Wayar Zulfa ya kira, bugu ɗaya ta ɗauka.
"Yaya ina gida... Ban daɗe da dawowa ba."
"Gani nan to."
Labeeb ya faɗi yana sauke wayar, a hankali ya janyo pillow ya sauke kan Zainab daga jikinshi. Ya gyara mata kwanciya. Goshinta ya sumbata yana kallonta.
Hangota yake tana 'yar ƙaramar ta. Hangota yai lokacin da komai shi ne yake mata. Yana buƙatar wani ya faɗa mishi bai yi kuskuren hukuncin da ya yanke ba.
A hankali ya ja mata ɗakin ya nufi na Zulfa. Ƙwanƙwasawa yayi ta ce mishi ya shigo. Yana. . .