Skip to content
Part 32 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Gaba ɗaya duniyar ta cakuɗe mishi waje ɗaya. Bai taɓa sanin tashin hankali irin wannan da yake ciki ba, ya ɗauka zunubanshi sun fara ƙarewa akan rabuwar su da Mamdud. 

Ya ɗauka zafi da ciwon hakan da yake yawo da shi a duk rana ya ishe shi. Ya yi zaton raɗaɗin na taimakawa wajen rage tarin zunubanshi na baya. 

Daga kalmomin Zulfa na jiya komai ya sauya. Daga kalmominta ya gane shi ɗin ba komai bane. Ya soma fahimtar bai isa ya ce zai ma ƙaddara wayau ba. 

Yau ɗin nan, yau ta zo mishi da salo daban, salo ta fannin da bai taɓa tunani ba. In jiya ya hango abinda zai iya faruwa tsakanin shi da Ateefa, ko a mafarki bai taɓa hango yiwuwar ace yana da ɗa ba. 

“El-labeeb ka fita don Allah…don girman Allah ka bar min ɗakin nan in ji da abinda yake damuna ba sai na ƙara da ganinka ba…”

Ateefa ta ƙarasa maganar wasu sabbin hawaye na zubo mata, tana jin iskar da ke cikin ɗakin bata wadatarta. Ga mararta da har lokacin wani irin azababben ciwo take yi. 

Ƙwaƙwalwarta ta kasa processing abinda yake faruwa a lokaci ɗaya saboda tashin hankali. Zuciyarta na jin kamar ta fito daga ƙirjinta. 

Ɓangarori da dama na zuciyarta ya kasu wajaje daban-daban. Cikin Zulfa, cikin da Asad ya tabbatar mata akwai shi. Ga yaron da ta gani, kamanin shi da komai na mata yawo a cikin idanuwanta. 

Wannan karo hawayen da suka zubo mata ciwon su har a tsokar jikinta take jinsu. Labeeb kam kallonta yake yana jin kamar ya rusa ihu. 

Shi ne yau Ateefa take faɗin ya fita ya bar inda take, numfashi ya ja yana fitar da shi a wahale kafin ya ce, 

“Wane tabbaci nake dashi na cewar ina barin ɗakin nan ba za ki yi wani abu stupid ba?”

Bata san lokacin da dariyar takaici ta kubce mata ba. Ta kasa tsaida abinda take ji akanshi. 

“Da gaske ka damu da halin da zan shiga? Da gaske ka damu da lafiya ta?”

“Ateefa…”

Labeeb ya fara, ta ɗaga mishi hannu tare da girgiza mishi kai. 

“No, ka barni in gama. Daga lokacin da na san da Zulfa a rayuwarka nasan ta fi min Mummynka matsala. 

Ban taɓa zaton in za ka bi mata za ka bita ba…”

Runtsa idanuwanshi Labeeb ya yi yana buɗe su, maganganunta sun mishi zafi ba kaɗan ba, sai dai in har tana mishi magana yana da sauran hope akan zamansu. 

Ko me za ta ce kuwa, zai saurara, zai jure, ko ya abin zai mishi ciwo, ba zai taɓa kai na rashinta ba, bai san ya yake ba amma yana tsoron rasa Ateefa. 

Ganin yadda yake kallonta yasa ta ci gaba da faɗin, 

“Ina son ji daga bakinka, ina son jin da gaske cikin Zulfa naka ne…”

Ta ƙarasa maganar tana roƙonnshi da idanuwanta, tana addu’a ya ƙaryata, ya ce mata wannan abin da ke faruwa wani mugun mafarki ne da za su farka daga shi su ci gaba da rayuwarsu yadda suka saba. 

Zuciyarshi gaba ɗayanta gaskiya take son furta mata, aurenshi ne a gabanshi yake kallo, kalaman da duk zai furta zai iya zama sanadin kubcewar matarshi. 

Ɓangare biyu ne suka saka shi a tsakiya suna ja, babu tambaya, babu tunanin komai. Zai iya miƙa rayuwarshi saboda ‘yan uwanshi, Ateefa da abinda ke cikinshi dukansu suna cikin rayuwar shi. 

Muryarshi can ƙasa, kamar mai koyon magana ya ce mata,

“Cikina ne!”

Har zuciyarta sai da tai tsayuwar wucin gadi tukunna ta ci gaba da dokawa da kalamanshi. Ba a kunnuwanta kawai take jin bugun zuciyar ba har cikin idanuwanta. 

Zata rantse har ɗan da ke cikinta shi kanshi zuciyarshi bugawa take saboda tashin hankali. Babu kalaman da za su taɓa iya fassara abinda take ji. 

Ta sha expecting El-Maska zai iya dawowa lokaci-lokaci, ta sha ji a zuciyarta kamar ta mishi kaɗan. Yanayin su da Zulfa ya sha ɗora mata ciwuka kala-kala. 

Tana da kishi, kishin da ko sujjada ta yi sai ta roƙi Allah da ya sauƙaƙa mata shi, don tana tsoron halin da zata shiga in labeeb ya ce zai auri Zulfa. 

Shi ne tsoronta mafi girma, don ta sha ganin yadda Zulfa ta fita matsayi a wajen Labeeb ba tare da ta zama matarshi ba. Ace da Zulfa ya ci amanar aurensu, abin ya girmi tunaninta. 

Ciwon ba kowa ne zai fahimta ba, sai wadda take son mijinta da dukkan zuciyarta, sai macen da mijinta ne komai nata, macen da ta miƙa dukkan farincikinta wajen mijinta ya ci amanarta ta wannan fuskar ne za ta gane. 

Wannan karon hawayen a zuciyarta suke zuba da ciwo marar misaltuwa. Kula Labeeb yayi bata numfashi, da sauri yakama hannunta yana fadin. 

“Tee…breath… Ki taimaka min don Allah.”

Ya ƙarasa yana jin wasu sabbin hawayen na tarar mishi a idanuwa, yau shi ne da arhar hawaye haka. Bai da lokacin mamakin hakan a yanzun. Tare suka ja numfashin suna sakinshi. 

Haka suka ci gaba da yi har tsawon wani lokaci kafin ta tsayar da idanuwanta cikin nashi. 

“Daga yanzun zuwa ko yaushe in zuciyata ta daina bugawa kai ne. Kai ne El-labeeb…”

Ta ƙarasa muryarta na maƙalewa. Tunaninta na ɗibarta zuwa wani lokaci can baya. 

**** 

Magana yake, ita ta buƙaci jin komai na rayuwarshi ta baya, ita ta nemi da ya faɗa mata komai, amma da duk kalma ɗaya da za ta fito daga bakinshi da yadda take ƙara jin kamar yana nisanta zuciyoyinsu. 

“Zan yi ƙarya idan na ce ko da wasa zan iya ƙiyasta yawan matan da na haɗa shimfiɗa da su. Yaran da ni ne namiji na farko a wajen su… Ina tsanar kaina a duk ranar da hakan ta faru. 

Idan yara fiye da goma Allah ya ƙaddara min samu a rayuwata Ateefa na gama zubar da su.”

Ya ƙarasa maganar yana kafe idanuwanshi da suke cike da wani irin yanayi akanta. 

“Me kike son sani kuma? Na faɗa miki iya abinda zan iya tunawa, in kika gujeni bansan me zan yi ba.”

Hawayenta ta sa hannu ta goge. Muryarta na rawa ta ce, 

“Zaɓa ma yarana uba managarci shi ne koyarwar addini na… Bansan ko zunubaina za su wanku ba in na ture wannan na karɓeka. 

Abinda ƙwaƙwalwata ke faɗa min daban da wanda zuciyata take faɗa min, ka yi nisan da ya wuce misali a ciki.”

Sauke numfashi ya yi. 

“Na faɗa miki aure shi ya fara canza ni, zai sake taɓa ni a karo na biyu, fiye da na farko sabo da matsayin ki a zuciyata. Zan ƙarasa canzawa, wallahi zan canza…”

Kallonshi take a tsorace, cire shi a zuciyarta abu ne da tasan da fitar ranta zai yiwu. Karɓar shi kuma abu ne da ke da shakku mai yawa. 

“Idanuwanka akaina haka, ban yarda da zuciyata ba ko ba ka kusa. Za mu yi waya.”

Ta ƙarasa tana buɗe murfin motar da shirin fita. 

“Ateefa… Zuciyata za ta samu nutsuwa ne kawai idan na ji amsarki.”

Labeeb ya buƙata muryarshi ɗauke da yanayin da yake ji. Juyowa ta ɗan yi ta runtsa idanuwanta ta buɗe su akan fuskarshi da ke mata kyau na ban mamaki. 

“Tare da rashin nutsuwar zuciyarka ka haɗa da sanin tawa kanta bata da nutsuwa. Babu ƙarya a son da nake maka. 

Zuciyata na tare da kai El-labeeb, banda zaɓi akan hakan, ka barni in zaɓi miƙa maka dukkan Rayuwata ko akasin haka.”

Kai kawai ya iya ɗaga mata, wani abu ne tokare tun daga maƙoshin shi har cikin Zuciyarshi. Yana kallo ta fice daga motar.

****

“Tee…”

Ya kira a karo na huɗu tare da taɓa ta, hakan da ya yi ya katse mata tunanin da take yi. Gajiya take ji da bata taɓa sanin kalarta ba. 

“In ba ka fita ba ni zan fita, i want to be alone. Ka barni don Allah.”

Ta faɗa a sanyaye. Yanayinta, abinda ke cikin muryarta duka sun haɗu sun ƙara mishi zafi. Miƙewa ya yi duk da ba haka zuciyarshi ke son yi ba. 

Tsayawa ya yi yana kallonta, amma sam ta ƙi ɗago kanta, idanuwansu yake son su haɗu, ya buɗe mata zuciyarshi, ta ga yadda ba zai taɓa yafewa kanshi hurting ɗinta da yayi ba. 

Yadda rayuwa bata zo mishi da wani zaɓin da ya fi abinda yayi ba. Ta ga yadda itace rayuwar shi gaba ɗaya. Ɗan tsugunnawa ya yi ya kai hannu ya ɗan ɗago fuskarta yana sumbatar goshinta. 

“Zuciyata na tare da ke, ajiyata na jikinki, tafiyar mu bata kawo nan cikin sauƙi ba. I need you Tee… Laifina nawa ne, karki raba shi da yaron mu…”

Yana ƙarasawa ya fita yana ja mata ƙofar. Sai lokacin ta ɗago kai da sauri, tsoro na mamaye ɓacin ranta. Tana jinta so empty. 

Buɗe bakinta tayi tana jin kukan da ya ƙwace mata amma sam sauti ya ƙi fitowa. 

“Na bi zuciyata sama da addinina…sonka shi ya kawoni nan… Sonka shi zai zama ajalina El-labeeb…”

Take faɗi tana wani kuka mai cin rai, hannuwanta duka biyun suna kyarma ta dafe cikinta dasu. Tana tunanin yadda ta kusan rasashi. 

Wani sabon kukan na ƙwace mata, har zuciyarta ta sha jin ko tana da ciki Labeeb ya ci amanarta za ta zubda cikin. Yanzun ne ta san ƙarya take yi. 

Yanzun take mamakin uwar da zata iya zuwa da saninta da hankalinta ta cire ɗan da ya fara samun wajen zama a mahaifarta. 

Ba ƙaramin bushewar zuciya za ta saka uwa aikata hakan ba. Idan shi ne da ɗaya tilo da take da rabon gani ta kira da nata a duniya fa? Girgiza kai kawai take yi. 

Zunubinta na zaɓa mishi uba mazinaci nata ne. Da shi zata rayu, zata iya yafe wa kanta wannan in har abinda ta haifa da ubangijinta suka yafe mata, don tasan akwai haƙƙin da ke tsakaninta da duk abinda ta haifa na kalar uban data zaɓa mishi. 

Zunubin kisa, ba zata iya rayuwa da kalarshi ba. Tana jin ƙaunar abinda ke cikinta da uwa ce kawai za ta iya fahimta. Kifa kanta ta yi da gadon tana jin kamar komai ya tsaya ko na minti ɗaya ne don ta samu sauƙi. 

***** 

Bakin ƙofar ɗakin Ateefa ya zauna, a ƙasa kan tiles ba tare da damuwa da hakan ba. Baisan Ateefa ce ƙarfinshi sai yanzun da idanuwanshi basa ganinta. 

Sai yanzun yake jin nauyin komai na danne shi, numfashin shi yake ji yana fita sama sama. Asad, Anees, Dawud, Jarood, duka ƙannenshi sun tsane shi. 

Numfashin shi bai sake yin sama-sama ba sai da ya tuna kalaman Mummy. Duk rashin kasancewarsu tare da su bai rage komai na matsayinsu a wajen shi ba. 

Yana gudun ɓacin ran iyayenshi, yana tsoron ɓacin ransu fiye da komai, ko don farin cikinshi bai taɓa tsallake maganar Mummy ba. Akan Ateefa ya fara mata musu. 

Shi ma ba don Dady ba dole zai haƙura, Mummy da kanta bata son ganin shi. Yaro! Yana da yaro da a iya tunanin shi ya kasa hango ta yadda akai hakan ta faru. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Ya shiga jerowa yana neman samun nutsuwa wajen Allah, har lokacin numfashin shi baya shiga da fita dai-dai. Wayar shi da ba zai ce ga lokacin daya sakata a aljihunshi ba ta soma ruri. 

Hannunshi na rawa ya fito da ita daga ciki, yana dubawa, zuciyarshi har rawa-rawa ta soma ganin Zainab ce. Da ƙyar ya iya ɗagawa. 

“Kana ina yaya?”

Yasan ƙannenshi dukkan su, daga muryarta yasan ta yi kuka, ya dagula komai, ya ɓata ran kowa.

“Ina asibiti Zee Zee . Kuka kika yi ko?”

Ya ƙarasa tambayar da sanyin murya. Sai dai kashe wayar ta yi maimakon ta amsa mishi tambayarshi. Ya sauke wayar daga kunnenshi ya ɗorata kan ƙafafuwanshi yana binta da kallo. 

Kafin ya rufe idanuwanshi kanshi na jujujjuya mishi, yana jin komai a hargitse. 

******* 

Lokaci-lokaci take duba wayarta tana kallon yadda har sha biyu ta wuce. Tun ƙarfe goma ta gama shiryawa. Tun da ɗankwali a kanta har ta cire ta ajiye.

Ta tabbata da heavy make up ta yi sai ta fara samun matsala a zaman da ta yi tana jiran Ishaq. Iya kunnuwa ya gama kunnata. 

Duk da ta san Dawud ya roƙa cewar tashin hankalin da ya shiga kan bikinshi, hayaniyar ta ishe shi har ƙarshen rayuwar shi, baya son a tara mutane. 

In da za a bar komai iya close family ɗinsu hakan zai fi mishi. Tana son kasancewa da family ɗinta. Su yi hira hakan zai mata daɗi. 

Tana son daga gidansu su je inda suka shirya walimar yammacin tare da ‘yan uwa gaba ɗaya. Bata yi ma Ishaq musu ba da ya ce gidan iyayenshi za su sauka har da ita. 

Shi ya ce mata ba zai daɗe ba, zai zo ya ɗauketa. Sau uku tana kiran wayarshi bai ɗauka ba, da ya ce ta tafi ne ma in ya daɗe bai dawo ba, ko motar wani cikin ‘yan gidansu da ta ara, tunda da guda ɗaya kawai suka zo daga Abuja. 

Ganin ɗaya saura minti biyar yasa ta miƙe ta shiga banɗaki ta ɗauro alwalar sallar Azahar. Tana fitowa Anisa ƙanwar Ishaq ɗin kuma autar su ta shigo ɗakin da sallama.

Zainab ta amsa mata, sam ko murmushi ta kasa ɗorawa akan fuskarta. 

“Hajiya ta ce a kawo muku abincin ku nan, ko za ku ci tare da mu?”

“Bai ma dawo ba Anisa, a kawo nan ɗin kawai.”

Anisa bata ce komai ba ta juya tana ja mata ƙofar, akwatin su Zainab ta buɗe ta ɗauko hijabi, tana sallah Anisa ta shigo ta nufi ɓangaren da dining ɗin yake ta ajiye musu abincinsu ta sake ficewa. 

Tana idar da addu’o’inta ta miƙe tana linke hijab ɗin, Ishaq ya turo ƙofar tare da yin sallama, zuciyarta ta doka kamar yadda har yanzun ta kasa sabawa da ganinshi. 

Kusan shekararsu ta biyu kenan da yin aure amma soyayyarshi kullum sabuwa takan zamar mata, in har za ta ganshi sai zuciyarta ta doka. 

Can ƙasan maƙoshi ta amsa mishi sallamar, tana harararshi. Dariya ya ɗan yi yana marairaice fuska. 

“Kin ga yadda kikai kyau kuwa?”

Ya ƙarasa yana tura mata air kisses. Hijabin da ke hannunta ta jefa mishi a fuska ya tare yana dariya. Kallonshi take tana ƙoƙarin ɓoye murmushin da ke son ƙwace mata. 

Ya iya ɓata mata rai, don yasan ba koyaushe fushinta yake yin tsayi ba. Hijabin ya warware ya sake naɗewa da kyau yana takowa inda take tsaye. Ajiye hijabin yayi akan gado. 

Ya sauke idanuwan shi cikin nata. 

“Ki yi haƙuri, ban cika maganata ba, na haɗu da friend ɗina ne. Mamanshi bata da lafiya sosai, ban ɗauka za mu daɗe ba shi yasa ban miki text ba. 

A mota na bar wayar, na fito na ga kin kira.”

Sauke numfashi ta yi, abinda ta fi so tare da shi kenan. Farko ta wahala don banda Labeeb ko su Anees tana jin basu haƙuri. Son da yake mata baya hana shi nuna mata ta ɓata mishi rai ko ta mishi ba dai dai ba. 

Ko yaushe za ta ɗauka zai ci gaba da shareta har sai ya ji haƙuri daga bakinta, tun yana mata nauyi har ya bari. Kamar yadda ko ya yasan ya ɓata mata zai mata bayani kuma ya ba ta haƙuri. 

“Zai wuce in ka barni na kwana a gida yau.”

Tun kafin ta ƙarasa yake girgiza kai. 

“Mun gama maganar nan tun a gida. Karki soma rigimar da mu duka za mu ji babu daɗi.”

Daƙuna mishi fuska ta yi, ya kai hannu yana ja mata hanci, ta ture shi tana wucewa. 

“Ka zo ka ci abinci ka kai ni.”

Ta buƙata a taƙaice tana nufar dining area ɗin don ta haɗa mishi. 

“Ke kuma fa?”

“Bakina salaf nake ji tun safe, ka ci abinka”

Da sauri ya ƙarasa inda take, cikin kunnenta yake faɗa mata maganar da sirri ne tsakaninsu. Dariya tayi tana sa hannu ta ture shi, ko motsi bai yi ba. 

“Allah ya shirya min kai… Cikina hanji ne kawai a ciki.”

Da murmushi a fuskarshi ya ce, 

“Ni me nayi kuma? Zamu gani koma menene dai, in ba za ki ci ba nima na ƙoshi. “

Sanin za su iya share rabin awa suna gardama kan ƙaramin abu yasa ta ƙarasawa ta haɗa musu abincin a plate ɗaya suka zauna suka ci. 

A gurguje ta ƙara gyara fuskarta, ta fesa turaruka da in ba kusa da ita ka zo ba ba za ka jisu ba. Sannan ta fito da mayafinta babba tana yafawa a saman kanta. 

“Kwalliyar nan tai yawa.”

Ishaq ya faɗi yana jin wani irin kishinta, musamman sanin za su shiga taro. Murmushi ta yi, wasu zasu ce kishin Ishaq a kanta yayi yawa. Ko kaɗan bai dameta ba. 

Tasan sonta ne a zuciyarshi ya kai mataki na daban. 

“Zan wanke fuskata in za mu fita.”

Ta ƙarasa da dariya. Harararta ya yi da sauri ya ɗora da faɗin, 

“Fuskar ki babu kwalliya ta idanuwana ce ni kaɗai.”

Dariya ta kama yi mishi, rigimar shi bata ƙarewa. 

“Mu tafi nikam.”

Miƙewa yayi tare da sauke numfashi. 

“Na so in ƙara watsa ruwa, muje in sauke ki in dawo.”

Ya ƙarasa maganar yana nufar ƙofa, Zainab ta bi bayanshi. Sai da suka fara faɗa wa mamanshi sun wuce tukunna suka fita daga gidan. 

**** 

Suna hanya ta sake dialing lambar din Mamdud, tun shekaranjiya da ta zo take kira a kashe. Ta tura mishi text shiru, tana so ta tambayi Labeeb wani abin ya ɗauke mata hankali. 

Ringing ta yi har ta yanke bai ɗauka ba, ta ja ɗan ƙaramin tsaki da ya sa Ishaq kallonta kaɗan ya maida hankalinshi kan tuƙin da yake yi da faɗin, 

“Ya dai?”

“Yaya Mamdud ne mana”

“Hmm…”

Kawai Ishaq ya faɗi, kafin ya ɗora da wani abu wayarta ta soma ruri, ɗagawa ta yi.

“Mun yi faɗa Yaya Mamdud, da gaske nake mun yi faɗa. Duka lambobinka a kashe, ka ga text ɗina ko reply ba ka yi ba.”

“Afuwan sweet sis…”

Mamdud ya faɗi daga ɗayan ɓangaren, yanayin muryarshi ta ji ta ce, 

“Me ya sameka?”

“Bakomai sis, zan kira ki dai zuwa anjima. You be safe, ki gaishe min da Ishaq.”

“Yaya…”

Zainab ta fara ta ji ya kashe wayar, sake dialing ta yi a kashe gaba ɗaya. Cike da rashin fahimtar me ke faruwa yasa ta faɗin, 

“Something is wrong.”

Dai dai lokacin da Ishaq ya yi parking a ƙofar gidansu, ya maida hankalinshi kan Zainab. 

“Kinsan bana son damuwar ki ko? Menene?”

“Yaya Mamdud ne, bansan me ya same shi ba, something is wrong…”

Ta ƙarasa tana jin wani abu ya tsaya mata a wuya. Hannunta Ishaq ya riƙo ya sumbata. 

“Babu komai in sha Allah, ko mu shiga gidan tare?”

Girgiza mishi kai ta yi, tana dumtse hannunshi da ke cikin nata saboda zuciyarta da take jin ta soma dokawa. 

“Za mu yi waya, love you.”

“Love you more.”

Ya amsa yana sake sumbatar hannunta kafin ta fice daga motar ta shiga gida. Da duk takun da take zuwa ɓangarensu da yadda gabanta yake tsananta faɗuwa. 

Da sallama ta shiga falon gidansu, ta ji shi wani irin shiru kamar babu mutane, takalmanta ta cire, a nan falo ta ajiye jakarta tana cire mayafinta ta ɗora akan kujera. 

Sallama ta sakeyi shiru. 

“Yaya Asad… Mummy…”

Take kira tana nufar ɓangaren su Asad din, har lokacin gidan bata ji alamar akwai motsin mutane a ciki ba. 

*****

Jingine da bangon ɗakin Anees ya samu Asad. 

“Asad…”

Ya kira a hankali, kanshi ya ɗago ya kalle shi, muryarshi kamar wanda aka shaƙe ya ce, 

“So nake na ji ka tashe ni daga baccin da nake ka ce min mafarki yau ɗin nan nake yi…”

Wani abu Anees ya ji ya sake tokare mishi zuciya, ji yake kamar ya karɓi ciwon da ɗan uwan nashi yake ji, baisan ya zai iya sama mishi sauƙi ba. 

Shiru ya yi yana kallonshi kawai, so yake yai mishi magana, tun taron su na farko bai sake magana ba sai da aka kawo ɗan Labeeb. 

Yana so ko yaya ne Asad ɗin ya raba damuwar da shi. 

“Ba mafarki bane ko Anees? Da gaske cikin yaya ne a jikin Zulfa…O.M.G!”

Ko ina na jikin Asad kyarma yake, sosai abin yake taɓa shi yanzun. Cikin banza ne a jikin Zulfa, jikin yarinyar da baisan lokacin da ya ɗauka da soyayyarta a zuciyarshi ba. 

Banda ciwon ƙaddarar da ta same ta, ta shafe shi ta fanni fiye da ɗaya, a gefe akwai abinda ya fi wannan ciwo, akwai abinda ya fi wannan zafi. 

Cikin da ke jikinta na Labeeb ne, ya rasa me ya fi mishi zafi, rashin tsammanin halayya irin haka daga wajen Labeeb ɗin? Ko kuma abinda yai musu su dukan su. 

Ƙafafuwanshi ne suka kasa ɗaukarshi, hakan ya sa shi zamewa ya zauna a ƙasa yana dafe kanshi da dukkan hannuwanshi yana jin kamar zuciyarshi za ta fito. 

Anees ne ya ƙaraso inda yake ya zauna shi ma. 

“Asad don Allah ka nutsu.”

“Babu inda nutsuwa za ta samu zama a zuciyata…”

Asad ya faɗi yana ɗago da kanshi.

“Sai da na ce ya aureta…wallahi na haƙura da ita don farin cikin shi…kai ka sani. Shi ya bani hope, shi ya nuna min baya sonta irin haka. 

Why? Yau na fara sanin tashin hankali a rayuwarmu…”

Sauke numfashi Anees ya yi. 

“Na ɗauka babu abinda zai min zafi bayan rasa Sajda. Akwai ƙaddarar da bawa baya iya tsallakewa. 

Ina son zuciyata ta yarda da cewar irin wannan ƙaddarar ce ta faɗa akan Yaya da Zulfa, sai dai haushin ya zai mana haka na son hanawa. 

Bansan me zan ce ka samu sauƙi ba Asad, wallahi ban sani ba.”

Anees ya ƙarasa maganar muryarshi na karyewa. Kai Asad ya ɗan ɗaga mishi, kasancewar shi anan ɗakin zaune da shi kawai ya isa. 

Haka suka zauna shiru na tsawon lokacin da ba za su iya cewa ba, don suna nan zaune kowa da tunanin da yake yi har suka ji an kira sallar Azahar. 

Nan cikin ɗakin suka yi sallar su tare, suka sake komawa suka zauna, suna nan ɗin dai suka ji an ƙwanƙwasa ƙofar da sallama. Anees ya amsa jin Zainab ce ya sa shi ɗorawa da, 

“Shigo…”

Turowa ta yi ta shigo tana faɗin, 

“Muryata ce bata da ƙarfin da nake zato ko kurame kuka zama da bana nan? Sai sallama nake tun ɗazu…”

Su dukkansu kallonta kawai suke yi, akwai wani abu tattare da yanayin su da ya sa bugun da zuciyarta yake yi ya ƙaru. Da sauri ta ce, 

“Ina Yay Mamdud? Me ya same shi?”

“He is ok. Ba shi bane ba.”

Anees ya amsata cikin sanyin murya, sauke numfashi Zainab ta yi ta ƙarasa inda suke itama ta zauna a ƙasa kan kafet ɗin. 

“To menene? Me ya faru?”

Kallon juna suka yi suna shawarar wanda ya kamata ya faɗa mata abinda ke faruwa. Kafin Asad ya ce, 

“Well, ko ta ina labarin ba mai daɗi bane, yaya na da yaro, yaron da bamusan ko ya akai ya same shi ba…”

Kamar saukar jirgin sama haka Zainab ta ji maganganun Asad. Cikin rashin fahimta ta katse shi da faɗin, 

“Wait… What?!”

Ɗan ɗaga mata kafaɗa Asad ya yi. 

“Zulfa na da ciki wata uku. Cikin Yaya…”

“Wane irin rashin hankali ne wannan? Yaya Anees ka ce ya bar min irin wasannan bana so! Bana so wallahi. Ta ina yaya zai samu ɗa? 

Duka kwanan cikin Anty Ateefa nawa? Ta ina ma za a ce ce Zulfa na da ciki. Cikin Yaya wai?”

Zainab ke faɗi cike da hargowa. Don ji take har numfashinta na wani sama-sama kamar zai ɗauke saboda tashin hankali. Ganinsu duka suna kallonta babu wanda ke shirin cewa maganar ta wasa ce yasa ta ɗorawa da, 

“Don Allah ku faɗa min maganar da zan gane.”

“Zainab muma so muke mu gane har yanzun. Yaya na da yaro, kamannin shi kawai za ki gani…yadda ya same shi ne muke son ganewa. 

Kuma da gaske zulfa na da cikin Yaya, daga bakin shi muka ji.”

Anees ya faɗi mata cikin sanyin murya, yana tsanar girman abinda kalamanshi suke ma Zainab ɗin. Yana tsanar abinda ke faruwa da su. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shi ne abinda Zainab take jerowa wasu hawaye masu zafi na zubo mata, har yanzun maganar ɗan Labeeb ya kasa zauna mata, cikin Zulfa take processing. 

Matsayi da girman ƙaddarar da ta samu Zulfa take juyawa. Ba don ta haɗa jini da zulfa ba, ba don girman ƙaunar da take mata ba, ko wadda bata taɓa gani ba ta ji ƙaddarar ciki irin haka ta faɗa mata sai ya tsaya mata a rai. 

Gaba ɗaya duniyar Zulfa ta birkice, mace ce kawai zata iya fahimtar hakan fiye da kowa. Rayuwa ta ‘ya mace na da daraja, akwai dalilai masu girma da Allah ya ɗaukaka darajarta don su. 

Sai dai kuskure ɗaya, rubutun ƙaddara mai wahalar gogewa zai iya tarwatsa darajar nan duk girmanta. Abu na farko da ke goge darajar gaba ɗaya shine abinda ya faru da Zulfa. 

Hawayen da ke zubar mata sun kasa tsayawa. Bata san lokacin da ta miƙe ba. Wani ɗaci take ji tun daga zuciyarta har kan harshenta.

Za ta iya miƙa rayuwarta don ganin cewar wanda yaima zulfa wannan abin ya wulaƙanta. Wasu sabbin hawayen ne suka sake zubo mata sanin babu ta yadda za ai ta yi hakan. 

Wannan illar Labeeb ne ya yi ta, shi da ya kamata ace yana can yana wulaƙanta wanda ya taɓa su har haka. Muryar Asad ta daki kunnenta da faɗin, 

“I want to hate him! Tun ɗazu nake so in tsane shi na kasa Zee…”

Hannu ta sa tana goge hawayen da suka zubo mata. 

“In har zuciyar Yaya wadda na sani ce na tabbata ya tsani kanshi….yana ina yanzun? Ina son jin komai daga bakin shi. 

In har ya taɓa mu haka bayanin daga wajen shi nake so…”

Zainab ta ƙarasa tana jin wasu hawayen takaici na zubo mata. Anees na jin kamar hawayen zai zubo mishi shi ma ya amsa ta da

“Nima ban sani ba.”

Wucewa ta yi ta koma falon, hannuwanta na kyarma ta zaro wayarta ta kira labeeb ɗin. Yana ɗagawa tambaya ɗaya tai mishi. 

“Kana ina Yaya?”

Tana jin amsar shi ta kashe wayar, bata damu da tambayar da ya yi mata cewar kuka ta yi ba. Ɗakin su Asad ta koma. 

“Me yake yi a asibiti?”

Ta buƙata muryarta a dake.

“Asibiti?”

Suka maimaita a tare suna miƙewa, kai ta ɗaga musu. Mukullin mota Anees yake nema, ya hango shi kan gado ya ɗauko, bai ce musu komai ba ya nufi hanyar waje.

Zainab da Asad suka rufa mishi baya. Mayafinta kawai Zainab ta ɗauka, nan ta bar jakar a falo don wayarta na hannunta.

Suna fita daga gidan su duka ukun suka ci karo da Dawud ya shigo, gaba ɗayansu yanayin shi suke kallo. Ga raunikan da ke fuskarshi. 

Ƙarasawa wajen shi Zainab ta yi, sai dai ta kasa magana, tsayawa tai a gabanshi tana wani irin kuka da Dawud ke ji har ƙasan zuciyarshi. 

Muryar shi a dakushe ya ce, 

“Don Allah ki bari Zainab, ki daina…”

Bata san ta yadda za ta daina kukan ba itama, in ita tana jin abinda take ji akan Zulfa, shi bata san me yake ji ba. Su dukkan su ciwon zai musu sauƙi da wani ne can ba Labeeb ba. 

Ganin ta ƙi bari yasa Dawud ɗan dafe kanshi da ke sarawa tare da yamutsa fuska. Baisan da me zai ji ba, abubuwan sun mishi yawa. Da ƙyar muryar Zainab ke fita tana faɗin, 

“Ka yi haƙuri, don Allah karka tsane mu… Ka yi haƙuri…Yaya na asibiti… Karka tsane mu.”

Tunda ta fara maganar Dawud ke girgiza mata kai, ko da wasa bai kawo su kusa da laifin Labeeb ba. Wajen ƙaunar kowa daban a zuciyarshi. 

“Kin ji shirmenki ko Zainab? Kin taɓa ganin ‘yan uwa sun tsani junan su?”

Kai kawai ta ɗaga mishi sabon kuka na ƙwace mata. 

“Ki bar kukan nan, na san El na asibiti, yana dialogue tare muka je.”

Shi yai ma zainab kwatancen inda zata same shi ɗin. Tukunna da kanshi ya ƙarasa inda su Anees ke tsaye suna kallon shi a tsorace. 

Dukkansu basu san me za su ce masa ba, bayan abinda Labeeb ya yi basu da baki sa idanuwan kallon shi. 

“Karku taɓa ɗauka abinda ya faru ya canza wani abu tsakanin mu.”

Sauke ajiyar zuciya suka yi, Asad na tunanin bai taɓa ganin kalar Dawud ba.

“Bansan me zance ba, wallahi na rasa dukkan kalamaina.”

Asad ya ƙarasa yana jin zafi a ƙirjinshi. Sosai Dawud ya kalle shi

“Kun nuna abinda ya faru ba damuwa ta bace ni kaɗai, hakan kawai ya isa. El na buƙatarku.

Bazan iya tsayawa ba tare da tunanin cire mishi haƙora ya zo min ba.”

Da sauri Anees ya ce, 

“Babu komai. Za mu je yanzun.”

Kai ya ɗan ɗaga ma Anees ya wuce yana barin su a wajen, Zainab ta sa hannu ta goge fuskarta. 

“Ban taɓa ganin mai ƙarfin zuciya irin shi ba.”

Da yarda da maganar Zainab a fuskar su gaba ɗaya suka shiga motar. Anees ya ja su zuwa Dialogue. 

**** 

Gida ya shiga ya sa hannun shi yana dafe kanshi da ke sarawa, ga jiri da ke ɗaukarshi. Abinda ya faru na sake mishi yawo, ɗakin Mami ya nufa ya sameta zaune kan darduma.

Da alama tunda ta yi sallah take zaune a wajen bata tashi ba. Zama ya yi dab da ita, Ummi yake kewa kamar ya sa ihu. Ba zai yi ƙarya ba.

A yanayin da yake ji ba Ummi kaɗai yake buƙata ba, har da Abba, abbanshi da ya rasa, su duka biyun yake jin yana buƙata. Ko da ya riƙe Khateeb a hannunshi yana jariri bai taɓa jin ya rasa mafita ba irin wannan karon. 

Ƙaddarar ta sauya fuska, ta juyo mishi ta yanayin da ko a mafarki bai taɓa tsammani ba. Ba don ya wuce hakan ya faru da shi ba. Sai don yanda ya ɗauki matsayin Labeeb a rayuwarsu gaba ɗaya. 

Kanshi sadde a ƙasa ya ce, 

“Ina kewar Ummi fiye da koyaushe tunda na rasata. Yau har da Abbana da na rasa Mami… Duka kewar su nake yi wallahi…”

Hawaye masu ɗumi ne suka zubo wa Mami, hannunta ta kai ta kama na Dawud kamar ƙaramin yaro, tana jin yadda take ƙaunarshi kamar daga jikinta ya fito. 

Da sauri yasa hannuwanshi duka biyun ya riƙe na Mami da su, sarawar da kanshi ke yi na tsananta, support yake buƙata ko yaya take kafin zuciyarshi ta tarwatse. 

Hannuwanshi da na Mami ya kai kan goshin shi yana faɗin,

“Bansan me zanyi ba, bansan me ya kamata in yi ba, na rasa hanya Mami, Ummi ta bar min kulawar su na kasa. 

Har yanzun na kasa daina jin cewa dana tashi na duba gas ɗin nan da kaina da Sajda na tare da mu a yau. 

Yanzun ina jin dana duba maganganun ki da Zulfa bata da wannan damuwar…”

Ya ƙarasa hawaye masu zafin gaske na zubar masa, su dukkan msu basu ji shigowar Zulfa ba sai da ta zauna. Dawud ta kalla da ke zubda hawaye kamar yaro. 

“Bansan da me zan ji ba in kana kuka akaina, ba don ina da kokwanto a lahirata ba dana roƙi Allah ya dauki rai…”

Bata ƙarasa ba Dawud ya saki hannun Mami yana rufe mata baki. Har lokacin hawaye ke zubar mishi. 

“Kina son in yi hauka kenan ko? Ko so kike in bar muku duniyar?”

Girgiza mishi kai Zulfa ta yi kuka na ƙwace mata. 

“In na sake rasa wani cikin ku… Zuciyata ba za ta iya ɗauka ba… Kar bakinki ya sake furta haka.”

Kai ta ɗaga ta sa hannu ta goge mishi fuska. 

“Ka bari kaima, don Allah ku yafe min… Ku yafe min don Allah, ku daina kuka saboda ni… Mami ku daina…”

Zulfa ta ƙarasa tana matsawa wajen Mami tana kwanciya a jikinta. Riƙeta Mami ta yi tana lallashinta, gaba ɗaya rayuwarsu na kara saka mata tsoron duniya da rikicin da ke cikinta. 

Miƙewa Dawud ya yi, da ƙyar ya kai kanshi ɗakin Tayyab, ya same shi zaune ƙasa ya jingina bayanshi da gadon ɗakin. Ko sallama Dawud bai iya ya mishi ba. 

Wucewa ya yi kan gadon ya hau har lokacin kanshi na sarawa. Ya lumshe idanuwan shi, yana jin Tayyab ya luluɓe shi. Bai buɗe su ba. 

Hutu yake so ko na mintina biyar ne, in har zai kula da ƙannen shi yana buƙatar ya ɗan huta kafin hawan jinin da aka gane yana da shi tun rasuwar Sajda ya ƙara hawa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 31Rayuwarmu 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.