Skip to content
Part 27 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

A hankali komai yake tafiyar musu, a hankali rayuwa ke zuwa musu da sauyi na dangana da rashin sajda. Kewarta na nan a kullum. 

Sai dai tare da kewarta akwai juriya da dishewar zafin rashinta. Soyayyar su gareta na cikin yawan addu’ar su dake samunta. 

Yanzun haka da Zainab da Zulfa suma sun samu gurbin karatu a KASU kamar sauran ‘yan uwansu. Sai dai inda Zulfa ke karantar ‘Microbiology’, Zainab kuma na karantar ‘Biochemistry’.

Wani lokacin sukan tafi tare da Zainab ɗin, wani lokacin kuma da su Asad ko Mamdud. Su kuma dawo da duk wanda lokacin tashin su ya zo ɗaya. 

Dawowar su Dawud ya sa Arif shaƙuwa da Khateeb sosai, hakan yasa shi yanzun kusan ko da yaushe yana can, wasu lokuta kuma zai je ya taho da Khateeb ɗin nan. 

Hakan ya ma Labeeb daɗi, baida matsalar wanda zai kula da Arif ɗin, duk da kulawar abinci kawai yake da buƙata a yanzun. Mami kuma ta ɗauke mishi wannan. 

Daga nan Kauru inda suka gama shooting ɗin wani scene gidanshi na Barnawa ya wuce, ya ɗan fi mishi kusa, babu tunanin komai ya fito yasa mukulli ya buɗe kwaɗon gate ɗin ya dawo ya shigar da motarshi yai parking sannan ya fito ya sake kullewa. 

Tunda ba shi da Maigadi yanzun yasa yake kulle ko ina kafin ya tafi. In banda Mamdud babu wanda yake da wani mukullin gidan. 

Takawa yayi ya karasa ciki yasa mukulli ya buɗe gidan. Ya shiga da sallama duk da yasan ba kowa a gidan. Nan falo kan kujera ya watsa mukullan yana tsayawa ya cire takalmanshi. 

Gidan ya gani tas, yasan Mamdud ne zai sa a share shi haka. Kitchen ya nufa, komai tsaf an goge duk ƙurar nan, ya ɗauki kofi ya buɗe fridge ya ɗauko strawberry yoghurt ya fasa ya tsiyaya ya rufe ya mayar. 

Nan ya tsaya ya shanye ya saka kofin cikin wajen wanke-wanke inda duk tarin cups da plates ɗin da ya ɓata kafin ya tafi babu ko ɗaya. 

An wanke su an shirya tsaf. Fitowa yai daga kitchen ɗin ya nufi wata ƙofa cikin falon ya tura inda zata kaishi ɗan wajen hutawa na gidan. 

Ya ja kujera ya zauna yana jin yadda iska ke kaɗa shi. Yanayin ne yai mishi daɗi yasa yake jin kamar ace Zulfa na nan su sha hira abinsu. 

Wayarshi ya ɗauko daga aljihun shi, har zai kirata yai tunanin ko tana aji. Baya son ya dameta. Inta taso daga makaranta yasan zatai mishi text ko ta kira ta faɗa mishi. 

Gajiya yai da zaman ya tashi ya dawo falo ya kwanta kan kujera. Komai na jikinshi wani iri yake mishi. Ga kanshi yayi wani irin dumm. 

Numfashi yake fitarwa da sauri sauri, tun bayan rasuwar Sajda sai da ya kusan kwana arba’in bai sha komai na maye ba. Inda duk yasan zai iya zuwa ya samu temptation baya zuwa. 

Amma ina, sai da takai ta kawo koya akai mishi magana zai yi snapping. Dole ranar sai da ya sha ƙwayoyi tukunna ya ɗan samu ya ji dai dai. 

Tun lokacin yake ƙoƙarin faɗa da addiction ɗinshi. Amma da ƙyar yake iya sati bai sha ba. Babu shiri ya miƙe ya nufi ɗaya daga cikin bedrooms ɗin inda yasan yakan ajiye ƙwayoyinshi. 

Zuwa yai ya ɗauko guda biyu ya jefa a bakinshi yana totsa sannan ya dawo falon ya zauna yana maida numfashi. Yana tsanar kalar addiction ɗin nan da ya kasa bari. 

Kwanciya yai kan kujerar yana jiran high ɗin da kwayoyin kan bashi ya same shi. Bai fi mintina biyar ba ya ji kama motsi. Da sauri ya buɗe idanuwanshi yana miƙewa. 

Ƙarar da ta yi ta soma dokar mishi kunnuwa kafin ya sauke idanuwanshi kanta. Sanye take da riga da wando tai rolling kanta da mayafi da takalma dogaye a ƙafafunta. 

Kallonta Labeeb yake yi, zulfa kan saka riga da wando sosai. Sai dai in bata ɗora jacket ba to rigunanta dukkansu sukan zo har gwiwarta. Ba kamar na wannan ba da rigar take guntuwa. 

Kallonta yake sosai, ya jima bai ga mace kalarta ba. Kuma bai taɓa jin wadda kyanta ya zauna mishi irin na yarinyar dake tsaye a gabanshi ba. 

Sai da zuciyarshi ta gama kallonta tsaf tukunna mamakin yadda akai ta shigo ya zo mishi. 

“Ta ina kika shigo? Wacece ke?”

Ya jero mata tambayoyin a lokaci ɗaya, wani ɓangare na zuciyarshi na kawo mishi Mamdud ne ya bata mukullin gidan. Ranshi ne ya ji ya ɓaci. 

Har warning yaima Mamdud kar ya sake ya kawo mishi mata cikin gidan nan, saboda sam baya son ƙazantar zina a cikinshi. Yana son wajen da zai kwanta yai sallah babu ƙyamata. 

Ita kam shiru tayi sai ware mishi manyan idanuwanta take da suke cike da tsoro. Ga bakinta da ya fi komai kyau a jikinta ta ƙara tsuke shi. 

“Mamdud ya kawo ki ko?”

Labeeb ya tambaya jin bata da niyyar bashi amsa. Da sauri ta ɗaga mishi kai. Wani dogon tsaki Labeeb ya ja yana ɗorawa da, 

“Get out! Wannan ya zama ranar ƙarshe da ƙafafuwanki za su tako nan…”

Ai bata ma jira ya ƙarasa ba, da gudu tai hanyar ƙofa, baisan me yasa zuciyarshi ta doka da tunanin karta zame ta faɗi ba saboda dogayen takalman da ke ƙafarta. Amma lafiya ƙalau ta fice. 

Kitchen ya nufa ya ɗauko ruwa ya sha saboda maƙoshin shi da ya ji ya bushe da baida alaƙa da ƙishin ruwa. Sannan ya dawo falon ya zauna. 

Jin abin ba nayi bane yasa shi tashi ya nufi ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ɗakin. Kanshi tsaye banɗaki ya wuce ya sakar ma kanshi ruwa masu sanyi ko zai samu sauƙin yanayin da yake ji. 

Amma sai ka ce ya tunzura yanayin. Fitowa yai ɗaure da towel da kuma wani yana tsane jikinshi. Safe ɗin kayan ya duba, gaba ɗaya kayan mamdud ne. 

Hakan yasa shi fitowa ya nufi wani bedroom ɗin inda ya samu kayanshi, wasu suspenders ɗin ya sake ɗauka ya saka, glasses kawai ya ɗauka ya saka ma idanuwanshi bai ɗauki malfa ba ya fice.

Gidan ya rufe ya nufi Naf Club kamar koda yaushe, yarinyar da ta fara yima idanuwanshi ya ɗauka. Rage abinda yake ji kawai zai yi da ita ya sallameta.Auren da yayi yasa baya wuce iya hakan. 

***** 

A hanyarshi ta komawa gida yai sallar Isha’i ya kuma tsaya a hanya ya sa ma cikinshi wani abu tukunna ya wuce. Da sallama ya shiga. 

Duk su Zulfa na falon suka gaishe da shi, sama sama ya amsa don yana son ya fara sauke ma Mamdud abinda yake cikinshi tukunna. 

“Ina Mamdud?”

Ya tambaye su, da hannu Asad ya nuna mishi cewar yana ciki, su dukansu hankalinsu na kan fim ɗin da suke kallo. Ɓangaren su Labeeb ya ƙarasa. 

Babu ko sallama ya tura ɗakin. Mamdud na kwance yana kallo a TV ɗin da ke ɗakin nasu. 

“Kai… Ni ka bani tsoro wallahi.”

Mamdud ya faɗi yana hararar Labeeb ɗin. 

“Wa ka kai min gida? Mamdud na ɗauka na faɗa maka bana son ka kai min kowacce macce wannan gidan?”

Cike da rashin fahimta Mamdud ke kallonshi, yana cikin jin daɗinshi Labeeb ɗin ya zo ya ɓata mishi rai. Ya tsani yadda ya wani tsare shi da idanuwa kamar ɗanshi. 

“Ban gane me kake nufi ba.”

Mamdud ɗin ya faɗi. Cike da kallon da ke fassara karka raina min hankali Labeeb ya ce, 

“Really? Baka gane me nake nufi ba? Yarinyar da ka kai min gidana na Barnawa.”

Ƙaramin tsaki Mamdud ya ja. Yasan gidanshi ne ba sai ya nanata mishi ba cike da isa da nuna iko. 

“Masu gida… Rabona da gidan nan tun ranar da ka ce in kai maka kayanka…babu yarinyar da na kai.”

Sosai Labeeb ke kallonshi, kafin ya ji tsikar jikinshi ta miƙe ganin da gaske Mamdud yake bai kai kowacce yarinya ba. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Mukullan gidan dana baka fa?”

Har lokacin Mamdud ya rasa abinda ya haɗa shi da wannan tambayoyin da Labeeb ya katse mishi kallonshi yake mishi su. 

“Gasu nan cikin drawer. Ɗauki abinka…don Allah ka matsa daga nan kallo nake.”

Mamdud ya ƙarasa da alamun takura a muryarshi. Matsawa Labeeb yayi ya zauna gefen gadon yana jin kamar an watsa mishi ruwan kankara. 

Yadda Mamdud ya mayar da hankalinshi kan kallon da yake bai ce mishi komai ba shima haka yai shiru zuciyarshi cike da tsananin fargaba da mamakin yarinyar ɗazu. 

Ya jima nan zaune kafin ya fita falo, sun kai wajen ƙarfe ɗaya suna shiririta da su Zulfa, sai da ya duba agogo tukunna duk ya kore su sanin suna da makaranta da safe. 

Sa’adda ya shiga ɗaki Mamdud har yayi bacci, shi kam Labeeb saida yai wanka ya fito tukunna ya kwanta, gaba ɗaya zuciyarshi bata da nutsuwa.Ta inda yarinyar nan ta bi ta shigar mishi gida na bashi mamaki, ya jima yana tunanin har bacci ya ɗauke shi. 

***** 

Zainab yasa ta haɗa mishi tea mai kauri. Ba yadda bata yi ba ya haɗa da wani abu ya ce mata tea ɗin kawai yake marmarin sha. Da cup ɗin riƙe a hannunshi yana juya cokalin a ciki da ɗayan hannun yake takawa zuwa falon. 

Yana farkawa da tunanin yarinyar nan cikin ranshi. Al’amarinta ya ɗaure mishi kai ba kaɗan ba. Waje ya samu ya zauna yana kurɓar tea ɗin a hankali saboda zafin da yake da shi. 

Bai ga fitowar Dady ba sai muryarshi da ya ji. 

“Labeeb har an tashi?”

Miƙewa Labeeb yayi da murmushi a fuskarshi. 

“Dady… Ina kwana…bansan ka zo ba.”

Murmushi Dady yayi yana ƙarasawa inda Labeeb ɗin yake, kujera ya nema ya zauna sannan shi ma Labeeb ɗin ya zauna wajen da ya tashi. 

“Da sassafe na shigo duk kuna bacci, Zainab kaɗai ta san dawowata. Ya aikin?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Labeeb yayi. 

“Alhamdulillah…Za mu je Lagos ma, amma ina tunanin sai ƙarshen watan nan.”

Addu’a Dady yai mishi suka ɗanyi hira kaɗan kafin su yi sallama Dady ya fice. Labeeb yafi kewar Mummy, saboda sosai sukan yi waya da Dady. 

In Labeeb bai kira shi ba, yakan kira su gaisa kusan kullum. Kamar tunanin yarinyar nan jira yake Dady ya tafi ya dawo mishi. 

Sauke numfashi yayi, ya miƙe yana nufar ɗakinshi, gaba ɗaya baya jin daɗin komai, ga Zulfa tunda safe suka fita makaranta ita da Asad. Zainab ma ce ta ce mishi sai sha ɗaya da rabi zata fita. 

“Kai baka da makaranta ne yau?”

Ya tambayi Mamdud da ke kwance kan gadon ƙafafuwanshi na ƙasa. Kafin ya ƙarasa ya ajiye kofin tea ɗinshi gefe ya ɗauki remote. 

Sai da Mamdud ya miƙe, hannu ya kai ya ɗauki kofin da Labeeb ya ajiye, da sauri Labeeb ya kawo hannu, ƙafafuwanshi Mamdud ya janye ya mayar kan gadon yana matsawa sosai. 

Kurɓar tea ɗin yayi ya amsa labeeb da faɗin, 

“Akwai… Bana jin zuwa ne… Umm… Tea ɗin nan ya min daɗi.”

Ganin Labeeb yana zagayowa yasa Mamdud miƙewa tsaye kan gadon yana dariya tare da sake kurɓar shayin. 

“Ranka zai ɓaci…ka fita ka haɗo naka mana… Ka ban tea ɗina Mamdud.”

Labeeb ya faɗi yana hararar shi, maimakon ya sakko daga kan gadon sai ma dariya da ya kama yi. Dole Labeeb ya fita daga ɗakin, wannan karon da kanshi ya shiga kitchen ɗin ya sake haɗo wani tea ɗin ya koma ɗaki. 

“In zo ka ƙara zuba min?”

Mamdud ya tambaya yana ƙarasa maganar da dariya. 

“Zo in ƙara maka…”

Labeeb ya faɗi yana daring ɗinshi da idanuwa da ya ƙarasa. Girgiza kai Mamdud yayi yana dariya. 

“Bar abinka…”

“Da gaske ka zo in ƙara maka.”

Labeeb ya faɗi, sake girgiza mishi kai yayi. Sosai Labeeb ke shan tea ɗin kafin cikin ƙaramar murya ya ce, 

“Jiya da nake tambayarka ko kakai yarinya gidana… Wata na samu a gidan Mamdud, budurwa haka, it’s just… Ina mamakin yadda ta shiga.”

Ɗan ware idanuwa Mamdud yayi. Cike da mamaki yake kallon Labeeb. 

“Wata fa… Kuma gidan a kulle yake? I mean baka manta ba last fitarka?”

“Ko da naje ni na buɗe ko ina…abin na bani mamaki ne, na tambaya ko kai ne ka kaita ta ɗaga min kai. 

Sai kawai na kore ta, Shi yasa ka ji ina tambayarka jiya…”

“This is scary…kuma kana cikin hankalinka? Ko dai gizo-gizo tai maka?”

Wani kallo Labeeb ya watsa mishi. 

“Koƙi-ƙoƙi tai min ba gizo-gizo ba. Ka ji ba raina min hankali, ina faɗa maka abu za kai min iskanci… Ni fa jikina yake bani aljana ce, mu koma mu duba yau.”

“Ku koma? As in kai da wa?”

Mamdud ya tambaya yana ware idanuwa.

“Ni da kai mana.”

Tun kafin ya ƙarasa Mamdud ke girgiza mishi kai yana faɗin,

“No… Kar ma ka ƙarasa… Ok fine ka ƙarasa… Babu inda zanje, can idanuwanka ne sukai maka gane-ganenka. 

In kana son dubawa ne ka je kai kaɗai, ko ku tafi da Zulfa.”

‘Yar dariya Labeeb yayi. 

“Banza matsoraci.”

“Eh na ji ɗin. Allah ya bada sa’a.”

Hira suka ci gaba dayi da Mamdud ɗin ba don batun yarinyar ya bar zuciyarshi ba, fuskarta ta samu waje ta manne mishi. Shi da Mamdud ɗin suna dawowa masallaci ɓangaren su Dawud suka nufa. 

Basu ga Hajiya Beeba ba, babu wanda ya damu da ita dama suka nufi wajen Mami, sai da suka ci abinci sannan suka sake fitowa. Gida Mamdud ya koma. 

Labeeb kam duk da zuciyarshi na dokawa haka ya ɗauki mota ya sake nufar gidanshi. Zuciyarshi zata samu nutsuwa ne kawai inya sake duba gidan. 

Hannuwanshi har rawa suke wajen bude gate ɗin, ya shigar da mota yai parking ya sake kullewa. Duk wata addu’a da ta zo mishi karantawa yake har ya buɗe gidan. 

Sai ya ji maƙoshin shi ya bushe, zuciyarshi kamar zata fito daga ƙirjinshi. Da ƙarfin hali ya tura gidan ya shiga da Bisimillah. Tun daga bakin ƙofa ya kwance takalmanshi. 

Sosai yake yawata idanuwanshi cikin ɗakin bai ganta ba. Hakan yasa shi ƙarasawa ya buɗe bedrooms ɗin gidan ɗaya bayan ɗaya bata ciki. Sauke wani numfashi mai nauyi yayi. 

Kamar wanda yai aiki haka ya ji jikinshi. Duk ya bi ya gaji. Kitchen ya nufa ya ɗauko kwalbar giya ɗaya ya dawo da ita falo ya zauna, duk yadda akai yarinyar jiya Aljana ce.

In ba Aljana ba baiga ta yadda za’ai ta shigo mishi gida ba. Buɗe kwalbar yayi bai ko nemi kofi ba ya kafa kai, bayason yadda duk wani abu cikin kanshi yake baibaye da tunanin ta. 

Sai da ya ga kayan da ke ɗakin sun soma juya mishi, ya ji iskar ɗakin kanta na zuwa mishi a slow sannan ya ajiye kwalbar ko tureta yai ma bazai gane ba. 

Ya kwanta kan kujerar da yake zaune, kusan ƙafafunshi a ƙasa suke, wata irin kwanciya yayi saboda ba gane daɗin kwanciyar yake ba. Asalima yana wata duniya ce da baya gane duk wannan abubuwan. 

Kafin ya ji shiru cikin kanshi, komai ya tsaya cak. Ba zai ce ga iya lokacin da ya ɗauka yana bacci ba, abu ɗaya zai iya bambancewa, da gudu da rarrafe ya haɗa zuwa bedroom, da ƙyar ya ƙarasa toilet kafin ya soma sheƙa amai. 

Sai da ya amayar da duk wani abu da ke cikinshi ga ciwon kai da ya kawo mishi ziyara kamar ya cire kan ya ajiye gefe ɗaya ya ɗan huta. 

A galaɓaice ya miƙe ya cire kayan da ke jikinshi, da shower gel ya wanke su saboda ba zai iya tsayawa ɗauko wani sabulu ba. 

Yana gamawa ya ɗauraye ya shanya yai wanka tukunna, bai damu ba wannan karon, cikin kayan Mamdud ya samu riga da three quarter ya saka. 

Agogon ɗakin ya kalla, huɗu har da rabi. 

“Damn…”

Ta furta ƙasa-ƙasa yana komawa toilet yayo alwala ya zo ya gabatar da sallar Asr, kanshi kamar zai ɓalle, haka ya tallabo goshin shi yayo falo. 

Sai dai me, baiga kwalbar giyar da ya ajiye ba, abin ya ɗaure mishi kai, kitchen ya nufa ya sami kwalbar ajiye cikin kwandon shara, haka babu kofin da ya sha strawberry yogurt jiya.

Cikinshi ya ji ya ƙulle, da sauri ya baro kitchen ɗin ya fito ya ɗauki mukullan motar shi da na gidan ya samu ya ɗaura takalmanshi.

Jikinshi na ɓari ya kulle gidan, tabbas Aljanu sun sami wajen zama a ciki, shi ne tunanin da yake a hanya. Dama ance gida in babu mutane ciki Aljanu na samun wajen zama. 

Bai taɓa yarda ba sai yanzun. AC ɗin motar bai hana zufa karyo mishi ba, da ƙyar ya lallaɓa ya ƙarasa gida. Da Zulfa ya soma cin karo tana zaune da take away a gabanta na dankalin turawa, plantain da ƙwai. 

Zama yayi gefenta. 

“Aljanu sun samu wajen zama a gidana…”

Ya faɗi mata yana maida numfashi, ɗago kai ta yi ta sauke idanuwanta cikin nashi tana tauna abinda ke bakinta a hankali. Gyara zama Labeeb yayi.

“Kinsan Allah Aljanu fa, kin ga an wanke kayan wanke wanken dana ɓata, jiya kuma na ga wata yarinya a gidan da…”

Dariya Labeeb ya ji data sa shi juyawa, Asad ne a tsaye. 

“Aljanun ne suka wanke kwanoni…”

Ya faɗi yana dariya tare da zama gefen zulfa yasa hannu ya ɗibi dankalin da take ci tare da ɗorawa da, 

“A sako labarin daga farko don Allah… Yaushe za ai releasing fim ɗin?”

Yake tambaya yana kai hannu zai ɗauki lemon da ke gaban Zulfa ta janye tana daƙuna mishi fuska. 

“Da na ce in siyo da kai haka kace ka ƙoshi…”

Murmushi Asad yayi yana sake sa hannu ya ɗauki plantain ɗaya, da gaske yake baya jin yunwa. Yanzun ma baisan me yasa yasa mata hannu ba. 

“Maganan gaske nake kana mun wani shirme…wai ba za ku jini bane kam?”

Labeeb ya ƙarasa ganin hankalin Zulfa da Asad ɗin na kan rigimar da suke kan abinda take ci. Jin me ya faɗa yasa suka maida hankalin su kanshi. 

Duk abinda ya faru ya faɗa musu, banda part ɗin buguwar da yayi. Sosai suke taya shi jin tsoro. 

“Gaskiya karka koma gidan nan kai kaɗai. In suka cutar da kai fa? Ko ka faɗa ma Dady yasa ai addu’a tukunna.”

Cewar Zulfa, Asad ya karɓe zancen da faɗin, 

“Wallahi kam, karka sake komawa sai an yi addu’a.”

Zainab ce ta shigo da sallama, suka amsata, ganin yadda fuskarsu take very serious yasa ta tambayar ko lafiya tana neman waje ta zauna. 

Asad ne ya bata labari. Cikin mamaki ta ce, 

“Taɓ gaskiya ka yi ƙoƙari, da ka koma daka sake ganinta fa? Hu’um… Yaya Asad yaushe zamu?”

Ta tambaya tana kallon Asad. 

“Kun sha omo wajen practical yau ko?”

Ya tambaya yana mata kallon da ke fassara bata da hankali. Dariya ta kama yi tana miƙewa. 

“Ni kam a gajiye nake sai….”

Wayarta data yi ringing ta katse mata maganar da ta yi shirin faɗa. Zaro wayar ta yi daga jakarta ta duba, murmushi ta yi bata ɗaga ba ta nufi hanyar ɗakinta da sauri. 

“Waye yake kiranta?”

Labeeb ya tambaye su babu wasa a muryarshi, saboda sam yadda Zainab tai murmushi bai mishi ba. 

“Ni ya zan yi in sani? Ka ji Yaya fa…ba duka muke zaune anan ba.”

Asad ta faɗi, zulfa kam dariya kawai tayi, miƙewa Labeeb ɗin yayi yana nufar hanyar ɗakin Zainab. Da sauri Zulfa ta miƙe tana ɗaukar sauran lemonta. 

“Ba da ni za a kalli wannan dramar ba.”

Ta faɗi tana nufar ɗakinta. Asad ma miƙewa yayi ya nufi nasu ɓangaren. Labeeb kam bakin ƙofar ɗakin Zainab ya tsaya ya saka kunnenshi jikin ƙofar ɗakin. 

Amma ko motsinta bai ji ba balle abinda take faɗa. Wani abu yai mishi tsaye a wuya, dole ya haƙura ya nufi nashi ɗakin da wata sabuwar damuwar, yasan yadda jami’a take. Sam bayason wani kusa da Zainab. Karatu ta je yi, shi ɗin yake son tayi. 

**** 

Kamar yadda su Asad suka bashi amsa haka ya samu Dady ya faɗa mishi ana tsorata shi a gidanshi na Barnawa. Addu’a dady yasa aka je aka yi a ko ina na cikin gidan. 

Duk da haka Labeeb bai sake komawa ba, ba don yana tsoron wani abun ba. Sai don bai samu lokaci ba. Haka suka shirya shi da Mamdud suka nufi Lagos. 

Zuwansu, yanayin aikin da Labeeb ɗin yake yi. Duk wani time free da zai samu a Polo club suke rallewar su. Kwata kwata ya fita batun yarinyar da yake ɗaukar Aljana ce. 

***** 

Nine starts ya biya ya siya lemuka, sabulun wanka da shower gel sai ƙananan abubuwan da ya tuna zai iya amfani da su ya nufi gidanshi na Barnawa. Wani lokacin yana buƙatar jin shiru, musamman in sun yi satuka wajen aiki, zai ji a duniya babu abinda yake son ji banda shiru, baya son jin motsin komai. 

Lokuta irin haka yakan ji kamar ace wani aiki yake, a ɗan company ko wani waje inda zai je kullum ya dawo gida. In da zai shiga duk inda yake so babu wanda ya damu da shi. 

Amma ina, don ma yanayin shigarshi da malfar da yake fita da shi yasa wani lokacin ba’a saurin gane shi. Amma dole akwai inda baya shiga sai da securities. 

Ya tsani komai na dangane da aikinshi. Yakan hango wata rana ya ajiye acting ya samu wani abin daban. Malfar shi ya sake ja ƙasa ganin wasu na kallonshi. 

Hankalinshi a kwance ya shiga gidan yana sauke numfashi jin wani shiru da ya ziyarci kunnuwanshi, lumshe idanuwanshi yayi yana feeling yanayin. 

Kafin ya nufi kitchen ya buɗe fridge ya jera lemukan da ya siyo a ciki. Ya kwashi sauran kayan yana nufar ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ya shiga toilet ya ajiye sabulun a mazaunin shi. 

Ya fita zuwa ɗayan ma ya saka, sannan ya sake fita zuwa na ƙarshen, yana turawa idanuwanshi kan gadon suka sauka kafin zuciyarshi tai wani tsalle da yasa shi dafe ƙirjinshi babu shiri. 

Kwance take kan gadon, faɗuwar shower gel ɗin hannunshi da sabulun yasa ta ɗagowa da sauri, kallon Labeeb ɗin take idanuwanta cike da tsoro. 

Wani yawu Labeeb ya haɗiya, ƙafafuwanta ya fara kallo ko zai ga kofato, ganin yatsu kamar nashi yasa shi jero Ayatul Kursiyyu kafin ya taka ya ƙarasa wajen gadon. 

Bakinshi na rawa ya ce, 

“Ke mutum ce ko Aljana?”

Tambayarshi ta sa ɗan guntun murmushi ƙwace mata, ɗan ƙaramin lotsawar dake gefen bakinta kamar dimple bai wuce idanuwan Labeeb ba. 

Baisan me ya cire mishi tsoron da ke zuciyarshi ba, amma murmushin da ta yi ya musanya shi da ɓacin rai. Ta shigo mishi gida, baisan ko ta yaya ba, har tana da ƙarfin halin jin nishadi da tambayarshi. 

“Gab nake da kiran ‘Yansanda in har baki fara gaya min wani abu ba…ta ya kike shigo min gida? Ta ina? Me kikeyi?”

Sake ware mishi idanuwa tayi tana shagwaɓe fuskarta da tai mishi kyau. 

“Ta ƙofa, babu abinda nakeyi, i just need wajen da zanyi bacci…”

Wata irin murya take da ita, yanayin muryar da komai na samun wajen zama cikin kunnuwanshi, yanayin na son ɗauke mishi hankali da maganar da suke yi. 

Al’amarinta na ƙara ɗaure mishi kai ta wani fannin. Ta wani kuma yana ƙara ɓata mishi rai. Yana tunanin ko stalker ce, ko ɗaya daga cikin masu sonshi ne ta gano gidanshi. 

Amma inda ta samu mukullai ne yake bashi mamaki. Muryarshi bayyane da abinda yake ji ya ce, 

“Ta ƙofa? Bacci? Fuck that, sai akace gidana ne zai zama wajen baccin ki? Kinsan me… Tashi… Ki tashi na ce ko!”

Ya ƙarasa a tsawace yana ganin yadda ya firgitata, miƙewa tayi, doguwar rigace a jikinta wannan karon, itama bata ɓoye yanayin surar jikinta ba. 

‘Wannan yarinyar bom ce.’

Ya faɗi cikin kanshi yana ɗauke idanuwanshi daga kanta, har sai da tazo wucewa ta gefenshi. 

“Idan na sake ganinki zan sa a kulle ki.”

Idanuwanta da suke cike da hawaye tasa cikin nashi kafin ta ɗan ɗaga mishi kai ta wuce. Sai da ya ga ta ja ƙofar tukunna ya sauke numfashin da baisan yana riƙewa ba. 

Da sauri ya bi bayanta yana son sake tabbatar da mutum ce, hanyar fita daga gidan ya ga ta nufa kafin ta tsaya dai dai gate ɗin. Ga mamakinshi takalman da ke ƙafarta ta cire. 

Yana tsaye bakin ƙofa yana kallon ikon Allah. Haɗe su tai ba zai hango ko tayaya ba, ta cire mayafin dake kanta, leƙawa ya ga ta fara yi ƙila ta ga ko da mutane. 

Kafin ta naɗa mayafin jikin hannunta, takalamanta ta ɗiba ta watsa waje, hannunta tasa ta kama ƙarfen gate ɗin , bazai ce ga yanda akai ba. 

Sama ya ga ta maƙale, kafin ta kama bangon da ke haɗe da ɗakin Maigadi, sai gani yai ta dira, sakin baki yayi cike da mamaki. Baisan sa’adda, 

“Wow…Just wow…” 

Ya suɓuce mishi daga baki ba, mamaki ya ƙi sakinshi har ya koma cikin gidan ya zauna babu abinda ke mishi yawo cikin kai banda wannan. Yanzun yasan yadda take hauro gate ɗin. 

Yadda take buɗe ƙofar gidan ne mystery yanzun. Mamakin kowacece yarinyar yake yi. Sai lokacin ya tuna yana da kuɗi a cikin gidan. 

Da sauri ya miƙe, ɗakin da suka yi sharing shi da zafira ya nufa, ya janyo inda ya ajiye kuɗin, duk da baisan ko nawa bane ba, bai ga alamar an ɗauka ba. 

Har ya kwashe su sai kuma ya mayar ya ajiye, inda abinda ya shigo da ita kenan zata ɗiba, don ba zai ce ga tun sa’adda take shigo mishi ba. 

Ƙila da basu haɗu sau biyun nan ba, ba zai taɓa sanin tana shigowa ba ma. Tare da wannan tunanin, da mamaki akwai tsoro-tsoro cikin al’amarin yarinyar. 

Kwanciya yayi duk da ba bacci yake ji ba. Yana buƙatar hutunne. Bai kunna kallo ba don shirun yake son ji. Ya jima sosai a gidan yana hutawa kafin ya ɗauki mukullan shi ya kulle gidan ya wuce. 

Sa’adda ya ƙarasa gida yamma tayi sosai, baƙuwar mota ya gani a gidan. Jeep ce baƙa babba, da alama sabuwa ce ma. Tunani ɗaya ya zo mishi. 

Mummy ce ta dawo da motar, tashi yai parking gefe ya fito cike da nishaɗin jin daɗin dawowar Mummy ɗin ko da ba zata jima ba. 

Da sallama ya shiga gidan, amma me, Ishaq ne zaune shi da Zainab a ƙasa kan kafet ɗin falon, da tablet a hannunsu shi da Zainab, kowanne cikinsu ya kama ƙarshen tablet ɗin. 

Earpiece ma ɗaya ne suke sharing, sai robobin ice cream a gabansu da tarkacen ciye-ciye. Kallon yanayin zaman su Labeeb yake yana jin wani sense na protectiveness na shigar shi. 

Kaɗan ya rage ƙugunsu ya haɗu, bama su ji sallamar shi ba balle shigowar shi. Abu ɗaya zuciyarshi take son yi, ta ɗauke Ishaq daga kusa da Zainab ta watsa shi can nesa da ita. 

Amma kamar an dasa shi a wajen, gyara zama Zainab ta sake yi yana ganin yadda kafaɗarta ta gogi ta Ishaq yana jin contact ɗin har cikin ranshi. 

Ɗan ɗagowa Ishaq ɗin yayi, yai mata murmushi, abin ya ishi Labeeb, da sauri ya taka yana ƙarasawa, sai lokacin Zainab ta ɗago dakai, earpiece ɗin da ke kunnenta ta cire. 

“Yaya… Sannu da zuwa.”

Ta faɗi, kasa amsata yayi saboda jin da yake kamar ya kwaɗa mata mari, bata san halin maza ba, bata san su ɗin ba abin yarda bane. Zainab bata da hankali. 

Da gwiwar hannunta ta zunguri Ishaq ya ɗago kanshi da sauri, sai da ya rama yana turo mata baki alamar ya ji zafi tukunna ya maida hankalinshi kan Labeeb da ke tsaye yana jan numfashi a hankali yana mayar wa.

“El-Maska…ka ƙaraso ka tsaya nan kana huci kamar wanda ya sha gudu.”

Ishaq ya faɗi da murmushi a muryarshi da Labeeb ke son ɗauke mishi. Yasan sarai abinda yake yi. Don Labeeb na karantar fuskar shi tsaf. 

“Bamu waje Zainab.”

Labeeb ya faɗi idanuwanshi tsaf kan Ishaq. Jin yai amfani da cikakken sunanta yasa babu musu ta miƙe, tasan ranshi a ɓace yake amma bata ga dalili ba. 

Ita dai bata yi wani abinba, ƙila can a waje wani ya taɓa shi, Ishaq ta kalla. 

“Kana nan?”

Ta buƙata, zai amsa Labeeb ya rigashi da faɗin, 

“Tafiya zai yi.”

Daƙuna ma Labeeb fuska tayi tana son nuna mishi kar ya kwafsa mata a gaban Ishaq, shima da idanun yake nuna mata ta bar wajen in bata son haka ya faru. 

Sai da ta sauke numfashi tukunna ta tsugunna ta ɗauki robar ice cream ɗinta, yana kallon yadda idanuwan Ishaq ke yawo a kanta. 

Tana barin wajen labeeb ya ƙarasa ya zauna inda ta tashi, sosai yake kallon Ishaq ɗin. 

“Na rantse da Allah in ka taɓata… In ka taɓa ta zan manta akwai danganta ka a tsakanin mu… I will end you!”

Dariya Ishaq yayi ko alama bai nuna maganar Labeeb ɗin ta ma shige shi ba, hannu yasa yana tare shi. 

“Get out of my face El-Maska… Ƙanwata ce nima.”

Ishaq ya faɗi, wani kallo Labeeb ke watsa mishi, sam zuciyarshi ta kasa nutsuwa da Ishaq ɗin. Baya son kowanne namiji banda su kusa da Zainab. 

Inda akwai makarantar mata zallah can zai kaita, to sai dai ya bar ƙasar da ita, ko ina hankalinshi bazai kwanta ba. Gara ma anan kusa inda zai iya ganinta. 

“Da gaske nake Ishaq, stay away from her!”

Ice cream ɗinshi ya ɗauka yasa cokalin a ciki ya ɗibo yana sha.

“Saboda me?”

Ya buƙata. Gab Labeeb yake da kai mishi duka in ya ci gaba da mishi magana gatsal cikin rashin damuwa haka. 

“Saboda na ce, saboda ƙanwata ce.”

Ajiye robar Ishaq yayi, muryarshi da fuskarshi babu wasa yace ma Labeeb. 

“Zan iya fahimtar protectiveness ɗinka. Amma ina ganin kamar yana wuce misali. Mace ce… Ko bani ba ba zaka iya kareta daga sauran maza ba. 

Eventually dole zata kula samari ko kana so ko baka so, yarda da ita shi ne abinda ya kamata kayi, ba ‘yar shekara huɗu bace ba. 

I like her, ba kaɗan ba kuma, and we are dating maganar da nake maka yanzun. Zaka ci gaba da ganina kusa da ita lokaci zuwa lokaci. 

Deal with it…”

Ishaq ya ƙarasa yana miƙewa saboda Labeeb ɗin ya gama ɓata mishi rai. Yana yi kaman zai lalata Zainab ɗin ko wani abu. Babu kalar matan da bai gani ba. Wanda suka fita da wanda basu kaita ba. 

Daga tsayen ya sake kallon Labeeb da faɗin, 

“Ka daina ɗaukar duk maza kalar ku ɗaya. Ka daina ɗauka abinda kakeyi shi kowa yake yi. Shekarun dana ɗauka a ƙasar waje baisa ni zubda addini na ba…”

Wani waje kalaman Ishaq suka tsaya ma Labeeb a ƙirjinshi suna ƙona wajen da wani raɗaɗi mai zafi. Gaba ɗaya babu ƙarya a maganganun Ishaq. 

Yana kallo har ya fice, amma baisan meyasa hakan yai mishi zafi ba. Ya gaya mishi maganganun da sukai mishi ciwo ba kaɗan ba. Gaskiya ne kallon ‘yan iska yake ma duk samari. 

Kallon kowanne saurayi yake kamar duk hali ɗaya suke da shi , musamman wanda zasu zo wajen Zainab ko kusa da ita, yasan akwai nagari sosai, in ya kalli su Asad yana ganin hakan. 

Amma su ƙannenshi ne, ba zai taɓa kawo wannan tunanin akan su ba. Bai damu ba in hakan ya zama son kai. Akan su zai yi komai da ya fi haka ma. 

Zainab da Ishaq dating suke yi bai ma ko ji labari ba balle ya sani. In haka ne baisan iya lokacin da suke ɗauka tare da juna ba. Tsoro na gaske ya cika mishi zuciya. 

Anees ne ya shigo da sallama, zuciyar Labeeb ta sake dokawa sai lokacin tunanin ba kowa a gidan ya faɗo mishi. Daga Zainab sai Ishaq, su biyu kacal cikin gida. 

Tunanin abinda zai iya faruwa yasa zuciyarshi barazanar tsayawa. Maimakon amsa sallamar Anees sai cayai. 

“Tun yaushe kuka san Ishaq na dating Zainab?”

Ɗan daƙuna fuska Anees yayi, tambayar na zuwa mishi da bazata. Kafin ya ɗan ɗaga kafaɗa. 

“Kawai nai assuming ne saboda yana yawan zuwa tun bayan bikin ka.”

Rai a ɓace Labeeb ya ce, 

“Ku duka babu wanda yai tunanin ya faɗa min.”

Da mamaki Anees ya ce, 

“Ban ɗauka wani abu bane ba… He is family shi yasa ban damu ba.”

Miƙewa Labeeb yayi. Su dukansu basu da hankali. 

“Su kaɗai na samu cikin gidan nan zaune suna kallo Anees kana faɗa min he is family? In bana nan ku ya kamata ku kula da Zee Zee.”

Ɗan ɗaga hannuwanshi Anees yayi. 

“You are overreacting yaya. Ba abin faɗa bane ba…”

Komai ƙara tunzura Labeeb yake. Ji yake kamar ya kwaɗa ma Anees mari. Mamdud ne ya shigo. Ganinsu tsaye cirko-cirko yasa shi tambayar ko lafiya. 

“Yaya ne yake fada kan Ishaq da Zee Zee.”

Anees ya amsashi a gajiye .

“Ba dating suke ba? Dazun ma naje ɗaukarta mu dawo gida don tare mukai closing ta ce min ya mata waya za su fita.”

“What?! Wai meyasa ku duka baku da hankali? Duka nawa Zainab ɗin take da zata fara kula samari? Harkai Mamdud ta ma faɗa maka za su je wani waje da wani ƙato ka barta kuma. 

Ku duka kun kyauta… Yayi dai dai. Hankalina sai ya daina kwanciya na bar Zainab a ƙarƙashin kulawarku.”

Labeeb ya ƙarasa maganar cikin ɓacin rai yana nufar ɗakin Zainab. 

“Ko wani ya ɓata mishi rai a waje? Don Allah ni me na yi Yaya Mamdud? Zan hana Zainab kula samari ne?”

Sauke numfashi Mamdud yayi. Yasan dalilin faɗan Labeeb shi. Tsoronshi na kar ai ma Zainab abinda yake ma wasu ne yasa shi ɓoyewa bayan faɗan da yake musu. 

“Maybe, har da stress kuma. Zan mishi magana karka damu ka je kai hidimarka.”

Mamdud ya amsa Anees ɗin ganin damuwar da ke fuskarshi. Wucewa Anees ɗin yayi kam don a gajiye yake, faɗan Labeeb yasa ya nemi yunwar da yake ji ya rasa. 

Labeeb kuwa ɗakin Zainab ya wuce, bai ko ƙwanƙwasa ba balle sallama ya tura ƙofar, tana tsaye tana waya, ware idanuwa tayi tana ɗan sauke wayar daga kunnenta a hankali ta ce, 

“Yaya mana… Waya nake don Allah.”

Ƙarasawa yai ya kai hannu zai karɓi wayar ta janye. Kashewa ta yi tana kallon Labeeb kamar zata fashe da kuka. 

“Da wa kike waya?”

Ya buƙata yana tsare ta da idanuwanshi ranshi a ɓace. Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Ishaq.”

Ɗan ɗaga kai yayi. 

“Bana son sake jin kun je ko ina da shi. Banason sake jin ya zo wajenki a gidan nan. Karatu kike Zee Zee bana son duk wani abu da zai yi distracting ɗinki.”

“No Yaya… Please wallahi zanyi karatuna. I promise ba abinda zai yi distracting ɗina. Ka bari mu yi exams ka ga grades ɗina tukunna…”

Zainab ke roƙonshi, girgiza mata kai yake. Yana ganin hawayen da ke taruwa cikin idanuwanta, kafin su gangaro kan kuncinta. Hannu yakai zai goge mata yana tsanar shi ne ya sata kuka da kanshi. 

Ture hannunshi tayi, muryarta na rawa ta ce, 

“I like him…i really do Yaya.”

Wani abu ne ya tsaya mishi a wuya. Sosai yake kallon fuskarta. 

“Ka yi haƙuri…”

Ta furta tana rufe bakinta saboda kukan da ke shirin ƙwace mata. Ta rasa meye matsalar Labeeb ɗin haka. Me yasa yake son hana ta ganin Ishaq. 

Shi kaɗai yake rage mata damuwa da kewar da take ciki. Don ma su Asad basu cika fita ba saboda ita. Zasu zauna a gida kusa ko da yaushe suna ɗebe mata kewa ko da basu yi hira ba takan ji motsin su. 

“In yi haƙuri ba za ki iya abinda na ce ba ko me?”

Labeeb ya tambaya zuciyarshi na rawa ganin amsar ta tun kafin ta furta. Cikin kuka ta riƙo mishi hannu. 

“Yaya don Allah… I need you to be ok in dating ishaq… Karka ƙwace min damar nan…”

Yasan abinda ya kamata yayi. Muryarshi can kasa yace. 

“Da karatunki da Ishaq wanne kika fi so?”

“Su duka…”

Ta amsa tana kallon fuskarshi cike da tsoro don bata taɓa ganinshi haka ba. Bata taɓa ganin yanayin shi irin na yau ba. Kamar ba yayanta ba. 

Hannu yasa cikin aljihun shi ya zaro wayarshi. Zuciyarshi na wani zafi-zafi. In har tun yanzun Zainab ta zaɓi ta tsallake maganarshi saboda Ishaq nan gaba baisan me zai faru ba. 

Lambar Mummy ya dubo yai dialing yana addu’a ta ɗaga cikin zuciyarshi. Har sai da ta kusan yankewa tukunna ta daga da fadin. 

“Hello… Labeeb zan kiraka b…”

Bai bari ta ƙarasa ba ya ce, 

“No… Ba zan iya jira ba Mummy. Yanzun za mu yi magana.”

Jin ya ambaci Mummy yasa zuciyar Zainab tsinkewa. Sosai ta fara kuka, bata ɗauka abin yayi girma haka ba da har zai kira Mummy. Sakin hannunshi tayi ta koma kan gadonta ta zauna tana sharar hawaye. 

“Lafiya dai ko? Lafiyar ku ƙalau?”

Mumy ta tambaya da damuwa a muryarta. 

“Lafiyar mu ƙalau. Inason ki kira gidan su Ishaq. In da gaske yana son Zainab su yi magana da dady… Kar ya sake tako ƙafarshi gidanmu sai an sa ranar auren su da Zainab.”

Da mamaki Mummy ta ce, 

“Ranar aure? Ishaq? Labeeb kasan me kake faɗa min? Zainab ɗin duka nawa take? Ka bari jibi zan dawo mu yi magana.”

Girgiza kai Labeeb yayi. 

“In dai ba yau za ki dawo ba. Ko ki faɗa min inda kike ni in zo yanzun mu yi maganar nan a waya za mu yi ta Mummy.

Am not asking…kin bar min kula da Zainab tun bata iya wanka da kanta ba. Baki taɓa damuwa da duk hukuncin da na yanke akan ta ba. 

Baki taɓa saka min baki ba don Allah wannan ma ki barni. In har kina ganin na isa da Zainab za ki min abinda na roƙa Mummy. 

Wallahi hukuncin da zan ɗauka in na sake ganin shi kusa da ita mu duka ba zai mana daɗi ba.”

Wani numfashi Mummy ta ja da Labeeb ya ji shi har ta cikin wayar. 

“Alright zan kira Dadynka tukunna.”

“Zan kira shi da kaina yanzun. Ki kira gidansu Ishaq kawai.”

Labeeb ya faɗi yana kashe wayar. In ya zo maganar kula da ƙannenshi zaiyi abinda ya ga zuciyarshi zata nutsu. Ba zai taɓa sauraren kowa ba har mummy da kanta kuwa. 

In akanshi ne ba zai iya mata musu ba. Amma akan wannan maganar a shirye yake da yin komai. Da gaske yake baisan me zai yi ba in ya sake ganin Ishaq kusa da ƙanwarshi. 

Lambar Dady ya kira. Bugu ɗaya ya ɗaga suka gaisa. 

“Dady… Mummy zata kiraka zuwa anjima, ƙila za a zo neman auren Zainab….”

“Ma sha Allah. Toh Alhamdulillah, ikon Allah…”

Dady yake faɗi. Sosai ya ji daɗin maganar yai musu fatan alkhairi da sanya ma Labeeb ɗin albarka. Wayar Labeeb ya mayar cikin aljihunshi. 

Kallonshi Zainab take tana jin kamar komai a mafarki yake zo mata. Ƙarasawa yai ya zauna a gefenta. Cikin kuka ta ce, 

“Yaya ka ce min mafarki nake”

Kallonta yayi. 

“Idonki biyu… In ba aurenki zai yi ba ba na son sake ganin shi. Zan ɗauke ki daga ƙasar gaba ɗaya if i have to…”

Kuka ya sake ƙwace mata, kamata yai ya kwantar da kanta a jikinshi tana kuka sosai. 

“In suka turo fa Yaya? Me yasa za kai min haka? Bance maka aure nake so ba. Ban ma san ko ina sonshi ba. 

Duka watanmu nawa? Bansan ko yana sona ba, we… We are just getting to know junanmu.”

Sauke numfashi Labeeb yayi ya ɗago ta daga jikinshi. Yana tallabar fuskarta. 

“Zaku ko yi son juna bayan aurenku. Zee Zee banyi haka don in takura ki ba. Ba za ki fahimci dalili ba yanzun… Maybe nan gaba…wata rana ki gane. 

For now abinda nake so ki fahimta shi ne ina sonki… Ina ƙaunarki fiye da rayuwa da kanta. Ki yarda kome zan yi is for your own good. 

Don Allah ki yarda da ni, karki yi faɗa da ni akan wannan… Please.”

Ya ƙarasa muryashi na karyewa yana jin kamar ya goge ranar da Ishaq ya shigo rayuwar Zainab ya ja musu zuwan wannan ranar. 

Bai taɓa kawo ma ranshi faruwar hakan ba. Bai taɓa kawoma ranshi tunanin yima Zainab aure a shekaru ƙasa da sha takwas ba. Ko kaɗan bai hango ba, babu yadda zaiyi. 

Kare mutuncinta da darajar ta shi ne sama da komai a wajen shi. Yasan zuciyar shi fashewa zata yi in wani abu ya taɓata ta wannan fannin. Auren shi ne kwanciyar hankalin su gaba ɗaya. 

Mayar da kanta tai jikinshi tana ci gaba da kuka. Riƙeta yai kawai ba tare da ya sake cewa komai ba. Kuka tayi sosai har bacci ya ɗauketa. Gyara mata kwanciya yayi yana mata pillow da cinyarshi. 

Baya son barin ɗakin ya rasa dalili. Yana nan zaune kiran Mummy ya shigo wayarshi. Tambaya ɗaya tai mishi. 

“Sauran wata nawa semester ɗin nan tasu ta ƙare?”

Mummy ta tambaye shi. Tunani yake ko sun yi wata biyu da fara karatun su. 

“Sai dai in tambayi su Asad…”

“Barshi zan kirasu da kaina.”

Mummy ta faɗi tana kashe wayarta. Sauke numfashi labeeb yayi yana dan gyara zama. An kusan awa a tsakani Mummy ta sake kiranshi. 

Muryarta natural ta ce, 

“Zasu samu Dadynku gobe in Allah ya kaimu. Mun ma yi magana da shi, sai ka fara shirin auren ƙanwarka nan da wata huɗu tunda abinda kake so kenan!”

Buɗe baki yai zai yi magana Mummy ta kashe wayar. Yasan haushin shi take ji ko da muryarta bata nuna hakan ba. Don ma ishaq ya fito daga ɓangarenta shi yasa abin yazo da sauƙi. 

Yasan da daga wani waje ne. Da muguwar wahala Mummy ta amince da auren. Ɗan dafe kai labeeb yayi yana rasa abinda ya kamata ya ji. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 26Rayuwarmu 28 >>

1 thought on “Rayuwarmu 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.