Kasancewar gidan cike yake da mutane, don ranar za a kawo lefe yasa duk suka bar gidan. Mamdud da Labeeb gidanshi suka nufa tare.
Suna shiga Labeeb ya shige ɗaki ya kwanta yana jin kamar an markaɗashi saboda gajiya. Sauran sati biyu kenan bikin Zainab don yau ma aka kawo lefe.
Amma gaba ɗaya tun farkon watan babu wanda ya zauna a cikinsu, a je nan a je can. Bai taɓa sanin haka hidimar biki take ba sai yanzun.
Da ya tambayi Mummy kome yasa nashi bikin ba ai hidima haka ba. Dariya ta yi ta ce mishi ɓangaren mata su ne da biki dama. Na mace ya fi hidima, ya kuma gani yanzun.
Mamdud ma baisan Ateefa na gidan ba sai da ya ga wayarta ajiye kan kujera. Ɗan ture wayar yayi gefe ya zauna tare da sauke numfashi a gajiye.
Baisan me yasa shi son ɗaukar wayar Ateefa ba. Swiping yayi ya ga ta buɗe babu key a jiki. Gallery ɗin wayar ya shiga ya soma kallon hotuna.
Pictures ɗinta ne sun fi kala ɗari. Sosai tai mishi kyau a kowanne, ɗaya bayan ɗaya yake kallon su har ya gama. Fita yayi daga folder ɗin ya shiga wata.
Wani irin dokawa zuciyarshi ta yi ganin hotunan Labeeb, hotuna ba biyar ba, ba goma ba. Hotuna ne kusan sun fi na Ateefa ɗin yawa.
Jikinshi babu inda baya kyarma, fita yayi ya shiga call log. Babu kiran kowa sai na Labeeb ɗin. Sai nashi da basu da yawa, ta yi saving lambar shi da ‘Yaya’ ta Labeeb kuma da sunanshi.
Bai ga duhu cikin idanuwanshi ba, bai ji duhu ya mamaye duk wani lungu da saƙo na zuciyarshi ba sai da ya shiga messages ɗin wayar.
Sai da ya ga kalaman da suke tura wa juna. Numfashin shi ya ji yana barazanar ɗaukewa. Babu shiri ya miƙe da wayar a hannunshi.
Da ƙyar yake ganin hanya, ya nufi ɗakin da Labeeb yake kwance, tunda yake a duniya bai taɓa sanin ƙunci makamancin wannan ba. Bai taɓa sanin zafin cin amana haka yake ba sai yanzun.
Ƙafa yasa ya tura ƙofar kamar mai shirin karyata, hakan yasa Labeeb miƙewa daga kwanciyar da yayi babu shiri. Ƙarasawa Mamdud yayi ya jefa wa labeeb wayar da faɗin,
“Why? Me yasa!?”
Wayar labeeb ya ɗauka da rashin fahimta ya ce,
“Me ya same? Me ke faruwa?”
Inda Mamdud na da bindiga a lokacin babu abinda zai hana shi harbe Labeeb. A yadda yake ji babu abinda ba zai iya ba.
“Karka raina mon hankali…Ateefa nake nufi!”
Murmushi Labeeb yayi.
“Shi ne za ka karya mon ƙofa? Chill, zan faɗa muku dama, ya kai two months yan…”
Walkiya Labeeb ya gani ta gifta mishi kafin ya ji wani ziiiii cikin kunnenshi na haggu, sai da ya runtsa idanuwanshi yakai sau huɗu yana buɗe su tukunna ya gane marin shi Mamdud yayi.
Hannu Labeeb ya kai yana shafa kuncin shi cike da mamaki.
“How dare you? Ina sonta! Ko ba ka ji ba? Ina sonta!! El-labeeb Maska, ba za ka haɗa soyayya da ni ba.”
Zuciyar Labeeb yaji ta yi tsaye a ƙirjinshi, duk wani jini da ke jikinshi na ɗaukar sanyi. Mafarki yake yi, addu’a yake Allah ya bashi ikon farkawa daga wannan mummunan mafarkin.
Mafarkin da bai taɓa mai muni irinshi ba. Ta yaya za a ce yarinyar da yake so ita Mamdud yake so. Bama zai yiwu su haɗa soyayya da Mamdud ba.
“Mafarki nake… Mafarki ne.”
Yake fadi a fili. Kafadarshi Mamdud ya kama ya jijjiga.
“Ba mafarki kake ba. Ka kalle ni El-Maska, me yasa sai ita!? Ba ka ganin dubban matan da suke dai dai kai?”
Kallon shi Labeeb yake yana jin yadda zuciyarshi ke matsewa dam a ƙirjinshi. Sam baya son yarda cewa da gaske ne soyayya suka haɗa da Mamdud.
Sakin shi Mamdud yayi yana saka hannunshi duka biyun ya dafe kanshi da yake jin kamar zai tarwatse. Don labeeb ya ƙuntata mishi yasa ya zagaye ya fara soyayya da Ateefa.
Don ya nuna mishi a kodayyaushe zai samu abinda yake so. Cikin ihu Mamdud ya ce,
“Nasan ka isa… Na sani El-Maska! Ba sai ka nuna min isarka akan yarinyar da na ɗauki burin rayuwa da ita ba! She is mine! Mine!!”
Girgiza mishi kai labeeb yake yana ganin yanda gaba ɗaya ya haukace.
“Ban sani ba, wallahi ban sani ba…”
Labeeb yake faɗi muryarshi ɗauke da da na sani da ko kaɗan Mamdud bai yarda ba. Ji yake kamar ya shaƙe shi ya mutu ya huta.
Labeeb kuwa tashin hankalin da yake ciki ba zai taɓa rubutuwa ba. Gaba ɗaya kamar an kama duniyar da yake ciki an birkitata haka yake ji.
Sam ko alama bai gani ba, kallo na biyu idanuwanshi ba za su fara yi ma Ateefa ba in da yasan Mamdud na sonta, zai yi nisa da ita, ba zai taɓa barin sonta yai mishi zurfi haka ba.
Yanzun ma ba zai iya ba, ba zai iya haɗa soyayya da Mamdud ba, kusancin su ya fi mishi soyayyar Ateefa. In har zaɓi za a ba shi, zai ɗauki Mamdud ko da son ateefa zai kashe shi.
Miƙewa yayi zuciyarshi kamar zata fito waje, da zai iya da ya cireta ya ajiye gefe ya ɗan samu sauƙi, daga inda yake tsaye ya ƙwala ma Ateefa kira.
Sai da ya kirata sau uku, a na huɗu ta amsa, kallonshi Mamdud yake cike da tsana yana jiran ganin abinda zai yi kuma. Shigowa ɗakin Ateefa ta yi.
Yanayin su na nuna mata akwai abinda yake faruwa.
“Ban sani ba…”
Labeeb ya sake maimaitawa yana kasa haɗa ido da Ateefa. Kallon shi tayi kafin ta kalli Mamdud idanuwanta cike da tambaya.
“Baisan ina sonki ba yake nufi.”
Ware idanuwa Ateefa ta yi kafin ta ƙarasa fahimtar abinda Mamdud yake nufi. Girgiza mishi kai take cike da tashin hankali.
Tana jin me ke faruwa da ita haka, wacce irin rayuwa ce ta tsinci kanta a ciki haka. Ta yaya ma Mamdud zai ce yana sonta. Bayan ko a kalamanshi bai taɓa nunawa ba.
Ganin kallon da take mishi ya sa shi faɗin,
“Yes ina sonki Ateefa, daga ranar da na fara ganin ki nasan ina sonki. Ban faɗa miki bane na jira in ƙarasa karatu in samu abinda zan iya riƙe ki da shi…”
“Ka bari Yaya Mamdud…Don Allah ka ce min wasa kake yi…”
Ateefa ke faɗi muryarta na rawa, rufe idanuwanta ta yi ta hango su ita da Mamdud, ji ta yi cikinta ya juya, ko babu Labeeb ba ta jin zata taɓa iya yin soyayya da Mamdud.
A zuciyarta gaba ɗaya kama Yaya Musty take ganin shi. In har zata iya soyayya da Yaya Musty to zata iya soyayya da shi.
Cike da tashin hankali Mamdud ke kallon Ateefa, hawaye ne suka zubo mata.
“Bazan iya sonka haka ba Yaya Mamdud, kayi haƙuri, a idanuna da zuciyata matsayinka daban yake…”
Ta ƙarasa da kuka tana juyawa ta bar ɗakin. Labeeb kanshi a ƙasa har ta fice ya rasa abinda ya kamata ya ji. Ya rasa me ke shirin faruwa da su.
Ƙarar doka ƙofarta har cikin zuciyarshi Mamdud ya ji, kafin ya soma jin duk wani mahaɗi na zuciyarshi na rabewa da junansu, yanayi ne da ba kowa zai fahimta ba.
Yanayi ne na sai wanda ya kalli abu ɗaya tal da ya rage mishi a faɗin duniya ya ƙi shi zai gane. Ita kaɗai ta bashi hope na cewar zai yi aure ba tare da gorin komai ba. Ta kowane fanni ita ta dace da shi.
Kallon Labeeb ya yi, a karo na biyu ya sake nasarar tarwatsa mishi rayuwa, sai dai wannan karon gaba ɗaya burin shi na rayuwa ne Labeeb ya ƙwace.
“I am going to hit you hard El-Maska. Zan lalata abinda yake da kusanci da kai.
Ka rubuta ka ajiye zan taɓa zuciyarka kamar yadda ka taɓa tawa. I will destroy you!”
Da sauri labeeb ya ɗago yana kallonshi cikin tashin hankali.
“Baka nufin abinda ka ce Mamdud. Wallahi ban sani ba, bazan taɓa yin kusanci da abinda kake so ba in na sani.
Don Allah ka saurare ni, ko yanzun Ateefa take sonka zan haƙura.”
Wata irin dariya Mamdud yayi, ji yake kamar zai mutu, kamar bai da wani dalili na zama a duniya kuma.
“Ba ka ji kanka ba? Ba ka ji me ta ce ba? Bata sona irin yadda ni nake sonta. Ta yaya zata soni ma bayan ga ka? Ka haɗa komai da ba ni da shi!.
A karo na biyu ka yi min abinda kake so! Guess what? Shekara nawa ina handling maka abubuwa? Ina son pay ɗina.”
Ware idanuwa Labeeb ya sake yi cike da wani sabon tashin hankali, ya rasa me ya shigi Mamdud haka, ya mishi uzuri ɓacin rai na iya saka komai.
In ya huce ya dawo hayyacin shi sun fi fahimtar juna. Yanzun zai mishi duk abinda yake so.
“To, please just calm down. Don Allah ka daina magana cikin fushi.”
Labeeb ke roƙonshi kamar zai yi kuka
“No! Ina son kasona, ba ko yaushe za ka samu abinda kake so ba.”
Mamdud ya faɗi cikin hargowa, ba zai rasa komai ba gaba ɗaya. Dole ya biya shi wahalar da ya yi ta shekaru tunda maci amana ne shi.
“Wallahi sai ka biyani tunda ba ka da amana….ya ma za ka yi min haka? Duk matan da za su yi komai don su sameka sai Ateefa, kawai don ka nuna min za ka iya.”
Mamdud ke faɗi cike da wani yanayi a muryarshi da ya sa Labeeb gane sambatu yake.
“Wayar na hannunka ai. Ka ɗibi ko nawa kake so.”
Labeeb ya faɗi muryarshi can ƙasa, kuɗi ba komai bane a wajenshi, in duka wanda ya tara Mamdud yake so zai bar mishi, sai ya yi aiki ya tara wasu.
In dai duka ‘yan uwanshi na tare da shi, komai mai sauƙi ne. Yana kallo Mamdud ya zaro wayar daga aljihunshi yana danne-danne. Da alama transfer yake yi.
Yana gamawa ya cilla wayar kan gadon da ke ɗakin tare da faɗin,
“Na ɗauki miliyan biyar. Ina son gida da mota!”
Ɗan girgiza kai Labeeb yayi. Yanzun ya sake tabbatar da cewa Mamdud ba cikin hayyacin shi yake ba. Nawane miliyan biyar cikin tarin kuɗin da ke account ɗinshi.
A gajiye ya ce,
“Kasan inda takardun duka gidajena suke. Kasan inda mukullai suke, duk wanda yai maka ka ɗauka.”
Ficewa Mamdud yayi daga ɗakin. Labeeb ya dafe kanshi da ke wani irin ciwo, kallon da Mamdud yai mishi kafin ya fita yasa shi kasa zama. Wayoyin dake kan gadon na Ateefa da ɗayar tashi da Mamdud ya ajiye ya ɗauka.
Ya fito daga gida, sai da ya kulle ko ina tukunna ya fitar da motarshi ya ajiyeta ya kulle gate ɗin. Kanshi tsaye gidansu Ateefa ya wuce.
****
Saida ya samu yaro ya aika tukunna ta fito. Fuskarta har ta kumbura saboda kukan da ta sha. Haka ta buɗe motarshi ta shiga ta zauna.
Wayarta ya ɗora mata akan cinya. Muryarshi a dakushe ya ce,
“Bansan kalar son da nake miki ba Ateefa, alƙawarin farko dana fara miki shi ne na gina soyayyar mu akan gaskiya.
Ina son ji daga bakinki, ko kaɗan in akwai soyayyar ɗan uwana a zuciyarki?”
Juyawa ta yi ta kalli Labeeb da jajayen idanuwanta. Muryarta na rawa ta ce,
“Ban taba nufin zama sanadin samun matsala tsakanin ku ba. Zan fahimta in za ka janye daga maganganun ka.
Ban taɓa hango cikar alƙawurr
anka ba dama don…”
Katse ta yayi.
“Tambayarki nayi, amsa kawai nake son ji.”
Duk da ba a hargowa yai maganar ba zata iya karantar ɓacin ran da ke muryarshi, ita kanta nata ran ba a daɗi yake ba. Ƙiris zuciyarta ke jira ta ji yace ba zai ci gaba da soyayya da ita ba.
Bata taɓa ɗaga burinta akan komai ba sai Labeeb. Bata taɓa hango fita daga rijiyar da take ba sai da Labeeb ya miƙo mata igiya. Bata taɓa jin ƙamshin farin ciki kusa-kusa ba sai da kalamanshi.
In ya ƙwace duka wannan a lokaci ɗaya ba ta da tabbas kan abinda zai iya faruwa da ita, kallon da Mamdud yai mata, abinda ta gani a idanuwanshi tasan ta rasa shi shi ma.
Ɗacin rashin shi ya tayar mata da na Yaya Musty. In Labeeb ya ƙara mata da na wani matsala zata samu, sai da ta goge fuskarta sannan ta ce
“Ban taɓa sonshi haka ba. Ko da babu kai bana jin zuciyata zata taɓa son shi irin haka.”
Wani dogon numfashi Labeeb ya sauke yana jin kamar zuciyarshi za ta fashe. Zai lallaɓa Mamdud, zai haƙura, da yardarshi zai auri Ateefa.
“Za mu yi waya. Zanje gida yanzun.”
Ya faɗi, yanayin kallon da take mishi a tsorace yasa shi faɗin,
“Soyayyarki ba ta canza ba. Ba abinda zai canza mu Tee. In sha Allah.”
Kai ta ɗaga mishi kawai ta fice daga motar don in ta yi magana kuka za ta yi. Tana fita Labeeb ya ja motar zuwa gida. A falo ya ci karo da Anty Jamila ƙanwar Dady.
Gaisawa suka yi, rabon da ya ganta har ya manta, in ba wani muhimmin abu ake ba basu cika zuwa ba, ba ya jin zai iya gane kalar ‘ya’yan su.
Tun suna yara rabon da ya ga wasu. Kila dai ko yanzun bikin Zainab ya ga wasu daga cikinsu, tunda ga iyayen har sun zo. Kanshi tsaye ya wuce ɓangaren su.
Ɗakin ya shiga. Takardu ya gani watse akan gado. Ya ƙarasa yana tatatarawa, ya ga Mamdud ya dauki wasu daga ciki, girgiza kai Labeeb yayi wani abu na tokare mishi zuciya.
Ga takardar gidanshi da Mummy ta siya musu tare da su Asaad nan yabari, a fim yakan fito part ɗin da soyayya ta haukata shi. Yau a gaske yake ganin abin ya faru akan Mamdud.
Ko kaɗan da Ateefa na son shi da ya janye. Ko yanzun ta ce zata so shi zai bar mishi ita, zai yi nisa da su in har hakan na nufin samun farin cikin Mamdud. Sai dai in ya janye yanzun baisan halin da Ateefa za ta shiga ba.
Ba zai bari ta rasa su duka biyun ba. Tana da su gaba ɗaya ma rayuwarta babu stability. In ta rasa su baisan halin da za ta shiga ba. In wani abu ya sameta ba zai yafe wa kanshi ba.
Kwanciya yayi yana jin zazzaɓi ya rufe shi saboda tashin hankali. Zulfa yake son magana da, sai dai ba yadda zai fara faɗa mata wannan abin.
Tsakanin su da Mamdud ne, in ba Mamdud ya zaɓi ya faɗa ba, babu wanda zai ji cikin ƙannenshi. Bai san iya lokacin da ya ɗauka a kwance ba.
Ya dai kira wayar Mamdud babu adadi bai ɗauka ba. Ƙarshe ma kashewa ya yi, dole ya haƙura ya tura mishi text:
‘Very worried. Please be okay. Ka dawo gida don Allah mu yi magana.’
****
Daren ranar Mamdud bai dawo gida ba. Haka kwanaki uku bayan nan. Zuciyar Labeeb har bugawa take kar wani cikin ƙannenshi su tambaye shi ina Mamdud ɗin.
Baisan amsar da zai basu ba, kira da text ya mishi su babu adadi, duk inda yasan zai same shi ya je amma shiru. Har faɗawa ya yi saboda tashin hankali.
Mummy sai da ta kula ta tambaya ya ce mata hidima ce kawai. Sai dai abin da ke ɗaure mishi kai babu wanda ta tambaya cikin ƙannenshi.
Fita zai yi daga gidan yanzun ma ko Allah zai sa ya ci sa’ar samun Mamdud ɗin ya ci karo da arif da shirgin ledojin rich bites a hannunshi.
“Daga ina haka Arif?”
“Mumy ta aike mu da Yaya Mamdud shi ne muka biya rich bites muka siya abu.”
Sauke numfashi Labeeb ya yi.
“Yana lafiya dai ko? Mamdud ɗin.”
Labeeb ya faɗi muryarshi ɗauke da wani yanayi. Kallonshi Arif yayi yai murmushi cike da rashin fahimtar ko me yasa Labeeb zai mishi wannan tambayar.
“Yana lafiya mana.”
Ya faɗi yana wuce Labeeb ɗin. Wani ɗan sanyi labeeb ya ji. Fushin da shi kaɗai Mamdud yake yi kenan. Murmushi yayi a karo na farko a kwanaki ukun nan.
Hidmar shi Labeeb ya ci gaba da yi, tunda har faɗanshi tsakaninsu kaɗai ya tsaya ya san zai huce. Wuyarta su haɗu, abin ya ɗan mishi sauƙi, bai dai sake komawa wajen Ateefa ba.
Amma sukan yi waya, sukan yi waya sosai. Yasan da kuɗi wadatattu a hannunta, kuma abubuwa sun mata sauƙi. Hajja ta rage tsanarta tunda ta sanadinta suna samun alkhairai wajen Labeeb ɗin.
Ko a ido Labeeb bai saka Mamdud ba sai ranar daren ɗaurin auren Zainab. Shi ma a wajen dinner tukunna ya ga shigowar shi, har ranshi yai kewar Mamdud.
Sai ma an kira ɗayar wayarshi ya ɗaga yai magana da mutane da kanshi sannan yakan ji rashin Mamdud ɗin. Da sauri ya bar inda yake yana ƙarasawa wajen Mamdud.
Dakatar da shi Mamdud yayi da faɗin,
“Wallahi bana son ganinka. Ko kaɗan bana son ganinka, saboda Zainab nake nan. Karka zo kusa da ni, karka min magana inhar kana son mu bar wajen nan lafiya…”
Ya ƙarasa yana raɓa Labeeb ɗin ya wuce, yana jin kamar ya ɓatar da shi ya huta. Har ranshi baya son ganin Labeeb, yana jin ya tsane shi, tsanar da bai taɓa yi ma komai ba.
Ya rasa komai ta dalilin Labeeb, ya rasa mutuncin shi, ya rasa burin shi, yana kuma gab da rasa yaran da yake ƙauna da dukkan zuciyarshi.
Kwana biyu da ya ga basu nemeshi ba, ba ƙaramin tsoro ya ji ba, ya ɗauka labeeb ya fada musu wani abu. Sai gashi Zainab ta kirashi maganar cards ɗin da suka kai.
Sai kuma ga Mummy ta nemeshi ita ma. Kafin nan sauran, da Labeeb yaja mishi ya rasa su suma da ba zai iya misalta kalar tsanar da zai mishi ba.
Har Mamdud ya wuce Labeeb ya kasa ko juyowa. Yana ɗaukar abin nan wasa, da gaske ne Mamdud baya son ganinshi, ya ga hakan a fuskarshi, ya ji tsanar da yai mishi a muryarshi.
Sosai jikinshi ya mutu, don duk wani abu da akai wajen dinner ɗin kawai wuce mishi yake. Sai dai idanuwanshi na kan Mamdud har aka tashi kafin nan ya ɓace mishi.
Sa’adda suka koma gida uku na dare. Ɗakin Arif suka koma su duka har da Anees saboda mutanen da ke cike da gidan.
Bai gwada kiran Mamdud ba, ko da zai ɗaga. Text ya tura mishi:
‘Ban taɓa hango faruwar haka a zaman mu ba. Abinda na yi bance zai yafu lokaci ɗaya ba. Sai dai na ɗauka za ka saurareni Mamdud, na ɗauka kasan dukkan halayena, kasan me zan yi kasan meye bazan yi ba.
Bansan yadda zan baka haƙuri ba, ka yafe min don Allah. Ina buƙatar abokantakar ka. Ina buƙatar ɗan uwana, i need you to be okay akaina da Ateefa.’
Saida ya ga report cewar message ɗin ya shiga tukunna ya kwanta, amma ko runtsawa bai yi ba. Kan kunnenshi akai kiran sallar Asuba, shi kaɗai yasan ɗacin da yake ji a zuciyarshi.
Bai iya cin komai ba har suka shirya suka tafi wajen ɗaurin aure. Ƙarfe goma daidai aka ɗaura auren Ishaq da Zainab kan sadaki dubu ɗari biyu.
Hotuna Labeeb yake da jama’a ba don yana so ba, ga ciwon kai da ya addabe mishi. Ga wani yanayi na cewar Zainab ce yau aka ɗaura ma aure.
Zainab ɗinshi, ‘yar ƙanwarshi, yau kulawarta gaba ɗaya ta tashi daga ƙarƙashin shi ta koma wajen Ishaq. Sai da ya zo tafiya tukunna ya hangi Mamdud suna dariya da su Asad.
Bai gwada zuwa wajensu ba ya shiga mota ya koma gida. Yasan Mummy ta faɗa mishi Zainab da Ishaq Abuja za su zauna don can yake da gidanshi. Kuma a can yake aiki.
Fararen kayan da ke jikinshi ya cire don sun ishe shi, ya sake watsa ruwa. Kayan da ya fito da su tun kafin su fita ya ɗauka kan gadon Arif ya saka a jikinshi.
Yana cikin ɗaura belt ɗin suspenders ɗin ya ji an ƙwanƙwasa ɗakin.
“Shigo…”
Ya faɗi, Zulfa ce hannunta ɗauke da plate da cokali. Murmushi yayi, ta yi kyau cikin atamfarta da ba zai ce skirt bane ko zani.
“Kin yi kyau.”
Ɗan guntun murmushi kawai tayi. Shima ya mata kyau.
“Kamar jira kake ku dawo, har ka sake kaya.”
Ɗan daƙuna fuska yayi.
“Zafi nake ji shi yasa. Ga nauyi kuma.”
Girgiza kai zulfa ta yi tana ajiye mishi abincin.
“Nasan baka ci komai ba…”
Kafin ya amsata ta fice daga ɗakin, sauke numfashi yayi ya zauna ya ɗauki plate ɗin. Jalof ɗin shinkafa ce sai ƙamshi take.
Kaɗan ya ɗan ci, shi ma don Zulfa ce ta kawo, Arif na shigowa ɗakin ya zauna yana ci da santin ya mishi daɗi. Labeeb bai kula shi ba har ya gama ya ɗauki plate ɗin ya fice.
Ateefa ya kira ya ji yadda ta tashi don ba su yi waya ba. Agogon wayar ya duba, har sha biyu ta yi. Lokacin gudu yake mishi yanzun, numfashi ya ja, bai kai da saukewa ba ya ji an turo ƙofar.
Sauke numfashi yayi yana kallon Zainab, sanye take da riga fara ƙal, baya iya ganin takalmin da ke ƙafarta don har ƙasa rigar ta rufe.
Kanta da mayafi da baisan yadda akai aka maƙala shi ba, shi ma ta bayanta har ƙasa yake, ta gaba kuma ya rufe mata fuska ya sakko har kan ƙirjinta, ƙamshinta duk ya cika ɗakin.
Wani karyewa zuciyarshi ta yi saboda kyan da ya ga ta yi. Hannuwanta da suka sha ƙunshi ta sa tana ɗage mayafin ta ɗora shi a saman fuskarta, a hankali ta taka har inda yake.
Tsugunnawa ta yi gabanshi yasa hannu yana shirin kamata don gani yake kaman za ta yi squeezing kayanta, ƙi ta yi sai da ta kai ƙasa. Kallonshi take idanuwanta cike taf da hawaye.
Wayarshi da ke ajiye a gefe ya ɗauko, ya buɗe camera ya ɗauketa hotuna a haka yadda take. Muryar Zainab cike da tsoro ta ce,
“Tafiya za mu yi Yaya.”
Cike da rashin fahimta Labeeb ya ce,
“Ina kuma za ku je?”
“Gidana, yanzun za a kaini…”
Ta ƙarasa hawaye na zubo mata, zuciyar Labeeb ta yi wani irin dokawa. Kallonta yake yana rasa abinda zai ce.
“Ka kira su Yaya Mamdud in musu sallama…”
Ta ƙarasa kuka mai ƙarfi na ƙwace mata, kanta ta ɗora akan ƙafafuwanshi. Kuka take mai cin rai, a ‘yan watannin nan tasan tana son Ishaq.
Sai dai bata da tabbaci akan alƙawurran shi. Yau za ta bar gidansu, zata bar yayyenta, za ta bar komai na rayuwar da ta saba da ita zuwa wata baƙuwa da babu tabbas a cikinta.
Wani abu ne yai ma Labeeb tsaye a zuciya, sai yanzun da lokacin da yasan ya miƙa rayuwar Zainab hannun wani daban ya tabbata yake jin kamar ya yi kuskure.
In Ishaq ba mutumin kirki bane fa? In ya ɗauketa daga gidansu a mutunce ya je ya wulaƙantata fa. Runtse idanuwanshi yayi ya buɗe su. Wayar da ke hannunshi ya danna.
Text iri ɗaya ya tura ma su Anees da Mamdud, don ba zai iya magana ba. Yasan Mamdud ko ya kirashi ba ɗagawa zai yi ba.
Ba a fi mintina sha biyar ba Anees da Asaad suka shigo, sanye da fararen shaddoji sai dai sun cire manyan rigunan. Zainab na jin shigowar su ta miƙe.
Anees ta fara hugging tana kuka kamar za ta shiɗe. Da ƙyar ya samu ya ɗagota daga jikinshi.
“Tsoro nake ji Yaya Anees…in na tafi kuma baya sona fa?”
Zainab ke faɗi tana ci gaba da kuka. Asad ya kalla yana rasa me zai ce don shima gab yake da yin kuka. Ƙarasowa Asad yayi yana tallabar fuskar Zainab.
“Muna tare da ke ko ina kike Zee Zee, ina Abuja ina Kaduna? Flashing kawai za ki min da gudu zan ƙaraso. Ishaq na sonki ok? Babu wanda ba zai so ƙanwata ba.”
Kai take ɗaga mishi. Cikin kuka ta ce,
“Zan yi missing ɗinku… Kullum zan yi kewar ku….bansan me yasa yaya ya min aure tun yanzun ba.”
Anees da Asaad suka kalli Labeeb lokaci ɗaya, don su ma basu ga dalili ba, dukkansu ji suke kamar su rufe shi da duka. Zai yi magana Mamdud ya shigo da sallama.
“Yaya Mamdud sai yanzun?”
Zainab ta faɗi hawaye na zubo mata. Hannuwanshi duka biyun Mamdud ya haɗe yana faɗin,
“Yi haƙuri Zee Zee, traffic jam…”
Kai ta ɗan ɗaga ta ce musu,
“Ku yafe min. Just in…”
“Zainab!”
Labeeb ya kira cike da kashedi. Tana sake karya mishi zuciya. Miƙewa yayi daga zaman da yake ya ƙarasa yana kama hannuwanta.
Ganinta yake tana yar ƙaramarta, lokacin yana kamata ya kaita school in yana nan. Har wanka ya sha yi ma Zainab. Yau ita ce da igiya uku ta aure.
“Kirana kawai za ki yi in kina buƙatata, wallahi in yai miki wani abu…”
“Nasiha fa za kai mata yaya.”
Anees ya faɗi yana basu dariya gaba ɗayansu, kafin Labeeb ya harare shi.
“Serious magana nake a wajen nan kasa na manta.”
Dariya suka sake yi. Sumbatar Zainab ɗin yayi a goshi.
“Allah yasa auren nan shi ne alkhairinki Zee Zee. Ina ƙaunarki fiye da Rayuwa da kanta.”
Murmushi ta yi sabbin hawaye na cika mata idanuwa, takawa ta yi tai tsaye a gaban Mamdud, hannu ya sa a aljihunshi ya zaro wani abin hannu guda biyu.
Abinda ya tsaya siye kenan. Gold ne duka, ko su Labeeb da ba sanin shi suka yi ba sun san zai yi tsada sosai.
“Ban taɓa ganin amaryar da ta yi kyau kamar ki ba…”
Asad ne yai tari, Mamdud ya harare shi.
“Sorry…”
Ya faɗi yana murmushi. Kan Zainab Mamdud ya mayar da hankalinshi ya miƙa mata abin hannun guda biyu. Karɓa ta yi ta sa a hannunta, kuka na hanata magana.
“Sabuwar Rayuwar ki ba zata taɓa yin dai-dai da wannan da za ki bari ba. Farin cikin su daban-daban ne. All you need shi ne ki bashi chance, nasan ba wanda zai iya hakan sama da ke.
Dukkanmu muna nan. Kira kawai za ki yi, we got your back, we always will. Ina ƙaunarki kinsani ko?”
Kai ta ɗaga mishi sabbin hawaye na zubar mata, Anty Jamila ce ta leƙo kai.
“Ku yi sauri, ita kawai ake jira.”
Sumbatar su ta yi. Sai dai ko ba aure akanta abinda ba zata iya yi ma Mamdud ba kenan, bangles ɗin da ke hannunta na hagu ta ciro duka shidan.
Ta bar nashi, miƙa mishi ta yi.
“Ka ba ma matarka.”
Ta faɗi muryarta a dakushe, hannu Mamdud yasa ya karɓa yana sauke idanuwanshi cikin na Labeeb yana barin ya ga yadda ya ruguza hakan.
Ya ga yadda hope ɗin nan ya ɓace daga idanuwanshi, ɗauke fuska Labeeb ya yi, ciwon na zame mishi biyu, ga na tafiyar Zainab ga na Mamdud. Kuka take kamar ranta zai fita sa’adda su Anty Jamila suka dawo suka fitar da ita.
Asad ne ya soma barin ɗakin, kanshi a ƙasa, Labeeb na kallonshi, da alama shi ma kukan yake yi kafin Anees ya bi bayanshi.
“Bansan ya zan yi in gyara tsakanin mu ba. In ka sani ka faɗa min Mamdud.”
Tsaki kawai Mamdud ya ja yana ficewa daga ɗakin. Labeeb ya sauke ajiyar zuciya yana kwanciya kan gadon. Inda shi ya samu yai kukan ma da abin ya mishi sauƙi.
BAYAN KWANA SHIDDA
A karo na babu adadi yake sake duba akwatinan kayan Arif ko ya manta wani abu. Ji yake kamar a fasa tafiyar nan, amma Mummy banda farin ciki babu komai a fuskarta.
Ko da aka gama hidimar bikin Zainab cewa ta yi babu inda za ta sake zuwa sai ta ga tafiyar Arif. Da an zauna bata da magana sai ta yadda take alfahari da samun Arif a yaranta.
Har mamaki Labeeb yake, yadda tarbiyar Arif za ta kasance ba shi bane matsalar Mummy. Matsalarta ɗaya ne, ta samu yaro extraordinary irin Arif.
Yaron da za ta yi alfahari da shi. Ya zama wani abu shine burinta. Kayayakin yake mayarwa ya ji Mummy na mishi wani irin kira na tashin hankali.
Da gudu ya fito daga ɗaki, ran Mummy a ɓace ta ce,
“Wacece Ateefa?”
Zuciyar shi ya ji ta doka. Yana tunanin ina kuma mummy tasan Ateefa. Muryarshi na rawa yace.
“Yarinyar da nake son in aura ce Mummy.”
“No ka ce mun shegiyar da bata da asali. Labeeb kana da hankali kuwa? Kasan me kake son yi? Kana son cakuɗa min zuri’a da marar asali.
Yanzun da Mamdud bai faɗa min ba haka za ka kwaso mana rashin tunanin nan cikin gida? Na ɗauka ka yi hankali”
Ran Labeeb ya ɓaci sosai. Ya wa Mamdud uzuri, amma anan ko kaɗan ya kasa. Ta yaya zai faɗa ma Mummy wannan maganar bayan yasan halinta tsaf.
Magana zai yi Asad ya shigo.
“Me akai wai?”
Ya tambaya. Cikin ɓacin rai Mummy ta ce,
“Ka tambayi shashashan yayanka gashi nan. Yaron nan ya rasa wa zai jajibo yana son ya aura sai shegiya! Yarinyar da bata da asali.”
Duk da Asad ya ji zafin cewar bakin Mummy ya soma ji, Labeeb bai faɗa musu ba, bai hanashi faɗin,
“Ba ita ta yi ba ai. Beside in ba auran irin su aka yi ba ya ake so su yi? I think in dai tana da tarbiya da hali me kyau aurenta ba wani matsala bane.”
Sauke numfashi Labeeb ya yi. Mummy ta saka salati.
“Rashin hankalin naku iri ɗaya ne kenan. Bari Dadynku ya zo. Ni kam ba da yawuna za ai wannan rashin hankalin ba.
Ka fara neman wata yarinya daban ba wannan ba. M”
Mummy ta ƙarasa tana wucewa ɗaki tana ta faɗa. Asad ya kalli Labeeb.
“In ka faɗa mana ba zamu taɓa judging ɗinka ba. Farin cikinka shi kawai muke buƙata Yaya.”
Cikin sanyin murya labeeb yace.
“Ka yi haƙuri, ba ƙin faɗa muku na yi ba, abubuwa ne suka yi yawa, na bari a gama duk wannan hidimar ne tukunna. Thank you.”
Ɗan ɗaga kai Asad yayi.
“Saboda me yasa ba Zulfa ce ba wannan karon ma?”
“Saboda me sai na sake faɗa muku? Babu soyayyar nan tsakanin mu.”
Labeeb ya amsa shi. Murmushi Asad yayi da Labeeb bai fahimci ma’anar shi ba.
“Ka ƙyale Mummy. Ka yi abinda zai sa ka farin ciki. Muna tare da kai.”
Kai kawai Labeeb ya iya ɗaga mishi, yana barin wajen ya zaro wayarshi daga aljihunshi ya kira Mamdud. Wannan karon ɗagawa ya yi.
“Mu duka ba zamu same ta ba El-Maska. Wallahi kaɗan kenan. Yadda zuciyata bata zauna lafiya ba taka na ba zata taɓa zama ba.”
“Bansan me kake so da ni ba, amma ka fara crossing limit…”
Labeeb ya faɗi yana controlling ɗin ɓacin ranshi.
“Au haba? Tun yanzun? She rejected me! Saboda kai, ku duka ba zaku zauna da juna ba. Ka riƙe wannan.”
Ya ƙarasa yana kashe wayar. Sosai ran labeeb ya ɓaci. In ba Mamdud ba waye har ya isa ya yi gigin mishi wannan haukan. Bai sake kiran Mamdud ɗin ba.
Ba zai biye mishi ba, bai kamata ace duk sun yi hauka cikin ɓacin rai ba. Kamata ya yi ace ɗaya daga cikin su ya zama mai hankali.
Har dare Mummy ko inda Labeeb yake bata kallo balle tai mishi magana, Asad ya faɗa ma Anees abinda ke faruwa. Su duka suka sake tabbatar ma da Labeeb ya yi duk abinda zai saka shi farin ciki.
Suna bayan shi in buƙatar hakan ta taso. Da wuri ya wuce ɗaki ya kwanta, sai da ya kira Zainab ya ji lafiyarta kafin ya kira Ateefa.
Sun daɗe sosai suna hira har dare ya raba, don sai da ya ji bacci ne a muryarta sannan ya ƙyale ta. Yau ma bai samu bacci ba.
Ya kuma yi wa kanshi alƙawarin ƙoƙarin barin kayan maye. Yana son gyara rayuwar shi, in har zai fara tara iyali. Haka yaita juyi da ɓacin ran Mamdud har gari ya waye.
Wata hidimar suka shiga kuma, don ƙarfe goma jirgin su Arif zai ɗaga zuwa Jordan. Shi da Mummy za su tafi, Labeeb yaso raka shi Mummy ta ce ita za ta je.
Dole ya haƙura, ya san ya je daga baya. Suna shirin fita daga gidan ne kiran Ateefa ya shigo wayarshi. Silent ya sakata yana fita da sauri tukunna ya ɗaga .
Kasa magana tayi saboda kukan da take. Duk ta ɗaga mishi hankali, sai kashewa ta yi tai mishi text cewar ya buɗe whatsapp ɗin shi.
Da don tura hotuna kawai ya buɗe. Ba lokacin chatting yake da shi ba. Jikinshi na ɓari ya kunna data. Hotuna ne suka shigo wayarshi sun fi talatin.
Dukansu baisan sa’adda aka ɗauke su ba, kuma dukansu ƙazaman hotuna ne nashi da mata, da ya san babu wanda zai iya samun ɗaukarsu sai Mamdud.
Daga ƙasa ta rubuta;
‘Haka ka so samu ka yi gaba ko? Na gode.’
Dafe kai Labeeb yayi, Mamdud ba zai barshi ya ji da tafiyar Arif ba sai ya ɗora mishi sabon hawan jini. Text ya tura mata saboda su Mummy da suka fito.
‘Za mu yi magana. Zan zo gidan anjima kaɗan.’
Ya mayar da wayar aljihunshi. Bai da nutswa don haka Anees ne ya ja motar har Airport. Ga mamakin Labeeb, Mamdud suka samu ya riga su isa.
Cike da fara’a suka gaisa da Mummy, bayan shi ko gaisuwar shi Mummy ɗin bata amsa ba yau. Labeeb na ji ta ɗora da faɗin,
“Ka taya ni yi wa sakaran abokinka faɗa. Ya nemi yarinyar da zan iya kira surukata kafin in dawo.”
Murmushi Mamdud ya yi.
“In sha Allah Mummy.”
Yana sauke idanuwanshi cikin na Labeeb. Kallonshi kawai Labeeb ya yi bai ce komai ba. Bai yarda da kanshi ba a yanayin ɓacin ran da yake ciki.
Tsugunnawa ya yi yana hugging Arif.
“Zan kira ka kullum. Ka kula da kanka sosai, banda ƙin yin sallah akan lokaci, banda bad friends.”
Sake maƙale shi arif yayi.
“I will miss you da yawa.”
“Muma haka. Karka bani reason ɗin zuwa in dawo da kai gida.”
Dariya Arif ya yi yana faɗin,
“In sha Allah. Love you.”
“Matsa mu samu namu hug ɗin.”
Anees ya faɗi, miƙewa Labeeb ya yi yana basu waje, yana kallo suka yi wa Arif sallama kafin Mummy ta kama hannunshi suka wuce ciki. Asad ya cillo ma labeeb mukullin motar.
“Yawo zamu da Yaya Mamdud.”
Ya faɗi, basu jira amsar shi ba suka wuce gaba suna nufar motar Mamdud ɗin da ya juyo yai ma Labeeb wani murmushi sannan ya wuce shi ma.
Kamar zuciyar Labeeb za ta faɗo ƙasa haka ya wuce ya shiga motar, gidan su Ateefa ya nufa, ya mata kira ya fi sha biyar, text kam ya fi biyar. Duka shiru babu amsa babu reply kuma.
Wani ya sake turawa:
‘Wallahi in ba ki fito ba anan zan yi ta zama.’
Shi ma sai da yai zaton ba zata fito ba, tukunna sai gata. Motar ya buɗe don ta shigo tai tsaye a bakin ƙofar.
“Tee… Don Allah ki shigo.”
Da ƙyar ya samu ta shigo ta zauna. Kafin ya ce wani abu cikin kuka ta ce,
“Saboda me za ka jani cikin soyayyarka da zurfi haka labeeb? Kasan yadda na ɗauki shekaru ina wa kaina alƙawarin ko kusa da kalar babana ba zan je ba saboda tsanar masu ire iren halin shi da na yi?”
Shi kanshi kamar zai yi kukan ya ce,
“Ba irin shi bane ba ni. Rayuwa ta mayar da ni haka…”
“Rayuwa kan baka zaɓi guda biyu a wasu yanayin. Karka ce min ba ka da wani zaɓi Labeeb.”
Haɗe kanshi yayi da gaban motar yana jin laifukan shi fiye da ko da yaushe. Akwai gaskiya a maganarta. Rayuwa ta bashi zaɓi, donmn an lalata shi zai iya amfani da hakan wajen ganin bai faru da kowa ba.
Sai dai ina, zuciyarshi ta fi ƙarfin shi. Ba tare da ya ɗago ba ya ce,
“Ina da zaɓi. Na zabi halaka ne don ita ce mafi sauƙi a lokacin. Wallahi rabona da wata mace an fi watanni nawa.”
Hawaye ne sabbi suka zubo mata, ji take kamar zuciyarta za ta buɗe saboda ciwon da take. Kullum haka take wa mmasu hali irin na labeeb baƙar addu’a. Ashe da irin shi take soyayya.
“Karka ce min saboda ni ka shiryu… Ban kai ga tsanarka ba saboda bansan ya zan fara ba… Banda tabbas in ka ce min saboda ni ka bar neman mata.”
Sai lokacin ya ɗago. A hankali ya girgiza mata kai.
“Zai zama aikin banza kenan, ba saboda ke bane ba. Tun kafin in haɗu da ke ne, kuma ba mata kaɗai na bi ba, na yi shaye-shaye Tee, haɗuwa da ke ne na bari.”
Wasu sabbin hawaye ne suka zubo mata, kallonta Labeeb ya yi, tunda abin nan ya faru yaune ya ji hawaye sun cika mishi ido, ba zai iya rasata ba itama.
“Bance ki yarda da ni ba Tee, Amma don Allah karki guje ni.”
Kuka take sosai yanzun kam.
“Sonka ya riga ya min illa Labeeb, zuciyata ta kasa wannan tunanin tun ɗazu duk da nasan shi ne abinda yakamata in yi… Abu ɗaya nake son ka riƙe a ranka. Wallahi bazan taɓa zama da irin babana ba.
Bazan iya zama da mazina ci ba!”
Kafin ya ce wani abu ta buɗe motar ta fice. Haɗe kanshi yayi da steering wheel ɗin motar yana jin wani zafi zafi na daban. Kafin wasu hawaye su ɗigo mishi.
*****
Girgiza shi ya ji anyi. Ateefa na faɗin,
“Ka fita don Allah, ka barni kawai ka fita, bana son ganinka…”
Kallonta yake zaune kan gadon asibitin, zuciyarshi cike da ciwo marar misaltuwa.