Bayan Wata Hudu
Tsaye yake a ƙofar makarantar su Junior yana dubawa ya ga ko ta ina zai ɓullo. Agogon hannunshi ya duba ya ga sauran mintina biyar a taso su. In ya yi duba da canjin da ya samu na rayuwa sai ya ga kamar shekaru huɗu ne suka wuce mishi ba watanni ba.
Ba shi da wani lokaci yanzun da ya wuce na aikin da ya samu a Asad Pharmaceutical da ke nan Kaduna. Ba yadda Labeeb bai yi ba da ya kawo takardunshi ya samo mishi aiki ya ce shi zai nema. . .