.

Sajda kam hannayenta duk biyun tasa tana riƙe bakinta cike da mamaki kafin ta kai hannuwan ta murza idanuwanta. So take ta ga ko mafarki take kamar yadda takanyi da Abbanta.

Duk da waɗancan mafarkan masu firgici ne, ba kamar wannan da ke cike da kwanciyar hankali ba.

“Abba……”

Ta faɗi idanuwanta na cika da hawaye. ware idanuwa Abba yayi akan Sajda, yana kallon girman da ta yi, ko da ya shigo bai ji wani abu mai banbanci akan Dawud ba.

Asali ma baya jin kowacce dangantaka tsakanin su. Ya zo tafiya da su ne akan shawarar Hajiya Beeba. Domin a ganinta siyasar da zai shiga dole ya zamana su Dawud ɗin na tare da shi.

Perfect family da image yake buƙata, surutu zai yi yawa in aka gano yaranshi na zaman kansu. Ya kuma ga point ɗinta, don haka ma ya zo ya tafi da su.

Amma Sajda, ganin Sajda daban ne, ƙaunarta na nan wani waje a adane, tsoronta tun ranar da rashin lafiya ta sameta shi ya lulluɓe shi. Yanzun kuma ya yaye.

Tarau yake ganin ‘yar shi da ya fi shaƙuwa da ita duk a cikin yaranshi. Muryar shi a sarƙe ya ce,
“Sajda……”

Da gudu Sajda ta tafi wajenshi, buɗe hannayenshi yayi tana faɗa a ƙirjinshi, kuka take marar sauti, tana jin ɗumin mahaifinta a jikinta.

Ƙaunar shi da kewarshi na shekarun nan suna ƙara danne ta, tare da kewar Ummi, kullum cikin tunanin su take duk da bata ganinsu.

“Abba….. Abba karka barmu….”

Sajda take faɗi tana sake ruƙunƙume Abba kamar tana gudun da ta sake shi ɓacewa zai yi. Sosai take kuka tana faɗin kar ya barsu.

Da duk kalmar da ke fita daga bakin Sajda da yadda Dawud ke jin kamar ana soka mishi wuƙa a ƙirjinshi. Alƙawarin da ya ɗaukar wa Ummi ne ke ɗɗɗaure da jikinshi.

Shekara takwas da wani abu kenan da barinsu gidan Abba, bai taɓa zaton zai zo ya nemi su koma ɗin ba, tunanin wannan alƙawarin bai taɓa damun shi ba.

Sai yanzun, sai lokacin da bai taɓa zato ba.

Abinda hakan yake nufi a wajen su yake tunani, iskar da yake ja ya ji bata kaiwa inda ya kamata, ga kanshi da ke sarawa.

Khateeb, ta ina zaima Khateeb wannan bayanin, da ƙarancin shekarun shi babu abinda hakan yake nufi sai rikitarwa.

Duk a ɗaukarshi Mami ce mamanshi, bai taɓa sanin wata uwa banda Mami ba, Dawud yake kallo a matsayin babanshi. Ko abu aka basu a makaranta sukai ma iyayensu maza Dawud yake kawowa.

Ta ina zai fara mishi bayanin matsayin mutumin nan da ke tsaye a wajen shi, wacce amsa zai ba wa Khateeb inya tambaye shi me yasa baya nan duk shekarun nan?

Dafe kai Dawud yayi, komai ya sake dawowa sabo. Dai dai shigowar Khateeb da Tayyab. Da dariyar su. Ganin su tsaye cirko cirko yasa shi faɗin,

“Ya dai?”


Don sam bai kula da Abba da ke gefe ba. Kamar daga sama Tayyab ya ji muryar da yake tunanin ya manta a rayuwarshi, muryar da yake tunanin ta gama zuwa zuciyarshi balle ta hana shi zama lafiya.

“Tayyab…..”

Kamar wanda aka jona ma wayar wuta ya zabura, yana sakin hannun Khateeb da Mami ta kama, da sauri ya koma bayan Dawud ya tsaya.

Kallon Abba yake cike da tsoro a idanuwanshi, baisan me yazo yi ba, koma menene bai dame shi ba. Kawai ya fita shi ne matsalarshi. Baya son ganin shi ko kaɗan.

Yana tsoron ya fama mishi ciwukan daya daɗe yana jinya kafin su yi mishi sauƙin ciwo. Miyau ya ji ya bushe mishi a baki, da ƙyar, muryarshi na rawa ya ce,

“Ya me yake anan? Ba ma buƙatarshi, ka sani ai, we have you, bama son shi a kusa damu.”

Kama hannun Tayyab dawud yayi, ba don yai comforting ɗinshi ba sai don ya samu ƙwarin gwiwar da zai fuskanci Abba.

Alƙawarin da ke ɗaure dashi yasa bashi da wani kataɓus, bashi da wani ƙarfin gardama da maganar Abba ɗin. Ƙwace hannun shi Tayyab yayi daga na Dawud.

Ya taka inda Abba yake, ya sa hannu ya ɓamɓaro Sajda dake jikinshi.

“Ya tayyab….. Abba ne… Ka bari.”

Sajda ke faɗi. Bai ma saurareta ba ya sa ƙarfin shi duka ya janyeta daga kusa da Abban, muryarshi can ƙasan maƙoshi yake faɗin,

“Karki sake ki sashi a ranki sajda, he will only hurt you……”
Kuka Sajda take yi amma Tayyab ya ƙi sakinta sai da ya ƙarasa inda zulfa take sannan ya dafa kafaɗar Zulfa yana juyawa da su.

Juyowa zulfa ta yi tace ma Dawud,

“Tell him to get lost…..”

Kafin ta sa hannunta cikin na Tayyab suka wuce suna shigewa ɗaki. Shiru ya baƙunci falon. Kafin Khateeb ya kore shi da faɗin,

“Don waye wannan?”

Kallon shi Abba yake yi, akwai abinda yake tattare da yaron da ya ke mishi yawo, idanuwanshi,

yanayin fuskarshi,zuciyarshi ce ta doka da ƙarfi.
Kafin ya gama gane abinda ke faruwa dawud ya ƙarasa ya ɗauke Khateeb cak ya ɓoye shi a ƙirjinshi. Wucewa yayi da shi ya ajiye shi ƙofar ɗakin da su zulfa suka shige, ya buɗe kofar ya tura shi ya janyo ta.

Jikinshi babu ƙarfi ya koma, ƙofa ya nufa ya buɗe ta yana riƙewa a hannunshi.

“Dn Allah ka tafi!”

Dawud ya faɗi idanuwanshi na kafe a ƙasa. Don baya son ganin fuskar Abba ko kaɗan.

“Ku dawo wajena Dawud, ku dawo gida….”

Kalmar ‘Gida’ da Abba ya faɗi ya fi komai tsaya wa Dawud. Wai Abba ne yake kiran su koma gida. Wanne gida suke da shi yanzun daya wuce wannan da suke ciki.

Ko ina za a ɗauke su akai su a duniya ba zai taɓa zame musu gida ba, sun riga da sun rasa wannan shekaru masu yawa da suka wuce.

“Ka tafi…..”

Dawud ya sake nanatawa.

“Babu inda zani babu ku.”

Abba ya faɗi yana sake gyara tsayuwa.

“Ka tafi zamu zo da kanmu.”

Dawud ya faɗi yana jin kowacce kalma na tsaya mishi a ƙirji da wani irin ƙuna. Lokacin da yake tunanin komai ba zai sake taɓa su ba, lokacin da yake tunanin ya sama musu dai-daituwa a rayuwar su.

Kallon shi Abba yayi, kafin ya gyaɗa kai yana wucewa da faɗin,

“In baku zo ba zan dawo, zanyi amfani da komai akan wannan.”

Dawud bai ɗago ba, komai zai iya faruwa in ya ɗora idanuwanshi kan Abban a yadda yake ji yanzun. Fita abba yayi. Dawud ya tura ƙofar a hankali.

Kai-kawo yake cikin ɗakin yana ƙoƙarin fahimtar girman abinda ya sake ɓullowa a rayuwarsu.
“Karɓi ka sha Dawud.”

Mami ta faɗi tana miƙa mishi glass cup da ruwa a ciki, karɓa yayi ya shanye ya miƙa mata.

“In ƙaro maka?”

Ta tambaya, ya girgiza mata kai, gaba ɗaya tausayin shi ya cika mata zuciya.

“Ka zauna to.”

Babu musu ya ƙarasa kan kujerar da ke wajen ya zauna tare da dafe kanshi cikin hannuwanshi yana jin kamar yaita kurma ihu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 13Rayuwarmu 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.