Skip to content
Part 25 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Kallon mutane kawai Labeeb yake yana mamakin wai da gaske auren shi ne aka ɗaura. Sama sama yake ganin komai na wuce mishi. 

Haka suka yi ta hotuna, banda murmushin yaƙe da yake baya komai, asali ma kanshi jujjuyawa yake yi. Har suka gama da mutane suka bar wajen. 

Gaba ɗaya haka ranar ta zo ma Labeeb tana kuma wucewa da sauri kamar walƙiya. Ba don Mummy da ta kirashi take faɗa mishi gidan da ta siya mishi a barnawa zasu zauna ba in zaka saka mishi wuƙa baisan inda aka kai mishi amarya ba. 

Mummy ya faɗa ma ta gaya ma family ɗin yarinyar za su zo ɗaukar ta da mutanenta bayan Magariba zasu yi ‘yar ƙaramar walima. 

Hakan kuwa suka yi, da Magariba Zainab ya ba wa address ɗin wajen ya bar komai a hannunta. Ya ɗauki mota ya wuce gidansu Dawud don bai ga Zulfa ba. 

Daga ita sai Mami ya samu cikin gidan don Sajda na can. Suka gaisa da Mami. Waje ta basu. Labeeb ya tashi ya koma inda Zulfa take.

“Me kike nufi?”

Kallonshi tayi. 

“Kaina ke ciwo, hayaniya damuna zata yi shi yasa.”

Girgiza mata kai Labeeb yake. 

“Tam. Mu zauna anan.”

“Yaya mana.”

“Wallahi bazan je ba idan ba za ki je ba.”

Dafe kai Zulfa ta yi tana haɗiye kukan da take ji zai kubce mata. Sam ya kasa gane halin da zuciyarta take ciki. Miƙewa tayi ta nufi ɗakinsu. Ta shiryo cikin doguwar rigar da Zainab ta bata ta party ɗin.

Light make up ta ɗan yi ma fuskarta ta ɗauki abinda take bukata, tai ma Mami sallama ta fito. 

“Mu tafi.”

Ta ce ma Labeeb a taƙaice, bai ce komai ba ya wuce gaba ta bi bayanshi, har suka ƙarasa inda ake party ɗin babu wanda yai magana saboda ran Labeeb a ɓace yake. 

Baisan me yasa Zulfa ke mishi haka ba. Har ita zata ce ba za ta yi attending wani abu na bikinshi ba. Itama ta kula ranshi a ɓace yake. 

Suna shiga wajen kallo ya koma kansu. Bai kalli kowa ba ya ƙarasa ciki Zainab ta ƙaraso inda yake ta kama hannunshi. 

“I am going to kill you Yaya, you are late.”

Dariya kawai yayi yana binta har ta ƙarasa da shi inda Zafira take zaune. Sosai wajen ya ƙawatu, yadda babu mutane sai family ɗinshi sai kuma mutanen amarya ya mishi daɗi . 

Idanuwanshi ya sauke kan Zafira l, bata cika haske ba, amma ba zai yi ƙarya ba kyakkyawa ce ta shiga abokai. Waje ya samu ya zauna kusa da ita. 

Ƙamshin ta na mishi yanayin baƙunta.

“Na makara ko?”

Ya ce mata, juyawa tayi tai mishi murmushi, duka ba zata wuce sa’ar su Zulfa ba. 

“Tunda kana zaune a nan babu komai.”

Ɗan murmushi yayi kawai ba tare da ya sake cewa komai ba. Zainab ta ɗauki microphone ta soma magana. 

“Assalamu alaikum. Ku ɗan min haƙuri duk abinda na tsara faɗi just boom… Komai ya ɓace…”

Dariya mutanen wajen suka ɗan yi. 

“Banda abubuwa da yawa da zan faɗa da ya wuce Yayana ba kamar kowa bane, yayana guda ɗaya ne a cikin Yayye da yawa. 

Wasu za su ce na yi son kai, amma zance bana jin akwai Yaya kamar nawa. Zan bada tabbaci zai zama miji mai nagarta a wajen matar shi. Mutane kance ba a bada shaida akan mutum, zan bayar akan Yayana. Addu’ata a yau guda ɗaya ce….”

Zainab ta faɗi tana juyawa ta kalli Zafira da ke zaune, a hankali ta taka ta ƙarasa inda suke zaune. Sai da ta tsugunna gabansu. Ta kama hannun Labeeb ta saka cikin na zafira sannan ta ja wani dogon numfashi. 

“Addu’ata guda ɗaya ce, Allah yasa ki kula min da Yayana kamar yadda nake da tabbacin zai kula dake. Ina tayaka murna Yaya Labeeb.”

Zainab ta ƙarasa tana miƙewa ta kalli taron mutanen sannan ta ce, 

“Mun gode da halattar wajen nan.”

Ta nuna Asad da Anees da ke tsaye suna kallonta da microphone ɗin da alamar su ƙaraso su karɓa. Tafi wajen ya ɗauka, su dukansu suka ƙaraso Asad ya karɓi microphone din daga hannun zainab. 

Takawa tayi ta koma inda suka bari ta tsaya. Kamar daga sama ta ji muryar Ishaq. 

“Bansan kin iya speech haka ba.”

Juya idanuwanta tayi ba tare da ta kalle shi ba, duk da abinda take so tayi ɗin kenan. Shi ya dawo gabanta ya tsaya yana zuba mata idanuwanshi. 

“Kinyi kyau sosai.”

Ɗan murmushi tayi. 

“Nagode, excuse me kaɗan.”

Ta faɗi tana raɓashi ta wuce, murmushi Ishaq yayi, yanayin kominta na burge shi. Ba wani daɗewa akai ba, iya ‘yan gidansu ne suka yi bayani.

Anci, an sha an kuma rarraba kayayyaki. Sajda ta rufe musu taron da addu’o’in da yanayin sanyin muryarta kawai yasa su shigar kowa dake wajen. 

Zainab ta ƙarasa inda Labeeb da Zafira suke ta kama hannayen su ta kaisu wajen motar da tasa akai ma kwalliya mai tsari. Hankalin Labeeb gaba ɗaya na kan Zulfa. 

So yake yai mata sallama, amma ko giccinta bai gani ba. Ya kuma san Zainab ba zata barshi ya tafi ko ina ba. Hannunshi ma ta kama ta saka mishi mukullin mota.

Ta buɗe ma Zafira ta shiga, sannan ta kama hannun Labeeb ta zagaya da shi. Rungume shi tayi sannan ta sumbaci kuncin shi ɗaya bayan ɗaya. 

“Be happy big bro. I love you.”

“Love you more.”

Ya faɗi yana buɗe motar ya shiga. Ya ja su zuwa gidan su na Barnawa zuciyarshi a cunkushe da tunani barkatai. 

***** 

Hannu yasa ya mayar ma da Zafira gashinta da ya zubo kan fuskarta, bacci take sosai, don ko da yasa hannunshi ya shafi fuskarta bata motsa ba. 

Da ƙyar ya samu ta tashi tai sallar Asuba. Bai taɓa dauka wani abu zai canza tsakaninta da sauran matan da yake bi a waje ba sai daren jiya. 

Mamakin kalar nutsuwar da ya samu shi ne abinda ya hana shi bacci. Ya ɗauka mata duk kalarsu ɗaya ne. Sai jiya ya gane matarka da aka ƙulla igiyar aure tsakanin ku koda babu soyayya tana da banbanci tsakanin ta da matan banzanka na waje. 

Tattare da nutsuwar da yakan samu a wajen matan shi na waje yakan zo cike da tsana, ƙyamata, da na sani da jin dauɗar zunuban da ya ɗauka na aikata zina. 

Zunuban da ko bacci yake yana jin nauyin su, sai gashi a karo na farko ya gane daraja ɗaya daga cikin dubban da ke tattare da matar da take halattacciya a wajenka. 

Har yanzun babu soyayyar Zafira ko ɗigo a zuciyarshi. Ya ɗauki abinda ya haɗa su a matsayin abinda ya dace yayi, da dabara ya zame hannunta da ke kan jikinshi ya sauko daga kan gadon. 

Lokaci ɗaya maganganun da Zainab ta yi daren jiya wajen partyn shi ya faɗo mishi. Zuciyarshi tai wata irin dokawa. Zainab ta bada shaida akanshi bisa abinda ta sani na halayyarshi. 

Ta bada shaida cewar zai riƙe Zafira da gaskiya a gaban mutane ba tare da shakkun komai ba. Dafe kai yayi. 

“Haba Zee Zee…”

Ya furta a hankali yana jin yadda Maganganunta suka sake ɗaure shi. Banɗaki ya shiga ya sake wanka ya fito. Three piece suit ya saka a jikinshi banda vest ɗin. 

Cikin kanshi yake calculating raba ɗakin kwana da Zafira don yasan akwai ranar da zai so kwanciya shi kaɗai. Turaruka ya duba, babu kalar nashi ko ɗaya, haka ya ɗan fesa wasu daga cikin wanda ya gani. 

Ya duba mukullin mota, har ya nufi ƙofa ya dawo, dube dube yake kozai samu ‘yar takarda da biro don ya bar mata saƙon cewa ya fita ya samo musu abinda za su karya da shi. 

Bai samu ba, sauke numfashi yayi a gefe ɗaya yana jin wata takura ta daban. Bai saba ma kowa bayanin cewa zai fita ba. In ya ga su Asad a falo yai musu sallama, in bai gani ba ya wuce abinshi. 

Yanzun ma da bai samu takardar da biro ba ficewa yayi tunda yasan ba daɗewa zai yi ba. Har ya sauka ƙasa ya ga babu mota ko ɗaya sai wadda suka dawo gida cikinta jiya. 

Sai yanzun cikin haske sosai yake ganin kwalliyar dake jikin motar, lumshe idanuwanshi yayi, yanzun ina zai je da mota haka. Wayarshi ya laluba ya tuna ya barta a ɗaki. 

Ɗan ƙaramin tsaki ya ja ya koma cikin gidan. Har ɗakin ya shiga ya ɗauki wayar, Mamdud ya kira wayarshi a kashe, har yai dialing number ɗin Zulfa yai sauri ya kashe kafin ta shiga. 

Asad ya kira ya faɗa mishi abinda zai siyo ya kawo mishi. Takalman ƙafarshi ya cire ya koma kan gadon ya zauna yana jingina bayanshi jikin kan gadon. 

A hankali Zafira ta buɗe idanuwanta ta sauke su kan fuskar Labeeb, ɗan guntun murmushi yai mata. 

“Hey lazy bones.”

Ya faɗi da wasa tattare da muryarshi, pillow ɗin da ke gefenshi ta ja tana kare fuskarta. Murmushi Labeeb yayi. 

“Zaki iya tashi ko in taya ki?”

Ya buƙata, pillow ɗin ta cire tare da girgiza mishi kai. Sauka ta yi daga kan gadon tana nufar toilet, Labeeb ya bita da kallo. Duk inda ake son mace takai zaphira ta kai don dai ko kaɗan baya jinta a ranshi ne. 

Yana nan zaune ta fito ɗaure da towel, wayarshi da kira ya shigo ne yasa shi ɗauke idanuwanshi daga kanta, ganin Asad ne yasa shi miƙewa ya fice daga ɗakin. 

Zafira da ke zaune a gaban mudubi tana kwalliya ta sauke numfashi. Huɗubar mamanta na dawo mata. 

“Maza irin El-labeeb Maska babu kalar matan da basu gani ba. Ba wani daraja za ki yi a idanuwanshi ba. 

Ki tabbatar kin kwashi rabonki kafin ya gaji da ke. Kuɗi ne zai shigar dake gidanshi, ba matsala bane su a wajen shi. Ki tabbatar kin cika account ɗinki kafin ki dawo min.”

Ɗan murmushi tayi, ba ita bace ta farko, mata biyar ne a gidansu, ita ce ta huɗu sai autarsu. Gaba ɗayansu babu wadda tai auren soyayya. Aure suke na jari, kyawun da suke da shi yasa hakan baya musu wahala. 

Inda antynta ta jera mata kayan da zata dinga amfani da su cikin gida lokacin da Labeeb yake nan ta nufa. Ta buɗe, wata doguwar riga ta ɗauko mai spaghetti straps kalar pitch ta saka. Ta tattara gashin kanta ta ɗaure shi ta gefe. 

Turaruka take feshe jikinta dasu Labeeb ya turo ƙofar. Ɗan ware idanuwanshi yai kan fuskarta kamun su yawata zuwa yanayin shigarta. Zafira ma shi take kallo.

Ta sha ganinshi a fina-finai. Ta kuma ganshi a daren jiya, sai dai yau ne ta samu damar ƙare mishi kallo cikin haske, ido da ido ba tare da matatar fim ba. 

Dogo ne tun jiya da ta ga kanta ko kafaɗarshi bai zo ba ta fuskanci haka, ba zaka kirashi da fari ba, sai dai yana da wani kalar hasken fata mai kyau. 

Zafira ba zata kira Labeeb mai kyau kai tsaye ba, inda duk namiji yakai a ƙirar jiki yakai, sai dai tasha ganin mazan da suka fishi kyan fuska da komai. 

Ɗan sumar da ke fuskarshi da kanshi sun ƙara mishi kwarjini na daban. Murmushi ya ɗan yi mata da ta kula da dimple guda daya a gefen kuncin shi na dama. 

Ƙarasawa yayi inda take, in zai yi zaman aure mai ɗorewa da wannan yarinyar dole ya koya ma zuciyarshi bata muhimmanci koya yake. 

Light sumba ya manna mata a laɓɓanta, yana jin yadda ƙamshin man leɓenta ya manne mishi a baki da wani yanayi da bai mishi daɗi ba. Ɗayan hannunshi da baya riƙe da ledojin da ya shigo da su yasa ya goge laɓɓan shi. 

Kallon da Zafira ta bishi da shi ne yasa shi jin rashin kyautawar abinda yayi. Cikin idanuwa ya kalleta. 

“Mu fita mu karya ko mu yi anan?”

Ya buƙata, ɗan ɗaga mishi kafaɗa tayi, alamar duk yadda ya gani. Kan gadon ya nufa ya ajiye ledojin ya zauna gefe, matsalarta ce. 

Duk inda ta kama mishi ya ci abinci, ci yake. Bai jirata ba ya fara aikama cikinshi, Kallonshi take tana mamakin kalar yangarshi da ga dukkan alamu baisan yanayi ba. 

Ta kuma ji wani iri da halin ko in kulan da yake nuna mata, ta sha jin labarin yadda angwaye ke tarairayar amarensu washegarin daren su na farko. 

Amma ko kaɗan daga cikin hakan bata samu ba. Maganar mamansu ta sake riƙewa sosai. Da gaske gidan El-labeeb Maska ba gidan da zatai zama mai ɗorewa bane. 

Ganin ba shi da niyyar ce mata ta zo su ci yasa ta ƙarasawa ta zauna a gefen gadon. Ɗan dankali ta ci kaɗan, sai farfesun nama da shima ba wani mai yawa ta ci ba. 

“Har kin yi me?”

Labeeb ya buƙata. 

“Na ƙoshi.”

Ta amsa mishi tana gyara zamanta kan gadon. Ɗan jinjina kai yayi. 

“Da mamakin kalar jikin ki in har hakane normal cin abincin ki.”

‘Yar dariya Zafira tayi. 

“Da gaske nake.”

“Na sani, cin abinci ba shi bane ke sa jiki ai, kawai halitta ne.”

Ta amsa shi da murmushi a fuskarta. Ɗan shiru yayi, ya kuma rasa kome zai sake cewa. Lallai akwai aiki, ranar farko ya soma rasa kalar maganar da zai yi da matar shi. 

Miƙewa yayi, ya tattara sauran abinda suka rage dama wanda basu taɓa ba ya fice ya ba Maigadi tukunna ya dawo. Inda ya tashi ya koma ya zauna. 

Shiru suka yi na tsawon mintina sha biyar, ba tare da wani yasan abinda zai ce ma ɗayan ba. Kafin yanayin ya ishi Zafira. 

“Ka yi shiru.”

Ta faɗi ba din tasan me yasa ta ce mishi hakan ba. Sai don ta kori shirun ɗakin kawai. 

“Babu abin faɗa ne shi yasa…”

Zame jikinta Zafira tayi tana kwanciya ta juya mishi baya. Sam yadda duk take ɗokin auren ya zo mata a wani iri. Ƙin zuwan Labeeb gidansu ko da sau ɗaya kafin auren ya isa ace ta gane shigowarta gidan ba zai canza wani abu ba. 

Kissing ɗinta da yayi ma hannu yasa ya goge laɓɓanshi kamar wanda ya goga wani abun ƙyamata. Ga mamakinta hawayen takaici ne ta ji sun tsiraro mata. 

Sauke numfashi Labeeb yayi, fita yake son yi ya bar gidan ya ɗan shaƙi wata iska ta daban da takurarriyar da yake ji cikin ɗakin amma yasan ko a rashin mutunci irin nashi ba zai iya barin ‘yar mutane ita kaɗai ranarta ta farko a matsayin matarshi ba. 

Agogonshi ya kwance ya ajiye gefe tare da rage kayan jikinshi, gefen Zafira ya kwanta, a hankali yasa hannunshi ya juyo da ita kamar bata da wani nauyi. 

Fuskarta yake kallo yana ganin hawayen da ke kai, hannu yasa ya goge mata su, cikin sanyin murya ya ce, 

“Ban taɓa kawo aure a rayuwata a wannan lokacin ba, sai kin yi haƙuri da ni, bansan ko ta yaya ba, i will try and make this work, kin ji?”

Kai ta ɗaga mishi kawai tana jin nauyin da zuciyar ta tayi ya ɗan yi sauƙi, ga jikinta ko ina ciwo yake. 

“Jikina ciwo yake.”

Ta faɗa a raunane. Lumshe idanuwanshi Labeeb yayi, yana jin ta ko ina auren nan cutar ‘yar mutane zai yi , bai saba after care ba, ya riga da ya saba da ya gama da mace zai tsallake abinshi. 

Dole ya koyi banbanta Zafira da sauran matan da ya saba da su, ta kowanne fanni suna da banbanci, ɗagota yayi gaba ɗaya ya kwantar da ita a jikinshi. 

Baisan kalaman da zai yi amfani dasu ba, don haka ya soma nuna mata kulawa ta hanyar da ya fi ƙwarewa, ya soma tura mata sabawa da shi mai tsayawa a zuciya. 

****

Ta nemi bacci ta rasa, koya ta rufe idanuwanta bata ganin komai sai Labeeb da Zafira. Yau tasan son da take mishi ya wuce dukkan tunaninta. 

Bata bari an tashi wajen partyn ba ta samu Mamdud ta ce ya mayar da ita gida. Bai ko tambayi dalili ba wanda hakan ba ƙaramin daɗi yai mata ba. 

Ko kayan jikinta bata cire ba take nan kwance, tun tana kuka da hawaye har ya kai basa fita. Zafi ne take ji a zuciyarta da wanda yasan ma’anar rasa abinda kake so ne kawai zai iya fahimta. 

Bata san yadda zata yi da zuciyarta ba, bata san yadda zata soma jinyarta ba, kamar yadda bata san yadda zata dinga haɗa idanuwa da Labeeb a koda yaushe ba. 

Sanin soyayyarshi ta mata nisa, ya zama mallakin wata, sanin soyayyar da take mishi ɓangare ɗaya ce. A idanuwanshi ita ƙanwa ce da babu abinda zai canza hakan. 

Tasan in yanzun ta buɗe baki ta ce tana sonshi ko baya jin hakan zai aureta don farin cikinta, sai dai ba zata taɓa risking abinda suke da shi don son kanta ba. 

Farin cikinshi na nufin komai a gareta, rufe idanuwanta tayi tana barin zuciyarta na ƙuna da hoton Labeeb da Zafira. Tana son zuciyarta ta fahimta ta haƙura. 

Labeeb ya mata nisan da ba zata iya kamoshi ba. Gabanta ya sha faɗin a tsarin rayuwarshi babu mata biyu. Macen da duk zai aura saiya tabbatar ta ishe shi. 

Zuciyarshi don mace ɗaya aka yita. Zai jirata komin tsawon lokacin da zata ɗauka bata zo ba. Da dukkan komai ya nuna mata Zafira bata da muhimmanci a wajen shi. 

Sai dai aure abune mai wahalar fahimta. Darajar shi mai girma ce. Zata iya canza komai. Ko bata canza ba bata jin zai sake auren wata. Tunda ya haƙura ya auri Zafira zai zauna da ita a kowanne yanayi.

Hawaye ne masu zafin gaske suka biyo fuskarta. A wani ɓangaren tana ganin laifinta ne. Ƙila da bata nuna mishi damuwarta kan yayi aure ba da bai amince ba. 

Wani ɓangaren kuma tana ganin auren zai zame mishi silar fita daga halakar da yake ciki. Haka bacci ya ɗauke ta cike da mafarkai marasa ma’ana. 

**** 

Kamar akan ƙaya haka ya ɗaure ma zuciyarshi yayi sati ɗaya ba tare da kowa ya samu lokacin shi ba sai Zafira. In ya fita to ya ɗauketa ne sun fita cin abinci. 

Yau kam da ya zamana ranar da zai bar garin ne jin shi yake a sama. Jin shi yake kamar wanda aka saki daga ɗaurin da akai masa. 

Rayuwar kwana bakwai ɗin nan kala daban ce da waddda ya saba. Shi ba El-labeeb ba shi ba El-Maska ba. Baisan yadda zai zama abinda ba zai cutar da Zafira ba. 

Maɓallan rigarshi yake ɓallewa ya ji ta rungume shi ta baya. Ƙamshin turarukanta da ya kasa sabawa da su har yanzun suka daki hancin shi. 

“Sai sauri kake kamar ka gaji dani…”

Ta fadi tana wani irin sauke murya da ya ɗan taɓa shi, kamota yayi ya dawo da ita gabanshi ta fuskance shi tare da ɗora hannunshi kan kafaɗarta. 

“Kin tabbata ba kya buƙatar driver da zai kaiki makaranta ya dawo da ke?”

‘Yar dariya tayi, duk da ba abinda ta so ji kenan ba. Ta san don kar ya amsa tambayar ne yasa shi canza maganar. Tun data samu gurbin karatu a Kaduna State University ita take kai kanta makaranta. Gashi har tana shekararta ta biyu. 

Jiya da ta faɗa mishi ita ma a satin zata koma makaranta, ta ga mamaki kaɗan a fuskarshi. Kamar bai kawo maganar makarantarta a ranshi ba. 

Hannu ta sa ta ja mishi hanci, ya ture hannunta yana yamutsa fuska. 

“Bana buƙatar driver.”

Kai ya ɗan ɗaga mata yana sauke hannuwanshi daga kafaɗarta. 

“In kuɗin da na tura sun miki kaɗan ki kira ni.”

Murmushi Zafira tayi, ko bai faɗa ba tana da niyyar hakan, duk da ya ce mata da wahala ya wuce sati biyu, dubu ɗari ya tura mata a account ɗinta. 

A gurguje ya ƙarasa shiryawa. Anees ya sa ya kawo mishi mota, ya bar ma Zafira ɗayar. Hannu yasa ya tallabo bayan kanta tare da da sumbatar ta. 

“Ki kula da kanki, call me if you need anything.”

“I will, kaima ka kula da kanka.”

Sake sumbatarta yayi kafin ya wuce, don ya ƙagu ya ji shi a wajen gidan. Kewar ƙannenshi da Zulfa yake ji kamar me. Gara su kullum sai ya kira kowa ya ji muryanshi safe, rana da dare. 

Amma wayar Zulfa a kashe. Ya tambaya Zainab ta ce mishi bata zo gidan ba. Yana fita dabara ta faɗo mishi, Dawud ya kira ya ce mishi ya turo mishi Zulfa gida. 

Sauri yake ba zai samu biyowa ba. Sannan ya ja motar ya nufi gida. Yana parking ɗin motarshi ya ci karo da Jarood da fara’a ya ƙaraso ya gaishe da labeeb din. 

“Jarood sai ina haka?”

“Ina ta sauri ne fa, zanje makaranta.”

“Shi ne ba zaka ɗauki mota ba? Tunda sauri kake.”

Da murmushi Jarood yayi. 

“Da friend ɗina zamu wuce ne shi yasa.”

Kai Labeeb ya ɗan jinjina mishi, yana tuna ya tura mishi kuɗi, ko ya sa Mamdud anjima. Sallama Jarood yai mishi ya wuce. 

Tun kafin su dawo gidan nan akwai shaƙuwa mai karfi tsakanin dukkan su. Family din Mummy ne baima san kwatar su ba ballantana. Yanzun kam yakan ji daɗi, ko ba komai ba zai yi watanni bai leƙa su ba. ‘Yar tafiya kawai zai yi ya shiga su gaisa. Ɓangarensu ya nufa. Da sallama ya shiga, sosai suka ji daɗin ganinshi. 

“Mun yi kewarka sosai Yaya.”

Arif ya faɗi da murmushi a fuskarshi. 

“Kai kaɗai dai, su ukun nan sun gaji da ni ai.”

Labeeb ya faɗi yana nuna su Asad da hannunshi. Dariya suka yi su dukkansu. 

“Yaya sai shining kake yi”

Zainab ta faɗi, riƙe baki Labeeb yayi tare da ware idanuwa, kafin ya juya ya ɗauki pillow ɗin kujera, da gudu Zainab ta dire ta bayan kujerar da take zaune tai ɗakinta tana dariya. 

Kallonsu Anees yayi. 

“Akwai sauran mai magana?”

Tare suka girgiza mishi kai, yana ajiye pillow ɗin Mamdud na shigowa. 

“Wai ta sake ka ka fito kenan.”

Dariya Asad yayi, Labeeb ya harari Mamdud. 

“Bansani ba. Ko sau ɗaya ka leƙo ni, kaima ka gaji da ni kamar su Asad ba.”

Murmushi Mamdud yayi. 

“Chill. In zo ku koro ni? Shi yasa nai zamana.”

Baki Labeeb ya buɗe zai yi magana sallamar Zulfa ta saka shi juyawa da sauri. Doguwar riga ce a jikinta light blue da ba zai iya cewa ɗinkata akayi ko ta kanti bace. 

Ta dai yi mata kyau sosai, ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana jin nutsuwar da yai kwana bakwai bai samu ba. Nutsuwar da ganinta kaɗai ke samar mishi. 

Fuskarta yake nazari, kwalliyar da ke jiki bai hanashi ganin rashin bacci da ramar da tayi ba, zuciyarshi yaji ta matse gefe ɗaya. 

Mamdud idanuwanshi a kansu yake. Ɗan guntun murmushi yayi, yana karantar soyayyar da ke tsakaninsu. Wani ɓangare can ƙasan zuciyarshi na jin daɗin yadda abu ɗayan nan ya ƙi daidaita a rayuwar Labeeb. Ba zai yiwu ace ya samu duk abinda yake so ba. 

Anees kam hankalinshi na kan Asad da ke kallon Zulfa, wannan karon ba tare da fargabar da yakan gani ba. Auren da Labeeb yayi ya canza wani abu tare da Asad. 

Yadda ya haɗiye wani yawu yana sauke idanuwan shi ƙasa da saurin gaske yasa Anees maida hankalinshi kan su Zulfa, hannunta ya gani cikin na Labeeb da yake janta yana nufar hanyar ɗakinta da ke gidan. 

Asad ya kalla, har lokacin idanuwan shi na sauke cikin hannayenshi kamar mai ƙoƙarin gano wani abu, jan numfashi Anees yayi, yana rasa abinda ya kamata yayi. 

Labeeb kam yana ganinsu cikin ɗakin Zulfa ya sa hannuwanshi ya tallabi fuskarta. Nata tasa ta sauke su tare da kauda kanta. 

“Ki faɗa min laifina wannan karon. Ya muka yi kan rufe wayarki?”

Ba tare da ta kalli fuskarshi ba ta amsa da faɗin, 

“Kana da mata Yaya…”

Wani abu ya ji ya taso mishi yai masa tsaye a wuya. Banda Zulfa babu wanda ya ba muhimmancin ɓata mishi rai da yawa haka. 

Kamar ta sani take amfani da shi duk sa’adda take so. 

“Sai akai me bayan wannan?”

Juyo kanta tayi ta sa idanuwanta cikin nashi, roƙonshi take da ya barta kawai. Ya bar maganar gaba ɗaya. Ya ƙyaleta tai jinyar abinda take ji a zuciyarta. 

Sai dai tana ganin yadda ranshi yake a ɓace, idanuwanshi ƙur cikin nata yana jiran amsarta. 

“Bana so tajie wani iri kana kira na.”

Duk buɗe bakin da zata yi ƙara ɓata mishi rai take, gashi kwata kwata ta birkita mishi tunani. Ya kasa fahimtar me take nufi. Muryarshi ta ƙara buɗewa saboda yadda ranshi ya ɓaci. 

“Ban ganki ba sati ɗaya, kin kashe wayarki, kina faɗa min duk abinda kike so. Me yasa kike son ɓata min rai Zulfa? Ko don ki nuna min za ki iya?”

Ɗan dafe kai ta yi da ya soma mata ciwo kamun ta sauke hannunta da faɗin, 

“Kayi haƙuri… Ba haka nake nufi ba.”

“Meye haɗin kashe wayarki da matata? Na ɗauka abinda kike so ne nayi? Saboda me zai canza wani abu?”

Idanuwanta ne suka ciko da hawaye. Kalmar matata da ya faɗa kamar ya zuba mata ruwan zafi a ƙunar da zuciyarta take yi ne. Ƙifta idanuwanta take yi da sauri sauri tana son mayar da hawayenta ciki.

Muryarta can ƙasa ta ce mishi, 

“Ka yi haƙuri don Allah. Kaina ciwo yake bana son yin hayaniya…”

Kalmar hayaniya na barin bakinta tana ganin kuskuren da ta yi na furtata. Sosai ta ga yanda hakan yai hurting ɗinshi wanda ya ƙara mata zafin da zuciyarta take yi. 

Gaba ɗaya a hargitse take, ga rashin wadataccen bacci, ko da Dawud ya faɗa mata yana kiranta tai niyyar ƙin zuwa. Zuciyarta ta kasa jurewa, gani take ko yaya zata samu sauƙi in ta ganshi. 

Sai gashi ta kasa controlling feelings ɗinta. Kishin shi na sa bata tauna maganar dake fitowa daga bakinta. 

“Yaya…”

Ta fara, hannuwanshi duka biyun ya ɗaga mata, alamar baya son ji, maida bakinta ta yi ta rufe, gab da ita ya matso, ba tare daya taɓata ba ya ɗan rage tsayinshi yana sumbatar kuncin ta. 

Kamshin shi ta ji ya canza mata, kafin ta ce wani abu ya juya ya nufi ƙofa, da sauri ta bi shi tana riƙo mishi hannu. Lumshe idanuwanshi yayi, ƙarshen ɓacin rai ta gama ɓata mishi rai. 

Ba don ita bace kafin ta ƙarasa kalmar da ta faɗa sai ya wanke mata fuskarta da mari me kyau. Ko kaɗan baya son raini, baisan me ya canza ba a kwanakin nan. 

Zulfa ta raina shi, ya ce karta sake kashe mishi waya. Bata ji ba, ya share wannan shi da kanshi take faɗa ma kanta na ciwo bata son hayaniya. 

Matsayin da taga tana da shi a wajenshi yasa hakan. 

“Kafin ranki yai mugun ɓaci ki sake min hannu!”

Ya faɗi muryarshi can ƙasan maƙoshi. Sakinshi ta yi, hawayen da take tarbewa suka zubo. Komawa ta yi ta cire mayafinta ta ajiye shi kan gado tare da jakarta kafin ta zauna. 

Komai ya jagule. Ta ƙagu watannin da suka rage a fara makaranta su cika. Ƙila karatu ya rage mata damuwar da take ji. Labeeb kam yana fita ya ja mata ƙofar ya ɗan tsaya na mintina biyu. 

Ya samu da ƙyar ya ɗora murmushi a fuskarshi sannan ya fita waje, sallama yaima su Anees. Sannan suka fita tare da Mamdud. 

“Zan taho zuwa jibi in sha Allah, sai mu dawo tare.”

Kai kawai Labeeb ya ɗaga ma Mamdud, don ba sosai yake gane me yake faɗa ba don hankalinshi ba a kanshi yake ba. Sallama Mamdud yayi mishi ya juya.

“Mamdud…”

Labeeb ya kira, juyowa Mamdud yayi. 

“Ka tura dubu talatin account ɗin Jarood please…”

Kai ya ɗaga mishi kawai ya wuce, buɗe mota Labeeb yayi ya shiga, ya jima kanshi haɗe da jikin motar yana maida numfashi bisa yadda ranshi ya gama ɓaci. 

Music ya buɗe ya cika motar, collection ɗin waƙoƙin Micheal Jackson ne. Hakan yasa shi sanin Mamdud ne last ɗin amfani da motar, shi ya saka disc ɗin. 

Bai canza ba. Don ba ya kunna kiɗan bane don ya saurara. Ya kunna ne don in yana jin wani abu cikin kannuwanshi zai rage mishi ɓacin ran da yake ji. 

Kan titin shi na zuwa Kano ya huce haushi, don Allah ne kawai ya kaishi lafiya a kalar gudun da yake yi. 

**** 

Tun zuwanshi yake ganin kiran Zulfa. Har tai ringing ɗinta ta yanke baya ɗauka. Text ɗin duk da zata turo mishi baya ko buɗewa balle zuciyarshi ta sa shi amsata. 

Matsayinta ba zai bar isarshi tai aiki akanta ba. Shi yasa zai horata ta haka. Duk da har da shi yake azabtuwa. Yana son ta gane matsayin shi tukunna. 

A daddafe yayi kwana biyun nan. Don ma aiki na cinye lokacin shi kusan gaba ɗaya har Magariba. Da sun gama yake komawa hotel ɗin da suka sauka ya kwanta. 

Duk wani party da aka gayyace shi baije ba. Baya jin zuwan shi kaɗai, ba wai tunanin Zafira bane bai faɗo masa ba. Baisan ya ɗan saba da ita ba sai da ya zo kwanciya ya ji babu ɗuminta. 

Ya kirata ne abin baizo mishi ba, banda ‘yan gidansu bai saba kiran kowa ba, duk me son yin magana da shi sai ya bi ta wajen Mamdud tukunna. 

Shima sai ta kama dole yake karɓa suyi magana. Mamdud ke masa handling komai, baisan ya zai yi babu shi ba. Lokuta da dama mantawa yake ba shi da alaƙa ta jini da Mamdud. 

Balle hasken fatarsu kan sa mutane da dama ɗaukar ‘yan uwane. Tsayi kaɗai ya fi Mamdud, sai kuma Mamdud na da dogon hanci, ga gashin kanshi kwance yake luf luf, kallo ɗaya za ka yi mishi ka gane bafullatani ne na asali ma kuwa. 

Gym da yakan ziyarta yasa jikinshi bai yi siririn nan irin na yawanci fulani ba. Da zaka gansu kamar zasu tsinke. 

Kamar yadda Mamdud ya faɗa, kwana biyu ya bi bayan Labeeb ɗin. Ƙarfe goma na daren ranar suka fita zuwa Bubble Club. Wani irin wild party ake yi. 

Ƙwayoyin da ke aljihun Labeeb ya juye cikin kofin lemon da ya karɓa, ya girgiza shi sosai ya jira suka narke kafin ya zuba ma cikin shi. 

Lumshe idanuwa yayi yana jin yadda gaba ɗaya jikinshi ke amsar saƙonnin da ƙwayoyin kaɗai ke samar mishi. Jin wata yarinya a jikinshi ne ya sa shi buɗe idanuwan shi babu shiri. 

Wata fitsararriyar shiga ce a jikinta, kafin yai magana ta haɗa bakinta da nashi, maimakon ɗumin da hakan ke samar mishi wani irin yanayi ya samu kanshi a ciki. Ɗumi ya ji jikinshi ya ɗauka kamar wanda aka kunna ma wuta take ci a hankali. Ko ina cikin kanshi ihun kalma ɗaya yake ji. Aure! Aure!! Aure!!!. Sam zuciyarshi wannan karon ta tirje. 

Rinjayar duk wani salo da yarinyar take amfani da shi take yi. Tana fada mishi linkin zunuban da zai ɗauka na zina da aure a kanshi. Wannan karon muraran take hasko mishi kabari buɗe a gabanshi. 

Ba zai taɓa iya keta haddin aure ba. Lalacewar shi bata kai ya ci mutuncin aure ba. Ƙirjinshi yake ji yayi nauyi kamar an ɗora mishi dutse. 

“Ba a bada shaida akan mutane, ni zan bada shaida akan yayana!!!”

Maganar Zainab ta dawo mishi, hankaɗe yarinyar da ke jikinshi yayi yana miƙewa m. Kwayoyin da ya sha ya ji kamar ya ɗibesu fiye da misali. 

Yasan barin wajen ne kawai mafita kafin yayi abinda zai sa shi tsanar kanshi fiye da yadda yake ji. Mutane yake turewa yana neman Mamdud. 

Can ya hango shi cakuɗe da wasu mata da maza. Yana ƙarasawa sun yi layi layi da cocaine sun naɗa abu za su shaƙa. Lokaci ɗaya ya ji abinda ya sha ya sake shi. 

Yasan gaba ɗaya rayuwar su akwai lalacewa a ciki, sai dai yana da limit, ko ƙwayoyin da yake sha yasan kalar wanda yake sha. Kuma suma yana fatan barin su don babu komai a ciki sai taɓewa. 

Cocaine, taba, da wasu kayan mayen abune da sam ko party yake a gidanshi ka shigo da su sai ka fita ko waye kai kuwa. 

Duk wanda ya gani yana shan cocaine yakan ji ƙyamatarta saboda yana ji da ɗan imanin da ya rage mishi fiye da komai. Fiye da ƙannen shi. 

Idan bai samu yaƙarashi ba, ba zai sha abinda zai rabashi da shi ba. Ganin Mamdud zai shaƙi cocaine ba ƙaramin taɓa mishi zuciya yayi ba. 

Ƙarasawa wajen yayi yasa hannu ya kaɗe cocaine ɗin da suka mai layi layi, wani irin duka daya ɗaga cikinsu ya kai ma Labeeb Mamdud ya tunkuɗe Labeeb ɗin. 

“No need for violence.”

Ya faɗi yana shiga tsakaninsu, yasan Labeeb ko bai sha cocaine ba ya fisu rikici, ya sha ganin rigimarshi bata ƙarewa da kyau. 

“Kasan dubu nawa ya zubar mana?”

Gayen ya faɗi rai a ɓace, hannu Labeeb yasa cikin aljihunshi ya zaro wallet ɗinshi, gaba ɗaya kuɗin da ke ciki ya zazzage musu ya ja hannun Mamdud suka fice daga club ɗin.

“What the actual fuck Mamdud? Cocaine? Yaushe ka fara taɓa wannan ƙazantar? Kasan illolin da zai iya maka kuwa?”

Labeeb ke tambaya yana jin kamar ya rufe Mamdud da duka. Dariya Mamdud yayi yana kallon yadda Labeeb ya haƙiƙance abin na bashi mamaki. 

Gabanshi yake ɗaga kwalbar giya, wani lokaci shi yake sawa ya miƙo mishi, gabanshi yake haɗa kalaluwan kwayoyi ya sha, gabanshi yake zaɓar mace su bar waje tare. Bai taɓa nuna ya damu ba sai yau. 

“Me yasa zai dameka? Me ya rage a rayuwata da bai lalace ba? Ba abinda kake so bane ba? Ka samu abokin lalacewa shi yasa ka janyo ni n…”

Bai ƙarasa ba Labeeb ya ɗauke shi da mari, me Mamdud yake tunani da zai yi rubbing mishi lalacewar da yayi a fuska. Har yana faɗa mishi abokin lalacewa yake nema. 

“In kana da shakku akan matsayina a wajenka zaɓinka ne Mamdud…ko da wasa kar bakinka ya sake fassara min dalilin kusanci na da kai!

Na ɗauka rayuwar nan zaɓinka ce, ban taɓa tanka maka ba, ban taɓa judging ɗinka ba. Baka nemi shawarata ba ka soma ɗaga kwalba. Baka nemi shawarata ba ka soma kwanciya da mata. 

Ban hanaka ba, amma nasan zaka lissafa magana nawa nai maka akai. Zaka iya ƙirga magana nawa ka faɗa min ka nuna min shisshigi nake maka a zaɓinka. 

Yauma na maka magana ne saboda bazan taɓa zama gefe kai wannan lalacewar ba. Ni da kai zamu kashe kanmu kafin ka zama ɗan cocaine…”

Kallon shi Mamdud yake yana riƙe da kuncinshi da har lokacin zafin marin da Labeeb yai mishi bai bar zugi ba. Ba marin bane ya ɓata mishi rai. 

Maganganun shi su suka fi mishi zafi. Har ƙasan zuciyarshi suka samu waje suka zauna daram. Har Labeeb na da zuciyar da zai nuna mishi kamar bada son ranshi ya lalace ba. 

Mota ya buɗe ya shiga ba tare da ya furta komai ba. Sauke numfashi Labeeb yayi, damuwar na haɗe mishi biyu. Bai taɓa kawo akwai ranar dazai daga ma Mamdud hannu ba. 

Wani iri duk yake jinshi. Zagayawa yayi ya shiga motar ya rufe, mukullin ya zura ciki, harzai murza ya fasa. Muryarshi can ƙasa ɗauke da yanayi mai nauyi ya ce, 

“Ka yi haƙuri Mamdud, zuciyata ba zata iya ɗauka bane. Na san hargagina bai isa ya hanaka kai abinda kake so ba. 

Ba ko yaushe nake tare da kai ba. Zaka iya shan duk abinda ka ga dama a waje babu yadda zanyi. Na tsani kaina Mamdud… Na tsani kalar rayuwar nan. 

Duk sa’adda zan ganka da mace mukan raba laifinne a tare, don girman Allah ba don ni ba karka sa na tsani kaina fiye da yadda nayi a yanzun. Stay away from cocaine don Allah.”

Jin Mamdud yayi shiru yasa Labeeb juyawa ya kalle shi, ya ma kauda kanshi gefe. 

“I am sorry fa, please don’t hate me…”

Labeeb ya faɗi yana jin kamar zuciyarshi zata fito, ya daɗe babu shakku a ranshi yana ƙaunar Mamdud kamar jininshi. Yanzun ma ya sake tabbatarwa. 

Sam baya son ɓacin ranshi, ace kuma shi da kanshi ne sila, in ba haƙura ya ga yayi ba bazai yafe ma kanshi ba. 

“Its OK.”

Mamdud ya faɗi yana jin ƙaryar kalamanshi na zama daram a zuciyarshi. Ba zai taɓa manta yau ba. Labeeb bai sake cewa komai ba har suka koma hotel ɗinsu. 

Banda sai da safe da yaima Mamdud bai ce komai ba. Yana kwanciya kiran Zafira na shigowa wayarshi. Sauke numfashi yayi ya ɗaga da faɗin, 

“Hello…”

“Hmm ka manta da ni ko? Ban ma san me yasa na kiraka ba.”

Yasan bai kyauta ba, ya kamata ko sau ɗaya ya kira, don shi mutum ne da ko ba zai ba da haƙuri ba yake karɓar laifinshi in har yayi ɗin. 

“Idan nace ban samu zama ba zan miki ƙarya, saboda haka zance miki abubuwa ne sukai min yawa kawai. 

Ya kike?”

Ɗan jim ta yi daga ɗayan ɓangaren kafin ta amsa shi da, 

“Da ban kira ba ba ka damu ka sani ba.”

Runtsa idanuwa yayi ya buɗe su. Zata ƙara mishi damuwa. 

“Me kike so in ce yanzun?”

Kashe wayar tayi. Har zai kashe tashi gaba ɗaya ya kwanta sai zuciyarshi ta hana. In zaman su zai ɗore dole ya koyi ajiye isar shi a gefe. 

Kiranta yayi harta kusa yankewa sannan ta dauka.

“Tunda ni na kira yanzun sai mu gaisa ko?”

“Hmm…”

Ta ce wadda ta fara isar Labeeb. 

“Ya kike?”

Ya sake maimaita tambayar da yai mata da farko. 

“Ina lafiya. Kaifa? Ya aikin?”

“Aiki na nan kamar ko yaushe, boring. Ya makaranta?”

“Makaranta gajiya.”

“Ko kuma kin faye raki ba.”

Yanajin dariyarta. 

“Ba wani raki, yau har 4 muna lectures fa, jikina ciwo kuma ina ta kewarka.”

Ɗan guntun murmushi Labeeb yayi, damuwar da ta yi mishi yawa yasa yau ko kaɗan bai ji rashinta a kusa da shi ba. Asalima kewar Zulfa ce ta mamaki a zuciyar shi. 

“Tunda kin gaji ki huta abinki. We talk da safe in Allah ya kai mu.”

“Alright, sleep well.”

Sumba ya manna matata cikin wayar ya sannan ya kashe da sauke numfashi mai nauyi. Text ɗin Zulfa ya soma buɗewa wanda duk ban haƙuri ne. Kashe wayar yayi da murmushi a fuskarshi har bacci ya ɗauke shi cike da mafarkinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 24Rayuwarmu 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×