Kallon mutane kawai Labeeb yake yana mamakin wai da gaske auren shi ne aka ɗaura. Sama sama yake ganin komai na wuce mishi.
Haka suka yi ta hotuna, banda murmushin yaƙe da yake baya komai, asali ma kanshi jujjuyawa yake yi. Har suka gama da mutane suka bar wajen.
Gaba ɗaya haka ranar ta zo ma Labeeb tana kuma wucewa da sauri kamar walƙiya. Ba don Mummy da ta kirashi take faɗa mishi gidan da ta siya mishi a barnawa zasu zauna ba in zaka saka mishi wuƙa baisan inda aka kai mishi amarya. . .