Skip to content
Part 28 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Wayar Zulfa ya kira, bugu ɗaya ta ɗauka. 

“Yaya ina gida… Ban daɗe da dawowa ba.”

“Gani nan to.”

Labeeb ya faɗi yana sauke wayar, a hankali ya janyo pillow ya sauke kan Zainab daga jikinshi. Ya gyara mata kwanciya. Goshinta ya sumbata yana kallonta. 

Hangota yake tana ‘yar ƙaramar ta. Hangota yai lokacin da komai shi ne yake mata. Yana buƙatar wani ya faɗa mishi bai yi kuskuren hukuncin da ya yanke ba. 

A hankali ya ja mata ɗakin ya nufi na Zulfa. Ƙwanƙwasawa yayi ta ce mishi ya shigo. Yana shiga kujerar da ke cikin ɗakin ya samu ya zauna yana maida numfashi. 

Kallonshi Zulfa take tana nazarin damuwar da ke fuskarshi. 

“Menene?”

Ta buƙata. Kallonta yayi daya sata ƙarasawa ta zauna kan hannun kujerar. Hannunta Labeeb ya kama yana dumtsewa cikin nashi. 

In yana gaban Zulfa ne kawai yake jin yana buƙatar kulawa, yana buƙatar a lallashe shi. Ita kaɗai ke fito wa da wannan ɓangaren nashi. 

“Yaya menene? Ka sa gabana nata faɗuwa.”

Zulfa ta faɗi a raunane. Don sam bata son ganin shi cikin damuwa. 

“Wani abu nayi Zulfa… Bansan ko shi bane dai dai. Akan Ishaq da Zainab…”

Kallonshi take tana jiran ya ƙarasa. 

“Yau nasan suna dating. Nasa anyi maganar auren su, nan da wata huɗu zan aurar da Zainab… Wata huɗu Zulfa… She is still young…..am just… Kuma hankalina ya ƙi kwanciya.”

Hannunshi da ke cikin nata ta sake matsewa ganin duk yadda ya rikice. ‘Yar dariya yayi. 

“I am freaking out kuma ni na ce su turo.”

A nutse zulfa ta ce mishi,

“Ka duba zuciyarka yaya. Kana da dalilin yanke hukunci haka, in har zuciyarka na faɗa maka daidai ne to hakanne. 

Ba za ka taɓa yin abinda zai cutar da Zainab ba…aure ta kowanne fanni da tarin alkhairai a cikinsa in ba yazo da wata ƙaddarar ba.”

Jinjina maganar Zulfa yake. Nashi auren ya zo da ƙaddara, duk da haka ya bar mishi alkhairi mai girma a ciki. Sosai yake duba zuciyarshi yana ganin ta ko ina auren Zainab shi ne kwanciyar hankalin shi. 

Miƙewa yayi yana zame hannunshi daga cikin na zulfa. 

“I love you so much… Ban san me zan yi ba in babu ke.”

Murmushin ƙarfin hali tai mishi bata ce komai ba har ya fice, ta sauke numfashi kalamanshi na zauna mata a zuciya ta fannin da ba zai taɓa fahimta ba. 

****

Ɗakin su Asad ya nufa, ya fi son ya faɗa musu da kanshi. Suji maganar daga wajen shi. Da sallama ya tura musu ɗakin, Anees na zaune kan kujera yana karatu, Asad na kan gado da system ɗinshi a buɗe yana kallo. 

A tsaye ya ce musu,

“Ku fara shirin auren Zee Zee nan da wata huɗu.”

Su duka kallonshi suke kamar yaren Japanese ne ya fito daga bakinshi ba Hausa ba. 

“What?”

Ya tambaye su yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya. Asad ne ya ce, 

“Wasa kake ko Yaya?”

Girgiza kai yayi. 

“Da gaske, ita da Ishaq nan da wata huɗu in sha Allah.”

“What?!”

Suka tambaya su duka. Murmushi Labeeb yayi har haƙoranshi suka fito. 

“Yep.”

Ya faɗi yana juyawa da sauri ya bar ɗakin. Asad ya diro daga kan gadon yana bin bayan Labeeb. Anees na binsu shima. 

“Yep! Really Yaya… Wallahi ka dawo kai mana bayani yadda za mu fahimta.”

Asad ke faɗi yana bin Labeeb ɗin da sai lokacin ya tsaya. Ya kalle su su duka. 

“Wanne part ne baku fahimta ba?”

Ya buƙata yana ɗaure fuska. 

“Duka”

Anees ya amsa. 

“Auren Zainab da Ishaq. Auren Zainab da Ishaq…. Nan da wata huɗu… Wata huɗu.”

Labeeb ya faɗi musu dallah dallah yana ɗorawa da,

“Ko baku gane ba har yanzun?”

Sun gane me yake nufi ba dai su gane dalilin aure haka daga sama ba. Kuma cikin ɗan lokaci. 

“Ita ta ce tana so? Yaya kasan dai Zainab bata da hankali ko? Na ɗauka ba biye mata zakai ba… In sonta ya hana ka faɗa mata sai ta gama makaranta tukunna ni zan faɗa mata.”

Asad ya faɗi yana shirin wucewa, Labeeb ya dawo da shi. Muryarshi can kasa yace. 

“No Asad… Ba ita ta zaɓa ba. Ni ne zan mata auren.”

Cikin ɓacin rai Anees ya ce, 

“Yaya ka zama Mummy kaima. Kasan halin Ishaq ɗin? Wanne tabbaci kake da shi yana sonta? Auren da ake ta sako yara… Watan ka nawa da sakin taka matar kaima…”

“Anees!”

Labeeb ya faɗa cike da kashedi. Tambayoyinsu duka kan hanya suke. Bai da tabbacin komai, baisan me yake ba sai abinda zuciyarshi ta yarda da shi. 

Cikin kanshi yana jin kamar auren Kuskure ne. Amma zuciyarshi na faɗa mishi wani abu daban. Asad ne ya karɓe da faɗin, 

“Kasan ba ƙarya ya faɗa ba… You have to… You need to cancel maganar nan…”

Cikin tsawa Labeeb ya ce, 

“Wai meye haka? Na nemi ku faɗa min abinda ya kamata ne ko me? Hankali kuka fini ko son Zainab ɗin? Babu abinda zan yi calling off kuna jina. 

Ku dukanku should be ok with it. Auren Zainab nan da wata huɗu. In ba maganar shirye-shiryen auren nan za ku fara ba kunnuwana basa son jin wani abu daban. 

Kar in ga kowa kusa da ɗakinta. Bacci take yi.”

Bai son kallon da suke mishi su dukansu kafin su juya su koma ɗakinsu. Gaba ɗaya a gajiye yake jinshi. Abu ɗaya yake da tabbas, auren nan yinshi za a yi babu fashi. 

Shi ne nutsuwar kowa. Ɗakinshi ya nufa yana shiga ya faɗa kan gado ya kwanta. Ta wani fannin yana jinjina ma iyayen da ke zama tare da ‘ya’yansu ko da yaushe. 

Kula da yara ya fi komai wahala da gajiya. Ba abu bane mai sauƙi. Ba kowane zai fahimci abinda yake ji ba sai wanda yake cikin yanayi irin wanda yake a yanzun.

**** 

“Ina Zee Zeen?”

Asad ya tambayi Zulfa, ɗan ɗaga mishi kafada tayi. 

“Na yi da ita ta fito komai bata ce min ba.”

Sauke numfashi Asad yayi, yana duba agogon da ke hannunshi, biyar har da rabi, yasan mutane na can sun taru. Yau sati ɗaya kenan da tsaida sa ranar Zainab. 

Ita da kanta ta ce musu in aure za ta yi tana son komai daban da na kowa. Tana son bikin da ba’a taɓa kalarshi a family ɗinsu ba. Labeeb ya mata alƙawari in duka account ɗinshi zai ƙarar zai mata kalar auren da take mafarki. 

Su dukansu tun ranar suke busy. Lectures sai wanda ya zama dole suke zuwa, suna planning party ɗin sa ranar ta. Suna tura invitations da shirye shirye. 

Sai yau ranar kuma ta ƙi fitowa su tafi wajen da za’ayi party ɗin. 

“Ku je kawai zulfa. A fara komai don Allah, zamu taho yanzun.”

Kai zulfa ta ɗaga mishi ta wuce, Asad ya sauke numfashi don jinshi yake wani sama-sama. Gaba ɗaya kwalliyar da ta yi ta daburta mishi lissafi. 

Karo ya ci da Mamdud.

“Asad wai baku tafi ba? El-Maska sai kirana yake… Gab yake da exploding.”

Ɗan dafe kai Asad yayi. 

“Anees na can fa, Zee Zee ce bansan meye matsalar ba. Ta ƙi fitowa.”

“Bari in mata magana.”

Cewar Mamdud. Da shakku a idanuwan Asad yake kallon shi. Murmushi Mamdud yayi. 

“I got this…”

Ya tabbatar ma da Asad. Kai ya ɗan ɗaga mishi, tukunna ya wuce. Ɗakin Zainab Mamdud ya nufa, ƙwanƙwasawa yayi kafin ya tura a hankali. 

Zaune take kan gadonta, jikinta sanye da doguwar riga, fara da stones farare sai ɗaukar ido suke. Tayi kyau sosai, duk da kwalliyar fuskarta simple ce. 

Don ya sha ganinta da kwalliya fiye da ta yau. Sai dai bai taɓa ganin ta yi kyau irin na yau ba. Tun zuwanshi yake ganin ita da Arif sun fi kowa kyau a gidan. 

Sosai suke kama da Mumynsu. Takalmanshi ya cire sannan ya ƙarasa inda take ya zauna. Cikin sanyin murya ya ce, 

“Sis ana ta jiranki…ki taso mu tafi.”

Ɗan juyo kanta tayi ta kalle shi, muryarta na rawa ta ce, 

“Bansan me yasa nake jin tsoro ba Yaya Mamdud. Ina jin komai na tafiya da sauri, ina jin komai na auren nan kamar ba dai dai bane. 

Ni ba aure nake son yi ba yanzun, bansan me yasa Yaya yake so ya aurar da ni ba…”

Ta ƙarasa idanuwanta na cika da hawaye, don kwana bakwai ɗin nan sama-sama tayi su. Har wayarta kashewa tayi don bata son tai magana da Ishaq ɗin. 

Kawai so take ta jita shiru, tayi tunanin abinda auren yake nufi da rayuwarta. Komai data tsara ba haka yake tafiyar mata ba. 

Kallonta Mamdud yake yi. A zuciyarshi akwai wajaje fiye da uku da suke jin haushin Labeeb kowanne ɓangare kuma da nashi dalilin. 

Amma ko ina ya duba cikin zuciyarshi ƙaunar su Zainab bata da shakku. Yana jinsu har cikin ranshi. Musamman Arif, ƙaunar da yake ma yaron ba zata faɗu ba. 

“How about ki bar El da wannan tunanin? Ki raba mana rashin tabbas ɗin mu ɗaukar miki? Tunanin da za ki yi ya zama na kalar kayan da kike so a cikin gidanki ne. 

Kalar kayan da za ku saka wajen biki, ni da El da su Asad za mu yi tunanin auren nan shi yafi dacewa da ke ko a’a. Baki yarda da El bane?”

Da sauri Zainab ta ce, 

“Na yarda da shi.”

“Yauwa to menene zaki dinga damuwa? Ko ranar ɗaurin aurenki, ko an ɗaura in ya ga auren bai kamata ba zai sa a warware. Right now bana son kina duk wannan tunanin…ki tashi mu tafi don nikam bana son in yi missing komai na engagement party ɗin ƙanwata….come on ina sis ɗina da bata missing ɗin party?”

Dariya Zainab tayi tana miƙewa tsaye, sai take jin kamar Mamdud ya sauke mata wani nauyi da ke tare da ita. Yasa ta ji komai zai zo da sauƙi. 

Takalmanta ta saka a ƙafarta, Farar alkyabbar ta da itama sai ɗaukar ido take ta ɗauka ta saka a jikinta tana jan hular ta saka a kanta. 

Wayarshi Mamdud ya ɗauko daga aljihu yana murmushi, tayi matuƙar kyau. 

“You look like a Princess.”

Mamdud ya faɗi yana ɗaukarta hotuna. Dariya tayi. 

“Na gode… Muje Yaya Mamdud.”

Ta faɗi, kai ya ɗaga mata yana wucewa ya buɗe ƙofar ta fara fita sannan ya bi bayanta. Da kanshi ya buɗe mata bayan motar ta shiga ya zagaya ya buɗe mazaunin driver suka nufi wajen. 

**** 

Suna ƙarasawa wajen Mamdud yai parking ya fito ya zagaya ya buɗe ma Zainab bayan motar ta fito. Taron mutane komin yawansu bai taɓa sa ta zama nervous ko makamancin hakan ba. 

Zata iya cewa su dukansu kamar abin a jininsu ne. Ko gaban dubban mutane za ta yi magana hankalinta a kwance. Sai dai yau a karo na farko ta ji cikinta ya wani irin ƙullewa. 

Idanuwan mutane take ji na mata yawo a karo na farko. Da ƙyar ƙafafuwanta ke motsi. Suna shiga cikin wajen, ƙawatashin da akayi bai hanata jin kamar ta juya ba. 

Kalle kalle take kafin ta hango Ishaq. Koda zuciyarta bata son shi gaba ɗaya abinda take ji a kanshi bana wasa bane ba. Ɗaruruwan mazan dake wajen. 

Taron mutanen da ke zagaye da shi bai hanata ganin shi ba, asalima bata ganin komai kusa da shi banda shi ɗin da kanshi. Yanayi ne da bata taba tsintar kanta ciki ba. 

Zata iya cewa har da kewarshi da ta yi kwana biyu da ko waya basu yi ba. Tsaye ta yi sai da Mamdud ya ce mata,

“Go…ki je sis.”

Juyowa ta yi idanuwanta cike da tsoro. 

“Ka rakani bazan iya ba ni kaɗai.”

Ɗan girgiza mata kai Mamdud yayi, sosai ta ware mishi idanuwanta. 

“I need my brother…ka rakani ko in juya.”

Yasan zata iya, nauyin kalamanta guda huɗun farko sun zauna mishi a wajen da ba zata taɓa gani ba. Zuciyarshi ta taɓu da abinda ya gani. 

A idanuwan Zainab ba shi da banbanci da su Asad a wajenta, yau ta nuna mishi, tana buƙatar shi kamar yanda take bukatar su Asad a rayuwarta. Baisan yadda zai ɗauki hakan ba. 

Jikinshi a sanyaye suke tafiya har suka ƙarasa inda Ishaq ɗin yake, sannan Labeeb ya kama hannun Zainab ɗin yana janta inda zata zauna. 

“Me kuka tsaya yi haka?”

Yake tambayar su biyun. Ɗan kallon Ishaq Mamdud yayi kafin ya ce, 

“Ƙanwata ba kamar kowa bace.”

Hararar shi Labeeb yayi. 

“Shi yasa kuka busar da mu a nan kenan?”

Dariya Ishaq yayi. 

“She is worth it ai…kin yi kyau sosai.”

Ya faɗi yana mata wani kallo da yasa Labeeb jin kamar ya kai mishi naushi, kujerar Zainab ya ɗan ja kaɗan a hankali daga mannewar da ta yi da ta Ishaq kafin ta zauna. 

Bata ce komai ba har lokacin, kanta a ƙasa, Labeeb na kallo Ishaq ya ja kujerarshi ya manneta da ta Zainab kamar yanda yake farko, magana zai yi Zulfa ta ƙaraso wajen ta ja hannunshi. 

“Kin kyauta min kenan? Laifin me nai za ki kashe wayarki?”

Ishaq ya tambayeta ƙasa-ƙasa. Wani abu da ke tsaye a maƙoshinta ta haɗiye. 

“Ina buƙatar lokaci ne ni kaɗai.”

Sauke numfashi Ishaq yayi. 

“Kin san dai zan fahimta in kika yi min ko da text ne ko?”

Shiru tayi don batasan me zata ce mishi ba. Tana buƙatar lokaci ita kaɗai, takan yi hakan lokuta da dama. Ba zata fara bashi haƙuri kan abinda bata san ranar barin shi ba. Kamar yadda ba zata so yai mata ba. 

Duka awa biyu aka ɗauka ko Zainab ta ce ɗaya da rabi da zuwanta. Komai a nutse aka gabatar da shi. Tsayawa faɗar abubuwan da akai zai zamana ɓata lokaci. 

Sai dai ranace da ba zata mantu a wajen Zainab da duk wani makusancinta ba. Labeeb ya tabbatar da ranar ta zama fiye da mafarkinta. Suna tashi bata jira tai sallama da Ishaq ba. 

Rigarta ta tattare da gudu-gudu, sauri-sauri take neman Labeeb, hangoshi tayi suna hotuna da mutane, bata damu da su ba, da gudu ta ƙarasa inda yake tai hugging ɗinshi. 

Dariya yai yana fadin. 

“Zee Zee slow down… Za ki kayar da mu.”

Ɗagowa tayi hawayen farin ciki na zubo mata. 

“Thank you… Thank you for today.”

Fuskarta ya kama bai damu da mutanen da ke ɗaukar su hotuna ba. Ya goge mata hawayen da ke fuskarta. 

“Zanyi miki dubu irinsu in har za ki yi farin ciki. Ke kadai ce kanwata, farin cikinki na nufin komai a wajena.”

Murmushin da ta yi mishi har zuciyarshi. 

“I’m not even jealous…”

Cewar Asad da murmushi ya ƙi barin fuskarshi, hannu Zainab ta miƙa mishi tana dariya, kama hannun yayi yana ƙarasawa ta gefe yai hugging ɗinta. 

“Ina taya ki murna little sis.”

“Sau nawa za ka faɗa?”

Ta buƙata tana turo baki, dariya suka yi dai dai ƙarasowar Anees. Da kayanshi iri ɗaya ne da na Asad, askin kansu da suka banbanta ne yasa ‘yan gidan ke gane su yanzun. 

Suma ce sosai akan Asad, Anees kam tun rasuwar Sajda ya rage tashi sosai har yanzun kuma bai barta kamar ta Asad ba, ɗan ɗaga girarshi yayi duka biyun. 

“Family hug ne babu kira?”

“Abinda zan tambaya kenan nima.”

Cewar Arif daya ƙaraso wajen, ɗayan hannunta Zainab ta miƙa mishi, kamawa yayi yana miƙa ma Anees nashi, riƙe suke da hannun juna. 

Circle suka haɗa suna matsawa, kallo ɗaya za ka yi musu ka ga farin cikin da ke fuskarsu gaba ɗaya. Hakan abune da sukanyi tun kafin haihuwar Arif. 

Tun Zainab na ƙarama in tana rikici Labeeb kan kama su, su haɗa hannayensu duka su yi circle suna jujjuyawa har sai kukan da take yi ya koma dariya. 

Girman da suka yi yasa suka bar abubuwa da yawa, fuskokin su Anees Labeeb yake kallo, hakan na tuna mishi yarintar su, yana tuna mishi abubuwa da dama da baisan yayi kewa ba sai yanzun. 

Yayi kewar yadda suke buƙatar shi a komai da za su yi a rayuwar su. Yana kewar yadda Zainab zata daina buƙatar shi nan da watanni kaɗan tun kafin lokacin ya zo. 

Wani irin yanayi yake ji da ba zai faɗu ba. Ƙaunar ƙannenshi yake ji kamar ya cinye su. Asad ya soma juya su, sosai Arif ke dariya saboda hakan abu ne da bai taɓa gani ba. 

Mutane da suka soma tafiya suka ci gaba da dawowa suna kallon su, sai dai ko kaɗan basu damu ba, cikinsu babu wanda ya nuna alamar yasan da mutane ma a wurin. 

Tsaye Arif ya hango Mamdud a gefe. Kallon su yake da wani yanayi a ƙirjinshi. Dukkansu suna jin ƙaunar junansu, suna jin yadda suka haɗa jini. 

Ko sau ɗaya, ko sau ɗaya a rayuwarshi yake so ya ji ya kalar shaƙuwa irin wannan take. Ya za ka ji ka kalli mutum kasan jini iri ɗaya ne a jikinku. 

Shisa yake da burin tara yara da yawa, yadda baisan kowa nashi ba a duniya yana burin tara zuri’a. Ƙila mata fiye da biyu. Yana jinshi duk wani iri. 

Jin Arif na ƙoƙarin ƙwace hannuwanshi daga cikin na Anees da Asad ya sasu kallonshi, sakinshi suka yi, da gudu ya ƙarasa ya kamo hannun Mamdud daya juya da niyyar tafiya. 

Janyo shi Arif yayi yana faɗin, 

“Circle ɗin bai yi complete ba.”

Haka Mamdud ya bi shi har suka ƙarasa, matsawa suka sake yi don Mamdud ya samu waje kafin su sake haɗe circle ɗin. Ya rasa kalar yanayin da yake ji. 

Har suka soma juya circle ɗin yanayi Mamdud yake ji da ya kasa gane kalar shi. 

“Ku yi a hankali…”

Labeeb ke faɗi yana maida numfashi. 

“Kawai tsufa ya fara kama ka.”

Cewar Asad, daƙuna mishi fuska Labeeb yayi, sun jima a haka kafin su saki hannun juna kowa na maida numfashi, Zainab tsugunnawa tayi. 

Dariya suke yi. 

“Ku da baku fara tsufa ba kenan.”

Cewar Labeeb yana dariya. Da ƙyar Anees ke maida numfashi yana jin cikin shi na juyawa. 

“This was fun da muna yara. Ku tuna min na ce bazan sake wannan shiriritar ba.”

Dariya Zainab tayi tana miƙewa. 

“No way Yaya Anees, zamu sake ko Yaya Asad?”

Da sauri ya girgiza kai. 

“Karku lissafa da ni.”

“Ku duka kun tsufa ne yasa…”

Arif ya faɗi yana musu dariya, kafaɗar Mamdud Labeeb ya kama yana faɗin, 

“Ku wuce mu tafi…”

Hanyar waje suke nufa basu damu da mutanen da har lokacin suke ɗaukar hotuna da recording ɗinsu ba. Saboda Labeeb ne, in har hakan baya damun shi basu ga dalilin da zai dame su ba. 

Duka duniya su taru a wajen, ƙaunar da suke ma jun ta girmi komai a wajensu, suna hanyar fita ne Labeeb ya ce, 

“Cikinku wa ya bada idea ɗin saka zobe?”

Kallon juna Asad da Anees suka yi. Wani numfashi Labeeb ya ja. 

“Ku biyun nan… Bansan ya zan yi da ku ba. Wa ya ce muku al’adar mu ce? A ina aka ce tiƙeƙen ƙato ya kama hannun Zee Zee ya saka mata zobe?”

Shiru suka yi suna kallon Labeeb, tari Arif ya soma da ya maida hankalinsu kanshi. Hakan da ya gani yasa shi faɗin, 

“Ba cousin dinmu bane?”

“Sai hakan ke nufin me?”

Labeeb ya buƙata yana tsare shi da idanuwa. 

“Na dauka it’s normal ai don ya riƙe hannunta.”

Da sauri Labeeb ya girgiza ma Arif kai da faɗin, 

“No… It’s not normal ko kaɗan . Cousins ne amma aure zai iya shiga tsakanin su.”

Ɗan daƙun fuska Arif yayi. 

“Kana kama hannun Yaya Zulfa ko yaushe. That is weird…”

Cije leɓe Labeeb yayi yana raba idanu. Su Anees me za su yi in ba dariya ba. Labeeb na wani ɓata fuska yace. 

“Bana son shirme, ku wuce mu tafi dare nayi.”

Asad dariya har ƙwarewa yake, sai da Labeeb ya tallafe mishi fuska tukunna ya matsa gefe da sauri yana dariya. Haka har suka je gida suna dariyar Labeeb ɗin. 

**** 

Suna ƙauyen Ikara Labeeb ya ji kanshi na wani irin juyawa. Kamar zai yi amai haka yake ji, ga ciwon kai, kula yai hankalin mutane na kan part ɗin da ake shooting. 

Malfar shi da ke kan ƙafarshi ajiye ya ɗauka ya saka a kanshi yana ɗan janta ƙasa. Ya saka hannunshi cikin aljihun shi ya bar wajen. Motar shi ya hango ya ƙarasa inda take ya shiga ya ja ya ɗauki hanyar dawowa Kaduna. 

Hadari ne sosai a garin. Don har an fara iska. Labeeb bai ɗauka zai ƙaraso cikin Kaduna ruwa bai ɓalle ba, da ya ga alamu wani wajajen anyi ruwa. 

Kwanciya kawai yake son yi ko zai ɗan ji dai-dai. Tun jiya yake jin bashi da lafiya. Babu abinda ya iya saka ma cikinshi. Ko ƙamshin abinci baya son ji. 

Yayi niyyar biyawa Monarch don ya fi mishi kusa-kusa akan Dialogue ya fasa. Ba zai wuce stress ba kamar yadda yake faɗa ma kanshi. 

Bai tsaya ko ina ba sai da ya ƙarasa gidanshi. Don in ya je gida yasan su Zainab ba zasu barshi ba. Ko Zulfa saita sa ya je asibiti. Yana parking ya koma ya kulle gate ɗin sannan ya ƙarasa ya buɗe gidan ya shiga yana maida numfashi. 

Malfar da ke kanshi ya cire ya ajiye kan kujera tare da wayoyinshi da keys. Sannan Belt ɗin suspenders ɗin jikinshi ya kwance kasancewar yasan shi kaɗai ne a gidan yasa shi zare kayan anan falon. 

Daga shi sai boxers yake takawa zuwa kitchen ɗinshi. Fridge ya buɗe ya ɗauko robar coke. Bai bi takan kofi ba ya sha da bakin robar. Ya daure ya ajiye shi nan kan counter ɗin kitchen ɗin. Ya dawo falo. Wayarshi dake faman ruri ya ɗauka cikin buɗaɗɗiyar muryarshi da ta sake buɗewa ya amsa, 

“Mamdud yane?”

“Kana ina?”

Mamdud ya buƙata daga ɗayan ɓangaren. Ɗan murza goshin shi yayi yanayin shiru. 

“El-Maska kana ina? Ko baka jina?”

“Ina gida fa”

“What!”

Janye wayar daga kunnen shi El-labeeb yayi saboda ihun da Mamdud ɗin yai mishi cikin kunnen. Dama kanshi na ciwo.A hankali ya mayar da wayar yanajin yadda yake masifa da cewar,

“Wanne irin wulaƙanci ne mutane za su zauna jiranka. Kana sane da shooting ɗin nan fa ba…..”

Katse shi yai da faɗin, 

“Su yi wani abin daban. Ai holding nawa part ɗin. Kaina ciwo yake yi bacci zan yi.”

Bai tsaya jin masifar da Mamdud ɗin zai yi ba ya kashe wayar gaba ɗaya. Yana jan guntun tsaki. Sam baya son takura. Waje ya samu ya zauna a falon yana ɗan hutawa. 

Ya kai kusan mintina ashirin kafin ya miƙe. Bedroom ɗinshi ya wuce don ya watsa ruwa ya kwanta. Duhun da ke ɗakin bai sa shi kunna switch ɗin ba. Sosai kanshi ke ciwo ya ƙarasa kan gadon ya ɗan zauna ya huta tukunna ya shiga wankan. 

Yana zama ya ji ya zauna kan wani abu kamar mutum. Ƙara ya saki yana miƙewa. Ya tsorata ba kaɗan ba. Ba arziƙi ya lalubi switch ɗin ɗakin ya kunna.

Kwance take kan gadon tana ƙoƙarin kare idanuwanta daga hasken dake dakin. Lumshe idanuwanshi El-labeeb yayi yana ƙirga ɗaya zuwa goma cikin kanshi. 

Sa’adda ya buɗe su ya sauke kan yarinyar da ke kwance a ɗakin ta ma sake gyara kwanciyarta ta koma bacci. 

“Kutuma….”

Ya faɗi ranshi a ɓace. Ƙarasawa yayi kan gadon ya ɗauki pillow ɗin da ke gefe ya kwaɗa mata a baya. Miƙewa tayi tana yamutsa mishi fuska. 

“Ta ina kika sake shigowa? Wai ba ma nasa an canza min locks ɗin gidan nan ba.”

Murmushi tayi a kasalance wanda ya sake ɗaga mishi ɓacin ran da yake ji. 

“Meye abin dariya? Ban faɗa miki ‘Yansanda zan ɗauko miki ba in kika sake shigo min gida?”

A hankali ta miƙe. Ya bi fitsararriyar shigar da ke jikinta da kallo. Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Ban faɗa maka bacci kawai nake shigowa in yi ba? Godiya ya kamata ka yi min. Ko ba ka ganin gidanka a share? 

Yaushe rabon da ka ba flowers ɗin da ka ajiye ruwa? Yaushe rabon da ka sa a wanke maka toilets? Don nai bacci za ka min ihu.”

Ta ƙarasa tana raɓawa ta gefenshi ta wuce. Binta yayi da kallon mamaki, hartae kai ƙofa, ya bita da sauri ya sa hannu ya danne ƙofar da take shirin buɗewa. 

Yanayin da take kallonshi yasa shi jin wani iri saboda ƙarancin kayan da ke jikinshi. Ranshi ya gama ɓaci. 

“Babu inda zaki baki faɗa min ta inda kike shigo min gida ba, ban ma ji asalin me yake shigo da ke ba.” 

Muryarta na rawa ta ce, 

“Bacci nake yi kamar yadda na faɗa maka.”

“Na jiki, ban yarda bane kawai”

Ya faɗi. 

“Ta ƙofa nake shigowa. In ba ƙarya kake so in maka ba, bacci kawai nake in fita.”

Ta ƙarasa tana sauke idanuwanta daga cikin nashi. Lumshe nashi idanuwan Labeeb yayi yana rasa abinda ya kamata yayi. 

Gashi bayajin daɗin jikinshi, ba ma ya jin ƙarfin da zai ci gaba da magana. Sakin ƙofar yayi yana faɗin, 

“Bansan me zai faru in na sake ganinki anan ba. Na rasa meke shigo da ke ko ta yadda kike shigowa. Ki taimake mu dukan mu wannan ya zama na ƙarshe.”

Kallonshi tayi sosai da ya saka jikinshi sake ɗaukar ɗumi na daban. Wani ɓangare can ƙasan zuciyarshi so yake ya ce mata ta koma ta kwanta. 

Wani ɓangare so yake ya tsawata mata da kalar kayan da take sakawa. Baisan dalilin da ya sa hakan ya dame shi ba. Tunanin wasu mazan da abinda zasu fassara kayan da ke jikinta.

“Ka yi haƙuri.”

Ta faɗi tare da buɗe ƙofar ta fice tana ja mishi, kanshi da jikinshi ya jingina jikin ƙofar yana jin takun tafiyarta har ya bar ji, sauke numfashi yayi abinda yake ji na zamar mishi biyu. 

Jikinshi da nauyi ya ƙarasa kan gadon ya faɗa kai ya kwanta ruf da ciki yana jin kanshi kamar zai rabe gida biyu. Wata cida aka yi da ta sashi miƙewa ba shiri. 

Pillow ɗin da ke kan gadon ya janyo ya rungume jikinshi yana wata irin nutsuwa ta ban mamaki. Banda Zulfa babu wanda yasan tsoron tsawa yake ji kamar ranshi in ana ruwa. 

Kafin ya girma tsoronta yake ba tare da dalili ba. Yanzun kuma tsoron ya fi na da, sai zunuban shi su yi ta dawo mishi ya ga kamar tsawar zata faɗo akanshi ne duk idan an yi ta. 

Ruwa ake mai ƙarfin gaske. Sakkowa yayi daga kan gadon gabanshi na faɗuwa tunanin ko mintina biyar da fitar yarinyar nan ba ayi ba ruwan ya tsuge. 

Baisan me yasa yake jin duk babu daɗi ba. Shirin fita yake daga bedroom ɗin zuwa falo ya leƙa ya ga ko ta tafi ko tana nan ya ji an sake wata tsawar. 

Jikinshi babu inda baya ɓari ya koma kan gadon ya ja duvet ya rufe har kai yana dunƙule jikinshi waje ɗaya yana jin ina ma yana gida ne. 

Ko ba komai yasan ba shi kaɗai bane cikin gidan. Neman ciwon kan da yake ji yayi ya rasa. Tsoron da yake ji ya danne komai.

****

Farkon layin ya ce Jamal ya sauke shi ya wuce kawai don Mamdud ya ga hadarin ya haɗu sosai-sosai. Kawai so yake ya ƙarasa gidan in Labeeb na nan kenan ya sauke mishi ta cikinshi.

Haka yake gudu ya barshi yaita fama da mutane. Bayan ya karɓar musu kuɗi, shi kanshi tsawar da akai sai da ya ji ta har cikin cikinshi, gudu ya soma ganin ruwan ya sauko gaba ɗaya. 

Yana ƙarasawa ƙofar gidan idanuwanshi suka sauka kanta, tsugunne take ta haɗe jikinta waje ɗaya, bata yi kokarine kare jikinta ba, ko kokarine tashi ta nemi wajen fakewa ko ta nufi gida. 

Tsugunne take hankalinta kwance ruwan na sauka akanta, ko fuskarta bata sa hannu ta kare ba, sai rawar sanyi da take yi. Tunda Mamdud yake a rayuwarshi bai taɓa ganin mace me kyanta ba. 

Bai taɓa ganin macen data saka zuciyarshi shiga yanayi irin yarinyar da ke rakuɓe gefen gidan Labeeb ba. Babu tunanin komai banda nason taimaka mata ya ƙarasa. 

“Sannu…”

Ya faɗi don ya rasa abinda ya kamata ya ce mata. Duk ya daburce. Idanuwanta ta ɗago ta kalle shi kafin ta maida su ta sauke. 

“Ina za ki haka? Ba kya tunanin ruwan nan yai miki wani abu? Taso mu shiga ciki in ya ɗauke sai ki tafi.”

Sai bayan da yai maganar ya ga wautar abinda ya faɗi. Bata sanshi ba, bata taɓa ganin shi ba, zai ce ta bishi su shiga ciki, komai zai iya zuwa zuciyarta. 

“Kin ga na san baki sanni ba, yarda da ni zai miki wahala, ba sai kin bini cikin gidan ba, amma ki fito daga ruwan nan ko ɗakin maigadi sai ki fake.”

Sai da Mamdud yai tunanin ko bata gane me yake cewa ko kuma ta zaɓi ƙin yarda da taimakon shi ne kafin a hankali ta miƙe, tayi sharkaf, kayan jikinta manne da jikinta. 

Karo na farko Mamdud yaga mace a yanayin da take ya ɗauke idanuwanshi. Bai kuma san dalili ba, babu abinda yake so daya wuce bata abinda zata lulluɓe jikinta. 

Gaba ya shiga, motar Labeeb ya hango. Ya sauke numfashi, hannu ya sa a aljihunshi ya ciro mukullai. Ya gode ma Allah da tunda aka sake locks ɗin gidan da baisan dalilin Labeeb ba yake yawo da mukullan. 

Buɗe gate ɗin yayi ya soma shiga tukunna ita ma ta shiga ya kulle, ba don ita ba da da gudu Mamdud zai ƙarasa don sanyi yake ji sosai. 

A hankali yake tafiya yana tabbatar da tana biye da shi, baya son sake kallonta saboda yanayin kayan da ke jikinta. Suna ƙarasawa bakin ƙofa ya buɗe gidan ya shige. 

Ita ma ta shiga tai tsaye gefe ta rakuɓe, kulle ƙofar Mamdud yayi. 

“Bari in samo miki wasu kayan…”

Ya faɗi bai jira amsarta ba da gudu ya nufi ɗaya daga cikin bedrooms ɗin. Nan ƙasa ya cire kayan jikinshi tas, sannan ya nufi wardrobe ya buɗe ya samu riga da wando ya saka. 

Duba kayan da zai ba yarinyar yayi ya rasa. Wata jallabiya ya hango ya janyo ta ya fito falon tana tsaye inda yabarta. Miƙa mata rigar yayi ta girgiza mishi kai, idanuwanta na cika da hawaye. 

“Ba za ki zauna da kayan nan ba, sai su saki ciwo. Ki sake don Allah a shanya ya bushe kafin ruwan ya ɗauke.”

Mamdud yake roƙonta, yadda ya damu da ita lokaci ɗaya haka na bashi mamaki. Rigar ya ajiye mata ya juya ya nufi wani daga cikin bedrooms ɗin ko Labeeb na ciki. 

Ya tura ya shiga, aikam a ƙudundune ya samu Labeeb ɗin kan gado, pillow ya ɗauka ya kwaɗa mishi. 

“Dilla fito to”

Kanshi Labeeb ya buɗe ya kalli Mamdud. 

“Go away.”

Ya faɗi yana maida duvet ɗin ya rufe, duka Mamdud ya kama ya buɗe shi. 

“Kawai sai ka barni da mutane? In tahowa za ka yi me yasa ba zaka tsaya kai musu bayani da kanka ba?”

Sauke numfashi Labeeb yayi. 

“I am sorry. Bazan iya tsayawa bane ba, bana jin daɗi gaba ɗaya shi yasa. Wait ba dai cikin ruwan nan ka taho ba?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Mamdud yayi. 

“Jamal ya sauke ni, har na ga wata yarinya ma a ƙofar gidan nan. Mtsww ka ga yadda ta jiƙe. 

Tana falo ma.”

Ware idanuwa Labeeb yayi yana jin zuciyarshi ta doka.

“Menene?”

Mamdud ya buƙata, girgiza mishi kai Labeeb yayi yana sakkowa daga kan gadon ya nufi hanyar ƙofa. Riƙo shi Mamdud yayi da sauri. 

“Ƙara bata minti biyar ko tana sake kaya ne.”

Sake ware idanuwa Labeeb yayi. 

“Yaushe ka zama decent haka? Yaushe idanuwanka suka musulunta?”

Ɗan murmushi Mamdud yayi. Shi ma bai sani ba. Kawai banda wannan yarinyar. Komai nata daban ne yana ji a jikinshi. 

Dole suka tsaya shi da Mamdud ɗin na wasu mintina kafin su fita tare, tana tsaye da zundumemiyar rigar Mamdud a jikinta. 

Tunda Labeeb yake bai taɓa zaton haka jallabiya take da kyau ba sai da ya ganta sanye jikin yarinyar nan. Mamdud kam bai taɓa ganin wanda jallabiya taima kyau irinta ba. 

Murmushi ne a fuskarshi, Labeeb kuma babu walwala a tashi fuskar. Ƙarasawa Mamdud yayi inda take tsaye, a tsorace ta ɗan matsa. Sai ta ga ya tsugunna ya ɗauki kayan da ta cire ya wuce. 

Binshi a baya Labeeb yayi har bedroom ɗin, ya ganshi a toilet yana matse kayan yana shanyawa. Jingina yayi da bangon toilet ɗin cikin sanyin murya ya soma faɗa ma Mamdud komai daya sani kan yarinyar daga ranar da ya fara ganinta ya ɗauka aljana ce. 

Har zuwa ɗazu da ya koreta. Cike da mamaki Mamdud ya ce, 

“I am speechless.”

Kai Labeeb ya jinjina. 

“Abin yana ɗaure min kai, na kasa figuring ɗinta out. Ka ga har kuɗi nake da su a cikin gidan nan bata ɗauka ba. 

Bata ɗaukar komai, farko na ɗauka stalker ce, amma babu alamun ta sanni a fuskarta ma.”

“Akwai dai wani abun daban, amma da mamaki gaskiya. Ni ka tsorata ni ma wallahi.”

Dariya Labeeb yayi, yana jin zazzaɓin da ciwon kai na dawo mishi. 

“In an ɗauke ruwan nikam I want her out.”

Kai Mamdud ya ɗaga mishi. Yana ƙarasa shanya sauran kayan ya fita, tana zaune can ƙarshen falon kan tiles ta takure jikinta, kitchen ya nufa ya ɗauko coke ya ɗauko mata fanta da kofi ya taho. 

Zama yayi gefenta ya buɗe fantar ya zuba mata a kofi ya miƙa mata. Kai ta girgiza mishi, ɗauka yai ya kurɓa. 

“Babu abinda na zuba, kinga na sha ai.”

Hakan da ya faɗi ya sa ta yin murmushi kaɗan. 

“Na san ba cutar da ni za ka yi ba.”

Ta faɗi muryarta na sauka kunnenshi da wani sanyi. Ji yake kamar dama can yasan yarinyar nan. Yadda yake jin zamanta a zuciyar shi kamar ba mintina kaɗan yayi da saninta ba.

“Me yasa ba za ki sha ba?”

Cikinta da ya yi ƙara ya bashi amsa, sadda kanta ƙasa tayi a kunyace. Mamdud kuma ya miƙe ya nufi kitchen, cake ya samo mata da ƙyar sai apple guda uku daya ɗibo. 

Ba abinci suke ajiyewa ba in ba daga waje suka siyo ba. Ya dawo ya miƙa mata. Karɓa tayi ya ga dai bata ci ba. 

“Ko in tashi ki ci?”

Ya buƙata, a hankali ta ɗan ɗaga mishi kai, miƙewa yayi ya koma cikin falon sosai ya samu kujera ya zauna ya bata baya zuciyar shi na wani irin dokawa. 

So yake ya juya ko sau ɗaya yaga yanda take taunar cake ɗin amman ba zai iya hakan ba saboda ya fi buƙatar ta ci fiye da yadda yake son ya kalle ta. 

Sai da ya bata mintina sama da sha biyar sannan ya juya, sauran apple ɗaya a hannunta. Tashi yayi ya koma ya zauna a gefenta. 

“El-Maska yace min ya sanki, kina shigowa gidan nan.”

Da sauri ta kalle shi idanuwanta cike da tsoro da ya sashi faɗin, 

“Kwantar da hankalin ki. Babu abinda za mu yi miki. Me yasa kike shigowa?

Muryarta na rawa ta ce, 

“Na faɗa mishi. Wallahi bana taɓa muku komai. Bacci kawai nake yi.”

Da mamaki Mamdud yace. 

“Gidanku fa?”

Shiru tayi ya sake maimaitawa bata ce komai ba. Ya rasa me yasa yake son jin labarinta. 

“Kinyi shiru. Ya sunanki?”

“Ateefa…”

Ta faɗi muryarta can ƙasa. Maimaita sunan Mamdud yayi yana jin yadda ya zauna mishi a laɓɓanshi. 

“Me yasa ba zaki kwanta a gidanku ba? Inda gidan wasu mugayen ne fa?”

Shiru tayi tana zubar da ƙwallar da yake jin kamar yasa hannu ya goge mata.

“Komai zai iya faruwa. Da yaso zai kira miki ‘Yansanda, ko ya sa ai miki wani abu. In taimako kike buƙata bazan iya taimaka miki ba sai kin faɗa min wani abu. 

Shirun ki ba zai yi amfani ba Ateefa. Kiyi magana don Allah.”

Mamdud ke faɗi, fitowar hawayenta ne suka ƙara sauri. Muryarta na sarƙewa ta ce, 

“Bana samun yin bacci a gidan mu shi yasa. Bansan me yasa na shigo muku ba, kuyi haƙuri don Allah.”

Sauke numfashi Mamdud yayi. 

“Ina mamanki? Babanki fa?”

Da wani yanayi a muryarta ta ce, 

“Banda ko ɗaya daga ciki!”

Har cikin zuciyarshi ya ji maganganunta. Har cikin jikinshi ya fahimci halin da take ciki. Har cikin tsokar jikinshi yake son taimaka mata. 

“Na fahimta.”

Ya faɗi yana jin wani ɗaci na daban. Murmushi tayi na takaici ta sa hanunta tana goge hawayenta wasu na zubowa. 

“Uhm bana jin akwai wanda zai taɓa iya fahimta.”

Da sauri yace.

“Idan na ce miki banda ko ɗaya cikin mahaifana fa? Za ki yarda?”

Girgiza kai tayi. 

“Ba kamar ni ba. Nawa yanayin ya zo daban ne.”

Kallonta Mamdud yake, da son taimakonta akwai wani yanayi na daban tare da shi. So yake ta gane ya fahimci halin da take ciki. 

Yana jin irin ciwon da take ji amma tana ganin kamar nashi mai sauƙi ne. Yarda da ita ya ji a zuciyarshi lokaci ɗaya. Banda su Labeeb da babu mai tada mishi maganar asalin shi babu wanda ya taɓa faɗa ma. 

Sai ita yanzun da yake so ta gane ƙila nata mai sauƙine. Hakan yasa shi faɗin, 

“Karki yanke min hukunci baki ji nawa ba. Buɗe ido nayi na ganni a gidan marayu. Daga labarina da na sani yar da ni aka yi wani ya tsinta ya kai ni can. 

Bansan asalina ba, bansan me yasa baibarni nan na mutu ba. Akwai lokuta da dama da na yi roƙon in mutu da kaina saboda rayuwa ta yi min wuya. 

Kowa na gani a titi kallonshi nake, kallonshi nake ko zan ga kamanni, in ka cika kallona zuciyata zata fara roƙo da fatan za ka gane ni ka ce kasan ‘yan uwana. 

Banda kowa a duniya da zan kalla in ce jinina ne Ateefa. Karki yanke hukunci kan abinda baki sani ba…”

Mamdud ya ƙarasa yanajin ƙirjinshi kamar zai faɗo saboda ciwon da yake yi. Raunuka ne na shekaru da zama da su Labeeb ya ɓoye. Yanzun da kanshi ya sake buɗe su. 

Tunda ya buɗe baki ya soma magana kukanta ya tsananta. Sosai Ateefa take kuka tana kallonshi. Muryar shi da rauni Mamdud ya ce,

“Ina son taimakon ki duk da yau na fara ganin ki. Ina son jin meke faruwa da ke. Don Allah ki faɗa min.”

Ɗagowa ta yi ta kalle shi, sabbin hawaye na tarar mata a idanuwa, sai da tai kamar ba zata ce komai ba kafin ta buɗe baki da wani nisantaccen yanayi ta ce, 

“Kamar yadda na faɗa maka… Sunana Ateefa. Tunda na tashi a gidan da nake ɗauka na iyayena ne na gane ina da banbanci da sauran ‘yan gidan. 

Kalmar shegiya da ita kunnuwana suka soma buɗewa. Da kuma iya duk wani na gidan banda Baba da Yaya Musty suke jifana da ita a duk damar da suka samu. 

Ba ƙarya suka yi ba, ni ban zaɓi in zo a haka ba. Kafin in sani na ɗora laifin akan Mamana ne, sai daga baya na fahimci ‘yan fashi ne suka shigo gidanmu suka mata fyaɗe tana da shekaru sha shida a duniya. Babu wanda bai so ta zubda cikina da aka gane tana dashi ba ta ƙi. Wanda a tasowa ta naji dama ta ɗauki shawararsu. Babu rai a jikinta aka yi tiyata aka ciro ni. 

Aka cironi cikin duniyar da babu komai sai rashin adalci, ba laifina bane, ba laifin Mamana bane. Mutuwarta shi ne hutunta, bansan me yasa nake biyan zunuban da Ubana ya aikata ba. 

Kasan sau nawa na yi tunanin kashe kaina? Sau babu adadi, duk wanda zai zo neman aurena yana jin asalina yake gudu da kanshi. 

Wa zai auri ‘yar ɗan fashi? Ɗan fashin da babu wanda ya san duniyar da yake…”

Ateefa ta ƙarasa wasu hawaye masu ɗumi na zubo mata. Kallonta Mamdud yake yana jin sauƙi-sauƙin yadda ya taso. Gaba ɗaya gidan marayun babu mai mishi kallon ƙyamata. 

Baisan kowa nashi ba balle gorin da za su yi mishi yai masa ciwo. Ta wanni fanni rayuwa ta zo mishi da wannan adalcin. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Ina Baba?”

Wata dariya Ateefa tayi cikin kukan da take. Tunda Mamdud yake bai taɓa jin dariya kalarta ba. Babu wani nishaɗi a ciki. Kamar kiran sunan Baba da Mamdud ɗin yayi ya sa komai dawo mata. 

Shekaru biyu kenan. Shekaru biyu cif masu raɗaɗi da ciwo, masu ƙunci da ba zata manta ba. Kallon ranar da komai ya fara Ateefa take yi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 27Rayuwarmu 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.