Sa'a ya yi Zulfa na gida. A ɗakinta ya sameta zaune kan gado ta miƙe ƙafarta tana cin cheezy ta tara ledojin a gefe tana karatu.
Shigarshi yasa ta ajiye handout ɗin a gefe suka gaisa. Ya ja numfashi ya fitar da ɗan ƙarfi.
"Ya dai Yaya? Gajiya ko?"
Ta buƙata. Girgiza mata kai ya yi ya zaro wayarshi a aljihu ya cire key ɗin. Tana kallonshi yana danne-danne a waya kafin ya miƙa mata wayar yana saka hannunshi cikin fuskarshi.
Karɓa ta yi, hoton wata yarinya ne da Zulfa bata. . .
Excellent