Skip to content
Part 30 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Sa’a ya yi Zulfa na gida. A ɗakinta ya sameta zaune kan gado ta miƙe ƙafarta tana cin cheezy ta tara ledojin a gefe tana karatu. 

Shigarshi yasa ta ajiye handout ɗin a gefe suka gaisa. Ya ja numfashi ya fitar da ɗan ƙarfi. 

“Ya dai Yaya? Gajiya ko?”

Ta buƙata. Girgiza mata kai ya yi ya zaro wayarshi a aljihu ya cire key ɗin. Tana kallonshi yana danne-danne a waya kafin ya miƙa mata wayar yana saka hannunshi cikin fuskarshi. 

Karɓa ta yi, hoton wata yarinya ne da Zulfa bata sa ran zata girmeta da fin shekara ɗaya ko ma su zo tsararraki, sanye jikinta yake da farin hijabi, da gani bata san an ɗauki hoton ba. 

Hijab da rashin kwalliyar da ke fuskarta bai hana zulfa ganin kyanta ba. Musamman idanuwanta farare ƙal da su kamar tana saka musu wani abu. 

Zafi jikin zulfa ya ɗauka, wani irin zafi ne da baiyi kama da na zazzaɓi ba, saboda wannan daga zuciyarta yake fitowa yana ba sauran jikinta. 

Numfashinta ta ji ya daina fita yadda ya kamata, ga kanta da yai dimm, hannu tasa tayi gefe, kafin ta ci gaba da wucewa, hotunan yarinyar ne sun fi guda hamsin kuma da ɗayan wajen kala ashirin da farin hijab ɗin da ke nuna duk rana ɗaya aka yi shi. 

Haka ɗayan ma duka da shiga kala ɗaya ne. AC ɗin da ke ɗakin bai hana ta gumi ba. Rigarta ta kamo ta tsane goshinta. Zuciyarta kamar zata fito ta bar ƙirjinta. 

Sau biyar tana buɗe baki da niyyar mishi magana ta kasa saboda ji take babu sautin da zai fito daga bakinta banda gunjin kuka. Da kanshi ya ɗago ya zube mata idanuwan shi da ke cike da ruɗani.

“Wallahi sai daga baya na ga na ɗauki hotunan nan. Su duka, it’s like kome nake ji shi ne yai taking control kawai na ɗauketa. 

Bansan meke damuna ba, ko magana bana mata saboda abinda nake ji akanta yana min wani iri. Yau…yau nasan akwai matsala…”

Cikin idanuwan shi zulfa take kallon shi tunda ya buɗe baki, tana jin yadda ɓangare-ɓangare na zuciyarta ke rabuwa da ‘yan uwanshi yana tarwatsewa zuwa wajaje da suke da ciwon gaske. 

Tare da Zafira ciwo ne ɗan kaɗan da zuciyarta guda ɗaya saboda tasan baya sonta ko kaɗan. Abinda take gani a idanuwanshi ne ya tarwatsa mata zuciya gaba ɗaya. 

Yanayi ne da yakamata ya ɗauki shekaru yana gina shi. Ko wacece wannan ita ta shigo rayuwar shi da sa’a. Saboda soyayyar da yake mata irin wadda take shiga ce lokaci ɗaya ta samu waje ta zauna. 

A ɓangaren da soyayar da ita Zulfan ke mishi ta shekaru ce, asali ma da soyayarshi ta tashi, ita tata akwai haƙuri a ciki. Wannan kalar tashi ta lokaci ɗaya bata san komai ba sai gaggawa. 

“Da wata ta shiga zuciyata zan jata in rufe gam don na san babu wajen son kowa. Zuciyata don mace ɗaya aka yita”

Ta tuno maganganun shi wani lokaci da suna hira. Yau duk wani hope da take da shi akan Labeeb ya gama rushewa. Yau ya samu macen da yake jira. 

Yau tana nufin abubuwa da dama a wajenta. Yau tana nufin ta rasa Labeeb har abada. Yau tana nufin duk wani feelings da basu dangancin ‘yan uwantaka ba dole ta janye shi gefe. 

“Ya sunanta?”

Ta faɗi a hankali kamar mai koyon magana. 

“Ateefa.”

Labeeb ya faɗi da yanayin da ke nuna kamar sunan na da wani ɗanɗano mai muhimmanci kan harshen shi. Numfashi Zulfa ke ja a hankali tana fitar dashi. 

Sai da ta tabbatar za ta iya magana kafin ta ce, 

“Sonta kake yi yaya. Kana son Ateefa, ka faɗa mata kafin ka rasa ta.”

Ware idanuwa yayi yana ƙifta su da sauri-sauri akan Zulfa. Yanayin daya sa sauran manyan ɓangarorin da suka rage a zucyarta suka ƙara tarwatsewa. Sakkowa ta yi daga kan gadon ta kama hannunshi tana ɗago shi da faɗin, 

“Tashi ka je ka faɗa mata.”

So take kawai ya bar ɗakin. Ya fita ya barta ta ji da abinda ke damunta. Kallonta yake, akwai wani abu tattare da yanayinta da bai taɓa gani ba. 

Miƙewa yayi ya ƙwace hannunshi daga riƙon da tai mishi yana ɗaga su duka biyun da shirin riƙe mata fuska. Matsawa ta yi ta samu da ƙyar ta ɗora murmushi a fuskarta. 

“Ka fita min daga ɗaki Yaya. Ka je ka faɗa mata kana sonta kafin wani ya riga ka”

Daƙuna fuska yayi, sosai ta ƙara ja da baya. Yanayin fuskarta yake kallo yana kasa fahimtar ko me yake gani. Sai dai maganar da tayi ta cika zuciyarshi. 

Hakan yasa shi yin murmushi yana jin duk wani abu dake motsi a jikinshi na tashi da karɓar soyayyar da yake ma Ateefa. Ajiyar zuciya ya sauke. 

“Finally!”

Ya furta da murmushi a fuskarshi. Ƙarasowa Zulfa ta yi tasa hannu kan kafaɗarshi tana tura shi. Dariya yake sosai. 

“Zan fita Zulfa. Dama kun gaji da ni, soon zan bar muku gidanku and wannan karon zai zama daban saboda ina sonta…”

Ƙofa Zulfa ta buɗe tana nuna mishi hanya da hannunta, sai da ya ja mata kumatu ta ture hannunshi tana daƙuna mishi fuska. 

Kallonta yake ta ware mishi idanuwa. Dariya yai duk da yanayin da ke fuskarta ya tsaya mishi a wani waje a ƙirjinshi. Fita ya yi ya bar mata ɗakin, tura ƙofar Zulfa ta yi tana jin ƙamshin shi duk da irinshi ne a jikinta. 

Da ƙofar ta jingina fuskarta tana shaƙar shi tana jin kamar ƙamshin shi na jiki. Kuka take marar sauti zuciyarta na wani irin ciwo. 

Nan ta zame jikinta ta durƙushe ta saki wani gunji. Sosai take kuka numfashinta har tsaitsayawa yake, da ƙyar ta sake miƙewa ta kulle ɗakin daga ciki. Ta koma kan gado ta zauna. 

Pillow ta ɗauka ta saka fuskarta ciki tana sakin wani gunjin kuka. Daga abinda yai saura na zuciyarta kukan ke fitowa. 

“Na rasa shi… Bazan taɓa samun shi ba… Ina sonka Yaya… Don Allah ka dawo ka ce ni kake so… Ni ya kamata ka so ba Ateefa ba…mutuwa zan yi in ka auri Ateefa.”

Sambatu kawai take tana wani irin kuka mai cin rai. Abinda take ji wanda yasan zafin rasa abinda kake so ne kawai zai fahimta. Wanda yasan raɗaɗi da ciwon kallon wanda kake so yana son wata daban. 

Yau ta san dole ta haƙura da Labeeb, ba zai taɓa sonta yadda take son shi ba. Har abada a idanuwanshi da zuciyarshi ƙanwa ce, yau ta rasa mutumin da take da tabbas sonshi a zuciyarta har mutuwa ne. Ta rasa Labeeb. 

**** 

Mamdud ke tuƙin amma hakan bai hanashi ganin nishaɗin da ke fuskar Labeeb ba har suka ƙarasa Naf Club. Fita daga motar zai yi ya ce, 

“What is up with you yau ɗin nan?”

Murmushi Labeeb yayi har haƙoranshi suka fito.

“Me ka gani?”

Ya buƙata yana ɗan ware idanuwa. Girgiza kai kawai Mamdud yayi yana zare key ɗin motar ya fice. Dariya Labeeb yayi shi ma ya fito daga motar. 

Da nishaɗi marar misaltuwa a tare da Labeeb suka shiga Naf Club. Yanayin music ɗin da ke tashi a wajen yayi dai-dai da abinda yake ji. 

Hannuwanshi ya fara tafawa kafin ya soma rawa sosai, Mamdud kujera ya samu a bar ɗin wajen ya zauna yana kallon yadda shigowar Labeeb ɗin ta ja hankalin mutane. 

Yadda kowa yayi wajenshi suna rawa tare, ƙaramin tsaki ya ja. Wata yarinya da Mamdud ba zai iya tuna sunanta ba, amma dai yasanta ta ƙaraso. 

Jikinshi zata hau ya tureta da faɗin, 

“Ba abinda ya kawoni kenan ba.”

Taɓe baki ta yi tana watsa mishi wani kallo kafin ta wuce abinta. Normal haɗin da akan mishi bartender ɗin wajen ya haɗa ya miƙo mishi. 

Kuɗin Mamdud ya zaro a aljihunshi ya miƙa mishi tare da ture kofin yana girgiza kai. Ya jima da barin shan komai, haka ma mata, tun shigowar Ateefa rayuwar shi ya ajiye komai. 

Dama can bai taɓa hango ma kanshi rayuwa kalar wannan ba. Gyara zamanshi yayi yana kallon Labeeb na cashewa abinshi, sun cakuɗe waje ɗaya har da mata. 

Hannuwan wata tsaf a ƙugun Labeeb ɗin , bai ko nuna hakan ya dame shi ba. Wasu lokutan har mamaki yakan ba Mamdud, komai yanayi kamar abin ya zo mishi natural ne ba tare da koyo ba. 

Abin na bashi takaici ba kaɗan ba, miƙewa yayi yaje ya kamo hannun Labeeb yana janshi wata yarinya kalar shuwa ta kama ɗayan hannun Labeeb ɗin. 

Dariya Labeeb yayi yana kallon Mamdud da ke fassara ‘ka sakar mata ni’. Yarinyar Mamdud ya kalla, muryarshi a dake ya ce 

“Sake shi.”

Ganin ba da wasa yake ba yasa ta sake shi. Janshi Mamdud yayi suna barin floor ɗin rawar gaba ɗaya. 

“Gida zamu tafi.”

“What? Yanzun? Bamu daɗe da zuwa ba fa.”

Labeeb ya faɗi yana kallon Mamdud daya saki hannunshi yana nufar hanyar da za ta fitar da su daga club ɗin. Dole ya bi bayanshi yana mita cewar shi bai gama having fun ba. 

Ko kula shi Mamdud bai yi ba har suka shiga mota, fun ɗin da ya ga Labeeb na having ne yasa shi jin baya son zaman club ɗin kwata kwata, gara su koma gida su yi bacci. 

Gidan kuwa suka koma, ɗakinsu Labeeb ya wuce yana barin Mamdud a nan falo zaune. Sai da ya fara watsa ruwa sannan ya kwanta, bai jima ba bacci ya ɗauke shi.

**** 

Da Ateefa manne a zuciyarshi ya farka a safiyar ranar, sai dai jinta da yake bai hana mishi yin hidimarshi ta ranar lafiya ƙalau ba. Bai samu zama free ba sai bayan Azahar, komai bai sakama cikinshi ba duk ranar haka ya kama hanya yana nufar gidanshi. Sai dai yana mamaki, yasan ya kamata ace gabanshi na faɗuwa ko makamancin hakan. 

Amma bai taɓa jin tabbaci akan komai ba a rayuwarshi irin soyayyar Ateefa, ko ɗar baya ji na shakkun cewar ba zata amince da shi ba. Yadda yake ji, yanayin da zuciyarshi take ciki ya tabbatar an yita ne kawai don ita. 

Yana da yaƙinin ba zai ji hakan ba in har ba zai same ta ba. Parking yayi ya buɗe gate ɗin, sai lokacin ya kula hannunshi na ɓari a hankali. Murmushi yayi ya wuce ya shigar da motar. 

Sannan ya fito ya kulle gate ɗin yana nufar ƙofa, sai da ya murza handle ɗin ya ji a kulle tukunna yai amfani da mukulli ya buɗe. 

Bugawa zuciyarshi take yi da baida dangantaka da faɗuwar gaba, bugun zuciyarshi na soyayyar Ateefa ne, ƙafafuwanshi da nauyi ya shiga gidan tare da sallama. 

Bai ga kowa a falon ba, har zai wuce ya ji motsi ta wajen kitchen, hanyar ya nufa, tana tsaye tana jera cups ɗin da ta gama wankewa don yaga alama, hannuwanta jiƙe suke da ruwa. 

Kansu ya fara kafe idanuwanshi suna mishi wani kyau da yasan ba lallai idanuwan wani bayan nashi suga hakan ba. Muryarta da yaji can ƙasa ta ce, 

“Ina wuni.”

Yasa shi maida hankalinshi kan fuskarta, idanuwanta cike da shakku take kallonshi. Ji take zuciyarta kamar zata fito daga ƙirjinta da bugun da take yi.

Kallon da yake mata duk ya dagula mata lissafi, tana jin kusancin shi a ko ina na kitchen ɗin. Zata rantse yana shigowa iskar kitchen ɗin ta sauya. 

Idanuwanta ta sauke daga cikin nashi don suna ƙara mata bugun zuciya. Shi kanshi Labeeb tashi zuciyar bugawa take, yau zai zama karo na farko da zai ce ma mace yana sonta. 

Yayi hakan a styles kala-kala, a finafinai marasa adadi, sai dai wannan tashi rayuwar ce, a fim hakan na da sauƙi, sai masu kallo su ga kamar tunkarar budurwar da kake son yin sauran ranakunka na duniya da ita abu ne mai sauƙi. 

Ko shi a da yana ganin babu wata wahala a ciki, ya sha faɗa ma kanshi yana ganin yarinyar da yake so zai faɗa mata, sai dai a iya tunanin shi bai taɓa hango me zai fara cewa ba. 

Sai ma da ya ji laɓɓanshi sun yi nauyi, harshenshi na yawo cikin bakinshi kamar mai koyan magana yasan ba abu bane mai sauƙi. Ateefa kam batasan me ya tsayar da shi ba. 

Dama ta san ba lallai ya amsa gaisuwarta ba, tunda ba magana yake mata ba, ta dai ɗauka bayan abinda yai mata jiya ko yaya ne magana zata ɗan dinga haɗasu. 

Wani abu ta haɗiye da ya tokare mata maƙoshi. Kafin ta juya ta ci gaba da abinda take yi, duk da tana jin idanuwanshi na mata yawo, can ƙasan zuciyarta take addu’a Allah yasa Mamdud ya shigo. 

“Ateefa…”

Muryar Labeeb ta daki kunnen ta, yanayin yadda ya ja sunanta na sa tsigar jikinta tashi, a hankali ta juyo ta sauke idanuwanta cikin nashi. 

Sosai abinda take gani cikinsu yasa zuciyarta ci gaba da bugawa har cikin kunnuwanta tana jin ƙarar. Tunda Labeeb yake bai taɓa sanin rauni irin na yau ba. 

Yana kallon yadda tun kafin ya buɗe bakinshi zuciyarshi ke tare da Ateefa, abinda duk ta ga dama shi za ta yi da ita, wani tsoro na daban ya ziyarce shi. 

Muryarshi na rawa, ɗauke da yanayi me nauyi ya ce mata, 

“Bansan yanayi irin wannan ya fi komai wahala ba… Bansan ko akwai kalaman da ya kamata in faɗi kafin in furta miki ba. A script akan ba ni kalamai da yawa, kala-kala, bana son yin amfani da ko ɗaya, saboda ina son abinda duk zan faɗa ya fito daga zuciyata…”

Ganin yadda take kallonshi yasa shi sauke numfashi yana sake jan iska zuciyarshi na ci gaba da dokawa. Tunda ya buɗe bakin shi Ateefa zata rantse zuciyarta gab take da fitowa daga ƙirjinta. 

Zata rantse baccin wucin gadi ne ya ɗauketa, take mafarkin wata duniya da ta fi ƙarfinta, duniyar da ta girmi matsayinta. 

Sai da ya haɗiyi wani yawu don ji ya yi gaba ɗaya maƙoshin shi ya bushe kamar ya kwana bai sha ruwa ba, kafin cikin muryar da bai gane tashi bace yace 

“Ina sonki. Ina sonki Ateefa. Bansan tun yaushe ba, amma wallahi komai da nake ji kamar an halicce ni ne don na ji hakan!”

Girgiza kai take a zuciyarta, a zahiri kuma ta ƙame, babu inda ke motsi a jikinta, kallon Labeeb kawai take, maganganun shi na mata yawo. 

So take ya ce mata wasa yake sai dai abinda take gani a fuskarshi babu wasa a ciki. Ta ko ina ita da shi basu dace ba, ta kowace fuska ita ba sa’arshi bace. 

Bata hango ta yadda soyayyarsu zata ɗore ba, ballantana har ta kai su ga aure. Ko mintina uku baiba da furta kalaman da yayi. 

Ji yake kamar ya ɗauki awa uku a tsaye yana jiran amsarta. Kamar zai yi kuka ya ce, 

“Ateefa karki ce mun a’a. Ni bamai kuɗi bane can, nasan ban taɓa soyayya ba, amman zan saki farin ciki…”

Muryarta a dakushe ta amsa shi da, 

“Bakasan wacece ni ba, ta ko ina ba mu dace ba, banda asali…”

Ta ƙarasa tana wani irin sauke murya da ya taɓa mishi zuciya, girgiza mishi kai take hawaye na cika mata idanuwa. Tana jin ciwo na gaske a zuciyarta.

A karo na farko da rayuwa ta miƙa mata abinda take so amma ba za ta iya karɓa ba saboda kamar koda yaushe asalinta ya ja musu katanga. 

“Banda asali… Ban…”

Katse ta Labeeb yayi da faɗin, 

“Na san komai akanki. Bai dameni ba, ba ke kika zaɓi zama a haka ba. Waye ni da zan ɗora ayar tambaya akan asalinki? Ki soni, karki ƙi soyayyata. Da duk mintin da zai wuce na rayuwarmu tare zan nuna miki asalinki ba zai taɓa zame mana matsala ba.”

Wannan karon hawayenta zubowa suka yi. Tun ranar da ta sauke idanuwanta akanshi tasan zuciyarta ta samu matsala. Yanzun da yake a gabanta yana furta mata kalamanshi masu tsayawa a rai haka. 

Tunanin basu dace ba ɓacewa yake, tunanin asalinta gefe yayi saboda ya ga abinda ya girme shi. Da komai na Labeeb yake son yakai hannu ya goge mata hawayen dake fuskarta. 

Sai dai ba zai iya ba, a karo na farko da ya ji ba zai iya taɓa wata mace ba. Saboda Ateefa ba wata mace bace a wajenshi, macen da yake so ya aura ce. 

Yau ya gane abu guda ɗaya. Komin iskancin namiji, komin sha’awarshi da mace, in har da gaske tana da wani waje a zuciyarshi zai tsaya ya sameta ta hanyar da ta dace. 

Son dayake mata ba zai taɓa barinshi ya gurɓata mata rayuwa ba. Namijin duk daya neme ki ta hanyar banza ya ce maki yana son ki ƙarya yake. Maison ki ba zai taɓa janki zuwa ga halaka ba. 

“Hawayenki a zuciyata nake jin zubar su. In ba za ki iya…”

Kokawa Labeeb yake da sauran kalaman shi. 

“In ba za ki iya sona ba zan fahimta. Zan haƙura, sai dai bazan iya jure kukanki ba.”

Hannu Ateefa ta sa tana goge fuskarta. Bata taɓa zaton rayuwa zata zo mata haka ba. Da gaske labeeb yake yi sonta yake. Ta kasa ganin wasa a fuskarshi. 

Kallonta yake yana jiran amsarta, gumi ke karyo mishi da ya tabbata ba a wajen jikinshi kaɗai ya tsaya ba har a zuciyarshi. Baisan abinda zai yi ba in ta ce bata son shi. 

Kai ta ɗan ɗaga mishi a hankali, sai da zuciyarshi tai tsalle daga mazauninta kafin ta sake komawa. Da murmushi ya ce, 

“Kin amince?”

Kai ta sake ɗaga mishi tana ƙin yarda su haɗa ido saboda yanayin da take ji. Tsalle tsalle Labeeb yake son yi amma ba a gabanta ba. 

“Ina zuwa.”

Ya faɗi yana fita kitchen ɗin da baya baya kafin ya juya, bai tsaya ko ina ba sai daya ganshi cikin bedroom ɗin gidan ya tura ƙofar tukunna. 

Kamar ƙaramin yaron da aka ba abinda ya fi ƙauna haka yake tsalle yana dariya, kafin ya tsaya yana rawa da faɗin, 

“If you are happy say hurray!”

Bai ga haukan dayake ba saida yace. 

“Hurray!”

Tukunna abin ya ba shi dariya. Haukan soyayya yake, bai damu ba kuma. A gaban dubban mutane zai maimaita abinda yayi yanzun. Sai da ya tabbatar in ya je gabanta ba zai sake wani tsallen ba tukunna ya fito daga ɗakin. 

A kitchen ɗin ya sameta, kallonshi ta ɗan yi. 

“Me kayi?”

Ta buƙata, murmushi yayi, karo na farko da ya ji kunya. Shi da kanshi El-labeeb Maska ne yau da jin kunya a gaban mace. Abin mamaki yabashi. 

“Tsalle tsalle na yi.”

Ya amsata, in har zai kasance da ita har ƙarshen rayuwarshi, gaskiya ita ce matakin farko na gina musu zamantakewa mai inganci. 

Batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba. Kunya ta sake rufe Labeeb. 

“Dariya ko? Na ji daɗi ne shi yasa, kuma bana so in yi a gabanki.”

Dariya ya sake bata, ta juyo ta kalle shi tana jin yadda zuciyarta ta saba da shi kamar sun shekara. 

“Saboda me ka faɗa min to?”

Ta buƙata, jingina bayanshi ya yi a jikin ƙofar kitchen ɗin. Kafaɗun shi duk biyun ya ɗan ɗaga mata tare da faɗin, 

“Banda abubuwa da yawa da zan baki, shi ne na zaɓi in farawa da faɗa miki gaskiya.”

Murmushi Ateefa tayi. Ko mintina goma ba ayi ba da fara maganarsu, amma tana jin yadda da ya buɗe baki yake ƙara zurfi a zuciyarta. Wayarshi ta soma ringing. 

Ya zaro ya ga Asad ne. Da sauri ya ɗaga yana kai wayar kunnenshi. 

“Yaya ka zo.”

Asad ya buƙata. Da sauri Labeeb ya ce, 

“Lafiya dai ko?”

“Lafiya ƙalau, kawai magana ce, ba zata yi ta waya ba kuma.”

Sauke numfashi Labeeb yayi yana ɗorawa da,

“Gani nan zuwa.”

Ya sauke wayar. Ateefa ya kalla yana jin kamar ya ɗaga tafiyar da zai yi washegari don zai yi sati biyu bai ganta ba. Har ya fara jin kewarta. 

“Kina da waya?”

“Eh Yaya Mamdud ya bani. Bana amfani da ita ne kawai.”

Kai Labeeb ya ɗan ɗaga yana faɗin, 

“Za ki fara yanzun. In kin riƙe lambar ki bani, gobe da wuri zan yi tafiya, sati biyu zan yi ban dawo ba. Kewarki za ta yi min sauƙi in ina jin muryarki.”

Cikin sanyin murya ta karanto mishi lambarta. Wani abu na tsaya mata a wuya jin zai tafi har sati biyu, abin har mamaki ya bata. Shiru Labeeb ya ɗan yi kafin ya ce,

“Ki kula da kanki, na san Mamdud zai taya ni kula da ke.”

Murmushi tadanyi. 

“Kaima haka. Allah ya bada sa’a ya dawo da kai lafiya.”

Ya amsa da amin. Sai da ya ɗan yi tsaye na mintina biyu yana kallonta kamar yana son adana wani abu a zuciyarshi kafin nan ya juya ya tafi. Ateefa ta sauke wani numfashi da batasan ta riƙe ba. 

Sai da ya tafi tukunna ta ji komai da ya faru ya danneta. Ƙafafuwanta suka kama kyarma. Tsugunnawa ta yi a kitchen ɗin, da gaske Labeeb yana sonta, Labeeb ya nuna asalinta bai dame shi ba. 

Wasu sabbin hawaye ne ta ji sun zubo mata, don tasan ko asalinta bai dame shi ba. Da wahalar gaske dangin shi ma ya zamana hakan take a wajen su. 

**** 

Da sallama ya shiga falon, Zainab ta amsa mishi. Su uku kawai a falon, yanayin kallon da su Anees suke mishi yasa shi faɗin, 

“Me ke faruwa?”

Kallon juna suka yi su ukun, kafin su sake kallon Labeeb. In akwai abinda ya tsana bai wuce jira ba. 

“Kuna son ɓata min rai ne ko?”

Ya buƙata, wata takarda Zainab ta miƙa mishi, sai da ya cire takalmanshi ya ƙarasa tsakiyar falon tukunna ya karɓi takardar. 

ARIF IBRAHIM MASKA shi ne sunan daya fara jan hankalinshi. Kafin idanuwanshi su soma yawo kan takardar. Ya kasa fahimtar me yake karantawa. 

Sau huɗu yana sake bin takardar kafin ya ɗago kai ya sauke idanuwanshi kan Anees da ya yi saurin kauda kai. Can ƙasan takardar Labeeb ya sake kallo, sa hannun Asad ne akai. 

“Asad…”

Labeeb ya kira yana jiran bayani. Muryar Asad can ƙasa ya ce, 

“Baka nan ne. Kuma ana buƙatar sa hannun a lokacin shi yasa.”

Wani irin kallo Labeeb yake mai. Bai taɓa dukansu ba, amma yana jin da kusa yake da Asad sai ya kwaɗa mishi mari. 

“Kuma ba ka yi tunanin kirana a waya ba?!”

Labeeb ya faɗi yana ƙoƙarin controlling ɓacin ranshi kafin ya sake duba takardar da kwanan watan da ke kuasan sa hannun Asad. 

“Oh yayi kyau! Cikin ku wa yayi jagorancin tura min ƙani har Jordan ba tare da sanina ba?”

Da sauri Zainab ta ce, 

“Yaya exams akai musu, daga makarantar su Arif shi kaɗai ya ci, su shida aka ɗauka daga kowanne class, shi kaɗai ya ci.”

Kallonta Labeeb yayi. 

“Duk ban ji ba sai yau?”

Ya buƙata. 

“Muna ta so mu faɗa maka, ba ma zaton za ka amince ne.”

Anees ya faɗi yana kallon shi.

“Shi yasa ku kuka amince ko?”

Ɗan dafe kai Asad ya yi. Har ya sa hannu a takardar gabanshi na faɗuwa. Sunansu da na Labeeb ne a guardians ɗin Arif. Ko da aka kira lambar shi bata shiga ba su aka nema. 

“Yaya, Arif is gifted. Kai da kanka kasan haka, duka gidan nan babu kalarshi. In government ɗin garin nan ta ga haka har ta ɗauki nauyin karatun shi saboda me zamu hana?”

Babu abinda maganar Anees ta ƙara mishi banda ɓacin rai. Kallon su yake su duka yana mamakin yadda za su yanke hukunci babba haka bai sani ba. 

Abinda Anees ɗin ya faɗa gaskiya ne. Da suna ɗauka babu mai ƙoƙarin Zainab sai ga Arif. Wannan shekarar ya kamata ya shiga aji ɗaya a Secondary a shekarunshi da basu shige sha biyu ba. Amma yanzun ne yake gama aji uku. 

“Ina da kuɗin da zan kai Arif duk ƙasar da nake so. Ko banda su Mummy na da su. Magana kawai zan manta, ku duka ina da kuɗin da zan iya fita da ku na barku a nan ɗin. 

Saboda me za ku yanke hukunci akan Arif ban sani ba? In kun daina buƙatata a rayuwarku ne zan fahimta. Ku barshi shi ma ya kai munzalin da zai ji ba sai ya yi shawara da ni zai yi abuba…”

Yana ƙarasawa ya linke takardar kamar yadda Zainab ta bashi ya ajiye kan kujera ya wuce ba tare da ya basu damar cewa komai ba. Basu taɓa ɓata mishi rai irin na yau ba. 

Ya fi son su dukansu a kusa da shi. In da zai ga yadda tarbiyar su take tafiya. Bawai daga n shi yake da damar shirya su a hannun shi ba. Shiriyar kowa na hannun Allah. 

Amma kana buƙatar wanda zai kama hannunka ya taya ka zaɓen hanyar da ta fi. Shi da kuɗinshi ba zai tura Arif wata ƙasa ba. Ko da shekarunshi sun kai na su Anees balle ɗan ƙaraminshi haka. 

Wa zai kular mishi da shi. In ba shi da lafiya fa, waye zai duba shi. In wani ya ci zalinshi wa zai tare mishi. Kanshi har ya fara ciwo saboda zafin da ya ɗauka. 

**** 

“Sai da na ce muku kun yi mistake wallahi. Kun ga gashi ranshi ya ɓaci sosai.”

Cewar Zainab. Sauke numfashi Asad yayi. 

“Yaron nan zai zama wani abu in aka bashi damar fita daga ƙasar nan. Ko zanenshi ya isa ya ci abinci da shi m, amma anan, babu wanda zai damu. 

Na ɗauka in har mun sa hannu yaya zai amince. Bansan ranshi zai ɓaci haka ba.”

Jinjina kai Anees yayi, zai yi magana Arif da ke bayansu ya kuma ji me Asad ya ce ya karɓe zancen. 

“Zan ma yaya magana. Ni ban damu ba, ba na so ranku ya ɓaci…”

Kafin su bashi amsa ya nufi hanyar ɗakin su Labeeb ɗin. Da sauri su Asad suka miƙe gaba ɗayansu suna bin bayanshi. Zaune suka samu Labeeb ɗin a gefen gado. 

Arif ya fara ƙarasawa ya ce, 

“Yaya ka yi haƙuri. Sai da na ce in za kai faɗa abarshi, na fi son zama tare da ku fiye da karatun.”

Kallon shi Labeeb ya yi yana kamo hannunshi ya zaunar da shi akan ƙafarshi. 

“Bana son ka da nisa ne Arif. Dukan ku na fi son ku a kusa da ni.”

Ɗan murmushi Arif yayi. 

“Then zan zauna.”

Girgiza kai Labeeb yayi. 

“Ƙila cin jarabawar ka wani sign ne. Alama hakan ke nuna min cewar ya kamata ka bar ƙasar. Allah yasa ba kuskure nake yi ba Arif…Allah yasa tafiyarka alkhairi ce a rayuwarmu duka. “

“Ka yarda? Zan tafi?”

A hankali ya ɗaga ma Arif kai. Kowa na buƙatar a bashi dama in abu mai girma na ci gaba ya zo mishi. Ɗazun nan Ateefa ta ba soyayyar shi dama. 

Tsoron shi ba zai sa ya zama katanga tsakanin Arif da abinda zai iya zama nan gaba ba. Mummy bata bashi zaɓi ba, ba zai zama irinta akan Arif ba. 

Bai ji yayi dai dai ba sai da Arif yai hugging ɗinshi cikin kunnenshi ya ce mishi. 

“Thank you. I love you.”

“Love you more.”

Ya amsa shi, sannan Arif ɗin ya sake shi yana sauka daga jikinshi ya fice da murmushi a fuskarshi. Gyara zama Labeeb yayi yana zaro wayarshi daga aljihu kamar bai ga su Zainab na tsaye a wajen ba. 

Ganin share su da yake yasa su ƙarasawa suka jeru a gabanshi. 

“Kar ku sake ɓata min rai. Ku je abinku kawai.”

Zainab ta soma girgiza kai.

“Da n Allah ka yi haƙuri Yaya.”

“We are sorry, ba kaɗan ba da yawa. Kuma muna buƙatarka, ba yanzun ba kawai, har ƙarshen rayuwarmu. Akwai abubuwa da yawa da ba zamu iya mu kaɗai ba. 

Tsoron ɓata maka rai yasa takardar ta daɗe ba ka gani ba. Tambaya Anees wallahi cikina ya ƙulle kafin in kira ka. Ko Anees?”

Ɗaga kai Anees ya yi. 

“Ba shi kaɗai ba, da munsan ranka zai ɓaci da yawa ba za mu yi ba.”

Kallon su yayi, zuciyarshi bata san yadda za ta yi fushi mai tsayi da su ba. Ƙaunarsu ita ce raunin shi. Sonsu shi ne vulnerability ɗinshi. Sauke numfashi yayi. 

Su kansu sun ga ya haƙura, gefenshi Asad ya zauna, Anees na ƙarasawa ya zauna a ɗayan gefen, tsugunnawa a gabanshi Zainab ta yi suka zuba mishi ido. 

“Yaya!”

Suka faɗi su duka ukun. Pillow ya kai hannu ya ɗauka ya soma jifan Zainab da ke gabanshi kafin ya sake lalubo wani yana faɗin, 

“Za ku fasa masu n kunne…”

Sai dai kafin hannun shi ya kai Asad ya riga ya miƙa ma Anees yana sake ɗauko wani, da gudu Zainab ta miƙe ta ɗauki pillow ɗin da ya jefeta da shi ta zagaya ta ɗauke ɗayan tana cillashi nesa. 

Zagaye Labeeb suka yi, ya haɗe fuska, ya buɗe baki Anees ya soma doka mishi pillow ɗin a fuska, kafin yasan me ke faruwa ko ta ina yake jin pillow ɗin. Dariyar da yake ta hana shi magana. 

Mamdud ne ya shigo ɗakin. 

“Mamdud give me a hand…”

Ɗayan pillow ɗin Mamdud ya ɗauko ya taya su. 

“Mamdud cewa na yi ka taimaka min.”

Girgiza mishi kai Mamdud yayi yana dariya da faɗin, 

“No way… Ina bayan ƙannaina.”

Hayaniyar da suke ne yasa shigowar Zulfa gidan ta yi ɗakin. Salati ta saka tana ajiye jakarta bakin ƙofa. 

“Taron dangi kukai mishi ko…wallahi ku ƙyale shi.”

Ta faɗi tana ƙarasawa, pillow ɗin hannun Zainab ta soma fisgewa, tana harar Asad, dariya yayi yana wurga pillow ɗin kan gado ya kuma karɓe na hannun Anees da ya ɗan ware mishi ido. 

Da ido shi ma ya bashi amsar da ke fassara ‘Zulfa ce’ murmushi kawai Anees ya yi. 

“Yaya Mamdud kaima ka shiga black list.”

Dariya Mamdud ya yi. 

“Haba sweet sis. Ni ɗan kawo agaji ne.”

Labeeb da ke maida numfashi ya ce, 

“Traitor!”

Yana harar Mamdud ɗin, hannun Labeeb zulfa ta kama da faɗin,

“Taso mu tafi.”

Ba musu ya miƙe yana binta. Anees ya kalli fuskar Asad da yadda yake bin hannuwan Zulfa da Labeeb da kallo. Ɗan taɓa shi yayi suma suka fice daga ɗakin zuwa falo. 

Labeeb kam hannun Zulfa ya sake dumtsewa cikin nashi kafin ya saki da sauri yakai hannunshi kan goshinta yana kula da yadda fuskarta take a kumbure. 

“Zazzaɓi kike yi Zulfa.”

Ya faɗi cike da damuwa. Murmushin ƙarfin hali ta yi mishi, da ace zazzaɓi ne kawai da abin ya mata sauƙi. 

“Stress ne kawai. Da na huta shikenan.”

Cikin idanuwanta ya kalla. 

“Anya? Mu je asibiti.”

‘Yar dariya ta yi. 

“Ba sai mun je ba, watsa ruwa kawai zan je in yi in kwanta.”

Ba don ya so ba ya ce, 

“In har kika tashi bacci bai sauka ba za mu je asibiti.”

“Deal…”

Ta faɗi tana wucewa abinta, sai da ta biya ta ɗakinsu inda Zainab da Mamdud ke zaune suna gardama da bazata ce ko ta mecece ba, jakarta da ta bari ta ɗauka ta fice ta barsu. 

Asad ya kalli Labeeb, muryarshi ba wasa ya ce, 

“Ka yi hakuri Yaya.”

Ɗan murmushi Labeeb yayi. 

“Ya wuce, kar ya sake faruwa dai. Yaushe ne tafiyar?”

“Sati ɗaya bayan bikin Zainab.”

Kai labeeb ya ɗaga mishi, cikin kanshi yake lissafi. Satika shida ya rage bikin Zainab. Har mamakin yadda lokacin yaja haka yake yi. Da nauyi a zuciyarshi ya fice daga gidan.

BAYAN WATA ƊAYA 

Labeeb zai iya cewa abinda yasa ranakun watan sukai mishi saurin wucewa don yana da abu muhimmi da zai yi a kowacce rana ne. 

Dole ya ɗauki hutun aiki saboda hidimar bikin Zainab. Hatta Mummy da kanta ta dawo gida, Dady ne kawai bai kai da dawowa ba. 

Tunda Labeeb yake bai taɓa sanin nutsuwar zuciya irin yadda yake ji ba a yanzun. Rabonshi da wani abu na kayan maye tun ranar da ya faɗa ma Ateefa yana sonta. 

Club da party babu wanda ya fasa. Mata ne ko rage zafin da yake da su ya daina. Soyayyarta ta nutsar da shi, daga ranar da ya faɗa mata yana sonta bai sake taka gidanshi na Barnawa ba. 

Ateefa a wajenshi ba kowace mace bace. Yana son komai tare da ita ya zamar musu dai-dai. Don yana Bauchi ma da suka yi waya ya sa tai mishi kwatancen gidansu. 

Can yake zuwa duk idan yana da lokaci su sha hirarsu. Kasancewar gidansu ba damuwa suka yi ba. Musamman ganin Labeeb ɗin na sakin kuɗi, yasa bai cika zuwa da yamma ba. 

Don ba shi da wadataccen lokaci, sai dai bayan isha’i. Ko kusa Mamdud bai taɓa kawo ma ranshi komai ba, suna haɗuwa da Ateefa kamar yadda suka saba. 

Sonta banda ƙaruwa babu abinda yake yi a zuciyarshi. Bata faɗa mishi suna soyayya da Labeeb ba dan har ranta ta ɗauka ya sani, tana jira ya fara mata maganar ne da kanshi. 

Don sosai take jin kunyar ita ta fara tayar mishi da maganar. A zuciyarta bashida banbanci da Yaya Mustapha. 

Labeeb bai faɗa mishi bane saboda babu wanda ya sani banda Zulfa. Yana son ya ɗan bar abin a zuciyarshi na wani lokaci, kafin ya sanar da su. Ya ga ya ture bikin Zainab da kuma tafiyar Arif. 

Don in suka sako shi a gaba ba za su barshi ya sha iska ba. Musamman Mamdud da yakan ce zai ga macen da zata nutsar da zuciyar Labeeb ɗin waje ɗaya. 

Banda ramewar da Zulfa ta yi ba za ka ce wani abu na damunta ba. Labeeb yayi ta faɗa, ta ce kawai hidimar makaranta ce ta ramar da ita. 

Ganin babu abinda ya canza a yanayin mu’amalarta ya sa Labeeb ya ƙyaleta. Beside in wani abu na damunta tana faɗa mishi ko bai tambaya ba. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 29Rayuwarmu 31 >>

1 thought on “Rayuwarmu 30”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.