Skip to content
Part 29 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Kwana biyu da Baba ya bata wasiƙun da Mamanta ta bar mata guda biyu kafin rasuwarta. Kwana biyu da hargitsewar komai na rayuwarta.

Kwana biyu da sanin wacece ita. Tayi kuka kamar ranta zai fita. Kukan da babu wanda ya lallashe ta banda Yaya Musty. Babu wanda ya damu da tana yi banda shi da Baba.

Ranar ta lallaɓa ta je makaranta, tana aji shida. Tana dawowa ta ga su Hauwa na tsaitsaye a ƙofar gida ita da Fadil suna kuka. Tun kafin tasan abinda ke faruwa ta ƙarasa wajen su hawaye na cika mata idanuwa.

“Hauwa me ke faruwa?”

Ta buƙata, harara Hauwa ta watsa mata tana ci gaba da sharar hawaye. Fadil Ateefa ta kalla, zata mishi magana ta ga Yaya Musty da wani abokinshi sun kamo Baba, Hajja ta biyo bayansu tana kuka.
Batasan lokacin da ta yarda jakarta ba, da gudu ta ƙarasa inda suke tana faɗin,

“Baba! Baba!! Yaya Musty me ya samu baba?”

Bai ce mata komai ba sai da aka buɗe mota aka shiga da Baba ciki tukunna. Kama hannunta Yaya Musty yayi.

“Ki kwantar da hankalinki. Ba shi da lafiya ne, asibiti za mu je yanzun, ku koma gida muje mu dawo.”

Kai kawai ta iya ɗaga ma Yaya Musty har suka shiga motar suka tafi. Sai lokacin ta ɗauki jakarta ta koma ciki. Ko abinci bata ci ba. Yaya Musty kaɗai ya dawo ya faɗa musu an kwantar da Baba.

A cewar likitoci stroke ne ya same shi. Sosai suka ci kuka ranar. Su kaɗai suka kwana a gida.

Washegari kamar yadda Ateefa ta saba ita ta yi dukkan ayyukan gidan.

Ta haɗa kayan kari da Yaya Musty ya zo ya tafi da su asibiti. Roƙonshi tayi da ya je da ita ta ga Baba.

Ya lallaɓata dan Hajja ta mishi kashedi kar ya sake ya kwaso musu shegiyar nan ya zo da ita.

Ateefa na kallo da yamma Fadil da Hauwa suka shirya suka tafi. Ta ci kukanta ta haƙura. Ita kaɗai ta zauna gidan har Isha’i. Ganin sun dawo suna kuka yasa ta tambayarsu ya Baban amma babu wanda aka samu ya ko kalleta balle ya amsata.

Haka ta ƙyale su. Ranar ko ɓarawon bacci bai sace ta ba. Sai da Asuba, tana idar da sallah. Ihun kukan Hajja ya fito da Ateefa daga ɗakin da gudu.

Tasan tashin hankali kala-kala a rayuwarta amma bata taɓa sanin makamancin wanda ta ji lokacin da aka shigo da gawar Baba cikin gidan aka shimfiɗe ta ba.

Kallon gawar take, lokutan da ya sha ɗagata tana kuka yake share mata hawayenta take tunawa. Lokutan da Hajja ta hana ta abinci ya ɗauki nashi ya bata.

Lokacin da babu abinda ya hana ta sha fiyafiyar da ta siyo sai kalamanshi. Irin lokutan nan take tunawa. Bata san menene sauƙin rayuwa babu Baba a cikinta ba.

Bata san me yasa mutuwa ke da rashin adalci har haka ba. Tana buƙatar Baba, Baba shi ne komai da ta rasa a rayuwarta. Baba kan sa ta ji tabon da ke manne da ita na mata sauƙin kallo a kullum.

Wani shiru take ji cikin kanta, tana kallon hatta Yaya Musty na wani irin kuka. Ganin babu mai wani ƙwari yasa Ya Musty kiran Ateefa.

Da ita aka kama gawar Baba aka shigar da ita ɗakin shi. Ita yasa ta haɗa ruwan da duk abinda ake buƙata ta kai mishi ɗaki don yaima Baba wanka.

Ko da aka kawo likkafani, hatta da zare da allurar da akai amfani da su aka ɗinka Ateefa ce ta zura zaren cikin allura ta miƙa. Har aka gama haɗa Baba tsaf.

Ita kaɗai aka bari da gawar suka fita shigowa da makara. Kallonshi take yi kwance tana ganin kamar zai motsa. Baba mutumin kirki, mutum mai kazarniya.

Mutumin da bata taɓa ganin ɓacin ranshi ba. Dole stroke ya kamashi lokaci ɗaya. Sosai take kallon yadda aka naɗe shi tsaf. Tana tunanin ita kanta lokaci take jira ai mata haka.

Gani tayi an shigo da mwkara an ɗauki Baba an saka ciki, sai lokacin take ganin da gaske ne. Da gaske Baba za a je a saka a kabari. A rufe shi, da gaske wannan ita ce ranar ƙarshe da zata sake ganin shi.

Wani gunjin kuka Ateefa ta saki tana zuwa ta kama makarar ta riƙe. Kuka take tana fadin.

“Don Allah ku ƙara jira ko zai motsa… Wallahi banda kowa sai shi, banda inda zan ji sauƙi in babu shi… Rayuwata ta ƙare in kuka fita da shi daga gidan nan.

Baba karkai min haka, Baba ka tashi, ina zan kai tabon shegiya da kowa yake kallona da shi in baka nan? Baba kaine ubana, kaine komai nawa… Wayyo Allah na… Baba… Don Allah ku tsaya.”

Kuka take kamar zata shiɗe, har Yaya Mufty duk dauriyar da yake sai da ta sa shi kuka, Yaya Musty ya zo ya kamata da ƙyar ya ɓamɓareta daga jikin makarar.

Duka take kai mishi.

“Yaya Musty ya za ka bari su tafi da shi? Don Allah ka ce su ɗan tsaya, ƙila zai tashi… Wallahi bansan inda zankai rayuwata in babu shi ba…wai me yasa ku duka ba ku da adalci ne?”

Riƙeta Yaya Musty yayi sosai, shi ma kuka yake yana faɗin,

“Ateefa ya rasu, ba zai tashi ba. Baba ya rasu.”

Kuka suke yi tare, nan ya barta Kwance suka tafi kai Baba. Kwana ukun da suka zo bayan nan a gigice suka wuce mata.

****
Ɗan taɓata Mamdud yayi ganin ta ƙura ma waje ɗaya ido tana ta zubda hawaye. Sai lokacin ta kalle shi tana jin wani ɗaci a zuciyarta.

Zafin mutuwa daban yake. Babu wanda zai taɓa fahimta sai wanda aka taɓa. An ce yakanyi sauƙi a hankali, amma ita duk sa’adda ta tuna sabo take jinshi.

Hawayenta ta goge sannan ta ce mishi,

“Ya rasu…”

Shiru Mamdud yayi. Duk lokacin da kake tunanin taka rayuwar na da wahala sai ka ci karo da wanda tashi jarabawar in aka miƙo maka ko kwana ɗaya ba za ka iya yi a cikinta ba za ka gaza.

Da gaske ne Allah baya taɓa ɗora maka abinda ba za ka iya ɗauka ba. Sai dai addu’ar imani kawai. In Allah ya ɗora maka ya baka Imani da ƙarfin jurewa.

Miƙewa Mamdud yayi ya ɗauko ruwa ya zuba mata a kofi yana jin kamar ya ɗauketa su ɓace zuwa wata duniyar inda babu wani abu da zai sake taɓa ta har ƙarshen rayuwarta.

Sosai ta sha ruwan. Baya son sake tambayarta wani abin kuma. Ya isa haka na yau. Don yana ji a jikinshi fiye da ɗazu, yau ba shi bane ƙarshen haɗuwarsu. Ƙaddarar da ta haɗa su mai girma ce.

*****

Labeeb da ke tsaye bakin ƙofa dukkan maganganun su akan kunnenshi suke yi. Ji yai gaba ɗaya sun ƙara mishi rashin lafiya.

Musamman Mamdud, baya son damuwar shi ko kaɗan. Ya kuma ji ciwo ba kaɗan ba da Mamdud ya ce ma Ateefa ba shi da kowa a duniya bayan yana da su.

Fita ya ƙarasa yi daga ɗakin. Lokacin ruwan ya soma ɗaukewa. Ateefa na ganinshi ta miƙe tana faɗin,
“Yamma na yi, ina kayana zan koma gida.”

Inda Labeeb ya fito ya nuna mata, da sauri ta wuce. Magana Mamdud zai yi yadda Labeeb ya nuna yasa shi yin shiru. Sai da ya juya ya ga Ateefa ta shige tukunna ya kalli Labeeb.

“Bansan ji kake kamar ba ka da kowa a duniya ba sai yau. Ashe ba ka da kowa ban sani ba?”
Ɗan dafe kai Mamdud yayi zai yi magana Labeeb ya ɗaga mishi hannu.

“Na ji abinda nake buƙatar ji, she is welcome duk sa’adda take da buƙata. Sai in faɗa ma su Zainab su canza zaman su da kai ko za ka soma jin kana da ‘yan uwa.”

Yana ƙarasawa ya nufi hanyar fita daga gidan. Kiranshi Mamdud yake bai ko juyo ba ya fice daga gidan. Zai bishi ya ji maganar Ateefa.

Dole ya fasa. Yana jin tashin motar Labeeb ɗin,

“Ba ka faɗa min sunanka ba.”

“Mamdud… And za ki iya dawowa duk sa’adda kike so. Ki ci duk abinda kike buƙata.”

Kai ta ɗan ɗaga mishi.

“Na gode sosai. Zan tafi.”

Ɗan ɗaga mata hannu yayi ya komawa ɗaki da sauri, babu kuɗi a jikinshi, dubawa yai, dubu huɗu kawai ya gani ya ɗauko ya dawo.

Bama Ateefa yayi.

“Ki riƙe a hannunki kina siyan wani abu in kina buƙata.”

Idanuwanta cike da hawaye ta ce,

“I can’t.”

“Yes you can and you will. Ki karɓa don Allah.”

Karɓa ta yi. Tare suka fita daga gidan. Ana yayyafi sama-sama har lokacin. Sai bayan ya tare mata mashin ta hau ta tafi ne yana kulle gate ɗin gidan yayi tunanin bai ko tambayi address ɗinta ba.

Gashi har sun ɓace ma ganinshi. Mashin ya tare yana ji a jikinshi zata dawo. Gida ya nufa don tunda yake bai taɓa ganin ran labeeb ya ɓaci irin na yau ba.

Bai zata yana jin me suke faɗa ba. Kuma gaskiya ya faɗi. Labeeb ba zai taɓa fahimta ba. Suna ƙaunarshi, shima kuma yana ƙaunar su. Amma iya tasu ƙaunar bata isa cike mishi gurbin da ‘yan uwanshi na jini suka bari ba.

Wannan waje ne da babu wanda zai cike shi. Ƙila wata rana inyai aure ya haihu ya ga yaranshi. Wanda suka fito daga jikinshi ya ji wajen ya cike.

Baima damu da jin Labeeb ɗin ba kamar yadda ya damu da su Asaad su ji kome ya faɗa. Baya son duk abinda zai taɓa su har ranshi. Da wannan tunanin ya ƙarasa gida.

*****

Yana sallama a falon su dukansu ya samu zaune banda Arif, idanuwa suka zuba mishi. Kafin a hankali Zainab ta amsa sallamar.

Ƙarasawa yayi ya zauna kusa da Asad yana kallo ya matsa gefe. Shirun ne yaima Mamdud yawa.

“Guys! Seriously?”

Ya faɗi yana kallon su.

“Da kai yake magana”

Anees ya faɗi, ɗan ɗaga mishi kafaɗa Asad yayi yana ci gaba da latsa wayar shi.

“Sis har ke ma?”

Miƙewa Zainab tayi.

“Wallahi bansan me zance maka ba Yaya Mamdud… I am so mad kana shigowa i feel like punching you. Haka kake faɗa ma kowa? Haka kake cewa baka da kowa? Me za mu yi to make you feel yadda muke ji a kanka?

Asibiti kake so mu je a ɗibi jinin kowa a saka a jikinka a ɗiba naka a saka a namu? I’m……. Oh Allah!”
Ta ƙarasa ta miƙe ta wuce ɗakinta tare da doko ƙofar da ƙarfi. Anees ma miƙewa yayi yana nufar hanyar nasu ɓangaren.

Kafin Asad ya sauke numfashi shima ya miƙe da faɗin,

“I feel useless yau ɗin nan. Kamar… banma san me zance ba.”

Labeeb da ke kwance cikin kujera Mamdud ya kalla, yana rasa ko me yake ji akan abinda ya faru yanzun. Zuciyarshi gaba ɗaya ta ɗauki laifin ta ɗora akan Labeeb.

“Zaka iya barin abun nan tsakanin mu da ka so, ba saika sako su ba. Ransu ya ɓaci hankalinka ya kwanta.”

Mamdud ya ƙarasa cikin sauke murya. Miƙewa zaune Labeeb yayi cikin mamaki yake kallon Mamdud da ƙarfin hali irin nashi.

“Wow Mamdud. Yanzun kuma nine da laifi ko? Banma ɗauka kana da bakin da za kai min magana ba wallahi.”

“Mtswww”

Mamdud ya ja tsaki ya miƙe da shirin wucewa. Hannunshi Mamdud ya kama ya janyo shi da ƙarfi ya dawo da shi tare da miƙewa.

Ranshi ya gama ɓaci gaba ɗaya, cikin fuska ya kalli Mamdud.

“Kai kaɗai ne! Kai kaɗai ne za ka mkn tsaki ban fasa maka baki ba. Bana so ko kaɗan kuma ka sani. Kamar yau babu abinda yake maka daɗi daya wuce ɓata min rai.”

Wani ɓangare na zuciyar Mamdud yana jin kamar bai kyauta ba, sai dai akwai ɗayan ɓangaren da ke jin daɗin ɓacin ran Labeeb. Ɓangaren da ke son rinjayar ɗayan.

Wucewar dai Mamdud zai yi ba tare da ya ce komai ba, Labeeb ya sha gaban shi. Inda shi ne yai mishi laifi zai bashi haƙuri.

“You have to apologize. Laifi Kai min.”

Labeeb ya ƙarasa yana ɗan murza goshin shi saboda kanshi da ke ciwo ga zazzaɓi me zafi da yake ji har cikin idanuwanshi, ga ɓacin ran Mamdud.

“Yi haƙuri.”

Mamdud ya faɗi wannan karon yana juyawa ya zagaya ta bayan kujerun ya wuce. Sam Labeeb baya jin wani saurin ƙarfin da zai yi faɗa da Mamdud ɗin.

Jiri ma yake ji yana ɗibarshi. Da sauri ya koma kan kujera ya kwanta yana rufe idanuwanshi. Baisan iya lokacin da ya ɗauka a haka ba.

Kawai dai yana jin sosai ba shi da lafiya kafin ya ji sallamar Zulfa. Ya kasa ko buɗe idanuwa. Yadda ta ji ya amsa sallamar da ƙarfi yasa ta cire takalmanta ta ƙarasa tana faɗin,

“Yaya?”

Cike da alamar tambaya. Bai amsata ba, tsugunnawa tayi a gabanshi ta kai hannu tana taɓa fuskarshi. Zuciyarta ta doka jin wani irin zazzaɓi da ke jikinshi.

“Yaya baka da lafiya ka zo nan kai kaɗai.”

Ta ƙarasa kamar zata yi kuka. Wuyanshi ta sake taɓawa, har ya fi fuskarshi zafi, hannunshi ta kama tana ƙoƙarin miƙar da shi zaune.

Da ƙarfin hali ya tashi, ya buɗe idanuwanshi da har sun canza launi kan zulfa. Magana zai yi yaji amai ya taho mishi gaba ɗaya.

Sai dai ba wani abu a cikinshi. Da sauri zulfa ta kama shi.

“Innalillahi… Yaya tun yaushe baka da lafiya? Yaya Asad! Yaya Mamdud! Wai ba kowa ne?”

Zulfa ke faɗi, don har lokacin Labeeb na kakarin amai. Ta san halinshi sarai, sai ciwo ya ci ƙarfin shi suke sani. In ma yayi a tsaye har ya warke babu wanda zai ji.

In ba ka kula da ya rame ba, Mamdud ya fara fitowa, kafin yai magana Zulfa ta watsa mishi wani kallo tare da faɗin,

“Wai kuna gidan ashe? Kuna kallon ba shi da lafiya za ku barshi shi kaɗai.”

Zulfa ta faɗi, tana jin kamar ta kwaɗa ma Mamdud ɗin mari. Da sauri ya ƙaraso inda Labeeb ɗin yake, ya sa hannu yana kama shi.

Har ta cikin rigarshi kana iya jin zafin jikinshi. Zuciyar Mamdud ta doka, yanzun ya gama yima Labeeb rashin mutunci ashe ma ba shi da lafiya.

Ji yai kamar ya koma ya goge abin da yai mishi.

“Asad!”

Mamdud ya kira, su duka har Zainab jin yanayin kiran yasa suka fito da sauri, kowa da inda ya taba jikin Mamdud.

“Faɗa za mu yi sosai yaya. Bari ka warke.”

Zainab ta faɗi muryarta na rawa, ɗan murmushi kawai Labeeb yayi. Anees ma cewa yayi,
“Bansan me yasa kake mana haka ba.”

Muryar labeeb can ƙasa ya ce,

“Ku yi haƙuri na daina.”

Kama shi Asad yayi yana rasa me yasa yake musu haka. Me yasa Mamdud ma yai musu abinda yai musu, su duka sun ɓata mishi rai yau ɗin.

Zame hannun Asad ɗin Labeeb yayi yana miƙewa. Da ka gani kasan ƙarfin hali ne saboda jiri ke ɗibarshi.

“Karka sake ɓata min rai Yaya.”

Asad ya faɗi yana kama hannun shi, ganin su dukansu kowa ya bi bayansu yasa Anees komawa ya ɗauko mukullin Jeep ɗin Labeeb ɗin da bai cika fita da ita ba.

Ta ɗakin Arif ya biya, yana kwance da headphones a kunnenshi yana karatun Qur’an. Da alama shi yake ji yana bi. Ya ga shigowar Anees, sai da ya kai Aya tukunna ya zame headphones ɗin ya kalli Anees.

“Yaya ne ba shi da lafiya zamu tafi asibiti.”

Da sauri Arif ya diro daga kan gadon ya saka takalmanshi. Bai ma damu da cewar ba na fita bane ba.

Iya wanda yake amfani da su cikin gida ne don ya tsani ya ji ya taka ƙora ko ya take.

Suna hanyar fita ne yake ce ma Anees.

“Me ya samu yayan?”

Cike da damuwa.

“Zazzaɓi ne, nasan za ka so binmu yasa na taho da kai , bana son damuwar nan.”

Anees ya ƙarasa suna nufar motar. Har suka shiga Arif bai sake cewa komai ba. Anees ke tuƙin, bai ɓata lokaci ba sanin inda Labeeb ke ganin likita yasa shi nufar Dialogue kai tsaye.

*****

Ganin yawansu yasa likitan buɗe baki. Sai dai kafin ya ce wani abu Zainab ta riga shi da faɗin,

“Karma ka soma furtawa, wallahi babu inda zamu koma, in shiru ne za mu yi shiru, zamu bi duk wani rule, amman babu inda zamu je.”

Ta ƙarasa tana zuba mishi idanuwanta. Kallon su Asad yayi ya ga alamu kala ɗaya ne a duk fuskokin su. Inda Labeeb yake suna nan.

Sauke numfashi yayi yana kallon Labeeb da ya ce mishi,

“Ko nai magana ba zasu saurare ni ba.”

Murmushi likitan yayi kawai. Kalar ƙaunar da ke tsakanin su na burge shi. Da ƙyar ya samu suka fita daga ɗakin, Mamdud da zulfa ne suka tsaya, kafin shi ya haƙura ya fita ya bar zulfa.

Sosai aka duba Labeeb, gardama yaso yi jin likitan ya ce zai riƙe shi ko kwana biyu ne saboda ba abinda ya haddasa mishi ciwon kan da zazzaɓi banda stress.

Ganin taron dangin da akai mishi yasa shi dole ya haƙura aka bashi gado. Zainab da kanta ta dinga kiran su Dawud da Jarood ta faɗa musu.

Kafin awa ɗaya ɗakin cike yake da cousins ɗinsu jin Labeeb ɗin ba shi da lafiya. Don su Jarood hardae warmers ɗinsu na abinci da lemuka suka zo.

Dawud ma fruits ne ledoji da lemukan suka zo da su. Har kan gadon Labeeb ɗin sai da wasu suka zauna. Ƙarshe ma tashi yayi zaune duk da ƙarin ruwan da ke jikinshi.

Nan suka yi sallar Magariba suka dawo, sai da likita ya shigo ya ga yawansu, Labeeb ɗin da ake so ya samu hutu har da shi ake surutu.

“Aikam maza maza duk ku tattara ku fita. Ku da ake so ya samu hutu.”

Likitan ya faɗi yana kallon su, kafin ya nuna Labeeb da ɗan littafin dake hannunshi.
“Kai kuma bacci za ka yi yanzun nan.”

“Ohhh nooo”

Su jarood suka faɗi suna kallon likitan.

“Da gaske nake duka gida zaku tafi.”

Dawud ya kalle su.

“Yeah duka ku tashi mu tafi. Kuna ji an ce hutu yake so, sai mu dawo da safe in Allah ya kaimu.”

Dole suka tattara, don akwai wani abu tattare da Dawud ɗin da ke sa ka kasa mishi garda. Amma me, iya wajen mota su Asad suka raka su, don ita zulfa tana kusa da Labeeb ko fita bata yi ba.

Sannan suka koma. Sai bayan sun dawo sallar isha’i ne Mamdud ya ke ce musu,

“Ya kamata ku ci wani abu.”

Kowa gefe ya kalla, Labeeb na ta bacci lokacin. Ganin haka yasa Zulfa cewa,

“Me akai da ban sani ba?”

“Bama magana da Yaya Mamdud. Zuwa yai yana cewa ba shi da kowa, as in ‘yan uwa ko ɗaya, blah blah blah sauran ba shi da amfani.”

Zainab ta faɗi, Arif da Zulfa suka kalli Mamdud da yayi wuƙi-wuƙi da idanuwa. Sam baya son kallon da Arif yake mishi. Kowa ya ji haushin shi banda Arif. Yaron daban yake a wajenshi.

“Don Allah ku yi haƙuri. Ba haka nake nufi ba.”

Mamdud ya faɗi yana kallon su. Girgiza mishi kai Zulfa ta yi.

“In ni na ji haushi and na ɗauka kana kallona kamar cousin ɗinka. Su bansan me za su ji ba.”

“Sosai ban ji daɗi ba.”

Arif ya faɗi muryarshi cike da disappointment. Haƙurin dai Mamdud ya sake basu, babu wanda ya ko kalle shi. Daga Arif sai Asad suka ɗan ci abincin da su Jarood suka kawo.

Su sauran Fruits kawai suka ɗan taɓa. Dukansu kusan a zaune suka kwana. Ganin baccin da Arif yake yasa Mamdud ya kamashi ya kwantar da shi ya yi mishi matashi da cinyarshi.

Shi ko runtsawa bai yi ba. Asalima babu komai a zuciyarshi banda tunanin Ateefa da ko wanne hali take ciki. Abin har mamaki ya bashi, ta samu waje tai mishi zaune a ƙirji.

*****

Washegari daga Mummy har Daddy sun dawo bisa jin Labeeb na asibiti. Tana zuwa ta ce su duka su koma gida ita ta zauna.

Kowa ɓata fuska yayi. An dai rasa wanda zai musa ne, amma ko motsi basu yi balle su nuna alamar suna shirin tafiya. A gajiye Labeeb ya ce,

“No Mummy ki je ki huta ke kam, ki barsu a nan.”

Girgiza mishi kai Mummy ta yi.

“Suna da makaranta, suna buƙatar su ɗan huta.”

Murmushi Labeeb yayi.

“Ina sane, it will work ki yarda da ni mummy. Ina buƙatar su a nan, tare da ni. Ki je ki huta abinki.”

Kallon Labeeb Mummy ta yi, maganarshi ta mata zafi. Yadda ya nuna zamanta da rashin zamanta duk ɗaya ne a wajenshi, kuma ƙiri-ƙiri ya nuna yana buƙatar ‘yan uwanshi. Kamar in babu su ɗin ba ma zai zauna a asibitin ba. Aikam kamar yasan abinda take tunani ya ce,

“In za ki zauna kuma to, amma suna fita zan bi su.”

Miƙewa Mummy tayi ba tare da ta ce musu komai ba ta fice, sauke numfashi Labeeb yayi a nutse, yana jin babu daɗi, yasan ran Mummy ya ɓaci ne.

Sai dai da ya kalli su Zainab ya ga yadda suka ji daɗi da bai bari Mummy ta kore su ba sai ya ɗan ji dama-dama. Yasan ƙannen shi. Baya jinsu don sun rasa classes na wasu kwanaki.

Yana jin da ya tura su makaranta da rashin nutsuwa a tattare da su, gara nan inda zai kula da sun ci abinci ko basu ci ba.

Kwanan shi uku a asibiti tare da su, nan suke kwana su duka. Mummy da Daddy sai dai su zo su ga jikinshi su koma. Ishaq ma haka.

Zuwanshi biyu, kowanne zuwa sai ya yo ledoji na kayan ciye-ciye, sai dai duka zuwan biyu yanayin kallon da yake ma Zainab yasa ko tashi raka Ishaq bata yi.

Da ƙyar aka sallami Labeeb da sharaɗin ya huta ko da kwana bakwai ne kafin ya je ko ina. Mamdud ya fi kowa jin daɗin sallamar labeeb.

Duk yadda zuciyarshi ke son zuwa ya duba ko Ateefa ta je gidan Labeeb, duk yadda ya qagu yaga ko lafiyarta bai sa shi barin asibitin ba.

Amma yanzun da suka dawo gida, ya ga jikin Labeeb ɗin da sauƙi zai iya zuwa ko ina yake son zuwa.

Bayan Wata Daya

Wata irin shaƙuwa ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin Mamdud da Ateefa. Ko me yake da Asr tayi yake barin shi ya nufi Barnawa don yasan lokacin ta tashi daga baccin da take yi.

Ranshi ya ɓaci da ya ji rainon yara har biyu take na Baraka da take zawarci a gidansu wadda yaya ce wajen maman Ateefa ɗin.

Kwanan da take jigila da su ya sa bata samun bacci, da safe kuma ta yi aikin gidan tas ta gama. Ba damuwa suka yi da su bata abinci ba.

Hajja ta sha faɗa, ba don alƙawarin da ta yi ma Baba ba da sai Ateefa ta bar musu gidan su don bata haɗa komai da ita ba. Maman Ateefa ita kaɗai babarta ta haifa ta kuma rasu bayan nan.

Ita ma maman Ateefa ɗin da ta rasu wajen haihuwarta. Hajja kance da Baba kaɗai Ateefa ta haɗa jini ya sa in za ta wuni a waje tana tangaririya indai ta gama musu aikinsu babu wanda yake damuwa da ita.

Basu damu ko maza za ta bi ba ta samu abinci ba kome. Takan sa kaya matsattsu duk da ta tsani komai tare da hakan. Su ne kawai hanyar dake janyo mata hankalin maza.

Wasu kan ɗauketa shan ice cream ko cin abinci wanda ta nan ne kawai take samu ta ci. In ba haka ba takan kwana da yunwa sai dai ko in Baraka wasu lokutan ta bata.

Yana ganin yadda take sako hijab yanzun. Hakan ya mishi daɗi ba kaɗan ba, daga ranar da ya sauke idanuwanshi kan Ateefa yasan zuciyarshi ta jima a ƙirjinshi tana harbawa ne domin jiran Ateefa.

Ta ko ina yake jin ita ce ta dace da shi. Ita ce matar da zai aura cikin sauƙi ba tare da an dubi asalinshi an yi shakku akai ba. Yanzun ma zaune suke cikin falon gidan suna kallo.

Ko Mamdud ya ce Ateefa na kallo, don shi assignment yake ragewa. Labeeb ya shigo gidan da sallama. Su dukansu suka amsa shi.

“Wanne irin gudu kayi haka?”

Mamdud ya tambaya yana duba agogon da ke ɗaure a hannunshi.

“Ina Zariya ina Kaduna? Ba gudun da na yi.”

Labeeb ya ƙarasa yana nufar kitchen ya fito da kofi a hannunshi da Mamdud ya bi da kallo sanin ko menene a ciki. Waje ya samu ya zauna nesa da su.

Yana jin idanuwan Ateefa a kanshi. Abinda yake ji kanta, yanayin yadda take manne a ƙirjinshi ko ina yake daga ranar da yaji abinda ke faruwa da rayuwarta yasa ko za su hadu a gidan baya kulata.

Asali ma da wahala yai fara’a a gabanta, fuskarshi a haɗe take kullum in har tana cikin gidan. Bai kalli inda take ba, hankalin shi na kan abinda yake sha cikin kofin.

Ateefa a nata ɓangaren, tun ranar da ta fara ganin Labeeb a cikin gidan shi, maganarshi ta farko, yanayin yadda fuskarshi take yi. Komai nashi ba ƙaramin burgeta yayi ba.

Haka ganinshi na biyu, bata taɓa ganin namijin da komai nashi kamar an yi ne don ta ji ya mata ba. Sai dai ta ko ina tasan bata dace da shi ba.

El-Maska, kamar yadda ta ji Mamdud na kiranshi. Allah kaɗai yasan ko sau nawa take maimaita sunanshi a zuciyarta a duk rana. Yanda ko kallon ta baya yi, lokuta da dama yakan yi kamar ma bai ganta ba, ko bai yi hakan ba ta san ita dashi basu dace ba.

Ba sai ya nuna mata ba. A ko ina na zuciyarta Mamdud ya maye gurbin da Yaya Musty ya bari. Tare da Labeeb zuciyarta bata san wannan ba. Da duk ganin da za ta yi mishi kamar ƙara tunzura abinda take ji yake yi.

Idanuwanta ta ji sun ciko da hawaye. Ita kuma haka tata ƙaddarar take, a wahale zata ƙare rayuwarta. Asali me kyau a kullum sai dai ta ganshi manne da wasu.

Rayuwa me kyau ma haka, ta jima da fidda rai da aure dama. Kafin ta ɗora idanuwanta kan Labeeb har daɗi take ji don a duk samarin da ta yi tana kula su ne kawai don hakan ya dace ta yi.

Amma ko kusa da zuciyarta babu wanda ya taɓa zuwa. Sai ƙaddadara ta haɗa ta da Labeeb. Ranar da ta fara wucewa ta gidanshi bata zata da kowa ba.

Ganin unguwar shiru yasa ta kama ta dira da niyyar zama ta huta, sai dai ba zata manta video ɗin da suka kalla da Yaya Musty gab da rasuwarshi ba.

Ɗankunnenta ta cire ta lanƙwasa da wani irin bugun zuciya ta zira shi cikin lock ɗin sai dai ga mamakinta buɗe gidan ta yi lafiya ƙalau. Harta shiga gabanta na faɗuwa.

Bacci ta yi sosai, ta dinga shiga ko ina na gidan. Ganin kurar da yayi yasa ta sharewa, tana ganin koba komai tunda ta shigo gidan mutane har tayi bacci ba tare da sanin su ba.

Abinda zata ɗan yi shi ne ta gyara musu gidan. Sai dai me  washegari ma sai ta tsinci kanta da son komawa. A haka ta ci gaba da komawa. Banda kofunan ɗin da takan ga an ɓata.

Wanda shi ne kaɗai alamun da take gani na cewar ana shigowa gidan sai kuma gado da zata gani a hargitse. Ashe ƙaddarar wahala ce ke fisgarta.

Ƙaddadar haɗuwa da Labeeb. Duk da ta wani fannin ƙaddadar ta zo mata da abu mai kyau. Samun Mamdud da yanzun ba ƙaramin rage mata zafin rashin Yaya Musty da Baba yake ba.

Sanadin shi ta daina zama da yunwa. Ta daina fargabar ko wanda zata bi cin abinci next shi ne zai zama sanadin ɓata rayuwarta.

Har kuɗaɗe yake bata. Wanda takan ɓoye tai hidimarta, ya bata waya sai dai bata amfani da ita, shi ma bai matsa mata ba. Ya dai ce dan in tana buƙatar shi cikin gaggawa ta neme shi ne.

Miƙewa Ateefa ta yi ta samu ta mayar da hawayenta da ƙyar.

“Tafiya?”

Mamdud ya tambaye ta. Kai ta ɗaga mishi.

“Zan ma Anty baraka wanki.”

Ta amsa shi. Duk da akwai gaskiya a maganarta, sai dai tasan Anty Baraka bata damu da ko ƙarfe nawa zata koma ba. Tasan dai ko ma yaushe ne wankin na jiranta kuma dole ta yi.

Ran Mamdud a ɓace ya ɗan ɗaga mata kai kawai. Don baisan me zai ce ba. Ji yake dama ya ƙarasa karatun shi ya samu aiki ne da ya faɗa ma Ateefa yana sonta.

Zai kuma aureta, amma yanzun dole ya haƙura, dole ta ƙara jure zaman gidan su da take na ɗan wani lokaci. Shi zai rabata da wannan ƙangin, tare da junansu zasu samu dukkan ƙaunar da suka rasa.

Zasu samu family ɗinsu da za su so. Kafin ya ga Ateefa yana da niyyar auren mata fiye da ɗaya. Shi yasa yake da burin tara kuɗi masu yawa, ya zama wani.

Yadda zai yi amfani da kuɗin wajen goge wani muni na asalin shi wajen dangin wacce duk zai aura. Amma tunda zuciyarshi ta buɗe ido kan Ateefa sai yake hango ita kaɗai ta ishe shi.

Har dariya yake shi kaɗai yana mamakin kalar son da yake mata lokaci ɗaya haka. Yana kallonta ta wuce shi tana nufar hanyar ƙofa.

Labeeb da ke jujjuya kofin shi da giyar da ke ciki yana jin me ta ce, abin ya tsaya mishi. Ɗan miƙewa yayi ya zaro wallet ɗinshi, dubu biyar ya ɗiba.

Muryarshi can ƙasa ya ce,

“In kika bata kuɗin wankin zata barki?”

Da bai yi amfani da kalmar jinsin mace ba Ateefa ba zata taɓa ɗauka da ita Labeeb yake ba. Daga ita har Mamdud kallon shi suke, shi kuma idanuwan shi kafe suke kan Ateefa.

Amsarta yake jira don ya tsani maimaita magana. Banda Mummy da ‘yan gidansu babu wanda zai wa magana ya ji shi ya kuma sake maimaitawa.

A hankali ta ɗan ɗaga mishi kai, Mamdud Labeeb ya miƙa ma dubu biyar ɗin ya miƙe abinshi ya shiga kitchen ya sake ciko glass ɗinshi ya dawo ya wuce bedroom.

Miƙewa Mamdud yayi yana tunanin ko ya aka yi wannan tunanin bai zo mishi ba. Ya samu ateefa inda take tsaye ta bi ɗakin da Labeeb ya shiga da kallo.

Kuɗin Mamdud ya bata, ta sa hannu ta karɓa, cikin sanyin murya tace.

“Na gode. Ka ce mishi na gode sosai.”

Murmushi Mamdud yai mata yana faɗin,

“Karki damu zan faɗa mishi. Ki kula da kanki.”

Kai ta ɗan ɗaga mishi ta juya. Ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya zauna ya ci gaba da assignment ɗinshi zuciyarshi cike da tunanin ta.

Labeeb kuwa yana shiga ɗaki kan mirror ya ajiye kifin ba tare da ya sake sha ba yai tsaye a tsakiyar ɗakin yana maida numfashi kamar wanda yai gudu.

Waje ya samu ya zauna gefen gadon ya dafe kanshi cikin hannuwa. Tunanin Ateefa za ta yi wanki, za ta yi wata wahala gaba ɗaya ba ƙaramin taɓa shi yayi ba.

Abin ya girgiza shi yadda baya zato. Mace ɗaya ce zai yi tunanin haka akanta ya ji abinda ya ji, Zulfa.

Jin yadda gaba ɗaya zuciyarshi tai rauni ya tsorata shi.

Miƙewa yayi yana ɗaukar wayarshi ya buɗe ƙofa ya fito. Mamdud ya bi shi da kallo.

“Mu tafi gida.”

Ya faɗi, girgiza mishi kai Mamdud yayi.

“Baka ga da mota na fito ba nima? Zan taho sai anjima.”

Mamdud ɗin ya amsa shi yana maida hankalinshi kan abinda yake yi. Wucewa Labeeb yayi ya fice daga gidan yana shiga motarshi ya zauna.

Yana so yasan me yake ji akan Ateefa, Zulfa yake buƙata, ita kaɗai yake iya faɗa ma duk wani abu da yake damunshi. Hanyar gida ya nufa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 28Rayuwarmu 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.