Skip to content
Part 4 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

“Wai har yanzun Abba bai dawo ba?”

Dawud ya tambaya yana neman wajen zama a falon. Kusa da shi Sajda ta koma. Bai ko kalleta ba. Idanuwanshi kafe kan Ummi. 

Da alamun damuwa a muryarta ta ce,

“Wallahi shiru. Har Isha’i na gabatowa. Bai taɓa daɗewa a waje haka ba.”

“Allah dai ya dawo mana da shi lafiya.”

Tayyab ya faɗa. Su duka suka amsa da amin. 

Zaune suke zugum. Babu mai abin faɗa. Dawud ya ji Sajda ta kwanto jikinshi. Dubata yayi ya ga bacci take yi. 

A hankali ya ke girgizata. 

“Sajda tashi ki yi sallar Isha’i tukunna.”

Da ƙyar ta buɗe idanuwanta. Ganin baccin bai saketa ba yasa Dawud kallon Zulfa ya ce, 

“Rakata tayie alwala.”

Miƙewa Zulfa ta yi ta kama hannun Sajda. Mashin ɗin Abba suka ji. Gaba ɗayan su suka nufi hanyar fita. 

Har sajda lokaci ɗaya baccin ya saketa. Ita da Zulfa riƙe shi sukai gam kamar wanda suka shekara basu ganshi ba 

“Sannu da zuwa.”

Ummi ta faɗi da murmushi a fuskarta. Murmushin ya mayar mata yana ɗan ɗaga mata kai. Sannan su Tayyab ma sukai mishi sannu. 

Ledojin da ke hannunshi suka karɓa suka wuce falon tare. Hira suka yi cike da ƙaunar juna. Abba ke musu albishir ɗin ya samu aiki. 

Faɗar farin cikin da kowa yake ciki a ranar ɓata baki ne. Litinin ɗin ta zo musu da sauyi mai girma. 

**** 

Bayan Wata Biyu 

Ta kowanne ɓangare na rayuwar su Dawud yana tafiya dai dai. Har sun yi hutun gama aji biyar sun koma makaranta.

Yanzun haka watannin da ya rage musu su zana jarabawar aji shida basu da yawa. Abu ɗaya ne ya canza musu. Shi ne basa samun lokacin Abba kamar da. 

Yanayin nisan wajen aikinshi yakan sa sa’adda zai dawo daga Ummi sai Dawud ne ba su yi bacci ba. Wani lokacin da Tayyab. 

Hakan na damun Ummi fiye da kowa. Tana kewar mijinta. Dn in ya dawo a gajiye yake shigowa. Washe gari kuma ita tana fama da hidimar yara.

Shi kuma yana shirin tafiya aiki. Don ma ya barta ta ci gaba da karantarwar da ta fara tunda ya kula tana so sosai. Duk da inda ya ce ta haƙura zata bari. 

Takan kula da yanayin shi ya ɗan canza. Sai ta ɗora alhakin hakan akan gajiya da yake fama da ita. Abinda bata san yana faruwa ba shi ne. 

*

Da safiyar ranar yana shiga office ɗinshi ya zauna Hajiya Beeba tana shigo mishi. Baya so har ranshi. 

Sai dai ta fi shi muƙami a wajen. Kuma ita ce sanadin samun aikinshi. Da murmushin nan nata da ya kasa gane ma’anar shi ta ce, 

“Har ka ƙaraso kenan. Dama zan wuce office ɗina ne na ce bari in leƙo mu gaisa.”

A daƙile ya ce, 

“Na gode.”

Yana ci gaba da buɗe files ɗin da ke gabanshi. Nuna mata yake baya buƙatarta amma ko ta gane bata nuna alamun hakan ba. 

“Anjima in zan fita cin abinci na biyo mu tafi tare.”

Wannan ne karo na yafi a ƙirga tun bayan fara aikinshi a wajen da take mishi tayin su fita cin abinci tare. Kamar ko yaushe amsar shi ta yau ɗin ma ita ce,

“Ki je abinki. Na gode . In ba za ki damu ba ina da aiki a gabana.”

Bai ɗago ba balle ya ga ɓacin ran da ke fuskarta kafin ya ji takun tafiyarta tana barin office ɗin. Sauke numfashi yayi. 

Matar nan ta ishe shi. Ta addaba ma zaman lafiyarshi. Ko bashi da mata kamar Aisha a gida. Hajiya Beeba bata yi mishi ba. 

Yana son mace mai kamun kai da kunya. Ba irinta ba. Kuma ya gane duk wani take taken da take yi. Jira yake ya gama tara kuɗin jarabawar Dawud ya bar aiki a wajen. 

Bai faɗa wa ko Aisha ba. Ya bar abin a cikinshi duk da yana damunshi ba kaɗan ba. 

****

Hajiya Beeba kamar yadda kowa yasanta da shi. ‘Yar asalin Zariya ce. Su huɗu ne a gidansu duk mata. Karatu ya kawota garin kaduna. Inda maimakon ta yi abinda ya kawo ta saita haɗa shi da yawo da ƙawayen banza. Kamar yadda Hausawa kance zama da maɗaukin kanwa. 

Nan Hajiya Beeba da ƙawayenta suka ci gaba da sheƙe ayarsu yadda suke so. Bata koma gida ba sai da ta yi cikin titi. Inda suka yi kaca-kaca da mahaifinta ya koreta. 

Hakan baisa ta hankalta ba. Sai ma ya sake bata damar dawowa kaduna da zama gaba ɗaya. Ta zubda cikin da ke jikinta ta ɗora daga inda ta tsaya. 

Akwai manyan mutane da take tare da su. Don Hajiya Beeba ta haɗa komai da mace take buƙata wajen kyau. Karatunta bai samu matsala ba. Bai kuma sha karo da yawon banzar ta ba. 

A halin yanzun za ka iya cewa ta samu nasarori a karuwanci. Tunda ta mallaki gidaje har huɗu. Motoci biyu, ga kuma aiki mai kyau. 

Komai na tafiya ne a bisa tsarinta kamar yadda take gani. Sai ranar da ta taka ƙafarta ta yi wa Alh. Mando rashin mutunci kan kuɗinta da take binshi. 

Inda kaddara ta haska mata Auwal. Tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin namijin da ya shiga zuciyarta lokaci ɗaya ba irin shi. 

Ta ga maza kala kala. Wanda suka fishi komai da wanda ma basu kaishi ba. Amma shi ɗin dai yai mata. Har mamaki take yadda take ji in ta ganshi. 

Abu ɗaya ne matsalarta har zuwa yanzun da take cikin motarta tana hanyar zuwa gidanta da ke Malali. Kwata kwata bata gaban Auwal.

In ya ganta ma yi yake kamar an aiko masa da saƙon mutuwa. Duk wata kissa da kisisina tata in tana gabanshi nemanta take yi ta rasa. 

Abin na damunta sosai. Maimakon ta yi kwanar da zata hau da ita titin gidanta sai ta juya zuwa gidan aminiyarta Huzai. 

***** 

Saida ta gama bata labarin duk halin da take ciki Huzai ta kwashe da dariya. 

“Wane irin iskanci ne kuma wannan huzai? Zan zauna in gama kwance miki cikina sai ki tusa ni gaba kina dariya”

Kallonta ta yi sosai. 

“Beeba kin bani mamaki wallahi. Wai akwai namijin da zai gagareki? Ke ce fa!”

Rausayar da kai gefe Hajiya Beeba ta yi. Tana wani fari da idanuwanta. 

“Ba za ki gane bane. Ni kaina mamakin abin nake yi. Da na ganshi sai in ji komai ya kwance min.”

‘Yar dariya Huzai ta yi irin tasu ta manyan ‘yan bariki kafin ta ce, 

“Ke dai ki ce miyanki ya guda kawai. Amma wacce irin soyayya a wannan shekarun. Dabaru za ki yi ki biya buƙatarki komai zai wuce.”

Gyara zama Hajiya Beeba ta yi tana jinjina maganar aminiyar tata. Kar dai gaskiya take faɗa. Auwal burgeta yake ba sonshi take ba. 

“Anya kuwa. Jiya da ƙyar nai bacci wallahi.”

Wata dariya Huzai ta yi. 

“Kawo kunnenki ki ji.”

Miƙa mata ta yi. Ta faɗa mata maganar suka yi dariya gaba ɗaya suna tafawa. 

“Kuma da kin ganshi kinsan yana cikin buƙata. Ke kinga wani tsohon mashin da yake fama da shi.”

Dariya suka sake yi gaba ɗaya. Huzai na faɗin, 

“Ai hakan kawai za a yi. Ko kin samu zaman lafiya.”

Hira suka ci gaba dayi kafin Hajiya Beeba ta miƙe da cewa,

“Dare na yi. Zan tafi gida nikam. Koya ake ciki zan zo in faɗa miki.”

Har ƙofa Huzai ta raka Hajiya Beeba. Ta ɗibo kuɗaɗe a jaka ta miƙa mata. 

“Ke kam ba kya gajiya da ɗawainiya.”

Cewar Hajiya Huzai tana ‘yar dariya. 

“Karki damu. Alhaji Bulama ya kawo su jiya. Dama ina shirin zuwa in kawo miki naki kason.”

Wata shewa suka yi tare da yin guɗa. Sannan ta wuce ta shiga motarta ta tafi. 

**** 

Tana zuwa gidanta. Maigadi ya buɗe mata ta shiga. Ta ga motar chairman a ajiye. Ranta ta ji ya ɓaci. A halin da take ji bata buƙatar kowanne namiji sai Auwal. Kamar yadda ta sani a falo ta same shi kwance kan kujera. Yana jin shigarta ya tashi yana washe baki. Ƙara tsuke fuska tayi. 

“Beeba manyan ƙasa. Kin ganni ko gida ban yi ba. Taron ƙungiya muka je. Ina dawowa na ce yau a wajenki zan kwana.”

Fuskarta babu walwala ta juya mishi idanuwanta. A yangace ta cire takalminta tana taku na jan hankali ta ƙarasa wajen shi. 

Zama ta yi a gefen kujerar da yake. Cikin kasala ta yi ƙasa da murya ta ce, 

“Gashi ka samu bana jin daɗi. Daga office gidan Huzai ma na wuce na kwanta na ɗan huta.”

Tun kafin ta rufe baki fara’ar shi ta dakushe. 

“Yanzun me kike nufi kenan? Na yi zuwan banza?”

‘Yar siririyar dariya ta yi. 

“Haba chairman. Tunda kake zuwa ka taɓa ƙin samu? Yau ɗin ma dai yanayi ne na yau da kullum.”

Miƙewa yayi yana ɗaukar babbar rigarshi da ke gefe. Tana kallon harzuƙar da yayi a fuskarshi. Amma bata da zuciyar ko da lallaɓa shi. 

“Ni zan wuce Allah shi kyauta.”

“Amin. Sai yaushe kenan?”

Ɗan kallonta yayi. Ya zaro rapper ɗin yan naira ashirin ya miƙa mata. 

“Ban sani ba dai. Kinsan siyasar nan da ta gabato. Ba lokaci sosai. Ga wannan ki je asibiti.”

Karɓa ta yi. Tana mishi far da ido cikin kissa. 

“Na gode sosai. Mu je in taka maka mana.”

Ba musu yai gaba. Ta bi bayanshi har suka fice daga ɗakin. Sai da ta ga ya shiga motar shi ya tafi tukunna ta dawo falon. Kan kujera ta kwanta. 

Auwal na ɓata mata shiri. Chairman abokin harka ne na mutunci. An jima ana tare. Nan kan kujerar bacci ya ɗauke ta cike da mafarkin Auwal.

**** 

Kamar yadda ƙawarta ta bata shawara washe gari tana zuwa office ta leƙa ta ga Auwal bai zo ba. Wucewa ta yi nata office ɗin ta zauna tana jira ya zo. 

Ta rasa abinda yasa gabanta yake ta faɗuwa. Ba wannan bane karo na farko da ta taɓa yima maza tayin abinda take shirin yi ma Auwal. Amman wannan ne karo na farko da abin yake mata wani iri. Karo na farko da take jin tsoron tunkarar wani namiji da buƙatarta. 

Huzai ta yi gaskiya. Koma menene dole ta yi settling abinda take ji akan Auwal ko zata samu zaman lafiya. Tun bayan da ta ganshi kowanne namiji wata mu’amala zata shiga tsakaninsu sai ta dinga ji kamar ace Auwal ɗin ne.

A karo na farko bayan shekaru masu yawa da ta yiaddu’a da dukkan zuciyarta. Tai addu’ar samun nasara akan Auwal.

***** 

Bubbuga shi Aisha take a hankali. Da ƙyar ya iya buɗe idanuwan shi. Cikin raɗa ta ce, 

“Ka tashi mu yi sallah.”

A gajiye ya ce, 

“Jikina duk ciwo yake. Ki min addu’a dai.”

Girgiza mishi kai ta yi. 

“A’a fa. Tunda ka tashi ko raka’a biyu ka samu. Wa ya ce maka mabuƙaci yana faɗin gajiya lokacin nema? 

Ka tashi kar Shaiɗan ya sake danne ka.”

Da murmushi ya ɗaga mata kai yana miƙewa. Banɗaki ya shiga ya wanke fuskar shi sannan ya ɗaura alwala. Sa’adda ya fito Aisha na kan darduma tana sallah. 

Raka’a biyu yayi. Bai yawaita addu’o’in shi ba yau saboda gajiyar da ke tattare da shi ya koma ya kwanta. 

Sai dai baccin ya mishi wuyar samu lokaci ɗaya. Yana kallon Aisha tana ta salloli abinta kafin daga bisani ta nutsu a zaune ta buɗe Qur’ani. 

A hankali take karatun. Yana saurarenta da wata nutsuwa ta daban na shiga zuciyarshi. Ƙaunarta dabance a wajen shi.

Duk daren duniya tun auren su sai ta tashe shi sun yi salloli da dare. Tun bai saba ba har ya saba. Don ko bata yi ranar shi takan tashe shi. In ya idar su yi addu’o’i tare. 

Yana saurarenta. A haka bacci ya ɗauke shi cike da mafarkai daya kasa gane kansu. 

****

Koda safe da ya tashi haka yake jin jikinshi ya mishi nauyi har ya gama shiryawa zai fita. 

Yau kam har bakin ƙofa Aisha ta raka shi. Saboda yadda ta ga yanayinshi kamar zazzaɓi ya kama shi. 

“In dai ka ji jikin babu daɗi ka dawo gida don Allah. 

Ba ma zan fita ba yau ko da za ka dawo.”

Fuskarta ya tallafa da hannunshi. 

“Sai ka ce wani yaro. Ki je aiki abinki. In sha Allah komai zai yi dai dai.”

Girgiza kai ta yi. 

“Na riga da na ce Dawud ya biya ya faɗa musu bazan je ba ma.”

Murmushi yai mata. Yana rasa abinda zai ce banda godiya ga Allah da mata mai ƙaunarshi har haka. Mashin ɗinshi ya hau yana tura shi zai fita. 

“Baka yi addu’a ba.”

Ta faɗi. Bai ce komai ba ya ɗan yo baya da mashin ɗin. Sai da yai addu’o’in fita da na neman tsari sannan ta ƙara mishi da wasu ya wuce. 

Baisan me ake a garin ba. Cunkoson da ke akwai yau yafi na kullum. Har ya kusan makara kafin ya isa wajen aiki yau. 

***** 

Yana shiga office ɗin ko zama bai kai ga yi ba ya ji an turo ƙofar. Ranshi ya ɓaci lokaci ɗaya sanin ko wace ce. Ga abinda ke ƙara ƙona mishi rai. Sam bata iya sallama ba in zata shigo. Sai dai kawai ya ganta kamar wadda aka aiko. Zama yayi. Fuskarshi babu walwala ya ce, 

“Lafiya?”

Bata amsa shi ba. Yana kallonta ta tako jikinta sanye da ɗinkin atamfa ta tsigara ɗauri. Da gyalenta da bai ga amfanin shi ba don rataye yake kan kafaɗarta ta dama. 

Kujera ta nema ta zauna tana fuskantarshi. Hannuwanta ɗaya cikin ɗaya tana wasa da su. Da alama akwai magana a bakinta sai dai ta rasa ta inda zata fara. 

Zuciyarta dokawa take da ƙarfin gaske. Har gumi take ji yana fito mata da batasan ko daga ina yake ba. 

“Ina da ayyuka a gabana. Lafiya?”

Ya sake tambaya da ƙosawa a muryarshi. Cikin idanuwa ta kalle shi. Muryarta na bata mamaki saboda rawar da take yi. 

“Da… Daman. Ina so in yi magana da kai ne.”

“Ina jinki”

Ya faɗi ba don yana son saurarenta ba sai don bashi da wani zaɓi. Yana kallon yadda take haɗiyar yawu. 

“Daman. Um… Ka ga ba ɓoye ɓoye. Tun ranar da na ɗora idanuwa akanka na rasa me nake ji. 

Auwal ban taɓa jin abinda nake ji ba kan wani namiji irin yadda nake ji akanka…… Kawai ina so…..”

Kallonta yake. Wanna karon shi yake jin gumin. Kafin ya katse ta da faɗin, 

“Na ji. Na kuma gode. Kiyi haƙuri Hajiya Beeba. Kin mun taimako ba kuma zan manta ba. Amma ina da mata har da yara huɗu. 

Ba kuma ni da ra’ayin ƙara aure. Ki yi haƙuri. “

Da duk abinda ke fitowa bakin shi da yawaitar ƙunar da zuciyarta take yi. Huzai ta yi kuskure. Da gaske son Auwal take. Musamman yadda ta ji wani kishi ya turniƙe ta. 

Muryarta a sanyaye ta ce, 

“Ban ce ka aure ni ba nima. Ba sai ka aureni ba. In dai za mu kasance tare bani da…..”

Miƙewa yayi tsaye yana mata kallon kin samu taɓin hankali. A zuciyarshi kuwa addu’ar neman tsari daga sharrinta kawai yake yi. 

A fili kuma ya ce,

“Hajiya Beeba. Subahanallah. Kina cikin hankalinki kuwa? Me kike nufi?”

Itama miƙewa ta yi tana ɗora hannayenta kan table ɗin da ke tsakanin su ta ce, 

“Abinda kake tunanin nake nufi. Zan biyaka ko nawa kake so. Ka faɗi price ɗinka in dai za ka biya min buƙatata…..”

Baisan lokacin da ya wanke ta da mari ba. Ba Hajiya Beeba ba. Shi kanshi mamakin marin yake yi. Kallonshi take riƙe da kunci. 

Tun kafin ya buɗe baki tasan zuciyarta ba zata taɓa barinta ɗaukar matakin wannnan rashin mutunci da yai mata ba. 

Wani irin kallon ƙyamata yake mata da shi ya fi mata ciwo fiye da marin ta da yayi. Yadda yake kallonta da tsana. Hakan yasa cikin ƙunar zuciya ta ce, 

“Ka daina kallo na haka. Kamar banbancin da ke tsakanina da kai wani babba ne.”

“Fitar min daga office….”

Ya faɗi yana kallonta kamar yana son sake marinta. 

“Wallahi saina same ka. Kai ba ka isa ka wulakanta ni ba.”

A tsawace ya ce, 

“Na ce ki fitar min daga office. Allah zai kare ni daga sharrin ki.”

Dariya ta yi cike da takaici. 

“Zan baka mamaki Auwal.”

Ta faɗi tana juyawa ta fice daga office ɗin tare da ja mishi ƙofar da ƙarfin gaske. 

Komawa yayi ya zauna yana dafe kanshi cikin hannuwanshi. Jikinshi ko ina kyarma yake. Bai taɓa ganin bala’i irin wannan ba. 

Bai ma taɓa ganin mace irin Hajiya Beeba ba. Babu tsoron Allah babu kunya a idanuwanta zata jefe shi da wannan baƙar maganar. 

Inalillahi yake jerowa babu adadi. Komai ya kwance masa. Yasan abinda zai yi. Yasan abinda ya kamata. Takada ya zaro ya ɗauki biro ya soma rubutu. Yana gamawa a office ɗin ya ajiye ya miƙe ya fice. Har ya ɗauki mashin ɗinshi yana jin gaba ɗaya komai ya kwance mishi. 

**** 

Kamar yadda Aisha ta fadi. Tana gida zaune abinta bata je aikin ba. Mashin ɗinshi ta ji. Da sauri ta fito gabanta na faɗuwa. 

Ta ɗauka jikinshi ne ya tashi. Ko bari ya kafe mashin ɗin bata bari ya yi ba ta kai hannu tana taɓa fuskar shi da wuyanshi.

Bata ji zazzaɓi ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana jero hamdala. Sannan ta ɗan matsa ya kafe mashin ɗin ya sakko. 

Fuskarshi take kallo. Hannuwanshi ya ɗora kan kafaɗarta yana kallonta. Yanayin kallon na taɓa ta har zuciya. Jikinta babu ƙwari ta ce, 

“Lafiya? Kana kallona kamar yau ka fara gani na.”

Sauke numfashi yayi mai nauyi tare da cire hannunshi daga kafaɗarta yana tallabar fuskarta da duk hannunshi.

“Ina ƙaunar ki Aisha.”

Kafin tai magana ya jata ƙirjinshi ya rungumeta. Bata ce komai ba. Sai ta zagaya hannuwanta ta baya tana riƙe shi sosai. 

Sun jima a hakan. Sai da ya ji wata nutsuwa da zai iya bayani sannan ya zame ta daga jikinshi. Hannunta ya kama suka wuce falo. 

Ƙasa ya zaunar da su kan kafet ɗin ɗakin. A nutse ya ce, 

“Akwai abinda ban faɗa miki ba. Bawai don ban yarda da ke ba. Ko baki kai in faɗa miki damuwata ba. Sai don dalilai masu yawa. Kin san Hajiya Beeba.Wadda tai sanadin samun aiki na.”

Kai ta ɗaga mishi da sauri alamar ta fahimta. Hankalinta gaba ɗaya akanshi. Hannu yasa ya murza goshin shi kafin ya ci gaba da faɗin, 

“Tunda na fara aiki a wajen. Kullum sai ta shigo min office da maganganu haka. Ya nake da sauran su. Mu je cin abinci tare. Bana so saboda yanayinta bai min ba. Sai yau…..”

Tauna nauyin maganar yake. Ba shi ya furta ba. Amma maimaitawar kunya yake ji. Da ƙyar ya ce, 

“Ta neme ni Aisha.”

Hannu ta kai tana riƙe bakinta tare da salati. Zuciyarta na dokawa da ƙarfin gaske. Ba don bata ji kishi ba. Tsoron daya kamata ne ya danne shi. 

“Allah ya kare ka daga kaidinta. Oh ni Aisha me duniyar nan take zama haka. Oh Allah na.”

Ta faɗi muryarta na rawa. A zuciyarta tana hango jerin tashin hankalin da zai iya samar mata miji da shaiɗan yai galaba akan su. 

Wani sabon tsoro ya sake ziyartarta da ta tuna washe gari zai koma office ɗin. Lokaci ɗaya tsanar Hajiya Beeba da take son jefa kokwanto a neman lahirar mijinta ya cika mata zuciya. 

Muryarshi ta katse mata tunanin ta. 

“Hmm. Hajiya Beeba abin tsoro ce. Nai niyyar barin wajen aikin dama nan da wata biyu. Kuɗin jarabawar Dawud kawai nake jira in haɗa. Kuma hakan ba zai yiwu ba. Allah zai kawo wata hanyar. Na bar musu takardar barin aikina.”

Girgiza masa kai Aisha take. Tana ɗora hannunta akan nashi. Cikin idanuwa ya kalleta. 

“Zama kusa da mace irinta haɗari ne. Ina gudun Shaiɗan Aisha. Har yanzun zuciyata wani iri take min.”

Matsawa ta yi ta rungume shi. Tana jin yadda yake sauke numfashi. Cikin kunnen shi take faɗin,

“Allah ya tsare min kai. Alhamdulillah. Allah ba zai hanamu yadda za mu yi ba. In sha Allah komai ya ƙare.”

Murmushi ya ɗan yi. Har ranta take ƙara wa Allah godiya. Bata son shi ko kusa da inuwar Hajiya Beeba. Ballantana ita kanta. 

A zaman su da shi bata taɓa ganin abinda ya tsorata shi haka ba. Tsoron shi ne ya sake girmama nata akan Hajiya Beeba. 

“In shaa Allah. 

.

Ya faɗi. Yana jin wata nutsuwar zuciya ta daban. Maganarta gaskiya ne. Allah ba zai hana su wata habyar ba. Sakin shi ta yi ta zauna hannunta riƙe da nashi. Har ranta take ma Allah godiya daya ƙetarar mata da shi daga sharrin shaiɗaniyar nan Hajiya Beeba. 

Kallonta ya yi. 

“Wallahi na gaji da aikin office. Da ina da jari yaya zan dinga bi. Kasuwancin ya fi min.”

Sakin hannunshi ta yi ta miƙe. Dama tunda ya ce ya bar aiki dabarar ta faɗo mata. 

“Ina zuwa.”

Da hannu ta nuna mishi minti biyu. Ta wuce ɗakin baccin su. Bata kai mintina biyar ba ta fito da takardu a hannunta. 

Zama ta yi da murmushi a fuskarta ta miƙa mishi takardun. 

“Ga jari nan.”

Karɓa yai yana yatsina fuska cike da mamaki. Dubawa ya yi. Takardun filinta ne. Iyayenta masu kuɗi ne sosai. Mahaifinta ya rasu da cikinta. Mahaifiyarta kuma ta rasu wajen haihuwa. Ko hotunansu bata taɓa sani ba. 

Ta taso a hannun kawunta ne. Filin shi kaɗai ta tsira da shi. Sun danne komai na dukiyarta. Shima don kar ace basu bata komai bane. 

Girgiza mata kai yake yana ɗora mata takardun kan cinyarta. 

“A’a kinsan abinda ba zai faru bane ba.”

“Saboda me? Da gaske nake yi ka siyar. A biya wa Dawud kuɗin jarabawar shi. A biya wa su Tayyab kuɗin makaranta na shekarar nan duka. Sauran kuɗin ka yi amfani da su.”

Murmushi yayi yana kallonta. 

“In biya ki yaushe? Kin ga ɗauke takardun nan ki adana.”

Sosai ta kalle shi. 

“Ni ba rance na baka ba. Kyauta na baka. Kuma ai amfanin mu ne duka. A iya zamanmu baka taɓa nuna min mugunta ba. 

Duk abinda ka samu namu ne gaba ɗaya. Saboda me abuna ba zai zama naka ba?”

Hannunta ya kamo ya riƙe ya ce, 

“Ba haka bane. Bazan iya karɓa bane ba. Wannan shi kaɗai kike da shi da za ki kira naki. 

Allah zai kawo mana wata hanyar.”

Kallonshi take ranta a dagule.

“Filin ne kaɗai zan iya kira nawa? Kaifa? Su Dawud ɗin fa? Meye amfanin ajiyar abin da zai iya amfanar mu gaba ɗaya? 

In baka karɓa ba zan ji kamar har yanzun bamu zama ɗaya ba. Kamar komai naka ba nawa bane ba. Kamar komai nawa ba naka bane.”

Takardun ta ɗauka daga cinyarta ta miƙa mishi. Hannu yasa ya karɓa yanajin sun mishi wani nauyi. Maganganunta sun taɓa mishi zuciya. 

Kallonta yake. 

“Bansan me zance ba….!”

Ya faɗi. Muryarshi ɗauke da wani yanayi. Dariya ta yi. 

“Ka ce Allah Ya sa albarka a cikin kasuwancin da za ka fara. Allah ya bamu lafiya da kwanciyar hankali ya shirya mana zuri’ar mu.”

“Amin thumma amin….”

Ya faɗi yana sumbatar hannunta da yake riƙe da shi. 

“Na gode Aisha. Allah yai min arziƙin da zan maida miki da wanda ya fi shi.”

Girgiza mishi kai ta yi. 

“Allah ya azurta ka. Amma bana son ka mayar min. Karka canza ƙaunarka a gareni. Wannan ya fi min kowacce irin kyauta.”

Dariya yayi. Yana jin ƙaunartan da take kira tana ƙara girma a zuciyarshi. 

“In sha Allah.”

Kanta ta kwantar a kafaɗarshi. Hannunta cikin nashi. Ƙaunar shi data yaran su na mata yawo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 3Rayuwarmu 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.