Skip to content
Part 33 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Ƙafafuwan shi Labeeb ya ja ya haɗe kanshi da gwiwa ya rufe idanuwanshi ko zai samu sauƙin juyin da kanshi yake yi. Babu abinda ke mishi yawo sai Mamdud. 

Yau yake ƙara jin rasa shin da yayi, daga maganganun Zulfa yasan Mamdud ya ruguza alaƙar su ta hanyar da ba ya jin za ta gyaru. 

Da yana da hope, yana da tunanin cewar a shekara da ɗori da suka yi Mamdud na faɗa da shi, tunda babu abinda ya canza tsakanin shi da su Asad, wata rana zai yafe mishi. 

Wata rana Mamdud zai gane daga shi har Ateefa ƙaddararsu ce ta zo a haka. Zai dawo su koma kamar yadda suke da. Abubuwa da yawa ne suke mishi yawo cikin zuciyarshi. 

***** 

Tafiya suke shi da Mamdud za su ƙarasa inda motarsu take, ya ga Mamdud ya koma baya da sauri. 

“Ina kuma za ka je?”

Labeeb ya buƙata, Mamdud bai amsa shi ba, titi ya ga ya tsallaka, ya tsaya yana kallon ko me zai yi. Wasu yara ne guda biyu ƙanana, dukkansu mata sanye da uniform. 

Mamdud ya kama hannayensu ya tsallako da su titin, ya yi tsaye sai da ya ga sun sha wata kwana tukunna ya ƙaraso yana faɗin, 

“Allah ya ba ka yara sai ka ga na sakin su kamar bakomai bane. Don Allah ya za a yi yaran nan su iya tsallaka wannan titin? 

In mota ta kaɗe su ko wani abu ya same su fa?”

Murmushi Labeeb ya yi yana mamakin kalar son yara irin na Mamdud. 

“Meye kake wani murmushi.”

“Son yaranka ya yi yawa.”

Dariya Mamdud ya yi. 

“Shi ya sa zan auri mata biyu. Don in haifo su da yawa. In zo gidanka in tattara naka duk in haɗa da su.”

Sosai ya ba Labeeb dariya. 

“You are welcome. Ka ga sai ni da matata mu samu damar producing wasu yaran.”

Girgiza kai Mamdud ya yi.

“Baka jin kunyata El-Maska”

Tari Labeeb ya yi, Mamdud ya kai mishi naushi ya kauce yana dariya.

*****

Sauke numfashi Labeeb ya yi, yana mamakin abinda zai sa Mamdud yai musu haka. Yana mamakin lokacin da zuciyar Mamdud ta sauya. 

Zuciyar shi da ya sani da tausayi da burika masu kyau. Ba tsana da burin ɗaukar fansa ba, Mamdud ɗin da ya sani ba haka yake ba. 

Mamdud ɗin da ya sani cikin hankalin shi ba zai yi musu haka ba.

‘I raped her!”

Kalaman Mamdud suka dawo mishi. Numfashi ya ja yana fitarwa cike da ƙunar zuciya. Kamar daga sama ya ji an dafa shi.

*****

Suna karya kwanar da za ta kaisu inda Dawud ya ce za su samu Labeeb suka hango shi zaune a ƙasa, ya haɗe kanshi da gwiwar shi. 

Ƙarasawa suka yi, har lokacin bai ko ɗago ba, da alama baisan ma suna wajen ba, Zainab ta fara dafa shi. Ɗagowa ya yi da sauri ya sauke idanuwan shi cikin nata. 

Tsakanin jiya da ta ganshi zuwa yau, ya yi zuru-zuru, kallo ɗaya za ka yi mishi ko baka sanshi ba ka fahimci babu nutsuwa ko alamar kwanciyar hankali a tare da shi. 

Gashin kanshi duk ya cukurkuɗe waje ɗaya. 

“Zee Zee…”

Ya kira muryarshi ɗauke da wani yanayi. Sai da ta haɗiye kukan da take jin yana shirin zo mata tukunna ta ce, 

“Me yasa Yaya?”

Girgiza mata kai Labeeb yake yi. 

“Babu… Banda dalili.”

Kai ta ɗan ɗaga mishi tana ɗorawa da,

“Da gaske yaro kake da shi Yaya?”

“Eh…karki tambayeni ko ta ya…wallahi har yanzun bansan daga inda ya fito ba.”

Labeeb ya ƙarasa yana ɗaga kanshi ya kalli su Asad. Sai yanzun maganganun da Asad yayi suke dawo mishi. Hannun shi ya kai ya kamo na Asad, bai mishi musu ba ya zauna gefen shi. 

Muryar labeeb na rawa ya ce, 

“Bansan kana sonta ba Asad, ban taɓa sani ba…”

Shiru Asad ya yi, ba shi da abinda zai ce ma Labeeb ɗin da ya wuce shirun. Numfashi Labeeb ya ja. 

“Tee za ta barni… Ta tsane ni ita ma…kuma nasan kun tsane ni…”

Ya ƙarasa yana dafe kanshi cikin hannuwanshi, gyara zamanshi Asad ya yi ya kama kafaɗar Labeeb ɗin yai hugging ɗinshi. 

Sosai Labeeb ya ruƙunƙume shi yana buƙatar comfort ɗin. Ta ko ina yake jin rayuwa na pulling ɗinshi. Asad so yake ya faɗa ma Labeeb bai tsane shi ba, amma wani ɓangare na zuciyarshi na cewa ya bar Labeeb ɗin ya ɗauka ya tsane shi na ɗan wani lokaci. 

Ɗagowa Labeeb yayi yana kallon su ɗaya bayan ɗaya. 

“I am sorry, so so sorry…”

Ya ƙarasa yana jin wasu irin hawaye masu ɗumi na cika mishi idanuwa. Zainab ta sa hannuwanta ta tallabi fuskar shi, lokacin hawayen da ke cike da idanuwanshi suka samu zubowa. 

“Mummy, Dady, duka fushi suke da ni… Fushin su yana ɗaga min hankali…Abin ya min yawa…”

Girgiza mishi kai Zainab take yi

“Ban tsaneka ba Yaya… Ina son in tsaneka saboda abinda kai wa Zulfa. Ta yaya za ka fara?… Gaba ɗaya rayuwarta ta lalace…duniyarta duka ta tarwatse Yaya… I want to kill wanda yai mata haka… Amma ni abin yake kashewa saboda kai ne…”

Ture hannuwan Zainab Labeeb ya yi daga fuskarshi yana jin wasu hawayen na zubo mishi. Wannan dalilin ya sa shi ɗaukar cikin jikin Zulfa a matsayin nashi. 

In family ɗinshi suka san na Mamdud ne, baisan abinda za su yi ba. In maganar ta wuce cikin gidansu, kamar yadda Mamdud ya faɗa ne da bakinshi. 

Ba rayuwar shi kaɗai Labeeb zai taɓa ba, har da ta Zulfa, har jarida sai ta shiga saboda ta haɗa jini da shi. Kaɗan ake jira a samu kuskure a tare da shi ko wani nashi. 

Yasan akwaidubban mutanen da ke da hotunan shi da na ahalinshi. Ko ina za su ga fuskar Zulfa. Duk inda ta wuce mutane za su kalleta. 

Kowa da yadda zai fassara abinda ya faru da ita. Zuciyarshi za ta iya ɗaukar tsanar ‘yan gidansu duka, za ta iya ɗaukar rasa Ateefa da abinda ke cikinta. 

Amma ba zai iya jure abinda gaskiyar cikin Zulfa za ta haifar ba. Zuciyarshi cike da rauni yake faɗin, 

“Zan gyara komai… I will fix this. Bansan ko ta yaya ba… Zan auri zulfa…”

“Ka makara Yaya… Abinda ya kamata ka yi ne tuntuni. Ya Allah… Tunanin me kake yi?”

Anees ya fadae yana jingina da bangon wajen. Ganin yadda Labeeb ke zubda hawaye kamar wani ƙaramin yaro ya sa Zainab miƙewa. 

Fuskarta ta goge kafin ta kalli Labeeb ta ce mishi,

“Ina Anty Ateefa ɗin?”

Da hannu ya nuna mata ɗakin da ke kusa da su, tura ɗakin ta yi tana shiga, hakan yasa Ateefa da ke kwance kan gadon ta ci kuka har ta gode wa Allah ta tashi zaune. 

Jajayen idanuwanta ta sauke kan Zainab da ta ƙarasa ta zauna a gefen gadon da Ateefa take. Ba ta da lokacin ɓatawa, ba ta da kalaman da za ta tsaya comforting ɗin Ateefa da su. 

“Yaya ya ce za ki barshi… Banda bakin da zan ce ki yafe mishi, I like you saboda Yayana na sonki, i like you more saboda yadda na ga kina son shi. 

Yayana yayi kuskure babba, don Allah ki bashi dama ya gyara…”

Ganin hawaye sun zubo ma Ateefa yasa na zainab ma suka zubo kafin ta ci gaba da faɗin, 

“Karki barshi… Kin ganshi can… Kuka yake wallahi. Kuka yake kamar yaro, abinda ban taɓa ganin yana yi ba. 

Ki yi mishi kowane irin hukunci amma karki barshi… Karki ƙara mishi ciwo fiye da wanda yake ciki…”

Zainab ta ƙarasa maganar kuka na cin ƙarfinta. Ita kanta Ateefa kukan take yi, kafin a hankali ta sauko da ƙafafuwanta daga kan gadon ta miƙe tsaye. 

Wajen ɗakin ta fito, Labeeb na ganinta, hankalin shi a tashe ya ware idanuwa akanta. Hannunta ya ga ta miƙa mishi da sauri ya miƙa nashi cikin nata.

Yana jin yanayin hannunta da yake da yaƙinin cikin hannuwa dubu zai iya ganewa. Yana jin yadda ta dumtse yatsun ta cikin nashi, ba shi da kalamai. 

Su dukkansu basu da kalamai, soyayyar su bata ginu akan wannan ba, da tuni ta ruguje, idanuwanshi da ke cike da hawaye yasa cikin nata, ɗan ɗago hannunshi ta yi alamar ya miƙe.

Ba musu ya miƙe ba tare da ya bari idanuwan shi sun sauka daga cikin nata ba. Kallon shi take ita ma tana tuna irin halin ya shiga kafin ya aureta.

Yadda ya ture surutan kowa saboda ita, yadda ya nuna mata ƙauna a duk ranakun da ta kasance tare da shi, yadda ya nuna mata asalinta ba komai bane a wajen shi. 

Ba za ta manta da wannan karamcin ba, kamar yadda ba za ta manta abin da ya faru ba yau. Yana da tarin bayanan da zai mata. 

Kallonta yake sosai, kallonta yake kamar yana tsoron da ya yi kuskuren ɗauke idanuwanshi daga kanta za ta ɓace. Yana tuna yadda ta fannoni da dama kasancewarsu tare ta fuskanci barazana. 

Akwai ranaku da ba zai manta ba, abinda ya ziyarci zuciyarshi na ɗaya daga cikin irin wannan ranar. 

**** 

“Ji nake kaman kar in tafi.”

Labeeb ya faɗi yana daƙuna fuska, dariya Ateefa take mishi. 

“Ba sati biyu kawai za ka yi ba? Kana magana kamar ba za mu dinga waya ba.”

“Um um ni waya yamin kaɗan…”

Ya faɗi yana kai hannu ya ɗauki coke ɗin gwangwani da ya kasa tuna lokacin da ya ajiye shi cikin motar, tun kafin ya bar shan kayan maye watanni huɗu da suka wuce baya ganin coke ya ƙyale. 

Yanzun abin ya zame mishi wani irin addiction, ko da sanyi ko babu. Wannan ɗin ma da ya fasa babu sanyin, sha yayi, sai yake jin kamar taste ɗin ya ɗan canza. 

Ateefa ya miƙa wa ta girgiza mishi kai. 

“Saboda nasa baki shi yasa ba za ki sha ba?”

Ware idanuwa ta yi. 

“Bana son sharri El-labeeb…”

Sake miƙa mata yayi, karɓa ta yi ta kurɓa sau ɗaya ta miƙa mishi, coke bai cika damunta ba, ko ta ce lemuka irin haka gaba ɗaya ba damunta suka yi ba. 

“Kowa na ma sunan saurayin shi style ke kam… Capital zero.”

Ya faɗi yana turo laɓɓan shi, dariya ta yi, har mamakin yadda yake sata dariya haka take yi. Ko me ya yi dariya yake bata, ko me ya yi jin shi take har ranta. 

Yanayin murmushin shi, yadda yake yi da bakinshi.

“Ina son sunanka, yana min daɗi, beside kaima ba wani suna ka bani ba ai.”

“Tee…”

Ya faɗi da sauri. 

“Still cikin sunana ka samo ai…”

“Ba wani, ke dai baki iya kula da ni bane kawai.”

Ya faɗi cikin sigar tsokana yana tsayar da idanuwanshi akanta, wani irin yanayi ne yake fisgarshi, wani abu yake ji da bai kamata ace yana jinshi ba a yanzun. 

Sauran coke ɗin da ke cikin gwangwanin ya ƙarasa shanyewa yana maida numfashi a hankali a hankali yana son calming abinda yake ji. 

“Ya dai?”

Ateefa ta buƙata ganin yanayin da yake jan numfashin shi da fitar da shi kamar mai ɗanɗana iskar ya ji ko tana da wani abin cutarwa. 

Muryarshi a dakushe ya ce, 

“Tafiya zan… Sai mun yi waya.”

Yana ɗauke idanuwanshi daga kanta, cike da rashin fahimta ta ce mishi. 

“Za ka tafi? Me yasa? Me yake faruwa? Ka kalleni El-Labeeb…”

Idanuwanshi da har sun fara sauya kala ya sauke cikin nata, yana mata wani irin kallo da ta kasa fassarawa, gaba ɗaya iskar da ke cikin motar tai musu kaɗan. 

Ita kanta wani irin yanayi take ji da ba shi da alaƙa da kallon da Labeeb ɗin yake mata. A hankali kamar kallon da suke ma juna wani abu ke jansu. 

Ihu zuciyar Labeeb take mishi amma abinda yake ji ya toshe komai, hannunshi yakai ya tallabo fuskar Ateefa da ta kasa ko motsi balle ta yi ƙoƙarin hana shi. 

Bakin shi ya haɗa da nata, ganin abin bana wasa bane, kamar wadda aka kwaɗa wa mari, ta tattara dukkan ƙarfinta ta ture Labeeb tana sa hannu ta goge bakinta cike da jin dauɗar abinda suka aikata manne da shi. 

“El-labeeb…na shiga uku…meye haka?”

Ta ƙarasa cikin kuka, ta buɗe murfin motar tana ficewa. Bata ga Mamdud ba sai da ta kusan cin karo da shi. 

“Bansan me zai yi ki gane ba zai canza ba, da zarar ya samu abinda yake so zai barki kamar sauran…”

Cikin ihu ta ce mishi, 

“Me kake so da mu ne? Me yasa ba za ka barmu mu huta ba?”

Dariya ya yi da ta sa ta fashewa da wani irin kuka ta nufi hanyar gidansu, kan idanuwan Labeeb komai ya faru. Ya kasa fitowa ne daga motar saboda gaba ɗaya jikinshi ya mutu. 

Gwangwanin coke ɗin da ke ajiye a gaban motar ya ɗauka yana ɗigo wanda ya rage kan harshen shi, taste ɗin abinda ke ciki daban da na coke ɗin da yake ɗanɗanawa. 

Mamdud ya kalla da ya ɗora hannunshi ɗaya kan ƙugunshi fuskarshi ɗauke da murmushi. 

“Har na cire rai za ka sha coke din nan kuna tare…”

Hannu Labeeb ya kai ya ja murfin motar, kafin ya murza key ɗin ya tayar da ita. Bazai biyewa rashin hankalin Mamdud ba, ko ya zai ɓata mishi rai zai ƙyale shi har ya gama haukanshi. 

******* 

Hannunshi da Ateefa ta ja ya katse mishi tunanin da yake yi.

“Na ɗauka samun zuri’a da kai shi zai hana ni tafiya, ban ɗauka sonka zai min dabaibayi ba…”

Ɗayan hannunta ta sa tana goge hawayen da suka zubo mata. 

“Bamu gama faɗan nan ba, zamu huta ne kawai.”

Kai ya ɗaga mata yana rasa kalaman magana, wani ɓangare na zuciyarshi na murna da rawar samun nasara ta wannan fannin. In har za ta zauna da shi, za ta daina faɗin za ta barshi. 

Sauran abubuwan ma yana da hope akansu. Zainab ce ta fito daga ɗakin, ta kalli wayarta kafin ta kalle su gaba ɗaya. 

“Kowa na da mintina talatin da ya rage mishi…sai ku shirya kowa na da babban acting ɗin da zai yi ƙarfe huɗu, acting ɗin da babu script balle director.”

Su duka da rashin fahimta a fuskarsu suke kallon Zainab. Ganin basu gane ba ya sa ta faɗin, 

“Walimar bikin Don ƙarfe huɗun yau.”

“Oh shit”

Asad ya faɗi.

“Ya za mu yi?”

Anees ya tambaya, Labeeb Ateefa ya kalla. 

“Bacci nake ji sosai, magungunan da aka bani sun fara aiki. Ku je abinku.”

Ta faɗi a gajiye, buɗe baki Labeeb yayi zai yi magana ta katse shi da

“Karka ƙure no El-labeeb, ko bana jin bacci ina son zama ni kaɗai.”

Kai ya ɗan ɗaga mata ba don ya so hakan ba. Sumba ya manna mata a goshi. 

“Eww…”

Asad ya faɗi, Anees ya harare shi. Ɗan ware idanuwa ya yi don bai ga abinda ya yi ba. Ɗaki Ateefa ta koma, su kuma suka kama hanyar fita daga asibitin. Su ukun motar da suka shigo suka sake shiga suka nufi gida. Labeeb kuma gidanshi ya nufa don ya shirya.

****** 

Suna shiga gida, Zainab ɓangaren su Dawud ta nufa, kanta tsaye ta nufi side ɗinsu tana sallama. Mami da ke ɗaki ta amsa mata. 

Tura ɗakin Mami ta yi ta shiga, ta sameta a zaune, Zulfa na jikinta a kwance, sai ta ji gaba ɗaya komai ya mata wani iri. Abinda take ta dannewa a zuciyarta ya dawo sabo. 

Ta rasa muryar gaishe da Mami. Kallo ɗaya ta yi wa fuskar Zulfa kuka ya ƙwace mata, ƙarasawa ta yi inda suke zaune, Zulfa ta miƙe Zainab ɗin na riƙeta a jikinta. 

Sosai Zainab ke wani irin kuka, Zulfa kam ta ma nemi hawayenta ta rasa. 

“Zulfa…bazan… Bansan me kike ji ba…”

“Hmm”

Kawai Zulfa ta faɗi, daga Allah da ya ɗora mata ƙaddarar nan sai ita ta san abinda take ji. Sai yanzun da Zainab ta ga Zulfa take jin inda Labeeb na kusa da ita sai ta kwaɗa mishi mari. 

Hannun da yake jikin Zulfa ta ji ya yi ɗumi, da sauri tana kuka take taɓa wuyan Zulfa da fuskarta. A rikice take faɗin, 

“Mami zazzaɓi take sosai, jikinta da zafi.”

Cikin sanyin murya Mami ta ce, 

“Na sani Zainab, mun je asibiti ai.”

Hawaye ne suka sake zubo ma Zainab, tana jin kamar ko da zazzaɓin ne ta karɓar ma Zulfa ta ji da abu ɗaya. 

“Da walimar Don za mu tafi… Bansan ko zan iya ba yanzun…”

Da sauri Zulfa ta ce, 

“Ku je…don Allah karku fasa saboda ni…ya kamata Yaya ya samu wani abu dai-dai a yau.”

Kai kawai Zainab ta iya ɗaga mata, ta miƙe tana fita daga ɗakin. Hannunta ta sa tana goge fuskar ta, a hanyarta ta fita ta ci karo da Tayyab. 

Kallonta ya yi a kasalance. 

“Tayyab…”

Ta faɗi muryarta na rawa. Bai amsa ba, kallonta dai kawai yake yi. 

“Laifin yaya ya shafe ni ko?”

Ta tambaya a raunane, shiru Tayyab ya yi, ba zai iya tantancewa ba, haushin kowa da komai yake ji, har da kanshi, saboda haka ba zai gane ba a yanzun. 

Ba zai kuma yi mata ƙarya ya ce ganinta bai ƙara ɓata mishi rai ba. Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafij ta ce, 

“Nasan mutane sun fara taruwa…huɗu ta kusa…ka shirya kaima…”

Ta ƙarasa tana wuce shi da sauri, saboda hawayen da suka zubo mata. Sai lokacin ma ya tuna da wata walima. Yasan yakamata yaje wajen ne don kar mutane su zargi wani abu. 

Su dukkansu suna buƙatar acting normal, Kamar komai lafiya ƙalau, zai iya hakan na awa biyu. Ɗakinshi ya nufa ya samu Dawud ya tashi zaune. 

Ba tare da ya kalle shi ba ya ce, 

“Walima ƙarfe huɗu …”

Kallon da Dawud yake mishi cike yake da fassarori kala-kala. 

“Da abinda yake faruwa da ni zan ji ko hayaniyar mutane? Kana da hankali kuwa Tayyab?”

Juyowa Tayyab ya yi ya kalli Dawud ɗin. 

“Mutane za su zargi wani abu idan bama wajen, tunda mun riga mun gayyace su.”

“Sai da na ce ko za a yi close family kawai.”

Dawud ya faɗi a gajiye. 

“Close family ɗin aka ba damar gayyatar mutum bibbiyu, ba wani yawa ke akwai ba, awa biyu ne kawai. We can survive awa biyu in zai ɓoye zargin wani abu daga mutane…”

Tayyab bai jira amsar shi ba ya shige toilet don ya yi wanka. Numfashi mai nauyi Dawud ya ja yana fitar da shi. Tayyab na fitowa daga wankan shi ma ya shiga. 

***** 

Tana shiga gida har ta wuce tsohon ɗakinta, sai ta fasa ta nufi ɓangaren su Mummy. Ɗakin Mummy ta tura da sallama. 

Zaune ta sameta akan gado ta tusa wani yaro gaba tana kuka, zuciyar Zainab tai wani irin dokawa, yau abubuwan da bata taɓa gani ba, bata taɓa zato bane suke faruwa a gidansu. 

Ƙafafuwanta babu ƙwari ta ƙarasa inda mummy take ta zauna a gefen gadon. Sauke idanuwanta ta yi kan yaron da ke bacci. Zuciyarta ta doka da wani irin mamaki, ba sosai ake samun kama irin ta yaron da take gani da Labeeb ba. 

Da ƙyar ta iya ɗauke idanuwanta daga kanshi ta mayar da su kan Mummy. Wani hanky da ke hannun Mummy tasa ta goge fuskarta. 

Muryarta a dishe saboda kukan da ta yi ta kalli Zainab ta ce, 

“Ke ma do you feel like na zubda ku? Su Asad sun faɗa min maganganun da suka fi wannan yaron na gabana tsaya min a rai…”

Shiru Zainab ta yi, cikin kanta take tunanin lokutan da za ta iya tunawa da Mummy take cikin rayuwarsu gaba ɗaya. 

Daga ita har Dady, sai dai a duk inda ya kamata ace memories ɗin Mummy ne ko Daddy a wajen Zainab bata hango kowa sai Labeeb, tana jin hawayen da suka zubo mata. 

Bata yi ƙoƙarin tarbesu ba, cikin kuka Mummy take kallon Zainab tace, 

“Ki faɗa min Zainab…”

Sosai Zainab take kallon fuskar Mummy, sosai take ganin abinda ya faru da Labeeb, da yadda zuciyarta take buɗewa da tunani da girman haushin abinda Mummy tai musu. 

Yanzu ne take ganin tarbiyarsu Labeeb ne, jinyar su shi ne, makarantar su, abincin su, buƙatun su. Cikin kulawa da su da basu tarbiya ya rasa wanda zai mishi haka. 

Miƙewa kawai Zainab ta yi da shirin barin falon, Mummy ta riƙo hannunta. Fisgewa Zainab ta yi, cikin kuka take faɗin, 

“Me kike son ji mummy?! Me kike so in faɗa miki?”

“E… Everything… Komai…”

Ta ƙarasa muryarta can ƙasa, goge fuska Zainab ta yi wasu sabbin hawayen na sake zubo mata. 

“Ta ina zan fara?… Ta yafda kika watsar da mu? Ko ta yadda bakisan tarbiyarmu ba? A duk sa’adda wani cikin ku, ke ko Dady za ku dawo…binku muke, duk inda kuke, all we want… A Rayuwar bai wuce kulawar ku ba… Lokacin ku… 

A duk wani abu na makaranta da iyaye ne suke je wa yaransu… Lokacin da na karya hannu… Lokacin da Yaya Anees bashi da lafiya… Dukkan mu… Kin san lokacin da kawai kike nan? 

Lokacin da kike ganin kina da ikon yanke mana hukunci akan yadda za mu yi da rayuwarmu….”

Ganin yadda duk kalmar da za ta fito daga bakinta ke ƙara bayyanar da tashin hankali a fuskar Mummy ya sa Zainab yin wani murmushin takaici, sabbin hawaye na zubar mata. 

“Oh Mummy, wannan kaɗan ne… Kinsan ƙiris ya rage na fara shaye-shaye? So so close…ba kya nan… In everything… Baki damu ba…yanzun ma kin damu ne kawai saboda wani cikinmu is not perfect..”

Zainab ta ƙarasa tana juyawa, tana jin yadda mummy ke kiranta amma ko juyawa bata yi ba, balle ta koma. Yaron Mummy ta kalla. 

Kuka take sosai, ko da wasa bata taɓa zaton rashinta na affecting ɗinsu haka ba. Gani take suna da duk wani abu da suke buƙata. 

Ita da Dadynsu sun wadata su da kuɗin da za su yi komai da suke so. Makaranta me kyau, abinci, sutura, kuma duk sa’adda zata gansu cikin farin ciki take ganin su. 

Zuciyarta take dubawa, gaskiyar da ke cikin maganganun Zainab na zauna mata da wani irin yanayi mai nauyin gaske. Kukan da take yi ba na halin da yaranta suke ciki bane tun ɗazu. 

Kukanta ya canza ne minti biyar da suka shige. Kukanta na ɓacin sunan da Labeeb ya ja mata ne. Kukanta na ɗazun na tunanin idanuwan da za ta kalli mutane da shi ne in maganar nan ta fita. 

Cike da wani irin yanayi tana kuka take faɗin 

“Meke damuna? What is wrong with me…wace irin uwa ce ni?”

Tambayoyin da take wa kanta kenan, possibilities na abubuwan da suka fi muni da za su iya faruwa da yaranta na watsar da su da ta yi suna zuwa mata da gudu suna giftawa ta idanuwanta da Zuciyarta. 

*****

Wajen ƙarfe huɗu da kwata su Zainab na tsaye a wajen motarsu, Jarood, Uzair, Aseem da mardiyya suka fito suma. Dukkansu sanye suke da kayan da suka tsara don ranar kawai.

Tsadar kayansu da kyawun su bai taimaka wajen ɓoye damuwar da ke fuskar kowanne daga cikin su ba. Babu wanda ya ce wa kowa komai. 

Suma waje suka samu suka tsaya, kafin Dawud da Tayyab suka fito suma, gaba ɗayansu, kalar kayan su dark brown ne. Amma na Dawud farare ne ƙal, har shiga idanuwa suke yi, suna shirin shiga motocin da ke wajen su tafi motar Labeeb ta shigo wajen.

Parking ya yi, ya fito, shima sanye da irin yanayin kayan da ke jikinsu, idanuwanshi da wani nisantaccen yanayi, kallon su yake ɗaya bayan ɗaya kafin ya sauke numfashi da faɗin, 

“Bansan ko za ku iya yafe min da wuri ba…Ku yi haƙuri da sanadina awannin da ya kamata ku yi farin ciki na yau na ɓata su…”

Babu wanda ya ce mishi komai, asalima motocin su suka shiga, Zainab , Asad, Anees mota ɗaya suka shiga. Dawud da Tayyab sai, Jarood, Uzair, mardiyya, da Aseem suma tasu motar daban. 

Ganin duk suna fita da motocin daga gidan ya sa Labeeb komawa cikin tashi motar yana ɗan dafe kanshi, shekararshi nawa yana acting amma yau baya jin zai iya. 

Emotions ɗin da yake ji sun mishi yawa, tayar da motar ya yi yana bin bayansu, duk da a hankali yake gudu da motar kamar baya son zuwa wajen. 

Don haka ya jima bai ƙarasa ba, ƙafafuwanshi da nauyin gaske ya shiga wajen, mutanen da ke gaba ɗaya cikin wajen ba za su wuce sittin ba. 

Don daga ɓangaren shi bai gayyaci kowa ba, ga mamakin shi hidima ake ta yi kamar yadda aka tsara, yawata idanuwanshi yake a wajen yana duba taron mutanen yana gane fuskokin ƙannen shi. 

Fuskokinsu da kowanne a ciki ya ɗora murmushin da yasan bai wuce ko ina banda fuskar su ba. Zuciyarshi ta yi wani irin dokawa da ya hango Asad tsaye shi da Mamdud. 

Bai zaci Mamdud na da taurin ran zuwa wajen ba, ko da wasa bai ɗauka haka ba, gabanshi na faɗuwa, cikin sauri yake ƙarasawa inda suke. 

Baya son Mamdud yasan abinda ke faruwa da su. Baya son ya ji Zulfa na da ciki, ko da wasa baya so. Yana ƙarasawa kusa da su yanayin da yake gani a fuskar Mamdud ɗin yasan lokaci ya ƙure. 

Asad ya kalli su biyun kafin ya bar musu wajen. Da wani irin yanayi da Labeeb ya kasa fahimta a fuska da muryar Mamdud ya ce, 

“Me kake shirin yi El-Maska?”

Muryar Labeeb a dake ya ce, 

“Ka gama yin iya ɓarnar da za ka yi Mamdud, wallahi zanga ƙarshenka wannan karon in ka ce za ka sake taɓa ta. 

Kuskurena ne da na ɓoye tsakanin mu a wajen su Asad…”

Muryar Mamdud can ƙasa ya ce, 

“Ina ƙaunar su wallahi, kaima ka sani.”

Girgiza kai Labeeb ya yi yana jin kamar ya shaƙe Mamdud. 

“Bansan waye kai ba a yanzun… Zuciyata na kokwanto akan sanin da na yi maka a baya… Ka cika alƙawarinka…ka taɓa min abinda ya fi zuciyata, ka taɓa min dukkan rayuwata…”

Kallon shi Mamdud yake har lokacin da wani yanayi a fuskarshi da Labeeb ya kasa fahimta, raɓa Labeeb ya yi yana wucewa ba tare da ya ce komai ba. 

Labeeb bai da sauran ƙarfin tsayar da shi, asali ma banda faɗuwar gaba da tsoron abinda sanin cewar Zulfa na ɗauke da cikin Mamdud ɗin zai haifar musu yake yi. 

Baisan yadda ya ƙarasa sauran awannin ba, zuciyarshi cike take fal da tunani, har suka yi hotuna banda flashes ɗin kyamarar da ke gifta mishi cikin idanuwanshi komai sama-sama yake jin shi. 

Har suka gama awannin da suka fi kowanne tarihi a rayuwarsu gaba ɗayanta. Ɓangaren Asad kam yana barin su Mamdud tsaye ya koma cikin taron ya hango Mardiyya zaune ita kaɗai.

Baisan me yasa shi ƙarasawa inda take ba, baisan abinda yasa shi zuwa ya ja kujera ya zauna kusa da ita ba. 

“Mardi…”

Ya kira a hankali yadda iya kunnenta ne zai ji, ɗagowa ta yi ta sauke mishi idanuwanta, sai yake ganin yana fahimtar yanayin da ke cikinsu. 

Yana jin kamar yasan abinda ke damunta, kamar ya fahimci abinda take ji. Miƙewa ya yi ya kama hannunta ya ɗagota, babu musu ta miƙe.

Janta yayi suka fita daga wajen gaba daya. Sai da ya samu inda babu hayaniya tukunna ya tsayar da su, ya saki hannunta yana searching fuskar ta da idanuwanshi. 

“Meke damunki?”

Ya buƙata, girgiza mishi kai ta yi idanuwanta na cika da hawaye, ɗan dafe goshi Asad yayi kafin ya ce, 

“Alright in ke ba za ki yi magana ba ni zan yi. Yau na gane yarinyar da nake so tun girmana na ɗauke da cikin Yayana…bai tsaya nan ba sai ga kuma ɗan Yayana an kawo gidan mu. 

Na ɗauka haukan wucin gadi ne ya same ni Mardi… Bansan me yasa nake jin kamar somehow muna cikin shigen yanayi ɗaya ba. 

Zo mu koma na fito da ke don in maimaita miki abinda nasan kin sani…”

Hawayen da suka taru idanuwan Mardiyya ne suka samu damar zubowa. Ji ta yi za ta iya faɗa wa Asaad komai, muryarta a rauna ne ta ce, 

“Ina son ɗan Maigadin mu.”

Ware idanuwa Asad ya yi, Mardiyya ta ɗaga mishi kai tana goge fuskarta da shanye kukan dake son ƙwace mata. 

“Bansan ya akai na fara ba, nasan daga ranar da na ganshi wani abu ya canza a tare da ni. Ba sai na faɗa maka ba, kasan yadda na raina ‘yan ƙauye. 

Ciki har da wasu daga dangin Mamana, kasan yadda nake wulaƙanta duk wani da ke ƙasa da ni. Nice yau zuciyata take dokawa ɗan Maigadi. 

Yaya Asad Allah ne ya nuna min ni bakomai bace ba, Allah ne ya nuna min kowane ɗan Adam abin darajtawa ne ko da bambancin matsayi. 

Danish sunanshi, ko sunana ya tsana balle ni ɗin kuma, yarinyar da a da ko abinci ta dafa bazan iya ci ba, ita yake so. 

Na ganta…a gabanta ya wulaƙantani… A gabanta ya nuna min ni bakomai bace…”

Mardiyya ke faɗi muryarta na rawa, bata san ya akai ba, kawai ji ta yi Asad ya yi hugging ɗinta. 

“Shhh… Mardi… Komai zai yi dai dai. Dukkanmu za mu wuce wannan lokacin… Am here…”

Kai take ɗaga mishi tana jin ta yarda da kalamanshi duk da zuciyarta ciwo take mata. Sun jima a haka, sai da dukkansu suka tabbatar za su iya controlling ɗin emotions ɗinsu tukunna suka koma ciki. 

A daddafe aka gama komai, a daddafe suka ƙarasa ranar, kowa da mamakin yadda hakan ya faru suka shiga motoci suka ja zuwa gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 32Rayuwarmu 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.