"Wai har yanzun Abba bai dawo ba?"
Dawud ya tambaya yana neman wajen zama a falon. Kusa da shi Sajda ta koma. Bai ko kalleta ba. Idanuwanshi kafe kan Ummi.
Da alamun damuwa a muryarta ta ce,
"Wallahi shiru. Har Isha'i na gabatowa. Bai taɓa daɗewa a waje haka ba."
"Allah dai ya dawo mana da shi lafiya."
Tayyab ya faɗa. Su duka suka amsa da amin.
Zaune suke zugum. Babu mai abin faɗa. Dawud ya ji Sajda ta kwanto jikinshi. Dubata yayi ya ga bacci take yi.
A hankali ya ke. . .