Skip to content
Part 34 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Sallar Magariba kawai ya yi, sai da ya kira Anty ya tambayeta asibitin da suke kafin ya faɗa wa Mami ya je duba Yumna. Tukunna ya sauko ya ɗauki mota. 

Sai da ya tsaya kan hanya ya siya musu fruits mai yawa tukunna ya ƙarasa. Da sallama ya tura ƙofar ɗakin. Daga ita sai Anty 

Idanuwanshi ya tsaida akan Yumna da take kwance tana bacci, fuskarta, yanayinta da komai suka zauna a zuciyarshi da wani yanayi na daban. 

Har a fatarshi yana jin igiyoyin da suka ƙulle su tare, yana jin hijabin dake tsakanin su ya yaye. Yana jin yadda zai kalleta duk yadda yake so, yadda ta zama halaliyar shi. 

A duk yau, ita ce abu na farko mai kyau da ya faru da shi, abu guda ɗaya da ya sa shi yake tsaye akan ƙafafuwanshi a yanzun. 

“Dawud…”

Anty ta faɗi a sanyaye, sai ya ji kunya ta rufe shi, sam ya manta gaishe da ita ya kamata ya yi. Ƙarasawa yai cikin ɗakin sosai ya ajiye ledar da ke hannunshi a ƙasa tare da faɗin, 

“Anty ina wuni? Ya mai jiki? Sannu da ƙoƙari.”

Cike da tausayawa ta kalle shi, da raunukan da ke fuskarshi. Tasan duk wahalar da suka yi kafin su kawo inda suke yanzun. 

“Da sauƙi, sannu kaima, Allah yasa yau ya zama ƙarshen wahalhalun ku.”

“Hmm…”

Kawai Dawud ya iya amsawa, addu’arta na taɓashi fiye da zatonta, yau zai zama ƙarshen wahala a rayuwar Yumna. Zai tabbatar da hakan. 

Sai dai bashida tabbas a tashi rayuwar da sabon hargitsin da ya kunno musu. Kujera ya ja ya zauna. A koda yaushe mutum ya zauna yakan samu wata nutsuwa ko yaya take. 

Musamman shi da ya samu awanni a tsaye, amma babu abinda zamanshi ya saukar mishi banda sabon tunani. Shiru suka zauna kowa da saƙe-saƙen da ke zuciyarshi. 

Kafin Dawud ya kalli Anty, ya san tana da nata iyalan da suke buƙatar kulawarta, iya ƙoƙari da karamci babu wanda bata yi musu ba. 

“Anty bazan iya gode miki ba, babu kalaman da zan yi amfani da su, addu’a ita kaɗai zan iya miki. 

Nasan kina da naki hidimomin, zan kwana da Yumna yau.”

Kallon shi ta yi sosai. 

“Bakomai wallahi, in kana da hidimominka ka je, zan iya sake kwana.”

Girgiza mata kai ya yi, Yumna na ƙarƙashin kulawarshi yanzun, tana cikin hidimonin shi. 

“Babu abinda zan yi.”

Sauke numfashi Anty ta yi ta miƙe, ‘yan kayanta ta tattara, dama jikinta sanye yake da hijabinta. Miƙewa Dawud ya yi yana zaro wallet ɗinshi, dubu biyar ya zaro. 

“Ki hau mota Anty.”

Da ƙyar ya samu ta karɓa, sai da ya ɗiba mata rabin fruits ɗin ya ce ta kai wa yara tukunna suka yi sallama da cewa za su yi waya.

Hannuwanshi Dawud ya sa ya dafe kanshi da su yana maida numfashi, sai yanzun ciwukan da ke jikinshi wanda ba daga ciki suke ba suke mishi zafi. 

Ko ina na jikinshi ciwo yake, ga jirin da yake gani. Magunguna yake buƙata, ya sani , pain killers da kuma na hawan jinin shi. 

Ba zai iya barin Yumna ita kaɗai ba, kar ta tashi tana buƙatar wani abu, sosai ya ja kujerarshi daf da gadon ya ɗora kanshi a jiki.

Sai yanzun yake tuna tun jiya da rana rabon cikinshi da wani abu, shi ma sai da Mami ta tsare shi tukunna ya ci. Shi kaɗai ma ya isa ya saka shi jirin da yake ji. 

Kwata-kwata bashi da appetite, tunanin cin wani abu ma neman saka shi amai yake yi. Ko ta ina komai baya mishi daɗi, duniyar ta birkice mishi. 

Buɗe idanuwanta ta yi a nutse, ta sauke su kan Dawud, murmushi ne ya ƙwace mata, ko ina na ɗakin take dubawa bata ga Anty ba. Ta kai hannu ya fi sau biyar ta taɓashi tana kasawa.

Don haka ta zaɓi ta ɗan bubbuga gefen da kanshi yake jingine, ɗagowa ya yi da sauri, yanayin da ya sa kanshi jujjuyawa. Dafewa yai da sauri yana faɗin, 

“Ya Rabb…”

Yumna da ke kallonshi bata san lokacin da ta kai hannunta kan nashi da ke dafe da kanshi ba tana miƙewa. 

“Menene?”

Take tambaya cike da kulawa, ɗayan hannunshi ya sa ya kama nata yana dumtsewa tare da bin hannuwan nasu da kallo, yana jin yadda yake da ikon yin hakan yanzun. 

Sadda kanta ta yi ƙasa a kunyace, da sauri ya kai ɗayan hannunshi yana ɗago mata haɓa. 

“Duk yau ke ce abu na farko da zuciyata ta nutsu da shi. Karki ɓoye min Yumna…”

Ya ƙarasa maganar da wani yanayi da ya sanyaya mata jiki.

“Ya jikinka?”

Ta buƙata muryarta can ƙasa. 

“Magunguna kawai nake buƙata…”

Miƙewa ya yi daga kan kujerar ya koma gefen gadon daf da ita ya zauna, kanta ya tallaba ta baya yana haɗa goshin shi da nata tare da lumshe idanuwanshi. 

Yana tuna yafda zuciyarshi ta tarwatse jiya da tunanin rasa ta, da ya ganta kwance bata numfashi. 

“Na ɗauka na rasaki kema, na ɗauka zan sake ci gaba da rayuwa da wata sabuwar kewar…”

Kallon shi take sosai, tana jin hucin numfashin shi a kan fuskarta, zuciyarta ke wani irin dokawa. 

“Allah ya kawo min kai lokacin da nake buƙatar tallafi, shigowarka rayuwata alkhairi ne. Da ba ka zo ba jiya, ƙila da bana na…”

Bai bari ta ƙarasa ba, idanuwanshi har lokacin suna rufe yana samun nutsuwa daga yanayin da suke, yakai hannunshi ya rufe mata baki, kafin ya sauke shi da faɗin, 

“Ina da hoton a zuciyata, ba sai kin tuna min yadda na kusan rasa ki ba.”

Duk da kunyarshi da take ji ta ture gefe ɗaya ta saka duka hannuwanta jikin kumatun shi. Mijinta ne, yau ta zama mallakin shi kamar yadda ya zama mallakinta. 

Bai bari komai ya tsayar da shi ba wajen tabbatar da haka, wani yanayin sonshi ya taso mata. 

“Banda abinda zan ba ka da dukkan karamcin da ka yi min.”

“Karki daina sona, shi kaɗai nake buƙata.”

Ya faɗi da sauri. Lumshe idanuwanta ta yi itama, har lokacin fuskokin su a haɗe suke. 

“Ka faɗa min damuwarka, ka kareni daga duniyarka na tsawon lokaci, ka bani dama in shigo ciki.”

Shiru ya yi yana jin buƙatarta, yasan abinda ya kamata ne, ta ji damuwarshi, sai dai zuciyarshi bata son ɗora mata nauyin raba damuwar shi. 

Baya son ta ji komai banda kwanciyar hankali. Jin yai shiru yasa ta sake riƙe fuskar shi sosai. 

“Karka barni a waje, duniyar ka ta zama tawa yanzun, ka karɓeni a matsayin mata, karka barni a ƙofar duniyarka…”

Yanajin yadda kalamanta da kansu suke buɗe mata ƙofa ba tare da izinin shi ba, matsayinta ya canza. Muryarshi da wani irin yanayi ya ce, 

“Zulfa ke da ciki, wata uku, sai yau na ji ba daga wajenta ba…a bakin mutumin da na yarda da shi da kulawarta fiye da kaina…”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shi ne abinda Yumna ta shiga jerowa tana sake riƙe fuskarshi sosai cikin hannuwanta, tana jin kamar ta karɓar mishi ciwon da bata san zafin yadda yake jin shi ba. 

Tasan yadda yake ƙaunar ƙannenshi, yadda baya son komai ya taɓa su, tasan raunin rashin Sajda ne farkon damar da ta samu ta shiga zuciyarshi. 

Bata taɓa zaton ɗazu da suka yi waya abinda ya faru da shi ba kenan, ta rasa abinda ya kamata tai mishi, ta kuma rasa kalamai, banda Innalillahi da take ta maimaitawa. 

“Cikin El ne Yumna…”

Wannan karon buɗe idanuwanta ta yi, fuskarshi ta saki ta raba fuskokin su, sannan tai hugging ɗinshi, sosai ta riƙe shi a jikinta. 

Hannunshi ya zagaya yana ƙara gyara zamanshi yai hugging ɗinta shima. Sosai zuciyarshi ke buɗewa, baisan lokacin da sabbin hawaye suke zubar mishi ba. 

Kewar Ummi da Abba na sake dawo mishi sabuwa. Muryarshi na rawa yana sake riƙe Yumna sosai a jikinshi yake faɗin, 

“Ƙanwata yumna… Ni ya kamata na tabbatar hakan bai faru da ita ba…laifina ne da na yarda da El har haka… Ummi ba zata taɓa yafe min ba…”

Kukan da ta ji yana yi ne gaba ɗaya ya karya mata zuciya, ita kanta bata san lokacin da kukan ya ƙwace mata ba. Ta rasa abinda za ta yi mishi ya samu sauƙi. 

“Wata ƙaddarar ba a kauce mata… Karka ɗora wa kanka laifin da ba ka da ikon yin komai akai… Ina sonka… Ina sonka sosai.”

Sake matse ta yai gam a jikinshi yana jin yadda hakan ke fifita mishi ciwukan da ke mishi ciwo. Sun daɗe sosai a haka, bata sake shi ba sai da ta ji jikinshi ya daina kyarmar da yake yi. 

Hannuwanta ta sa tana goge mishi fuskarshi. 

“Ina kuka kamar yaro ko?”

Ya buƙata cike da rauni, ɗan ture mishi kafaɗa ta yi, komin shi na burgeta, idanuwanta ta kai kan ledar fruits ɗin da ke ƙasa, saukowa ta yi ta ɗauka ta koma kan gadon da ita. 

Ledar da ke da gwanda ta fiddo ta miƙa mishi, ya girgiza mata kai. 

“Bazan iya jurar wani abu ya sameka ba, don Allah ka ci wani abu…”

Karɓa yayi, ba don yana so ba, haka ya shanye tas, ta sake buɗe mishi wasu tana bashi, sai da ta tabbatar ko yaya ne abinda yacin zai ɗan riƙe shi. 

“Ka je ka siyo magungunan da kake buƙata…Zan yi sallah kafin ka dawo.”

Kallonta yake yi, kafin ya ɗan ɗaga kai da faɗin, 

“Ba za ki buƙaci komai ba?”

“Ka je ka dawo babu matsala in sha Allah.”

Ta faɗi tana ɗan tura mishi kafaɗa da hannunta, miƙewa ya yi yana sake goge fuskarshi. Kafin ya nufi ƙofar ya fice daga ɗakin, 

Saukowa ta yi daga kan gadon ta nufi toilet a zuciyarta take jin babu macen da ta kaita sa’ar samun miji mai zuciya irin ta Dawud. 

***** 

Shima bai dawo ba sai da yai sallar Isha’i tukunna, sa’adda ya dawo tana zaune akan gadon. Ya samun waje ya zauna tare da ajiye ledar magungunan shi da ya siyo. 

Sai lokacin ya ɗauki takardarta ya dudduba, ya mayar ya ajiye, matsawa ya yi daf da ita, yana duba ciwukan da ke jikinta, ya taɓa wuyanta ko da zazzaɓi. 

“Kanki na ciwo?”

Girgiza mishi kai ta yi alamar a’a, sosai yake mata tambayoyi har ya ji abinda yake son ji, tukunna ya ɗauki magungunanta ya bata ta sha, shima nashi ya sha. 

Tukunna ya zaro wayarshi a aljihunshi ya kira Tayyab ya faɗa mishi yana wajen Yumna ɗin, a nan zai kwana kuma. Shiru suka yi su dukkan su. 

“Ko kina jin yunwa?”

Ya tambaya. 

“Na sha fruits ɗin nan, bana jin cin komai kuma.”

Kai ya ɗan ɗaga mata, ta ja jikinta tana hawa kan gadon sosai ta kwanta, don magungunan da ta sha har da wanda za su sakata bacci saboda hutun da take buƙata. 

Tana kwanciya likita na shigowa don ya sake ganinta. Sosai fara’arshi ta ƙaru. 

“Da ban shigo ba, Doctor Dawud Maska, ka ce patient ɗin a ƙarƙashin kulawarka take.”

Murmushin ƙarfin hali Dawud ya ɗora a fuskarshi yana miƙewa ya ba shi hannu suka gaisa. 

“Matata ce.”

Ya faɗa wa Doctor Yakub ɗin da babban likita ne, sun haɗu ne wajen wani taro na asibitin da Dawud ɗin yake aiki. Gaisawa suka yi ya fita yana musu fatan samun sauƙi tare da tsokanar Dawud ɗin. 

Komawa ya yi ya zauna a gefen gadon, Yumna ta kalle shi ta ce, 

“Ka kwanta mana.”

Hannunshi ya kai ya shafi gefen fuskarta. 

“Ke dai ki yi bacci.”

Girgiza kai ta yi, don tasan ya ma fita buƙatar baccin. 

“Don Allah ka kwanta…ko ba ka yi bacci ba ka ɗan huta.”

Baya son yawan surutu, tashi ya yi ya kashe musu wutar ɗakin, yai amfani da hasken wayarshi ya hau kan gadon sosai yana faɗin, 

“Tashi ki gani.”

Babu musu ta tashi zaune, kwanciya ya yi kan gadon, ya janyota ya kwantar da ita a jikinshi don ya musu kaɗan, sosai ta sake gyara kwanciyarta a jikinshi tana haɗe jikinta waje daya. 

Kunyar shi mai nauyi na saukar mata, addu’o’i yayi musu, wannan karon murmushin shi har zuciya da tunanin Ummi a duk lokacin da zai yi addu’ar kwanciya bacci. 

Tun Yumna na motsi yana sake gyara mata kwanciya har ya ji yadda yanayin kwanciyar ta ya canza a jikinshi, sumbatar goshinta ya yi. 

“Saida safe…”

Ya faɗi a hankali yana rufe nashi idanuwan ba don zai iya bacci ba, baya iya bacci da wani a kusa da shi, balle kuma Yumna a jikinshi take gaba ɗayanta. 

Ko shi kaɗai ne ba lallai ya iya bacci ba, babu abinda ke mishi yawo a idanuwanshi sai, Ummi, Sajda, Abba, Zulfa, da El. Su suke tsaye a zuciyarshi da ciwo mai zafin gaske. 

**** 

Bai taɓa sanin za ka iya jin bugun zuciyarka har cikin tafukan hannuwanka ba sai yau, da yake riƙe da steering motar shi yake jin yadda hannuwanshi da ke jiki suke fitar da numfashi nasu na musamman. 

Ko ta ina zufa ke fito mishi, baya jin komai cikin kunnuwanshi banda maganar Asad.

“Zulfa ciki take da shi wata uku, Yaya Mamdud cikin Yaya ne a jikinta!”

Tunda ya rufe bakin shi ko ina na jikinshi ke amsa maganar Asad, duk wani abu da yake faɗa bayan wannan ta iska yake wucewa cikin kunnenshi. 

Tashin hankali tun da ya buɗe idanuwanshi, tun kafin ƙwaƙwalwarshi ta soma fahimtar menene shi ya tsinci kanshi a ciki. 

Sai dai na yau ya sha banban da kowanne, dishi-dishi yake ganin titi, kanshi ke wani irin bugawa saboda rashin nutsuwar da yake ciki. 

Baisan yadda akai ya ƙarasa gidanshi ba, kawai ya ganshi a bakin gate ne, hannunshi na rawa ya yi parking din motar ya bude gate din, da ƙyar ya iya shigar da ita ya dawo ya rufe ƙofar. 

Da nauyi mai girma ƙafafuwanshi ke ɗaukar shi zuwa cikin gidan, yana tura ƙofar ya taka ƙafafuwanshi ciki ya tsaya komai ke dawo mishi. 

Abinda yake ta ƙoƙarin rufewa tun faruwarshi, abinda yake son da duk wani abu nashi ya zama mafarki, abinda yake sha wa mugayen ƙwayoyi don ya manta. 

Abinda ya sake gurbata rayuwar shi ya sa shi neman mata babu adadi a rana don ya goge tasirin shi daga jikinshi, girgiza kanshi yake yana faɗin, 

“Please no… No… Please… Ni mai laifi ne… Zunubaina na da yawa. Allah ka hukuntani ta hanya daban banda wannan…”

Ƙafafuwanshi ne suka kasa ɗaukarshi, a wajen ya durƙushe kan gwiwoyinshi, kanshi ya haɗa da tiles ɗin wajen yana sakin wani irin gunji kamar zuciyarshi za ta faɗo. 

Da ciwo marar misaltuwa yake kokawa da ƙwaƙwalwarshi don kar ta dawo mishi da ranar da baya son tunawa. Amma ina, ranar Talatar da komai ya faru ya soma dawo mishi. 

***** 

Zaune yake a ɗakinshi da kofuna guda biyu, sai robar ruwan da ya zuba ma kwayoyin da yake jira su ƙarasa narkewa. Cup ɗaya na lemo ya ɗauka ya kwankwaɗe. 

Yana jan iska mai ƙarfi ta hancin shi saboda yadda yake jin cocaine ɗin da ya shaƙa bata ƙarasa shiga inda yake son ta je ba. Babu abinda ke mishi yawo cikin kanshi sai hotunan Labeeb da Ateefa. 

Sai yadda ya gansu ɗazu sun fito daga Stop n Shop, yadda suke cike da farin ciki kamar komai na duniyar su dai dai yake tafiya. Ba farin cikin su bane damuwar shi. 

Zuciyarshi da ya rasa yadda zai yi yaƙi da ita, sosai yake jin abubuwan da yai ma Labeeb ɗin, sosai yake kewar abokantakar su. Yake kewar yadda zaman su yake. 

A wani ɓangare sosai yake jin wata irin tsanar yadda Labeeb ya kasance. 

“So fucking perfect…”

Ya faɗi yana zuba ruwan a kofi ya sha, me yasa Labeeb ba zai faɗa wa su Asad suna faɗa ba, me yasa zai barsu kamar komai lafiya ƙalau ne. 

Kullum, a duk rana da wani irin tsoro da bai taɓa sanin shi ba yake kwana yake tashi, tsoron na manne a zuciyarshi a duk kiran wayar ɗaya daga cikin su da zai yi receiving. 

Gani yake koyaushe suma zai rasa su, ko yaushe Labeeb zai iya abinda zai sa ya rasa su Asad suma, kamar yadda ya so Ateefa yasa ya rasa abotarsu. 

Kanshi ya dafe da hannuwanshi yana jan numfashi, wayarshi da ke ajiye kan kujera ya ji tai ringing. Ya ɗauko ya duba, ganin ‘Zulfa’ rubuce a jiki yasa zuciyarshi dokawa. 

Kamar ba zai ɗaga ba, har sai da ta kusan yankewa tukunna ya ɗaga ya kara a kunnenshi. 

“Yawwa… Don Allah inata kiran yaya. Ko kuna tare?”

Tsaki ya ja a zuciyarshi, kanshi na jujjuyawa da ƙwayoyin da ke bashi caji. Da kashewa zai yi sai ya yi tunanin gara ta zo, ya faɗa mata yama Labeeb abubuwan da ya san ba zai yafe mishi ba. 

Gara duk su sani ya daina zama da tsoron rasa su a kullum, in za su yafe mishi su yafe mishi wanda yasan ko kowa yayi son da Zulfa take ma Labeeb bazai bari ba. 

“Yays Mamdud…”

“Yana nan.”

Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. In ta gane gidan da yake shikenan, in bata gane ba ita ta sani, miƙewa ya yi yana tangadi ya ƙarasa bedroom ɗinshi. 

Yana shiga ya faɗa kan gado, baisan bacci ya yi ba, me ya faru, ƙwaƙwalwarshi ba za ta iya tuna mishi ba, abu ɗaya zai iya ganewa, sa’adda ya fito daga bedroom ɗin yamma ta yi sosai. 

Duhu ya fara yi, sama-sama yake ganin yarinya kwance kan kujera, ɗan sosa kanshi yayi, yana taɓe baki don baisan sa’adda ta zo ba ko sa’adda ya kirata. 

Kayan da ke jikinshi ya soma ragewa yana takawa ya ƙarasa inda take, hannu ya ɗan sa ya daki goshin shi don dishi-dishi yake gani. Faɗa mata ya yi ba tare da tunanin komai ba. 

Baccin da take sai da ta farka, tana ihu da ture shi, ƙwayoyi ke mishi aiki, sam baisan me yake yi ba har sai da burinshi ya cika akanta, bata iya ko motsawa. 

Kuka kawai take kamar ranta zai fita, gefenta yake kwance idanuwanshi a rufe yana jin kukanta na ƙara mishi ciwon kai na daban. 

Miƙewa ya yi da ƙyar ya sake nufar bedroom ɗin ya shiga banɗaki ya sakar wa kanshi ruwa mai sanyi, kafin ya samu ƙwayoyin suka ɗan fara sakinshi. Sai da ya tsarkake jikinshi tukunna ya fito.

Kaya ya samu masu matsakaicin nauyi ya saka a jikinshi, yana jin cajin da cocaine ɗin take bashi har lokacin kafin ya fito falon, kuka yake ji sama-sama. 

Ya ƙarasa fitowa cikin falon sosai, kallo ɗaya yai mata duk wani maye dake jikinshi ya sake shi, idanuwan shi kamar za su faɗo ƙasa saboda girman da suka ƙara. 

Ƙafafuwan shi su suka fara yin sanyi, dole ya tsugunna, da rarrafe yake ƙarasawa inda take, zuciyarshi ta yi wani sanyi, yana jin yadda take ƙoƙarin tsayawa a ƙirjinshi. 

Zama ya yi a ya tusata gaba yana kallo, yana son fahimtar abinda ya faru, hannunshi na rawa ya kai don ya taɓata a zuciyarshi yana addu’a, yana roƙon Allah ya sa abin nan ya zama wani mugun mafarki ne ba gaske ba. 

“Zan daina shaye-shaye…wallahi bazan sake kusantar wata mace da ba halal ɗina ba in har yau ya kasance mafarki…”

Mamdud ke faɗi ba tare da ya san kalaman a fili suke fitowa ba, hannu ya kai ya taɓata, da wani zafin nama ta miƙe tana bige hannunshi tana ihu

“Karka taɓa ni… Karka taɓa ni…Yaya Mamdud ka wargaza min duniyata… Ka raba ni da darajata… Allah ka ɗauki rayuwata… Allah karka bar idanuwana su fita waje… Wayyo Allah na…”

Zulfa ke faɗi da wani irin tashin hankali tana kuka kamar ana zare mata ranta. Mamdud baisan zafin mutuwa da ake faɗa ba tunda ba ta same shi ba. 

Sai dai ya san a duniya da wahala wata ƙaddara ta sake samunshi ya ji irin abinda yake ji a yanzun, Zulfa da yanayinta yake kallo yana irin addu’ar da ta gama. 

Gara mutuwarshi da ya wayi gari da sanin ya aikata abinda ya aikata a yanzun. Muryarshi da duk wata gaɓa ta jikinshi na kyarma yake soma faɗin 

“Zulfa…”

“Kar bakinka ya sake faɗin sunana… Wallahi Allah ba zai barka ba… Na shiga uku… Allah me yake faruwa da ni haka… Wace irin ƙaddara ce wannan?”

Ja take da baya tana wani irin kuka da ke tarwatsa komai da ke manne da zuciyar Mamdud, rayuwar shi ta lalace, ya lalata ta Zulfa. Ko mafarkin abinda yai mata yayi in ya tashi da safe sai ya bar garin don kar ya tabbata. 

Girgiza kai yake, yana kallo ta miƙe tsaye, wani gunjin kuka ta saki tana kasa tsayuwa, dole ta koma ta zauna tana kuka mai tsuma zuciya. Gaba ɗaya doguwar rigar da ke jikinta ta yi cuku-cuku. 

Mamdud ya kasa ɗauke idanuwan shi daga kanta, daga yanayinta da yake saka shi tsanar kanshi kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu. 

Ta yaya za a ce shi ne yai ma Zulfa wannan abin? Da wasu idanuwa zai kalli Labeeb? Da wanne idanuwa zai kalli su Asad, me zai ce musu. 

“Mafarki nake… Don Allah yau ya zama mafarki…”

Shi ne abinda Mamdud yake faɗa muryar shi na karyewa, yana kallon yadda zulfa ta rarrafo ta ɗauki mayafinta da jakarta, da rarrafen ta kai ƙofa ta dafa bangon tana miƙewa da ƙyar. 

Shi ma da ƙyar ya iya miƙewa, gaba ɗaya jikinshi ya yi sanyi. Binta ya yi kafin ta ƙarasa ficewa yana riƙe mata riga. 

“Zulfa…”

Wani irin mari ta ɗauke shi da shi, kafin ya san me yake faruwa ta sake ɗauke shi da wani irin mari wanda ya fi na farko, muryarta ɗauke da wani irin yanayi ta ce, 

“Ka ƙyaleni! Yaya Mamdud ka ƙyaleni! Ko ka ƙarasa kashe ni tunda babu abinda yai saura…”

Matsawa yai da baya, a haka ya ci gaba da matsawa har yai nisa da ita, tukunna ya dafa kujerar wajen yana zama, kanshi ya jingina da kujerar yana jin jan ƙofarta ya san ta fita daga gidan. 

Girgiza kanshi yake.

‘I am going to hit you hard El-Maska. Zan lalata abinda yake da kusanci da kai…’

Mamdud ke tuna kalaman da ya yi ma Labeeb ɗin, furuci ne da ya yi cikin fushi, ba don yana nufin abinda ya ce ba. Sai dai ya riga da ya zo akan gaɓa. 

Ya furta, Allah kuma ya ƙaddara faruwarshi, ya san ya taɓa abinda ya fi kusanci da Labeeb. Ya yi kuskuren da ba zai gyaru ba, ba ta haka ya so ya taɓa Labeeb ba. 

Ba wannan bane nufin shi, ba shi bane a zuciyarshi, faɗanshi da Labeeb ne, duk da ba kowane zai yarda ba, yana jin yadda komai ya ƙare. 

Yana jin yadda ya biyewa zuciyarshi, yana jin yadda komai ya ƙare, yadda ya rasa Asad, Anees, Zainab, Arif. Da faɗin sunan Arif ya ji wasu hawaye sun zubo mishi. 

Ko ina jikinshi ɓari yake, ya kasa yarda shi da kanshi ne yaima Zulfa fyaɗe. Ya kasa yarda sam wannan ƙaddarar ta faɗa mishi, ya kasa yarda da gaske ya yi abinda zai ja ya rasa Arif. 

Bai samu shekaru uku na rayuwar Arif ba, amma sauran a hannunshi yayi su, kusan shi ya raine shi, yana jin shi fiye da ƙani. Zainab…

Iska yake fitarwa ta bakinshi saboda ya kasa yi ta hancin shi, duk da AC ɗin ɗakin zufa yake sharkaf, sauran hawayen shi sun maƙale sun kasa zubowa.

Ƙirjinshi zafi yake yi, da sauri ya juya, ruwan da yake ajiye kan table ɗin ya kalla, an shanye fiye da rabi, hannu ya kai yana riƙe bakin shi cikin sabon tashin hankali. 

Abinda Zulfa ta sha kenan ya bugar da ita ya sakata barci har ya ɗauka ɗaya daga cikin matan da yake bi ne. Miƙewa ya yi ya ɗauki robar ya buɗe ya shanye, da gudu ya nufi kitchen ɗinshi yana buɗe-buɗe. 

Duk wani abu da ya iya ɗora hannunshi akai shanyewa yake. A ƙofar kitchen ɗin ya faɗi, tun yana ganin haske har duhu ya maye gurbin shi.

***** 

Girgiza kai Mamdud yake ya samu da ƙyar ya kwace kanshi daga tunanin da ya faɗa. Iska yake ja yana fitarwa kamar mai koyon yin hakan. 

Tun ranar, kwanakin wata ukun nan sun zo mishi da tashin hankali da babu kalaman da za su taɓa fassarawa. Da wayarshi tai ringing sai ya ji zuciyarshi ta zo mishi har cikin wuyanshi. 

Duk sa’adda zai ɗauki wayar ɗaya daga cikin su Asad a tsorace yake, a duk minti ɗaya na kowace rana da zai wuce yana zo mishi ne da tunanin rasa su. 

Yau ɗin nan da Labeeb ya zo Naf Club ya same shi da maganar Zulfa sai da hanjin shi suka hautsina. Ya ɗauka komai ya ƙare, cikin idanuwa ya kalli labeeby ya faɗa mishi yai ma zulfa fyaɗe. 

Kalaman kawai sun isa su ƙarasa wargaza abinda yai saura a zuciyarshi. Mari yai kaɗan, bai kamata Labeeb ya mare shi ba, ya faɗa mishi ne don ya ɗauki mataki. 

Don ya taimaka mishi yai masa hukuncin da ya kamata ko zai samu sauƙin abinda yake ji, ya rasa ƙwarin gwiwar bin Labeeb bayan ya fita daga club ɗin. 

Tashin hankalin shi bai ƙaru ba sai da Zainab ta kira shi, sai bayan sun gama wayar ne ma ya kula da text ɗin da tai mishi. Bai je party ɗin bikin Dawud don Wani abu ba. 

Ya je ne don yai ma su Asad kallon ƙarshe ba tare da ya ga tsanarshi a cikin idanuwan su ba, ya je ne ya gansu da ƙaunar da suke mishi don ya riƙe ta a ranshi. 

Ƙaunar da bai cancanta su yi mishi ba, sai dai zuwan ya ƙara mishi sabon tashin hankali da ya ninka fyaɗen da yai ma Zulfa. Jin cewar akwai cikin shi a jikinta. 

Jin cewar Zunubin da ya aikata zai shafi abinda ke cikinta, zunuban shi za su taɓa mutuncinta da darajarta, jin cewa ya gama tarwatsa rayuwarta. 

Ga illa irin ta lokaci, idan ya wuce ka ya wuce kenan, babu damar komawa baya ka gyara kuskuren da ka aikata, balle ya koma baya ya warware son zuciyar da ya bari ya fara rinjayar shi tun daga farko. 

Allah kaɗai ya san girman ƙaunar da yake ma yaran da ba nashi ba, Shi kaɗai kuma yasan girman son da yake ma yaranshi tun kafin ya haife su. 

Tunanin wani na nan, da ya cutar tun kafin zuwanshi, zafin da yake ji kamar ana soka mishi wuƙa a abinda ya yi saura a zuciyarshi. 

A karo na babu adadi Labeeb ya ɓoye zunubanshi, wannan karon ya ɓoye abu mafi girma daga cikin zunubanshi, yadda ya ga hukuncin da ya kamata ace shi yake fuskanta a idanuwan Asad, Zuciyarshi ta sake watsewa. 

Da komai yake son faɗa ma Asad ba laifin Labeeb bane amma ya kasa, kamar an dasa shi haka ya tsaya yana kallon shi. 

Bai taɓa ganin mutum kalar Labeeb ba. Sanin shi a rayuwarshi ita ce kyauta mafi girma. Labeeb ya nuna mishi muhimmancin ‘yan uwantaka, da zai iya komawa da ya sake komai. 

Labeeb ya karɓi ɗanshi da ke cikin Zulfa saboda ya kare abinda ya yi saura a darajarta. Da zai yi kuka wataƙila da ya samu sauƙin abinda yake ji. 

Ya rasa ina ya kamata ya tsayar da tunanin shi, ya rasa wanne daga cikin zunubanshi ya kamata ya soma dubawa, wanne ya kamata ya fara tubar wa. 

Dukkan su masu girma ne, ya rasa wa ya fi cutarwa, kanshi, Labeeb da zuri’arshi, ya rasa. Ko ta ina rayuwar shi ta yi ƙunci da muni. Yana nan zaune aka kira sallar Isha’i. 

Da ƙyar ya kai kanshi bedroom yai alwala, ko sallar Magariba sai lokacin ya yi ta. Kunya yake ji. In haka tashin hankalin duniya yake baisan yadda na ƙiyama zai kasance ba. 

In yana tunanin ba shi da idanuwan da zai kalli su Zainab da saboda shi sanin cikin Zulfa nashi ne ba na Labeeb ba, baisan da idanuwan da zai tsaya a gaban Allah cikin jama’ar duniya gaba ɗayanta da tarin laifukan da suke kanshi ba. 

Haka ya yi sujuda, sai lokacin hawayenshi suka soma zubowa, har ya idar da sallar basu daina zuba ba, jan jikinshi yai ya hau kan gado ya kwanta. 

Kuka yake marar sauti, kuka yake da ya fi kowanne ciwo, kukan da yake ji a ko ina na jikinshi, wayarshi da ke aljihunshi tai ƙara alamar shigowar saƙo, a yanayin da yake baisan abinda ya ja shi ya fito da ita ba. 

Arif ne, ya bude saƙon

“Na ƙagu in zo in ga dukkanku, awanni kaɗan ya rage in zo airport… Ina kewarku sosai… Love and missed you fiye da kowa.”

Wannan karon kukan ne ya fito mishi da sauti tun daga bayan maƙoshin shi. Bazai iya rasa su ba, ba zai ɗauki rashin su ba, yana ƙaunar Arif fiye da yadda yake son kanshi. 

Baisan mintinan da ya ɗauka ba, kuka dai yake kamar ranshi zai fita kafin wayarshi ta soma ringing, hannunshi na rawa ya duba, arif ɗin ne ya sake kira. 

Yasan irin kiran nan kaɗan suka rage mishi, ƙila ma wannan ne na ƙarshe da zai samu, da sauri ya ɗaga yana karawa a kunnenshi. 

“Lafiyar ka dai Yaya? Na ga ba reply? Nasan kome kake baka share saƙona.”

Arif ya faɗi da sanyin murya, kukan Mamdud ya sake tsananta, har Arif ɗin ya ji shi. 

“Yaya… Yaya Mamdud… Menene? Kowa lafiya? Don Allah kai min magana… Su yaya lafiyan su? You are freaking me out….”

Arif ya ƙarasa muryarshi na karyewa. Da sauri, cikin kuka, muryar Mamdud a dakushe yace 

“Kowa lafiya…”

“A’a kai ba lafiyarka ba… Dan Allah ka fadamun…me ya sameka?”

Hannu Mamdud ya sa yana goge hawayen fuskarshi wasu sabbi na sake zubowa.

“Laifi nai muku Arif… Laifi babba….bansan ko zan yafe ma kaina ba balle in nemi yafiyar ku…”

Mamdud ya ƙarasa maganar kuka mai sauti na sake ƙwace mishi, Arif ma kukan yake yi. 

“Family na yafe ma junansu, ko menene na yafe maka… Su Yaya ma nasan za su yafe maka… Wallahi muna ƙaunarka… Ina ƙaunarka sosai… Don Allah ka daina kuka.”

“Hmm…”

Kawai Mamdud ya iya faɗi, Arif ba zai gane girman laifin da ya aikata ba, ba zai taɓa fahimta ba. 

“Bari in kira Yaya in roƙe shi…”

Arif ya faɗi, da sauri Mamdud ya ce, 

“A’a… Ka barshi… Just… Don’t hate me… Don Allah karka tsane ni.”

Yana jin yadda Arif ya sauke numfashi. 

“Yaya Mamdud kai ka raine ni…ko Mummyna bata jure ba… Ya zan tsaneka? Don Allah ka daina bana so.”

Kai Mamdud yake ɗagawa ba don yasan ya zai daina kuka yake yi ba, ko ya zai daina jin abinda yake ji 

“Za ka zo airport ka ɗauke ni…promise za ka zo.”

Da ƙyar ya iya faɗin, 

“Zan zo Arif…Ina ƙaunarka fiye da rayuwa da kanta.”

“Ina ƙaunarka Yaya Mamdud… Be safe please.”

Kai kawai ya ɗagawa kamar Arif na ganinshi sannan ya sauke wayar daga kunnenshi. Dunƙule jikinshi ya yi kan gadon yana sake sakin wani kukan. 

Baisan lokaci na wucewa ba, kuka yake har aka kira sallar Asuba a kan kunnenshi. 

**** 

Sake matsawa ta yi jikin Mami akan gadon da suke kwance, ta kai hannunta kan cikinta tare da rufe idanuwanta, Zuciyarta tokare da yanayin da ta kasa fassarawa. 

Tana jin cikin kanta yadda komai yake mata yawo, kamar a mugun mafarki haka take kallon kanta, take kallon ranar data sauya mata rayuwa. Komai da ya faru ne yake dawo mata.

*****

Tun tana makaranta Labeeb ya kirata, yanayin muryarshi tasan yana cikin damuwa, jin tana makaranta yasa shi cewa ta bari sai ta dawo. 

Tun da ta fito daga class ɗinta na ƙarshe na ranar take kiran wayarshi bata samu, addu’a take Allah ya sa lafiya, don tasan matsalarshi yanzun bata wuce Ateefa. 

A zuciyarta babu abinda ya canza daga soyayyar da take ma Labeeb, ta dai haƙura da shi ne, a duk rana a shekarar nan da auren shi da Ateefa take jin yadda yai mata nisa. 

Tana ƙin sauraren kowa ne, tana laɓewa bayan karatu tana ƙin kula samari, ta san lokaci ya kusan zuwa da dole za ta samar ma wani mazauni a zuciyarta da bata san inda za ta matsar da Labeeb don shi ya zauna ba. 

Tana fitowa daga cikin makaranta tai tunanin kiran Mamdud, in har abinda take tunani ne, Labeeb matsala ya samu shi da Ateefa, ba zai nufi gida ba, wajen Mamdud zai yi. 

Shi ma da tun kamun auren Labeeb ya bar kwana gidansu, sai dai ya zo ya koma abinshi. Kiran wayarshi ta yi, aikam ya faɗa mata Labeeb ɗin na tare da shi. 

Ba tunanin komai ta tare mai Napep ya sauke ta a ƙofar gidan Mamdud ɗin, ta bi ta ƙaramar ƙofar gate ɗin ta wuce, ta mayar ta tura kamar yadda ta ganta. 

Yunwa ke damunta, tana zuwa za su fito da Labeeb su biya ta ci wani abu sai su yi maganar da za su yi, da sallama ta tura ƙofar da zata shigar da ita falon, sai ta ji gidan ya yi wani irin shiru. 

Ƙarasawa ta tu cikin falon ta zauna tana sauke numfashi, ruwa ta gani ajiye a roba, ta cika cup ɗin da ke ajiye ta kwankwaɗe ma cikinta. Sai da ta ajiye cup din ta ji wani irin taste da ya kama mata harshe.

Ko mintina biyu bata yi ba ta soma jin wani yanayi, kafin mintina biyar ɗakin ya soma jujjuya mata, tasan tana ihun kiran sunan Labeeb, sai dai batasan ko ya fito fili ba, ko iya zuciyarta ya tsaya. 

Jikinta gaba ɗaya ya gama mutuwa, kan kujerar ta faɗi, numfashin da take fitarwa kanshi na neman zamar mata aiki. Kafin ta ji wani irin shiru, komai ya tsaya. 

Bata sake sanin me ake ba sai da ta ji mutum akanta da wani yanayi marar daɗin faɗi, kafin zuciyarta ta gama gane me yake faruwa jikinta ya fara ƙoƙarin ƙwacewa daga abinda ke shirin faruwa da ita. 

Sai dai ko me tasha cikin ruwan ya riga ya gama lalata mata duk wani ƙarfi nata, tsoron da bata taɓa sanin akwai shi a duniya ba ya kawo mata ziyara. Kuka take tana ture shi ba tare da tana da nutsuwar ganin ko waye ba. 

Bata fahimci tashin hankali ba, bata san ɗacin mutuwa wajen shi daban ba sai da ta ji an rabata da mutuncin ta. A duniya macen da ta tsinci kanta cikin yanayin da take yanzun ne kawai za ta iya fahimta. 

Zuciyarta sai da tai tsayuwar wucin gadi, sai lokacin ta ware idanuwanta akan fuskar Mamdud, wata tsayuwar ta daban zuciyarta ta sake yi ganin kowa ya rabata da mutuncinta. 

Ganin kowa yai mata wannan aika-aikar, kallon shi take, fuskarshi na zama da tambarin da za ta ɗauka har mutuwarta manne a ko ina na jikinta. 

Wajenta da cikinta take jin Mamdud, take jin tsanarshi, azabar da take ji ba komai bace akan tashin hankalin da take ciki. Ba za ta taɓa komawa dai dai ba. 

Rufe idanuwanta ta yi, numfashinta take so ya tsaya, Allah take so ya ɗauki rayuwarta kafin ta fita waje idanuwa da kunnuwan wani su ji, su ga abinda ya faru da ita. 

Sam bata san tana kuka ba, don abinda take ji a yanzun duk ya girmi waɗannan abubuwan. Tana kallon shi ya miƙe ya bar falon, ko hannunta ta kasa motsawa. Kuka kawai take kamar zuciyarta za ta fito. 

Fuskarshi take kallo, yanayin shi take kallo, yadda yake ganinta cikin tashin hankali, duk wani abu da ya faru bayan nan wuce mata kawai yake yi. 

In ta ce ga yadda akai ta fito da kanta daga gidan ƙarya take, ko ina na jikinta kyarma yake, waje ta samu a bakin ƙofar gidan Mamdud ta zauna. 

Jakarta ta buɗe tana fito da wayarta, Labeeb za ta kira, ta girgiza kai, a firgice take, gaba ɗaya rayuwarta ta gigice, ba za ta iya faɗa mishi ba. 

Ba ta san me za ta ce ba, ba ta san yanda zasu kalleta ba, ita ta zo gidan Mamdud, ita ta ɗauko ƙafarta ta kawo ta gidan, me zai faru in ta faɗa. 

Kowa zai san Mamdud yai mata fyaɗe, Mami, Yaya, su Tayyab , duk ‘yan gidansu, numfashinta ne ya soma shirin ɗaukewa. Ba za ta iya kallon fuskokin su ba sanin sun san abinda ya faru da ita. 

Mutum ɗaya za ta iya kira, Nabila, ita kaɗai take jin za ta iya kira a wannan yanayin, tana wani irin kuka ta kira Nabila tai mata kwatancen inda take. 

Ko mintina ashirin ba ta yi ba ta iso da motarta, makarantar su ɗaya da Nabila, ba ajin su ɗaya ba. Wajen Matric suka haɗu har suka yi wata irin shaƙuwa ta ban mamaki. 

Tana fitowa daga mota kallo ɗaya taima Zulfa ta san ba lafiya ba, kamata ta yi ta saka ta a mota, bata tambayeta komai ba sai da suka je gida. Saida ta zaunar da ita. 

Tare suke kuka, kuka mai cin rai da ƙaddarar da ba za ta canzu ba, a gidansu Nabila tai wanka, ta sake kaya. Anan ta tabbatar Nabila tai mata alƙawarin abinda ya faru zai tsaya a tsakanin su. 

Nabila ta sauke ta har gida, daren ranar bata iya runtsawa ba, har gari ya waye, ko ya ta rufe idanuwanta bata ganin komai sai Mamdud.

Har da safe hannuwanshi take ji manne a jikinta, da kyar tai sallah tai wanka ta koma ta kwanta, ko da Asad ya ƙwanƙwasa mata ta fito ya sauketa a makaranta ya wuce aiki ce mishi ta yi bata da lectures sai sha biyu.

Bata iya ta fito ba, ba ta da lafiya, rashin lafiyarta kala ne na daban. Tana nan kwance Labeeb ya shigo ɗakin, tana sauke idanuwanta akanshi komai ya kwance mata. 

Wani irin kuka ta ji ya ƙwace mata, da sauri ya ƙarasa ya zauna a gefen gadonta. 

“Zulfa… Menene? Me akai miki?”

Yake tambaya a rikice, da ƙyar ta iya miƙewa daga kwanciyar da take, kanta ta ɗora kan kafaɗarshi, tana saka duka hannuwanta ta riƙo rigarshi. 

Wani irin kuka take da gaba ɗaya ya rikita shi, kuka take kamar za ta mutu. 

“Don Allah ki faɗa min ko menene.”

Bata san ta yaya za ta faɗa mishi abinda ya faru da ita ba, ta rasa kalaman da za ta yi amfani da su, da ƙyar muryarta ke fita ta ce, 

“Ummi… Yaya ina kewar Ummi…”

Riƙeta ya yi a jikinshi yana lallashinta, kuka ta yi kamar ranta zai fita. Da ƙyar ya samu tai shiru, ya kwantar da ita, zama ya yi don haka ta rufe idanuwanta kamar ta yi bacci. 

Tana jinshi har ya fita daga ɗakin, abinda take ji a zuciyarta in aka ajiye mata Mamdud aka bata wuƙa babu abinda zai hana ta kashe shi. 

Duk da ta ji kalamanshi, yanayin shi, ba a cikin hayyacin shi yake ba, amma hakan ba zai zama excuse na rabata da mutuncin ta ba.

***** 

Buɗe idanuwanta Zulfa ta yi, tun daga ranar komai ya canza mata, babu wanda ya kula da yadda ta kai sati biyu ko kuzarin kirki bata da shi. 

Babu wanda yasan yadda kullum take ƙoƙarin binne abinda ya faru da ita, yadda take son ta koma dai-dai ta kasa. Labeeb kawai ya kula da canzawarta. 

Tun yana tambaya har ya haƙura. Bata sake ganin Mamdud a zahiri ba, a baɗininta, a mafarkinta, kullum yana ciki. Nabila bata sake ɗaga mata maganar ba. 

Ko da bata ga period ɗinta a watan farko ba dana biyu bata kawo komai ba, takan yi wata uku bata ga al’adarta ba. Duk da babu mata da yawa irinta. 

Tana jin canji a jikinta, duk da babu ɗaya da ke nuna alamun tana da ciki kamar yadda ta kan ji mata sun yi , cikinta da yake shafe kamar zai haɗe da mararta ne da ta ga ya taso. 

Lokacin ta fara shiga tashin hankali, lokacin ta fara zargin abinda take son binnewa zai fito ba ‘yan gidansu ba kawai har duniya ma sai ta gani. 

Sake maƙale jikin Mami ta yi, komai ya jagule, da ta faɗa tun ranar ƙila da abinda yake faruwa yanzun bai faru ba, da Dawud da Labeeb basu yi faɗa akan abinda bai aikata ba. 

Laifinta ne, duk ita ta ja komai. Da bata ɗauki ƙafarta ta je gidan Mamdud ba, da ta faɗa ma ko Mami abinda ya faru da ita da wasu abubuwan sun kauce ma faruwar su. 

Bata san dalilin Labeeb na karɓar cikin da ke jikinta ba, shi ya fi komai ɗaure mata kai, ko da wasa bata kawo ma ranta ta haka yake nufin gyara komai ba. 

Sam hawaye sun ƙi zubo mata ko zata samu sauƙi. Asad… Zuciyarta ta kira mata, sai yanzun take ganin komai, duk wasu alamomi, duk wasu maganganun shi. 

Runtsa idanuwanta ta sake yi tana tausaya ma halin da yake ciki a yanzun, tana tausaya ma rayuwar su gaba ɗayanta. 

Cikin sanyin murya mami ta ce, 

“Zulfa kiyi bacci dan Allah… Tunanin nan ba zai canza komai ba…”

“Na kasa Mami…bacci ya daɗe da yi min nisa… Na daɗe bana samun shi yadda ya kamata…”

Zulfa ta faɗi, tana jin rashin Ummi a kusa da ita, tana jin tsanar Abbansu da kewarshi a lokaci ɗaya , kewarshi da ta jima bata ji ba. 

“Bansan me yasa nake jin kewar Abba ba…”

Ɗan dafa kafaɗarta Mami ta yi. 

“Komai ya kusan zuwa ƙarshe… In sha Allah Abbanku ya kusan dawowa gare ku…”

Mami ta faɗi da yarda mai girma a cikin muryarta da ta sa Zulfa faɗin, 

“Ta Yaya Mami? Mun rasa shi shekaru masu yawa ba tare da ƙasa ta rufe mishi ido ba…”

“Ki yarda da ni… Komai ya kusan zuwa ƙarshe… Za ku ga yadda Allah yake Ikon shi akan azzalumai. Allah ya bamu ikon cinye jarabawar ki shi ne damuwata… “

Mamin ta ƙarasa muryarta na karyewa. Shiru zulfa ta yi tana juya kalaman Mami ɗin, tana tunanin yadda za a yi Abbansu ya dawo wajen su.

Da tunanin duniya, rikicinta, ruɗani da jarabawar da indai kana da rai babu ranar da za ka daina fuskantarta fal a zuciyarta, kan kunnuwanta akai kiran sallar farko.

Tana jin yadda gari ya waye ba tare da ta san da me zai zo musu ba. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 33Rayuwarmu 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.