Sallar Magariba kawai ya yi, sai da ya kira Anty ya tambayeta asibitin da suke kafin ya faɗa wa Mami ya je duba Yumna. Tukunna ya sauko ya ɗauki mota.
Sai da ya tsaya kan hanya ya siya musu fruits mai yawa tukunna ya ƙarasa. Da sallama ya tura ƙofar ɗakin. Daga ita sai Anty
Idanuwanshi ya tsaida akan Yumna da take kwance tana bacci, fuskarta, yanayinta da komai suka zauna a zuciyarshi da wani yanayi na daban.
Har a fatarshi yana jin igiyoyin da suka ƙulle su tare, yana jin hijabin dake tsakanin su ya. . .