Skip to content
Part 26 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Hidimar su suka ci gaba da yi da Mamdud kamar komai bai faru ba. Sai dai su duka babu wanda ya sake zuwa wajen wani partyn. 

Daga wajen aiki hotel ɗinsu suke yi, kwanan Mamdud huɗu ya juya abinshi don ya ce ma Labeeb yana da test dama. Don haka shi kaɗai ya ƙarasa kwanakin shi. 

Wanda duk yadda kewar Zulfa ke ci mishi rai baisa ko ɗaya ya ɗaga wayarta ba balle ya amsa saƙonninta da ke shigo mishi babu adadi a rana. 

Suma yakan karanta su rage mishi damuwarta. Ranar Zafira tai mishi text cewar za ta yi hidimar makaranta kuɗin hannunta ba zasu isa ba. 

Mamdud ya kira yasa ya sake tura mata wata dubu ɗarin. Sai da ya tsaya ya ɗan saka ma cikinshi wani abu tukunna ya ɗauki hanyar komawa Kaduna. 

Text yai ma Zafira ya faɗa mata yana hanya. Wannan sati biyun shi ne kwanaki sha huɗu masu tsayi da ya jera ba tare da mace ba. 

Har mamakin kalar control ɗin da ya samu yake yi. Ya ɗauka aure ba zai taɓa zamar mishi mafita ba sai yanzun ya ga banbancin hakan. 

Har kasan zuciyarshi bayajin zai iya haɗa shimfiɗa da wata macen in ba Zafira ba. Ba zai iya sake cakuɗa kanshi da wannan ƙazantar da darajar aure a kanshi ba. 

Don haka yana shiga garin Kaduna gidanshi ya wuce. Sai dai me, Zafira bata gida. Tsayawa ya ɗanyi jim na wasu mintina, har ya zaro wayarshi da nufin ya kirata ya fasa. 

Ya faɗa mata yana hanya, maybe ko itama test ɗin suke yi. Ba zai so kanshi da yawa ba, don haka ya fita daga gidan ya nufi gidansu.

A falo ya same su gaba ɗayansu, har da Mummy, ɓangaren zuciyarshi da yake cike da yarinta ya soma tsallen ganin Mummy ɗin a gida. 

“Mummy…”

Ya faɗi da murmushi, ita ma murmushin tai mishi ya ƙarasa ya samu kujera ya zauna suka gaisa, Zainab na zaune kusa da ita ta naniƙe mata. 

Asad na gefenta, Anees kam yana zaune ƙasa gefen ƙafafuwanta. Arif ne kawai baya nan. 

“Ina Arif?”

Labeeb ya tambaya. 

“Sun fita da Dady yanzun.”

Zainab ta amsa shi. Wani murmushin ya sake ƙwace ma Labeeb. 

“Dady ma ya dawo?”

Ya tambaya kamar wani yaro, kai suka ɗaga mishi. Yau sosai suka sha hira da take faɗa mishi sai ta huta sosai. Za ta yi kwana bakwai koma fi kafin ta je ko ina. 

Fuskarsu kawai zaka kalla ka ga daɗin da hakan yake musu. Rabon da Mummy tai sati cikakke a gida har sun mata. Ko tana gari tana da meetings. 

Labeeb bai bar gidan ba sai bayan Asr, Mummy ta jibga mishi akwatina har biyu na tsaraba ya kaima Zafira. Gidan su Dawud ya wuce suka gaisa, ya ɗan samu mintina talatin kafin ya miƙe, yana fita Zulfa ta bi bayanshi. 

“Yaya…”

Ta kira, da murmushi a fuskarshi ya juyo ya kalleta. 

“Zulfa lafiya dai ko?”

Langaɓar dakai tayi gefe. Idanuwanta na cika da hawaye. 

“Haba Yaya, don Allah ka yi haƙuri. Ba zai sake faruwa ba.”

Bayanshi ya jingina da motar yana kallonta. 

“Pleasee…”

Ta faɗi hawaye na zubo mata. 

“Ya wuce… Give me a hug”

Ya faɗi yana miƙa mata hannayenshi. Hugging ɗinshi tayi tana jin ƙamshin shi da ta saba da shi ba kamar na ranar da zai tafi ba. Kafin ya ɗagota yasa hannu yana goge mata hawayen fuskarta. 

“Ya isa haka. Nayi missing ɗinki sosai.”

Ya faɗi yana saka idanuwanshi cikin nata da yanayin da yasa ƙafafuwanta yin sanyi. Zame jikinta tayi daga nashi tana komawa gefe. 

“Rannan wani turare ka sa marar daɗi.”

Dariya yayi. 

“Kin tuna min ma, sai na ɗauko turarukana, na Zafira nai amfani da”

Ɗan murmushi tayi da ya tsaya iya fuskarta. Sosai suka sha hirarsu sai da ya ga yamma tayi sannan yai mata sallama. Sai daya shiga mota ya nufi gida tukunna yanayin da yake ciki ya dawo mishi. 

Kiran magariba yaji ana yi kafin ya ƙarasa gida. Dan haka ya tsaya yai sallar magrib, kafin ya ƙarasa gida, amma me Zafira bata dawo ba har lokacin. Ranshi bai ɓaci ba tunanin rashin hankalinta kawai yake yi. 

Bai kuma kirata ba, yunwa da ya ji ta soma addabarshi, yasa shi ɗaukar mukullin mota ya sake fita ya nemi abinda ya ci yayi sallar isha’i tukunna ya dawo. 

A falo ya samu Zafira a zaune. Ko inda take bai kalla ba ya wuce bedroom. Kayan jikinshi ya soma ragewa yana ji ta turo ƙofar ta shigo. 

“Fushi kake?”

Ta tambaya tana wani shagwaɓe mishi fuska. Bai ko juya ya kalleta ba balle tai zaton zai mata magana. Sai da ta ga dama ta dawo mishi gida, shima sai ya ga dama zai kulata. 

Yana gama rage kayanshi ya shiga wanka ya barta a nan, daya fito ɗaure da towel bata ce mishi komai ba itama ta shiga wankan ta fito. Zama tayi tana murza ma jikinta mai. 

Yana kwance kan gado yana kallonta. 

“Daga makaranta gida na wuce. Sisters ɗina sun zo, ɗaya tana aure a Sudan ɗaya kuma Abuja, na daɗe bangansu ba shi yasa ban dawo da wuri ba. I am sorry.”

Miƙewa Labeeb yayi ya kamo hannunta ya dawo da su kan gadon. Ba jin abinda yasa bata dawo da wuri bane matsalar shi.

*****

Da ƙyar Zafira ta iya miƙewa wajen takwas da rabi ta shiga toilet tai wanka ta fito, sai lokacin ta samu tai sallah don ba tashin da Labeeb bai mata ba. 

Da ya isheta ma kuka ta saka mishi, dole ya ƙyaleta, kallonshi tayi, bacci yake hankalinshi kwance. Wani abu ya tsaya mata a wuya.

Gefen gadon ta zauna. Duk jiya ya hana mata bacci zai kwanta shi yayi nashi yanzun, hannu tasa kan kafaɗarshi ta ɗan girgiza shi kaɗan. 

Ya buɗe idanuwanshi ya sauke kan fuskarta, gani yai ta mishi wani fresh. 

“Yunwa nake ji fa.”

Ta faɗi tana shagwaɓe fuska. Baisan me take so yai mata ba. 

“Yanzun me zan miki?”

Sake taɓare fuska tayi tana girgiza shi. 

“Makaranta fa zan tafi, kaje ja nemo min abinda zan ci kafin in shirya…”

Maida idanuwanshi yayi ya lumshe, bai taɓa kawoma ranshi Zafira zata shiga kitchen ba. Yasan Mummy kalarta ta auro mishi. Sai dai in ba zata je ta girka ba sai dai ta fita ta nemo abinda zata ci. 

Girgiza shi ta ci gaba da yi. 

“Ki shirya inkin fita ki tsaya ki ci wani abu a hanya. Ki barni ni kam.”

Ya ƙarasa yana juya mata baya ya ja duvet ya rufe jikinshi. Kama duvet ɗin tayi tana kwarewa. Sake runtsa idanuwa Labeeb yayi. Zata saka mishi ciwon kai. 

Duvet ɗin ya laluba ba tare da ya buɗe idanuwanshi ba.

“Ki ƙyaleni na ce ko? Bana son yawan maimaita magana…”

Labeeb ya faɗi cike da kashedi. Sam bata jishi ba, hannu ɗaya yasa ya fisgota gaba ɗaya kafin ya soma birkita mata tunaninta gaba ɗaya. 

“I am sorry… Wallahi ina da lecture ƙarfe goma.”

Zafira ke faɗi. 

“Ki tari na ƙarfe ɗaya…”

Labeeb ya faɗi ba tare da ya saurareta ba. 

*

Aikam ba ita ta fita ba sai sha biyun rana. Lectures biyu take da shi a ranar, ɗayan ma ba sosai take attending ba dama. Don haka ta tsaya bank ta cira kuɗi ta wuce gida abinta. Fita suka yi da sisters ɗinta gyaran jiki da shopping. 

Labeeb yana gama baccin shi gida ya nufa, can ya ci abincin rana, ya samu Zulfa na gidan don haka zaman ya sake mishi daɗi, ga Mummy kamar yadda ta faɗa babu inda ta je. 

Bai yi niyyar tafiya ba, Mummy ta kore shi wajen shida. Su Asad na tsokanarshi wai shi yanzun ba ɗan gidan bane, baƙunta kawai yake zuwar musu. 

Yauma har ya koma Zafira bata nan, bata shigo gidan ba sai tara. Bata faɗa mishi dalili ba shi ma bai tambaya ba, duk da yana ganin rashin kyautawar abinda ta yi ɗin. 

Sai dai waye shi da zai mata magana, Mummy ma sai tai kwanaki bata nan, duk da ba haka yaso tashi rayuwar auren ta kasance ba. Har yara yaso ya tara. Sai dai babu wannan tsarin a zuciyarshi yanzun. 

Yana ganin wautar da zata saka shi haɗa yara da Zafira, haka zata watsar mishi da su kamar yadda Mummy tai musu, yaran duk da ba zai kula da su ba baiga amfanin haihuwar su ba. 

Daren suka raya kamar jiya, shi ne kawai abinda Labeeb ya damu da shi a tare da auren su. 

BAYAN WATA UKU

Idan Labeeb ya ce yasan wani abu waishi daɗin aure ƙarya yake. Nutsuwar da yake samu da Zafira yanzun ya daina, don wani lokacin sai dai in matsi ya mishi yawa ya nuna mata ƙarfi. 

Gaba ɗaya a takure yake jinshi, gashi babu damar ya wuce sati biyu wajen aiki da bai ga abinda zai dawo da shi ba. Bazai iya neman wasu matan ba. 

Ko sun ƙetare ƙasa ne da wahala su shige sati uku, ko kowa ya wuce shi yanzun dole ke sashi dawowa. Tunda suke bata taɓa tambayarshi zata fita ba. 

Kawai in ta fita da sunan makaranta sai lokacin da ta ga dama zata dawo mishi, inya nemi haƙƙinshi zata fara mita jikinta ciwo yake ta gaji. 

Ga kuɗi da yake mamakin me take yi da su, tura mata yake amma bata kwana uku bata tambaye shi ba. Yau ya dawo kasancewar ranar Asabar ce. 

Bai ma nufi gidan ba sai wajen tara da rabi. Yana gidanshi inda Mamdud ya haɗa party ɗin da Labeeb ya saba yi. Shi ya bar ma komai ya nufi gida. 

Sai dai me motar Zafira na cikin gidan amman ita bata ciki, wayarta ya nema a kashe, ƙarar mota ya ji yana zaune a falo da ya sa shi miƙewa ya nufi window ɗin ɗakin ya leƙa. 

Zafira ce jikinta sanye da wata doguwar riga da duk wani curve da ke jikinta saida ya bayyana sai wani ɗan mayafi da ta yafe kanta da shi. 

Bata taɓa fita da kaya haka a gabanshi ba. Duk kayan da zata fita da su na mutunci ne. Ranshi bai taɓa baci da halayyarta ba sai yau. 

Darajar aure na da girma, bazai yiwu da aurenta a kanshi tana abinda take so ba, in har Allah ya tashi kamata da laifi har da shi a ciki. 

Sai yanzun hakan ya faɗo mishi, don baya sonta bai kamata a ce baya kishin aurenshi ba. Yana komai don ganin ta ɓangarenshi bai ci mutuncin aure ba. 

Sai dai baya kula da yanayin auren ta ɓangarenta. Lumshe idanuwa yayi ya buɗe su, dai dai fitowar wani guy da ko bai kaishi sekaru ba kaɗan ne zai hana.

Hugging ɗinshi ya ga Zafira tayi tare da sumbatar kuncin shi duka biyun sannan ya faɗi wani abu da suka yi dariya gaba ɗaya. 

Window ɗin ya riƙe, don in ya fita ba zasu kwasheta da kyau ba. Ba laifin guy ɗin bane. Na Zafira ne, faɗanshi da ita ne, da ƙyar ya iya jurewa har ta shigo. 

“Daga ina kike? Waye wancan?”

Ya buƙata tana shigowa, sai da ta tura ƙofar ta nufi kujera zata zauna, da zafin na Labeeb ya ƙarasa ya riƙo hannunta. 

“Ba zama za ki yi ba amsani za ki yi. Bana son sake maimaita tambaya ta.”

Hannunta ta fisge. 

“Cousin ɗina ne.”

Cousin ɗinta, yake maimaitawa cikin kanshi yana jin kowanne second zai iya loosing control. Kai kawo yake cikin ɗakin. 

“Sai uban wa ya halatta miki rungumarshi? Bakisan da igiyoyin aure a kanki ba ne? Look at you! Kin ga shigar da ke jikinki ma kuwa?”

Cikin fuska Zafira ta kalle shi, bata saba ai mata faɗa ba. Rayuwarsu babu kwaɓa babu tsangwama ko kaɗan. 

“Saboda me zaka dinga min faɗa? Karka ce za ka zageni, menene don na mishi good night hug? Me kayan jikina suka yi?”

Numfashi Labeeb yake ja yana fitarwa a hankali. 

“Bar wajen nan Zafira. Ki bar wajen nan kafin mu duka mu yi da na sani…”

Duk da a nutse yai maganar yanayin idanuwanshi sun nuna mata ba da wasa yake ba. Da sauri ta nufi bedroom ɗinsu ta rufe. Ɗaya daga cikin bedrooms ɗin gidan Labeeb ya nufa. 

Sai da yai wanka tukunna ya kwanta, ya jima bai runtsa ba saboda ɓacin rai. Da ƙyar ya samu yai bacci. 

*****

Yana dawowa Asuba ji yayi ba zai iya komawa bacci ba, don haka ya kwanta falo yana kallon Harry Potter a MBC2. Baisan lokacin daya ɗauka ba, don suna cire part 2 suka mayar da 3.

Zafira ce ta fito sanye da doguwar riga loose a jikinta. 

“Ina zaki?”

Ya buƙata a taƙaice. 

“Tutorial.”

Ta amsa mishi a sanyaye. 

“Ba zaki je ba. In ƙawayenki ne invite them ku yi a gida. Ko kiyi ke kaɗai.”

Ware idanuwa Zafira tayi. 

“You can’t do that?”

Ta faɗi kamar za ta yi kuka, bai kulata ba kallonshi ya ci gaba da yi, ta jima tsaye kafin ta zagayo ta zauna a gefenshi. 

“Saboda me zaka hanani zuwa?”

Ta buƙata. Gyara zama yayi ya fuskance ta. 

“Saboda na isa. Kin ga daga yau shi ne rana ta ƙarshe da zaki fita da sunan makaranta ki biya wani waje. 

Daga school ko ina nan, ko bana nan ina son jin kina gida. In za ki je wani waje ki faɗa min tukunna. Zan samo driver da zai dinga kaiki. 

Kayan jiya inya wuce cikin gida ko ƙofar can karki wuce da shi. And about your cousin, seven inches kusa dake kar in sake ganinshi balle har jikinki yaje wajen shi.”

Tunda ya fara magana Zafira ta buɗe baki take kallonshi, miƙewa tayi da gudu ta koma ɗaki. Saida ya gama kallonshi tukunna ya tashi ya fita ya siyo musu abinda zasu karya da shi. 

Tura ɗakin yayi ya ajiye mata ya juya abinshi. Zafira kam tana jin shigowar shi, maman ta takira ta faɗa mata abinda Labeeb ɗin ya ce. 

“What? Shi ɗin banza, aure zaman kurkuku ne da zai kafa miki sharuɗɗa haka. Waye El-Maska ɗin? Me ya tara? Ki tafi makaranta abinki. Kin ji ni, sai ka ce ba jinina ba za ki zauna kina ma namiji kuka.”

Goge fuskarta Zafira ta yi, suka ƙarasa magana da Mummy da babu daya ta arziƙi a cikinta. Toilet Zafira ta shiga ta wanke fuskarta ta dawo ta sake kwalliya. 

Bata ɗauki ledar rich bites da Labeeb ya ajiye mata ba. Fitowa ta yi ta nufi ƙofa duk da 8gabanta na faɗuwa ta fice. Labeeb bai san bata gidan ba sai da ya tashi fita. 

Komawa ɗaki yayi ya kwanta. Yana jiran ta dawo, ranshi ya gama ɓaci, ya gaji gaba ɗaya. Auren ya ishe shi, ta gama kaishi bango. 

Bata shigo gidan ba sai bayan Magariba, a tsaye ta same shi, fisgota yayi ya jata duk ihun da take bai sake ta ba sai tsakiyar falo. 

“Ka ƙyaleni wallahi! Kai ka isa ka hanani fita, da uwarka za…”

Bata rufe baki ba ya ɗauketa da mari, tana ɗagowa ya sake ɗora mata wani da har sai da ta kusa faɗuwa. Ihu take tana zaginshi tana kai mishi duka. 

Hannuwanta duka biyun ya kama ya riƙe cikin nashi guda ɗaya. Kaf duniya banda Mummy ba ai macen da zata zage shi ba. Ko Mummy da kanta bata taɓa zaginshi ba. 

Zainab, Zulfa, basu isa ya sa doka su tsallake bai hukunta su ba balle ita da igiyoyi uku suka ƙulle su. Belt ɗin jikinshi ya kwnce ya ci gaba da zaneta da shi. 

Tun tana iya zaginshi har ta daina, sai da ya ga ta yi laushi tukunna ya ajiyeta, ɗakin shi ya nufa ya ɗauko mukullin motarshi. Ya dawo ya kama hannun Zafira, ganin ta ƙi tashi, banda kuka babu abinda take yi yasa shi sungumarta ya ɗora a kafaɗarshi. 

Dukan bayanshi take amma a banza. Ta gama ƙure haƙurinshi. Bayan motar ya buɗe ya sakata. Ya rufe, ya shiga ya ja motar. Bai zame ko ina ba sai gidansu da address ɗinshi tunda Mummy ta tura mishi sai yau yayi amfani. 

Buɗe mishi gate akayi. Ya shiga yai parking, sannan ya zo ya buɗe bayan motar ya fisgo Zafira ya rufe. Hannunta yake ja har cikin gidansu. 

Tana ganin sun shiga ta soma ihu kamar wacce ake yankawa, da gudu mama ta sauko daga kan bene, Zafira ta ruga ta faɗa jikinta tana wani irin kuka. 

“Lafiya? Zafira me ya same ki haka? Me ya sameta?”

Take tambayar Labeeb. Da ƙyar Zafira na kuka kamar zata shiɗe ta ce, 

“Mama dukana yayi…”

Da wani irin mamaki mama ta buɗe baki tana kallon Labeeb. 

“How dare you? Ka dakar min yarinya and have the guts ka shigo min gida? Kai ɗin banza! Wallahi sai ka saketa!”

“Ba sai kin rantse ba, na saketa saki ɗaya. Za ku iya zuwa kowanne lokaci ku kwashe kayan ku.”

Labeeb ya faɗi yana jin kamar zai kama da wuta saboda ɓacin rai.

“Sai ka yi da na sanin taɓa min yarinya wallahi!”

Juyawa Labeeb yayi ya fice daga cikin gidan, ba laifin Zafira bane, daga kalar tarbiyar da ta samu ne. Motarshi ya shiga kanshi tsaye gida ya nufa. 

Yana shiga gidansu kiran Mummy na shigowa wayarshi. Ya kuma san dalili, bai ɗaga ba ya ƙarasa cikin gidan. Part ɗin Mummy ya nufa ya ci karo da ita a falonta. 

“Me kayi haka Labeeb?”

Mummy ta tambaya. 

“Kiyi haƙuri Mummy, zagina tayi.”

“What? Zagi? Akan me?”

Zama labeeb yayi ya faɗa ma Mummy duk abinda ya faru. Yana ɗorawa da, 

“Kiyi haƙuri, na yi komai to make it work…”

Girgiza mishi kai tayi. 

“Don’t bother. Ya wuce kawai, sun kira sunata hayaniya yasa na ɗauka wani babban abu ne ya faru. 

Da baka taɓata ba dai, but ya riga ya faru. Kaje ka huta abinka.”

Sauke numfashi Labeeb yayi, yana miƙewa, ji yake kamar an sauke mishi wani ƙaton nauyi. Dama gudun shi ya ɓata ma Mummy rai kuma ya ga bata damu ba shima baiga dalilin da zai sa ya damu ba. 

Sosai su Asad suke mamakin ganin shi a gida kuma ya ce nan zai kwana, ƙyale su yai tukunna bai faɗa musu abinda yake faruwa ba. 

Ba kuma su fahimci komai ba suka gama shiriritar su ya tashi ya nufi ɗakinshi. Kwanciya yai yana mirgina kan gadon yana jin ƙamshin ɗakin da komai da yai kewa ba kaɗan ba. 

Wayarshi ya ɗauka ya kira Zulfa. Hira suka sha ya faɗa mata duk abinda ya faru, ga mamakin shi bata taya shi murna ba don gani yake abin murna ne. 

“Ko kaɗan baka kyauta ba. Ka zane ‘yar mutane idonka babu kunya Yaya ka kai musu ita gida ka sake ta a gaban mamanta. 

Wannan ba halin Yayana bane, yana kula da auna abinda zai yi kafin yayi shi.”

Jikinshi ya ji yayi sanyi da kalamanta. 

“Akwai kyautawa a abinda tai min?”

Ya buƙata. 

“Babu, ku dukanku baku kyauta ba. Amma ka fita laifi, tun farko ya kamata ka koya mata yadda zaku tsara zamanku…”

Katse zulfa yai da cewar, 

“Wai yaushe kikai hankali haka?”

Dariya ya bata, Shima dariyarta ta saka shi dariya. 

“Yaya serious magana fa ake…”

“Shhhhh. Bana son ji, ba dawo da ita zan yi ba. It was a mistake da ba zai sake faruwa ba. Murna zaki taya ni…”

Dariyar ta sake yi. 

“In zo mu taho?”

“Nope, da safe zan zo. Za mu yi abu da Sajda.”

Bai so ba. Haka dai suka sha hirarsu sannan suka yi sallama. Ranar bacci yayi daya jima bai yi kalarshi ba don jinshi yake free.

**** 

Saida safe yake faɗa ma su Asad abinda ya faru. Kamar su dukansu jira suke kowa ya ji daɗin mutuwar auren don sun san dama Labeeb ɗin ba sonta yake ba. 

Mummy ce data liƙa mishi. Yanzun sai abarshi ya zaɓi wadda zai yi farin ciki da ita. Kamar yadda Zulfa ta ce da safen ta zo a nan ma ta karya. 

“Shikenan yanzun ka zama bazawari?”

Cewar Asad, pillow Labeeb ya jefa mishi, Mamdud da ke shan tea sai da ya ƙware saboda dariya. 

“You guys. Wai ba za ku barni in sha iska bane?”

Zainab na dariya ta ce, 

“No, we are having fun, wallahi da gaske ne fa, in za kai next aure sai ka ce mata bazawari ne ni…”

Ta ƙarasa suna dariya, ita ma pillow ɗin kujera ya ɗauka ya jefa mata ta tare da hannu tana dariya. 

“Baba ka zama Tuwaris.”

Cewar Mamdud, ƙafa Labeeb ya sa ya kai mishi harbi. 

“Allah ku ƙyale min Yaya, kun dame shi, ku ko ‘yan mata baku yi ba, shi kam har da aure, you all are jealous”

Zulfa ta faɗi suna yin high-five ita da Labeeb. 

“Ewwww”

Zainab ta faɗi. Asad ya bude baki zai yi magana suka ga ‘Yansanda kamar daga sama har su takwas sun danno kai cikin gidan. Babu wani tambaya ko bayani biyu daga cikinsu suka yi kan Labeeb suka cakume shi. 

“Lafiya? Meye haka?”

Shi ne tambayar da dukkansu suke yi, da gudu Zainab tai ɓangaren mummy, mamaki ya hana Labeeb yin komai, yana ji suka saka mishi ankwa sai ka ce ya saci kayan wani suka jashi waje. 

Mamdud ne ya bisu yana faɗin, 

“Ya za ku tafi da shi ba bayanin komai? Me yai muku?”

“Za ka iya biyomu in kana son sani.”

Ɗaya daga cikin ‘Yansandan ya faɗi. Da gudu Mamdud ya koma ya nufi ɗaki ya ɗauko mukullin mota, dai dai fitowar Mummy tana waya. 

Ita da Mamdud suka fita suka bi bayan motar ‘Yansandan. Har Police station ɗin, suna ƙarasawa basu yi mintina goma ba sai ga Dady ma ya zo. 

Nan aka soma karanta musu sharrikan da su Zafira suka liƙa ma Labeeb ɗin. Sosai Mummy take faɗa. 

“Shi ne za ku shigo har cikin gida ku kama shi sai ka ce wanda yai kisan kai?”

Hannun Mummy dady ya ja ya mayar da ita mota ya zaunar don yasan in tana wajen ba za ayi maganar a nutse ba. 

“Ku gama, zanyi ƙararsu na cin zarafin yarona.”

Murmushi kawai Dady yayi ya koma suka soma maganar nutsuwa. Ba ƙananan kuɗi suka karɓa ba kafin su bayar da belin Labeeb ɗin.

Mummy na ta faɗa haka suka koma gida Dady na tausarta da faɗin tunda an karɓo shi abin duk zai zo da sauƙi. Da yammacin ranar gidansu Zafira suka aiko musu da sammacin kotu. 

“Aikin banza. Mu da muke da lawyers a hannu”

Cewar mumy tana ɗorawa da, 

“Sai kuma tabani kuɗaɗe na gaba ɗaya tunda bata da gadona wallahi.”

“Babu fa abinda za su yi, wulaƙanta Labeeb suke so suyi. Allah kuma ba zai barsu ba. 

Yanzun da yaron nan ba wani bane, bamai damuwa, amma har gari ya karaɗe da maganar an kama shi.”

Dady yake faɗi yana jin tausayin Labeeb ɗin. Sosai suke tattauna matsalar da shawarwari akai. 

****** 

Sati biyu suka ɗauka da ya zo musu a birkice kafin a gama shari’ar. Amma sam maganar bata mutu ba a wajen mutanen gari, kowa da abinda yake faɗa. 

Masu ƙarin gishiri da maggi wa labarin suna yi. Dole Labeeb ya ɗauki hutu na wata biyu. Don Mummy ma so tai ya bar ƙasar sai abin ya lafa shi ya ƙi. 

Daɗin shi ɗaya da Mummy ta furta da bakinta. Next time shi da kanshi zai zaɓo matarshi. Ko ba komai tare da auren Zafira ya zo mishi da wani alkhairin na daban.

**** 

Daƙyar ya samu ya ɓanɓare ta daga jikinshi yana maida numfashi. Ƙoƙarin sake janyo shi take ya hankaɗe ta. 

“Stay the fuck away!”

Ya faɗi yana matsawa sosai kamar tsoron yarinyar yake, hannu yasa ya dafe kanshi yana runtsa idanuwa. Ya rasa me ke damunshi haka. 

Tun bayan Zafira sam ya kasa haɗa shimfiɗa da wata, kamar auren da yayi ya canza wani abu tare da shi da ya kasa ganewa. Da duk wani salo da yarinyar zata yi mishi duk ƙwarewarta sai ya ji kamar dauɗa take liƙa mishi a jiki. 

Kamar hannuwanta na bar mishi alama a zuciyarshi da jikinshi. Dauɗar,zunubi da ƙazantar zina yake ji yanzun. Ya ji yadda zuciyarshi tai mishi haske da kalar nutsuwar da ya samu tare da Zafira.

Baya son zuciyarshi ta sake ziyartar duhun dake cikin zina. Sakko da ƙafafuwanshi yayi daga kan gadon. Ya ɗauki dogon wandonshi da ke ƙasa, kuɗi ya ɗauko ba tare da ya juya ya sake kallon yarinyar ba ya miƙa mata. 

“Tashi ki fita.”

Ya faɗi, hannu ta sa ta karɓi kuɗin, ta miƙe ta mayar da kayanta tana mamakin kalar El-Maska. Bata damu ba tunda ta ji dumus. Ficewa tayi daga ɗakin.

Yana jin dokawar ƙofarta ya sauke numfashi yana miƙewa ƙasa-ƙ)asa yake fadin. 

“Wani abu ya sake canzawa tare da ni.”

Ya jima yana zaune yana nazarin rayuwa kafin ya tashi ya shiga toilet ya tsarkake jikinshi ya ɗaura alwalar Asr ya fito. 

Yasan kafin ya kai masallaci an idar da sallah don haka yai sallar shi a gida. Wayar zulfa ya nema ta ƙi shiga. Sake fita yai daga bedroom ɗin zuwa falo ya kunna kayan kallo. 

Sai dai tunda ya zauna yake flipping tsakanin tasha zuwa wata tashar ya kasa samun abin kallo, Komai baya mishi daɗi tunda ya tashi, hakan yasa shi fita ya samo yarinya.

Sai dai bata ƙara mishi komai ba sai rashin jin daɗin da yake ciki. Kitchen ya nufa ya ɗauki kofi ya buɗe fridge ya ɗauko kwalbar giyarshi ya buɗe ya zuba.

Ya mayar ya ɗauko ƙanƙara ya fasa ya zuba ya ɗauki kofin yana girgiza shi don ƙanƙarar ta narke ya nufi hanyar falo, bai zauna ba wayarshi ta soma ringing. 

Ɗaukarta yayi kan table, ya ɗan runtsa idanuwa ya buɗesu ganin Asad ne, ɗagawa yayi da faɗin, 

“Hello Asad…”

Tare da cika bakinshi da giyar dake cikin kofin da kafin ya haɗiye Asad ya ce mishi,

“Yaya Sajdaa…Sajda ta rasu!”

Giyar da ke bakinshi ya furzar wadda ta fara wucewa ta shaƙe shi, tari ya soma yi sosai da ya saka shi sake kurɓ yana haɗiyewa da sauri sauri wani tarin na sake bin wani. 

Ajiye kofin yayi kan table, yana tarin ya ce ma Asad, 

“Ka ce…me? Sajda…menene?”

“Sajda ta rasu Yaya!”

Asad ya sake faɗi muryarshi na rawa. Girgiza kai Labeeb yake, lokaci ɗaya wani abu na zauna mishi a ƙirji, babu yadda za a yi ace mishi Sajda ta rasu.

Sauke wayar yayi daga kunnenshi wata irin zufa na karyo mishi, ko ina na jikinshi ɓari yake, ya rasa abinda zaiyi, gaba ɗaya komai ya kwance mishi. 

Ba ƙaramin kaɗawa mutuwar tai mishi ba, a lokaci ɗaya kuma da mamaki da tsoro, hannu yasa ya goge bakinshi yana tuna abinda ya aikata da shi mintina ko talatin basu yi ba. 

Tsikar jikinshi ce ta tashi, da ace shi ne ya rasu yanzun da wanne guzuri zai tafi? Me zai ce ma Allah, ta ina zai fara bayani. Zuciyarshi ke dokawa da sauri sauri. 

Yadda ruɗin duniya da gangar Shaiɗan ke kaɗa mishi tana mantar da shi cewar mutuwa bata nuna alama, bata bada notice, bata sallama balle ta jira sai ka shirya. 

Kome kake aikatawa in tazo cikin yanayin zata ɗauke ka, da wani irin sanyin jiki ya nufi bedroom ɗin ɗakin ya tura, gadon dake ciki yake kallo, da ɗakin gaba ɗaya. 

Da tunanin saiya sake sallar Asr a ranshi ya ƙarasa ya ɗauki mukullan, bama koda yaushe yake sallah a gidan ba saboda yadda dauɗar dake ciki tai yawa. 

Yakan ji tsananin kunyar ajiye goshin shi domin yima Ubangiji Sujuda cikin gidan da babu abinda ba ayi da mata. Da ƙyar ya iya kulle gidan ya fita da mota sannan ya kulle gate ɗin saboda babu maigadi.

A hankali yake jan motar zuwa gidan su Dawud kamar baya son ya ƙarasa, kamar in bai ƙarasa da wuri ba Asad zai kira ya ce mishi Sajda bata rasu ba. 

Amma ina, babu wasa a maganar mutuwa, babu ƙarya a cikinta, ko ba ayi a gabanka ba, ka je ka samu anyi, ankai mamaci tare da kai. Ko da bata zo cikin gidanku ba ka ga ta je kusa da shi. 

Sa’adda yai parking ɗin motarshi a ƙofar gidansu Dawud mutane yake gani da kuma hayaƙi da ke fitowa ta saman roof din gidan da hayaniyar mutane. 

Da ƙyar ya iya fitowa ya rufe murfin motar, tun bai shiga ba zuciyarshi kamar zata fito daga ƙirjinshi saboda dokawar da take. 

Tsabar tashin hankali a ƙofar gida ya cire takalmanshi ya shiga cikin gidan. Kallo ɗaya zakai ma Dawud da ke rungume da sajda ka fahimci tashin hankalin da yake ciki. 

Dubanshi ya mayar kan su Tayyab da ake shafama ruwa amma ko motsi basu yi ba daga shi har Zulfa. Kafin ya mayar da hankalinshi kan Dawud, yana zaune riƙe da Sajda a jikinshi. 

Khateeb na kwance kan bayanshi, Khateeb ɗin Labeeb ya fara ɗaukewa tukunna ya dawo. Da ƙyar ya samu Dawud ya ba su Mami sajda don ai mata wanka. 

BAYAN WATA ƊAYA 

Mutuwar Sajda ba su Dawud kaɗai ta canza ba. Har su, kallon kowa yake cikin falon, Zulfa kwance cikin kujera mai zaman mutum ɗaya ta dunƙule jikinta. 

Asad shi kaɗai zaune a ƙasa da remote a hannunshi. Fuskarshi kawai zaka kalla ka ga ramar da yayi, ya kuma san saboda Anees ne, don yana jin mutuwar Sajda fiye da su. 

Zaman falon ma sai dole yake yinshi. Mamdud kanshi ya nutsu. Ɗakin Zainab Labeeb ya juya ya nufa don za su tafi Abuja ranar yana son yi musu sallama. 

Sai da ya ƙwanƙwasa ta ce ya shiga tukunna ya tura, zaune ya sameta a ƙasa da wayarta a hannu tana danne-danne, kusa da ita ya zauna. 

“Zan wuce ne yanzun.”

Idanuwanta ta ɗago ta sauke kan fuskar shi. 

“Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”

“Amin, Asad zai muku komai na school ke da Zulfa. Inda yake da buƙatar sai kun je zai kai ku.”

Kai ta ɗan ɗaga mishi. Gaba ɗaya baya jin daɗin ganin su cikin yanayin nan. Babu yada zaiyi ne, bai san yazai musu ba. Jikinshi babu ƙarfi ya miƙe, har ya kai ƙofa ta ce, 

“Don Allah be safe… I love you.”

Muryarta da rauni a ciki, dawowa yayi ya tsugunna yana kallon fuskarta. 

“Look at me Zee Zee…”

Kallonshi tayi idanuwanta cike taf da hawaye. 

“Kawai ina jin tsoro ne, mutuwa na zuwa babu sallama Yaya…”

Zainab ta ƙarasa hawaye na zubo mata, hannu Labeeb ya sa ya goge mata su, shima tsoron yake ji, don tun rasuwar Sajda party ko ɗaya bai je ba. 

Haka zalika kayan maye babu abinda ya sake dira cikinshi. Tsoro sosai yake ji na duniyar gaba ɗayanta. 

“In sha Allah komai zai zama lafiya ƙalau. Bana son damuwar nan.”

Kai ta ɗan ɗaga mishi, hannu ya sa ya tallabi fuskarta kaɗan kafin ya miƙe da faɗin, 

“Love you more. Ki kula da kanki, da kowa.”

Sai da ta ɗaga mishi kai tukunna ya fice daga ɗakin, na Arif ya nufa, ya ƙwanƙwasa shiru, turawa yayi a hankali, ganin arif ɗin kwance yana bacci yasa shi ƙarasawa ya tsugunna ya sumbace shi a goshi tukunna ya fice. 

Sauke numfashi yayi yana nufar ɗakin su Asad, da sallama ya tura. Anees na zaune kan gadon su ya miƙe ƙafafuwan shi, bayanshi jingine da headboard ɗin gadon. 

Bai ko juyo ba, can ƙasa-ƙasa ya amsa sallamar Labeeb, ƙarasawa Labeeb yayi ya zauna gefen gadon. Cikin sanyin murya ya soma magana. 

“Rayuwa ba zata yiwu a haka ba Anees. You need to move on…Sajda addu’arka take buƙata fiye da wannan damuwar…in ka kulle kanka a ɗaki, ka daina hira, ka daina walwala ba zai dawo da ita ba…”

Juyowa Anees yayi yana kallon Labeeb. 

“Ya zan yi? Ko sau ɗaya da na faɗa mata in sonta yaya… Ko sau ɗaya…”

Anees ya ƙarasa muryarshi na karyewa. Ɗacin mutuwar Sajda na dawo mishi sabo, ji yake kamar ace duk lokacin da ya samu yayi spending tare da ita. 

Da ya san zata rasu da kullum sai ya je ya ganta ya faɗa mata yadda ya gama tsara komai na rayuwar shi da ita a ciki. Yadda ya hango musu rayuwa mai nisa shi da ita. 

Sai dai haka kowa yake ɓata lokacin shi wajen hango lokuta, wajen ganin kamar kana da dukkan lokacin da kake buƙata, sai dai baka sani ba, Allah ya gama tsara komai. 

Ƙaddarar ka ta daɗe da rubutawa ba kuma yadda zakai ka canza hakan. Abu daya za ka yi, kai amfani da lokacin da ka gani kawai, shi kaɗai kake da tabbaci akai. 

“Bansan me zance maka ba…wallahi ni kam ban sani ba Anees kawai bana son ganinka haka, gaba ɗayanku bana son damuwar ku.”

Labeeb ya faɗi kamar zai sa kuka, damuwar su ta fi komai ci mishi rai, inda zai iya zai karɓe dukkan damuwar don su suyi farin ciki. 

Ɗan murmushin ƙarfin hali Anees yai mishi. 

“Ka taya ni addu’a kawai, Allah zai yaye min. Ya fi mu son Sajda shi yasa Ya karɓeta. Allah zai bani juriyan rashinta… Beside mu duka lokacin mu muke jira.”

Kai Labeeb ya ɗan ɗaga mishi jikinshi na ƙara sanyi, sallama suka yi ya fice daga ɗakin zuwa falo, kan hannun kujerarar da Zulfa take labeeb ya zauna. 

Ɗago ido tayi ta sauke cikin nashi. 

“Me kika ci duk yau?”

Ya buƙata yana kallon idanuwanta da fuskarta da ta ƙara haske saboda ramewar da tayi. 

“Irish da tea ni da Zee Zee.”

“Kun kyauta…tafiya zanyi, za muyi sati uku ko fiye da haka, bana son in kira ace min ba kya cin abinci.”

Ɗan murmushi ta yi duk da bai kai zuciyarta ba, ji take kamar ta bishi, don ganin shi na ɗan sa ta ji sauƙi sauƙi. Sam bata jin daɗin zama cikin gidansu. 

Balle ma ta ga Hajiya Beeba. Ji take kamar ta saka ihu, komai ya canza, Tayyab sai ya wuni bai ce komai ba. Balle Dawud da sai dai yaita binsu da ido, Mami kanta ko ya kayan Sajda za su gifta sai tai kuka. 

“Allah ya dawo da kai lafiya…”

“Amin. Don Allah ki kula da kanki.”

Labeeb ya faɗi yana jin kama ya fasa tafiya. Don gani yake kamar in yana kusa ɗin yana ganin yadda take kullum hankalinshi zai fi kwanciya. 

“Asad zan wuce.”

Ɗan ɗago kai yayi. 

“Allah ya tsare.”

Kawai ya faɗi ya maida hankalinshi kan remote ɗin da ke hannunshi. Sauke numfashi Labeeb yayi. 

“Mamdud da gaske ba za ka je ba?”

Gyara kwanciya yai cikin kujera abinshi. 

“Sake tambaya kake don ka ji maimaicin abinda na faɗa ko kuma muryata kake son ji?”

Mamdud ya buƙata, murmushi Labeeb yayi. 

“Jerk…”

Ya faɗi yana miƙewa, Mamdud bai sake kula shi ba. Babu inda zai je ba don yana da wani abu da zai yi ba. Kawai bai yi niyyar zuwa bane. 

Labeeb yai wahalar shi shi kaɗai. Yasan yana so ya rakashi ne don ya tayashi handling wasu abubuwan. Sanin labeeb na buƙatarshi haka yana ƙara mishi wani jin daɗi na daban. 

Yana nan zaune Labeeb ya fito da jakarshi a hannu. 

“Mamdud please mana… Wallahi abubuwan za su min yawa in babu kai.”

Wani murmushi Mamdud yayi, El Labeeb Maska da kanshi yana sauke aji da matsayin shi yana roƙon shi.

“Karka dame ni. Ba inda zani fa.”

Sauke ajiyar zuciya Labeeb yayi, ya ja jakarshi ya fice. Yasan halin Mamdud kamar yadda ya san na su Asad, in ta kaɗo mishi da kanshi zai kirashi yace mishi yana hanya. 

**** 

Ya ɗauka Mamdud zai bishi daga baya, amma har ya gama satikan shi uku ya dawo, inba ma shi ya kirawo shi ba ko sau ɗaya bai neme shi ba. 

Don haka wannan karon da gajiya sosai ya dawo gida. Ga rashin bacci isasshe da baya samu, ya kuma ƙi yarda ya sha wani abu. 

Yana parking ɗin motarshi, babu abinda ya tsaya ɗauka ya nufi gida, kawai so yake ya ji shi kwance kan gadonshi. Da sallama ya shiga gidan. 

Baiga kowa a falon ba, ga yunwa yana ji ga bacci da gajiya, ruwa kawai ya tsaya ya ɗauka ya wuce ɗakinshi, yana shiga ya soma cire takalma tare da rage kayan jikinshi ya ajiye su. 

Ruwan ya buɗe ya sha tukunna ya ƙarasa kan gadon ya kwanta ya lumshe idanuwanshi tare da jan iska ya fitar ta baki yana jin yadda kwanciyar tai mishi daɗi. 

Wayar shi ya lalubo ya nemo lambar Zulfa yai mata text:

‘Kina ina?’

Yana shiga ta dawo mishi da reply. 

‘Sannu da zuwa. Ina ɗakina.’

Murmushi ya ƙwace mishi. 

‘Ya akai kikasan na dawo?’

‘Na ji a jikina ne kawai.’

Dariya yai kamar tana ganinshi. 

‘Na gaji sosai, bacci nake ji, ga yunwa kuma.’

‘Ka fara cin abincin sannan, karkai bacci da yunwa.’

Girgiza kai yayi yana rubuta, 

‘Nikam bacci fa…see ya.’

Ya saka wayar a key ya ajiye gefe ɗaya. Zuciyar shi na mishi wani yanayi da ya kasa fahimta. Bai fi mintina biyar ba tsakani, bacci ya soma ðaukarshi ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofar. 

“Oh goodness….”

Ya faɗi kamar zai sa kuka. 

“Ko waye ya tafi sai na tashi bacci…”

Labeeb ya faɗi, yana janyo wani pillow ya ɗora saman kanshi. Muryar Zulfa ya jiyo. 

“Wallahi Yaya ka zo ka buɗe min ko in ta ƙwanƙwasawa har sai baccin nan ya tafi.”

Yasan halinta, tsaf zata nemi waje a bakin ƙofar taita ƙwanƙwasawa, Zulfa kaɗai ke da matsayin takura shi haka, dole ya miƙe yana jin kanshi kamar zai faɗo ƙasa. 

Riga ya ɗauka ya saka, duk da singlet a jikinshi, inba ƙurewa tai ba, Zulfa bata ganin shi daga shi sai singlet, ko ya zai ɗora riga a sama, ya kuma rasa dalili. 

Ƙarasawa yai ya buɗe mata ƙofar, yana ci gaba da ɓalle maɓallan rigarshi tare da ware idanuwa akanta ganin hannunta riƙe da plate. 

Wuce shi tayi tana ajiye abincin a ƙasa, taliya ce da miya da kayan ciki, sai soyayyar plantain. 

“Bacci nafi ji fiye da yunwa…”

Labeeb ya faɗi, kamshin abincin na cika mishi hanci, ƙara cikinshi yayi, Zulfa ta harare shi tana girgiza kai. 

“Ga cikinka nan da kanshi yana faɗar gaskiya.”

Yamutsa fuska Labeeb yayi. 

“Kaina ciwo.”

“Zai daina, ka ci abincin sai ka kwanta.”

Bai ce komai ba ya ƙarasa ya zauna yana jan plate ɗin gabanshi. 

“Ya min yawa sai dai mu ci tare.”

Bata yi mishi musu ba don bata ci komai ba, cokali ɗaya sukai sharing, tai mamakin yadda ta ci abincin sosai. Suna gamawa ya ɗauko musu robar ruwan da ya sha suka sha. 

“Yanzun sai bacci ko?”

“Kinsan cikina kumburi yake idan na ci abinci na kwanta. Dole sai ya sauka.”

Ya ƙarasa yana wani sauke murya a taɓare da ya burgeta. Da alama baima kula da yadda ya sauke muryar ba. Kawai ya zo mishi naturally ne kamar komai. 

“Ka tashi kaita tsalle.”

Zulfa ta faɗi, dariya yayi. 

“Yarinyar nan ke ko? Sai in tashi inta tsalle haka kawai? Ke kika tashe ni ai.”

“Gara dai da ka ci abincin. Da kai bacci da yunwa inka tashi sai ka ji kamar baka da lafiya.”

Kallonta kawai yayi bai ce komai ba. Plate ɗin ta ɗauka tana miƙewa. 

“Ina za ki je? Aifa zama za ki yi ki min hira har sai baccina da ya gudu ya dawo.”

Wannan karon ita tai dariyar, abinda tun tafiyarshi bata yi ba, ware mata idanuwa ya sake yi daya sata murmushi yasa zuciyar ta shiga wani irin yanayi na daban. 

Son shi ba zai taɓa faɗuwa ba a wajenta, son shi wani ɓangare ne na jikinta da ta girma da shi, da kuma ta tabbata rabuwa dashi na nufin mutuwarta. 

“Yaya kai baccinka. Ni kam kallo nake fa.”

Girgiza kai yayi. 

“Da gaske babu inda za ki je. Gara ma ki zauna ki bani labarin me kike kallo.”

Buɗe baki tai za ta yi mishi musu ya sauke idanuwanshi cikin nata. 

“Ki zauna nacee.”

Ya faɗi cikin muryar da babu wajen musu. Dole ta koma ta zauna, shi kam miƙewa yayi ya koma kan gadon ya zauna yana miƙe ƙafafuwan shi. 

Sauraren Zufa yake tana bashi labarin Indian fim ɗin da take kallo mai suna Main Prem Ki Diwani Hoon. Zamewa yai ya kwanta. Zai rantse sautin muryarta kawai yake ji cikin kunnuwanshi. 

Gaba ɗaya hankalin shi na kan yadda fuskarta take canzawa in ta faɗi wani abin, yadda idanuwanta suke ƙara girma, yadda laɓɓanta ke motsi, babu abinda yake fahimta cikin labarin da take bashi.

A haka har bacci ya ɗauke shi cike da mafarkinta, da yadda komai nata yake mishi kyau. Ganin yayi bacci yasa Zulfa sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa. 

Duvet ta ja ta rufe mishi ƙafafuwanshi tana jin yadda zuciyarta ke wani yawo a ƙirjinta, yanayin nutsuwar fuskarshi da yana baccin na saukar mata da yanayi na daban. 

Takai mintina biyar tana tsaye tana kallonshi sai da ta ga ya ɗan motsa tukunna ta ɗauki plate ɗin da sauri ta fita ta ja mishi ƙofar a hankali.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 25Rayuwarmu 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×