Skip to content
Part 51 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Bayan Wata Hudu 

Tsaye yake a ƙofar makarantar su Junior yana dubawa ya ga ko ta ina zai ɓullo. Agogon hannunshi ya duba ya ga sauran mintina biyar a taso su. In ya yi duba da canjin da ya samu na rayuwa sai ya ga kamar shekaru huɗu ne suka wuce mishi ba watanni ba. 

Ba shi da wani lokaci yanzun da ya wuce na aikin da ya samu a Asad Pharmaceutical da ke nan Kaduna. Ba yadda Labeeb bai yi ba da ya kawo takardunshi ya samo mishi aiki ya ce shi zai nema da kanshi. 

Aikam da kanshi ya yi applying, ya yi interview ɗin. Kuma sai gashi ya samu, albashin shi na da kyau, ya ishe shi ya yi duk wata hidima ta rayuwa har ma ya yi saving ɗin wasu a account ɗin Junior da ya ware mishi. 

Ga shi yana jin daɗin aikin. Ƙarfe huɗu na yamma ya tashi. Ba ya fita sai takwas, da ya sauke Junior makaranta yake wucewa aiki shi ma. Sai biyar da rabi Junior yake tashi daga makaranta don a haɗe take da Islamiyya. 

Yana da awa ɗaya da rabi extra da yake taya Labeeb managing wasu abubuwan a kullum. Wasu weekend ɗin kuma yakan bi shi garin da yake don most weekends Junior na yinsu ne tare da su Mummy. Wata irin shaƙuwa ce ta shiga tsakanin su da yaron da zai ba ka mamaki. 

Shi yake kula da yaron shi, yake mishi komai. Wasu weekends ɗin rikici Junior yake sa wa Mummy sai ta kira Mamdud ɗin ya zo ya ɗauke shi. Yana ƙoƙarin yi mishi Hausa duk da ba ya mayarwa har yanzun yana jin wasu abubuwan. 

Makarantar da yake daga larabci sai turancin da dama yana jinshi don Mamdud ya ga alama da shi kunnuwanshi suka buɗe. A hakan duk Juma’a da yake ƙarfe 12 yake tashi daga aiki a ranakun, Mamdud yake zuwa ɗaukar karatun addini. 

Ba ya son ko kaɗan Junior yai mishi wata tambayar da zai kasa amsa mishi ta wannan fannin. Yana kuma son yin zurfi a ilimin addinin shi don sanin yadda zai kara samun kusanci da Ubangiji. 

Ta fanni me kyau rayuwa ta zo mishi da sauyi. Ganin yara sun fara fitowa ne ya katse mishi tunanin shi yana mayar da hankalin shi kan Junior da ya hango ya rugo da gudu, zuciyar Mamdud ta ɗauki haske da ganin shi. 

Da wani irin murmushi yake ƙarasawa, a duniya babu wani abu da ya fi ka ga farin ciki fal a fuskar ɗanka, ka ga idanuwanshi cike da ƙaunarka, ka ji shi a jikinka ya zagaya hannuwanshi ya riƙe maka ƙafafuwa lokacin da zuciyarka za ta cika fal da alfahari da addu’ar ganin girmanshi. 

Da addu’ar jin hannuwanshi a bayanka maimakon ƙafafuwanka. Tsugunnawa ya yi yana ɗago da Junior da ke dariyar farin cikin ganinshi, sumba junior ya manna mishi a kuncin shi da bakinshi duk danƙo. 

“Junior me ka ci haka?”

Mamdud ya tambaya yana dariya tare da tsugunnawa ya ɗauki basket ɗin Junior ɗin da ya ajiye a ƙasa sa’adda ya ƙaraso. 

“Chocolate and wafers.”

Ɗan ware idanuwa Mamdud ya yi yana juyawa ya buɗe bayan motarshi ya ajiye basket ɗin a ciki ya rufe yana faɗin, 

“Iyye… Shi ne ba ka rage mind ba.”

Daƙuna fuska Junior ya yi cike da wani yanayi da yai mishi iri ɗaya da fuskar Labeeb, sai yake ganin kamar Labeeb in ya mishi wani abu yana so ya ba shi haƙuri tun kafin ya furta za ka soma ganin abin a fuskarshi. 

Dariya Mamdud ya yi zuciyar shi cike da ƙaunar su biyun. Zillo Junior yake yana ƙoƙarin dirowa daga jikin Mamdud da ya sauke shi ba shiri. Kafin ya ce wani abu ya ruga da gudu, hakan ya sa shi binshi da kallo. 

Idanuwanshi na kan Junior da ya yi rungume wata, kafin ya ga ta sa hannu ta ɗauke shi, har lokacin idanuwanshi na kan Junior kafin ya mayar da su su tsaya cak kan fuskar matashiyar budurwar. Wani abu na mishi yawo a duk jikinshi. 

Kallonta yake tana faɗa wa Junior wani abu da ya sa shi dariya ita ma tana dariyar da gaba ɗaya ta cika fuskarta da idanuwanta. Ba fara bace ba, ba ma za ka sa ta a layin masu haske ba. Amma kyawunta ya cika wa Mamdud idanuwa. 

Yana jin zuciyarshi na buɗewa ta fannin da ya ɗauka daga kan Ateefa ta kulle, ta fannin da ya ɗauka daga dirar ƙaddararshi a kunnuwanshi ya mutu. Sai yanzun yake jin shi yana buɗewa. Yawu ya haɗiya yana son mayar da shi ya kwantar don tashin shi ba komai ba ne banda matsala. 

Yana kallon Junior ya nuno shi da hannu, kafin ta soma takowa tare da Junior a hannunta tana ƙarasowa inda Mamdud yake tsaye. Har zufa yake ji a tafukan hannuwanshi saboda yadda ganinta kurkusa haka ke tayar mishi da duk wani abu da yake tunanin ya mutu a tare da shi. 

“Ina yini…”

Ta faɗi, muryarta kawai abin sauraro ce, ba ta yi siririya kamar ta wasu matan ba. Amma ta yi mishi dai-dai a kunnuwanshi. Kafin ya amsa Junior ya ce, 

“Papi Aunty Fati.”

Da murmushi Mamdud ya ce, 

“Yau dai na ga Aunty fati ɗin Junior da nake shan labarinta kullum.”

Dariya ta yi a kunyace cikin yanayin da ya ƙara mata kyau. 

“Ai kam.”

“Ya ƙoƙari? Ya fama da rikicin Junior?”

Murmushi Aunty Fati ta yi. 

“Alhamdulillah… Junior bai cika rikici ba ma. Barshi da tambaya dai.”

Jinjina kai Mamdud ya yi yana jin yadda har lokacin ya kasa daina murmushi. Jin shirun da ya biyo baya ya sa Aunty Fati ta sauke Junior. 

“Bye-Bye”

Junior ya ce mata yana kallon Mamdud, murfin mota ya buɗe mishi ya shiga yana mayarwa ya rufe. Kawai sai ya tsinci kanshi da ɗauko wayarshi ya miƙa wa Aunty Fati. 

“In ba za ki damu ba please…”

A kunyace ta karɓa ta saka mishi lambarta ta miƙa mishi. Kiranta ya yi sai da ya ji ta shiga tukunna. 

“Daddy I wanna go home.”

Junior ya faɗi. Da sauri yace wa Aunty Fati. 

“Mun gode sosai.”

Kai ta ɗaga mishi. Ya zagaya ya buɗe motar ya shiga ya ja suka tafi. A hanya ya ɗan daki goshin shi da hannu. Bai san me yake tunani da karɓar lambar Aunty Fati da ya yi ba. Da tunaninta a zuciyarshi har suka ƙarasa gida. 

Junior da kanshi ya cire uniform ɗinshi ya ninke yana sakawa a jaka. Haka ma socks ɗinshi. Kafin Mamdud ya kama hannunshi zuwa bedroom. Wanka ya yi mishi ya ɗauko mishi Jeans da riga ya bashi ya saka. 

Ya sake kamo hannunshi suka fito. Ya san ya ci abinci haka ma sallar Asr a makaranta. Don haka falo suka dawo, jakar makarantarshi Junior ya janyo daga kan kujera ya zauna a ƙasa yana fito da text book ɗinshi na English da Arabic. 

Mamdud na kallonshi ya yi Home Work ɗinshi. In bai iya ba zai tambaye shi, tukunna ya mayar a jakar ya ɗauketa yana wucewa ɗaki ya kai ya ajiye ya dawo ya zauna kusa da Mamdud da ya canza channel ɗin daga BBC da yake kallo zuwa MBC 3.

Kusa da shi Junior ya zauna yana jingina kanshi da jikin Mamdud ɗin yai wani luf. 

“Junior kar ka yi baccin yamma ya sa maka zazzaɓi.”

Ɗagowa Junior ya yi yana daƙuna mishi fuska. Hakan yasa shi maimaita abinda ya faɗi da turanci. 

“Ba bacci nake ji ba.”

Junior ya faɗi da turanci yana komar da kanshi jikin Mamdud din. Cartoon ɗin da ake nunawa suke kallo har aka kira Magariba. Junior ma ya rigashi tashi yana kama hannunshi a dole miƙar da shi zai yi. 

Tashin ya yi suka nufi toilet ɗin tare da Junior, da sai da ya yi addu’ar shiga ban ɗaki tukunna. Tsaye ya yi daya kunna mishi fanfon ƙasan yana kallonshi. Niyyar alwala ya fara yi da yin Bismillah kafin ya soma yin alwalar, lafiya ƙalau ya cika ta. 

Sai da Mamdud ya sumbace shi tukunna ya ɗauko shi cak zai fito da shi, turjewa Junior ya yi. Sai da ya duba ƙafafuwanshi. 

“Wannan ne na dama?”

Ya tambaya yana son Mamdud ɗin ya tabbatar mishi. Ita ya sa a waje kamar yadda ya koya mishi. 

“Gufranaka, Alhamdu Lillahil Lazee Azhaba annil….annil…”

Daƙuna fuska Junior ya yi ya kalli Mamdud yana son ya tuna mishi. 

“Annil azaa wa’aafaanee…”

Maimaitawa Junior ya sake yi kafin ya fita yana ci gaba da yi kamar waƙa. Ɗaura alwala shi ma ya yi yana jin daɗin yadda komai na addini a wajenshi Junior yake koya. A hankali yake koya mishi komai. 

Yana ganin kuskuren da wasu iyayen suke yi. Har da duka suna korar yaran su da su je su yi sallah tunanin su koya musu yadda za su yi sallar bai taɓa zuwa musu ba. Da yaro ya je ya burbura alwala sai ya zo ya dungura sallah ko a jikinsu. 

Saura kaɗan ya rage wa Junior ya gama gane komai da yake buƙata na sallah. In akwai abinda Mamdud ya kula da shi shi ne, Junior na da ƙwaƙwalwa sosai. Zai yi ƙoƙarin cika mishi ita da abinda ya kamata. 

Tare suka je har sallar Isha’i tukunna suka dawo, Tea kaɗai ya haɗa wa Junior mai kauri ya sha don cewa ya yi ba ya cin abincin. Shi kaɗai ya ci taliyar da dankalin da ya soya ya juye wa maigadi sauran gaba ɗaya ya kai mishi. 

Sanin akwai makaranta washegari ne yasa shi kama Junior suka tafi bedroom ɗinsu. Sai da ya sa shi ya yi addu’ar bacci ya tofa tukunna ya kwantar da shi akan hannunshi na dama yana sake mishi wasu addu’o’in yana sumbatarshi. 

“I love you Papi.”

“I love you more Junior… Good night.”

Matsawa Junior yayi yana pillow da damtsen hannun Mamdud ɗin kafin ya rufe idanuwanshi bacci ya ɗauke shi. Rufe nashi idanuwan ya yi amma sam banda fuskar Anty Fati babu abinda yake gani. 

Wayarshi da ke Ajiye gefe ya ɗauko yana lalubo lambarta. Zuciyarshi na wani irin dokawa ya kira, bugun farko ta ɗaga kamar tana jiran kiranshi tare da yin sallama cikin yanayin muryarta da ta ƙara buɗewa. 

“Allah Ya sa ban tashe ki daga bacci ba.”

“A’a ban ma kwanta ba. Ina wuni? Ya Junior…”

“Gashi nan ya yi bacci.”

“A shafamun kanshi… Ya madam?”

Murmushi Mamdud ya yi saboda yanayin da ta yi tambayar ya nuna tana son sanin in akwai madam ɗin ne ko babu fiye da yanda take son jin lafiyarta. 

“Babu Madam fa…”

Shiru ta ɗanyi. Baisan me ya sa yake son faɗa mata komai game da shi ba, a lokaci ɗaya kuma yana tsoron abinda hakan zai haifar. Arif ne ya faɗo mishi, jikinshi ya ɗauki ɗumi da sanin lokaci ba ya jiranshi. Duk yadda ya so ya zame wa Junior komai yana buƙatar Mummy ko yaya ne. 

Ba zai rasa sama mishi ita ba, ba zai rasa wadda za ta dace da ƙaddararshi ba. Labeeb ya faɗa mishi ba zai ci gaba da zama a haka ba dama yai mishi gardama. Murmushi Labeeb ɗin kawai ya yi. 

‘In lokaci ya zo ba za ka san lokacin da buƙatar hakan za ta zo maka ba. Ƙaddararka ba ita za ta sa ka yanke hukuncin zama kai kaɗai ba. Idan har ba ka daina jin tsoron me mutane za su ce akan abin da ya a bayanka ba, zai ci gaba da zama barazana a tare da kai . Abinda ya faru dakai naka ne… Akanka ya faru… Ka karɓe shi. Zai daina tsorata ka.’

Lokacin da yake mishi maganar jinta kawai yake ba tare da ya fahimta ba sai yanzun ya gane abinda Labeeb ɗin yake faɗi. Abinda mutane za su ce ba zai taɓa canza tasowar shi a gidan marayu ba. Maganganun su ba zai bashi yara ba. 

Babu abinda Labeeb ya rasa amma mutane basu daina magana akanshi ba. Ƙaddararka kowacce iri ce a ko ina, a koda yaushe sai mutane sun samu abinda za su faɗa akai. Ya rage naka ka zaɓi ko maganganun su za su dame ka ko akasin hakan. 

Da murmushi a fuskarshi ya ja numfashi yana faɗin, 

“Bansan me na ji akanki ba Fatima. Ban damu da yau na fara ganinki cikin ƙasa da mintina sha biyar ba. Koma mene ne na ji shi… Bai da ma’ana har yanzun amma yana nan. 

Bana so ya yi nisan da zan cutu shi yasa zan faɗa miki abinda zan faɗa miki. Ni ba kowa bane ba… A gidan marayu na buɗe idanuwa na. Na samu asali a tare da iyayen baban su Junior. Na samu dukkan gata a wajen su. 

Na samu hatsarin da likitoci suke da tabbacin ba zan haihu ba shi ya sa kika ga Junior a wajena. Ba daga jikina ya fito ba. Amma ɗana ne… Bansan ko kin fahimci hakan ba…banma san ko kina da alƙawarin auren wani akanki ko babu ba…kawai ina son ki san ko ni wanene kafin ya yi nisa…”

Ya ƙarasa maganar yana jin ajiyar zuciyarta har ta cikin wayar. Shiru ya yi yana jiran ya ji ko me za ta ce. Yana jin wani irin ƙwarin gwiwa da bai taɓa ji ba a rayuwar shi. Hamdala yake yana godewa Allah da ni’imar da yake ciki. 

Lafiya, wadata, su Labeeb, da Junior da yake kwance yana bacci a jikinshi. Amsar da Fatima za ta bashi ba za ta taɓa canza komai ba. Zai kashe wayarshi, zai karɓi amsarta kamar yadda ya karbi sauran abubuwan da ke rayuwarshi, zai kuma goge lambarta. 

Zai sake fita gobe in Allah ya kaimu, zai ci gaba da buɗe idanuwanshi har sai zuciyarshi ta sake doka wa wata tukunna ya sake maimaitawa. Haka zai ci gaba da yi har sai ya samu wadda za ta yi dai-dai da rayuwar su shi da Junior.

“Banda alƙawarin auren kowa akaina. Iyayena suna da wadata, ni kaɗai ce ‘ya mace a wajen su… Ni ba hatsari na yi ba…ina da abinda allurar PCOS (Polycystic ovary syndrome) ba lallai in haihu ba… Chances ɗin kaɗan ne. 

Duk wani treatment da kuɗi za su iya an yi min. Duk namijin da zai ji baya dawowa… Bazan auri kowa ba tare da na faɗa mishi matsalata ba… Asalinka halinka. Shi ne abinda zan duba… Shi ne abinda iyayena zasu duba”

Lumshe idanuwanshi Mamdud ya yi, yasan ko menene PCOS yasan komai akanshi. Sai dai ko da ya ji tashi ƙaddarar sam ya manta akwai masu ita, akwai wanda ko tsinke bai soke su ba. Wasu ma babu wani PCOS da ke damun su. 

Kafin ya ce komai Fatima ta ce, 

“Kasan me?”

Girgiza mata kai yayi kamar tana ganinshi

“Na yarda ina da PCOS shi ya sa nake faɗa wa duk namijin da zai nuna wani abu akaina. Sai dai na fi yarda da cewar haihuwa kyauta ce… Kyauta ce da Allah yake ba wanda ya zaɓa. 

Wata cuta ko wasu likitoci basu isa su canza min hakan ba. Yara kyautar Allah ce…”

Junior Mamdud ya kalla. 

“Yara kyautar Allah ce Fatima…”

Ya maimaita yana yarda da kalamanta. Hira suke akan komai na rayuwa, mai muhimmanci da marar muhimmanci har sai da ya ji ta fara hamma tukunna yai mata sallama. Agogon wayar ya duba yana mamakin awannin da suka share suna hira. 

Bai ma san me da me suke faɗi ba. Kawai yana jin kamar zai iya hira da ita duk daren ne a sauƙaƙe. Murmushi ya yi yana kallon Junior da ke bacci. 

“Junior na kusan kawo maka Mummy In sha Allah.”

Wayar zai ajiye kira ya shigo. Labeeb ne, ɗagawa ya yi yana karawa a kunne. 

“Da wa kake ta waya tun ɗazun?”

“Me kika ce mummy?”

Mamdud ya tambaya. Zagin shi Labeeb ɗin ya yi. Dariya yake

“Kaima za ka tsare ni da tambaya kamar Mummy. Ni da Fatima ne…”

Labarin Fatima ya ba Labeeb ɗin da ya gama saurara yana ɗorawa da, 

“Gobe mu haɗu a gida mu faɗa wa Daddy…”

“Woo… Slow down sarkin sauri”

“Koma dai mene ne… Na gaji da ganinka haka. Aure nake son yi maka.”

Dariya Mamdud ɗin ya yi suka ɗan yi hira kafin su yi sallama. Bacci mai nutsuwa ya yi cike da mafarkin Fatima. 

**** 

Hannun Labeeb da ke kan cikinta Ateefa ta doke tana faɗin, 

“Ba za ka daina latsa min ciki ba ne wai?”

Dariya Zulfa da ta ƙaraso wajen tana miƙa wa Ateefa da ke tule kan kafet da tsohon cikinta kofin shayi ta yi. Ta zauna kan kujera tana naɗe ƙafafuwanta. 

“Zulfa ba unguwa za ku tafi ba na ji kin ce?”

Ware idanuwa Zulfa ta yi. 

“Ina zamu mu barki? Haihuwa any minute. Rufa min asiri.”

Hannu Labeeb ya ƙara sakawa kan cikinta, kamar hakan babyn da ke ciki yake jira ya motsa. 

“Zulfa…zo ki ji. Wallahi motsi yake yi.”

Wata dirkowa Zulfa ta yi tana tura hannun Labeeb ɗin ta ɗora nata tana jira babyn ya sake motsawa. Runtsa idanuwa kawai Ateefa ta yi tana rasa yadda za ta yi da su biyun. Tunda cikinta ya shiga wata takwas Labeeb bai ƙara karɓar aikin kowa ba ya dawo gida ya tare. 

Shi da Zulfa kamar su ne da cikin, haka suke isarta, musamman Labeeb da hannunshi ke kusan wuni akai yana jiran ya motsa su zo duk su dafe mata ciki shi da zulfa suna ƙyaƙyata dariya kamar duk duniya babu abinda ya fi jin motsin abinda ke cikinta a hannun su nishaɗi. 

Kamar ƙananan yara haka suka koma kan cikin. Ko motsin kirki ta yi sai su zo su tattare ta suna tambayar ko lafiya. Yanzun ma hararar su take yi amma ko a jikinsu, sun wani nutsar da hankalin su suna jiran su ji motsin babyn. 

Ture hannuwansu ta yi tana ajiye kofin shayin ta dafa ƙasa da dabara tana son miƙewa don fitsarin da take ji. Da sauri Labeeb ya miƙe yana kama hannuwanta ya taimaka mata ta tashi. 

“Kar ka biyoni… Kai zamanka a nan.”

Dariya ya yi yana bin bayanta. 

“Duk kun bi kun ishe ni. Na ƙagu babyn nan ya fito in huta da fitinarku…”

Ateefa take faɗi, ganin Zulfa a gefenta ya sa ta rufe bakinta kawai. Ba ta san yadda za ta yi da su biyun nan ba. Sai addu’a kawai. Tsaye suka yi a bedroom ɗinta suna jiran ta fito daga banɗakin. 

Tana fitowa ta gansu sun yi cirko-cirko suna kallonta. 

“Sannu…”

Labeeb ya faɗi, buɗe ba ki ta yi za ta amsashi wani azababben ciwo ya soki bayanta kamar an karya ƙashin wajen, azabar na sata runtsa ido tana kiran sunan Allah. 

Da sauri Labeeb ya ƙarasa ya kamata. Wani ciwon ne ya sake sukarta da ta rasa tsakanin mararta da bayanta a ina ta fi jinshi. Janta Labeeb या yi yana zaunar da ita, duk sun rikice banda sannu babu abinda suke mata. 

“Wai ba za ku daina min Chinese a saman kai ba ne?!”

Ta tambaya wani ciwon da ya sake sukarta ya sa ta riƙo Labeeb tana salati. Sannun su da suke mata kamar ƙara mata ciwon suke don da wani yare da ba ta fahimta yake zuwa kunnuwanta saboda azaba. 

Zulfa ce tai dabarar rugawa ta fita ta ɗauko mukullin motar Labeeb da ke falo tunda ya fita ya dawo. 

“Innalillahi… Zulfa… Naƙuda take yi… Me za mu yi? Tee… Sannu… Za ki sha ruwa?”

Labeeb ke faɗi a rikice, gaba ɗaya ya fita hayyacin shi. Musamman da ya ga yadda Ateefar ta runtsa idanuwanta ta dumtse mishi hannu da yanayin ƙarfin da bai taɓa sanin tana da shi ba. Banda sunan Allah babu abinda take faɗi. 

“Ka kamota mu tafi asibiti…”

Sai lokacin tunanin asibiti ya zo mishi, da ƙyar su biyun suka kama Ateefa da take jin azabar da tunda ta zo duniya bata taɓa sanin akwaita ba. Sai yanzun ta raina kanta, sai yanzun take jinjina wa duk wata macen duniya da ta ɗanɗani naƙuda ta ji yadda take. 

Da dabara suka kai waje Labeeb ya buɗe bayan motar suka saka ta a baya. Zulfa ta shiga, shi kuma ya zagaya ya zauna. Hannunshi kyarma yake ya kasa saka mukullin ma. 

“Yaya Labeeb… Yaya Labeeb!”

Zulfa ta kira. Juyowa yayi yana goge zufar da ke fito mishi a goshi. Idanuwanta ta sa cikin nashi. 

“You can do this… Babyn mu ne a hanya… Ka juya ka nutsar da hankalinka wajen kaimu inda za a taimaka mata. Shi ta fi buƙata a yanzun.”

Kai ya ɗaga wa zulfa ya samu ya tattaro duk nutsuwar da zai iya waje ɗaya ya tashi motar suka nufi Dialogue. 

**** 

Dole suka bar Labeeb a ɗakin tare da Ateefa. Zulfa kam ita ta kira su Dawud ta faɗa musu, kafin mintina talatin asibitin ya cika. Dawud shi da yumna da cikinta daya fara turowa. 

Tayyab, Mami, Khateeb da Mummy tare suka zo, sai Jarood da shi daga wajen aiki yake ma. Asad, Anees, Mardi da Uzair a mota ɗaya suka zo suma. Suna tsaye cirko-cirko. Babu mai magana sai wayar Zulfa da kan yi ringing lokaci-lokaci ta ɗaga ta faɗa wa Zainab har yanzun ba su fito ba dai. 

Zainab ji take kamar ta yo tsuntsuwa ta taho, saidai ko da haihuwa Ateefa ta yi Zulfa ba ta jin Zainab za ta zo. Ciki gareta da ya zo mata da laulayi mai wahalar gaske. Ishaq ba zai bari ta zo ba tunda ba wadatacciyar lafiya gare ta ba. 

Suna nan Mamdud ya zo da Junior. Sai da Zulfa ta ji zuciyarta tai wani irin dokawa. Rabon da ta ganshi har ta manta, jikinta har kyarma yake kuma Labeeb baya kusa da ita. Tayyab ta ji ya riƙe hannunta. 

“It’s OK…”

Ya faɗi ƙasa-ƙasa. Kai ta ɗaga mishi, duk da zuciyarta ba ta daina dokawa ba jikinta ya bar kyarmar da yake yi. Sai da Mamdud ya gaisa da kowa. Ita ce bai ce ma komai ba, don yadda tata zuciyar ke dokawa haka shi ma tashi ke yi. 

Duk da ya ji yafiyarta a wajen Labeeb bai hana ganinta sashi jin wani iri ba. Hannun Junior dumtse cikin nashi ya samu waje yai tsaye. Saboda Labeeb ya zo wajen nan. Saboda shi kawai. 

Bai jima ba Labeeb ya fito fuskarshi ɗauke da murmushi. Su duka suka yi kanshi kamar za su cinye shi da tambayar ko ta haihu. Kai yake ɗaga musu. 

“Mace…”

Ya faɗi ya kasa daina murmushi, hannuwanshi yake kallo da ya riƙe yarinyar shi. Kafin su haɗa idanuwa da Mamdud da ya jinjina mishi kai, su Zulfa suka fara nufar ɗakin suna cin karo da Doc ɗin da ta karɓi haihuwar Ateefar. 

“Ina za ku je?”

“Ganin baby…”

“Ku tsaya… Ku dukkan ku?”

Kai suka ɗaga mata. Tayyab na faɗin, 

“Ba za mu yi surutu ba… You have my word… Pleaseeeeee.”

“Pretty pleaseeee.”

Asad ya faɗi yana mata wani cute face. Numfashi ta sauke tana ɗaga musu kai. Su dukkansu suka shiga, Zulfa ta ƙarasa ta zauna a gefen Ateefa da kallo ɗaya za ka yi wa fuskarta ka san banda hutu babu abinda take buƙata. 

“Sannu da aiki.”

Zulfa ta faɗi tana jinjina mata. Kai kawai Ateefa ta iya ɗagawa, tana miƙa wa Zulfa babyn da ke hannunta. Karɓar babyn Zulfa ta yi naɗe cikin towel idanuwanta a runtse. Kallonta take, sabuwar rayuwa, zuciyarta na wani irin matsewa a ƙirjinta. 

Kafin ta miƙe da babyn, Asad ya ture kowa yana yo gaba. Dariya Labeeb ya yi. 

“Tsaya in goge hannuna…”

Asad ya faɗi yana goge hannunshi jikin wando ya ware su duka biyun yana miƙa wa Zulfa. Miƙa mishi ita ta yi tana gyara mishi zamanta. 

“A hankali…”

Kai ya ɗaga yana kallon fuskar yarinyar. 

“Bana jin nauyinta… O. M. G Mummy kar ta faɗo…”

Dariya suke wa Asad kafin Mami ta ƙaraso ta karɓeta daga hannun Asad. Addu’a tai mata sosai tana kai wa Mummy ita. Haka sai da kowa ya ɗauke ta sannan suka mayar wa da Ateefa yarinyar. 

Kowa ka kalli fuskarshi wani nisantaccen yanayi ne ɗauke da shi. Duk yadda rayuwa ta ɗauke su tai yawo da su. Duk yadda ta gwara su, da ƙaunar junansu ta ƙaraso da su waje mai nutsuwa irin yau. Kallon juna suke da sanannen yanayi. Zainab ce ta kira Zulfa video call ta haska mata yarinyar. 

“Awwn… Ni kaɗai ce bana nan.”

Ta faɗi kamar za ta yi kuka. 

“Ƙaunarki na nan tare da mu komai nisan da kika yi…”

Labeeb ya faɗi yana karɓar wayar suka gaisa ta mishi barka. Mamdud ya miƙa wa. 

“Wallahi kar ka sake a sa bikinka lokacin da ba zan iya zuwa ba.”

Dariya Mamdud ya yi. 

“Ke zaki zaɓi date da kanki.”

“You know kaine favorite ɗina ko?”

Kafin ya amsa Asad ya karɓe wayar. 

“Na ji me kika ce…”

Dariya ta kama yi kafin ta ce, 

“Wannan ne farko ko?”

“Shi ne farkon daidaitar komai in sha Allah. Rayuwarmu ba ta zo nan da sauƙi ba…”

“Rayuwarmu ba perfect bace…”

Anees ya ƙarasa wa Asad. 

“Sai dai da duk abinda ya faru gamu anan… Tsaye da ƙafafuwan mu.”

Dawud ya faɗi yana dumtse hannun Yumna a cikin nashi. Jarood na murmushi ya ce, 

“Zumuncinmu shi ne ƙarfinmu”

“Bana jin akwai faɗuwar da za mu yi in dai muna tare da juna mu kasa tashi…”

Tayyab ya faɗi yana kallon su.

“A tare daku na koyi abubuwa da yawa…”

Mami ta ce tana kallon su, ƙaunar su dukkan su na shigarta. Mummy ta sauke numfashi. 

“Rayuwarmu kenan… Cike da abubuwa kala-kala…”

“Babu abinda ban gani ba tare da ku. Babu abinda ban samu ba… Da ƙaunarku na kawo inda nake…da ƙaunarku zan kasance mai godiya ga Allah da ya sa na sanku…”

“Allah ya sa yau da duk sauran ranaku su ci gaba da zuwa mana da sauƙi, aminci da ƙaunar juna.”

Zulfa ta faɗi kowa ya amsa da amin. Tare da junansu sun koyi haƙuri. Tare da junansu sun koyi yafiya. Tare da junansu sun san ma’anar ƙauna da muhimmancin zumunci. Yau su ne anan. Rayuwar su ce anan. Ba anan ta fara ba….ba kuma anan za ta ƙare ba.

****** 

Epilogue

BAYAN SHEKARA BIYAR

“Ummi ruwa…”

Arif ya faɗi yana riƙo Ateefa da ke ƙoƙarin maida kayan da Iman mai sunan Mummyn su Labeeb wato Habiba ta janyo mata. Juyowa ta yi tana jin kamar ta kwaɗa ea Iman ɗin mari. 

“Ba na hana ki shigo min ɗaki ki min jaye-jaye ba?”

Shagwaɓe mata fuska Iman ta yi hawaye fal idanuwanta. 

“Hijabina ne ban gani ba wanda Ammu ta siyo min rannan.”

Iman ta faɗi hawaye na zubo mata. Arif ta kalla. 

“Sake min ƙafa. Ba akwai ruwa a gefen gado ba yanzun na fito da shi?”

“Don Allah Ummi ki ɗauko min.”

Iman ta faɗi wasu hawayen na zubo mata. 

“Za ki bani waje ko sai na kwaɗa miki mari?”

Ateefa ta faɗi fuskarta babu alamun wasa, wucewa Iman ta yi tana kuka. A bakin ƙofa ta ci karo da zulfa da a shekaru biyar din nan da suka wuce musu kamar wata biyar. Tun Labeeb na kaita asibiti har ta ce mishi su haƙura kan haihuwar.

Sai gashi da suka bar wa Allah komai yanzun ciki ne wata uku a jikinta. Iman na ganinta ta ruga da gudu wajenta. 

“Ammu…”

“Waye a gidan nan bai son zaman lafiya ya taɓa min Iman ɗina?”

Zulfa ta faɗi tana sa hannu ta goge ea Iman ɗin fuska. Dai-dai lokacin da Ateefa ta fito daga ɗaki, Iman ke faɗin 

“Ummi ce ta ƙi ɗauko min hijabina da kika siyo min…”

“Kin ga kayan da yarinyar nan ta janyo min? Nama hana ta kawo min kayanta ɗakina ba ta jin magana.”

Riƙe Iman Zulfa ta yi tana murmushi. 

“Tun da ba ki ɗauko mata hijabin ba sai kin samin ita kuka?”

Labeeb ne ya shigo da sallamar shi. Da gudu Iman ta ƙarasa tana tarbarshi. 

“Abbu sannu da zuwa.”

Ɗagata yayi yana ƙarasowa inda suke, banda sajen da ke fuskarshi shekarun nan biyar haka suka wuce basu nuna komai a jikin shi ba. Kamar yadda ya ce musu baisan yadda zai yi wani abun banda harkar fim ba, sai dai akwai acting ɗin da ba zai iya ba yanzun saboda yaranshi. 

Akwai abubuwa da yawa da zai ajiye domin kare mutuncin su. Don haka kacokan ya matsa wa sauran sabbin stars da ke tasowa waje ya koma ɓangaren production. 

“Har yanzun ba ku shirya ba wai?”

Ya tambaya yana kallon su. 

“Ni hijabina kawai zan ɗauko.”

Zulfa ta faɗi m. 

“Abbu… Ummi ta ƙi ɗauko min nawa.”

Ateefa ya kalla.

“A ɗauko mata hijainta”

“Ban ganshi ba nikam… Ba ma na jin yana ɗakina.”

Ware mata idanuwa Labeeb ya yi. 

“Don Allah ki duba mata tunda shi take son sawa.”

“Kai da zulfa kuna ɓata yarinyar nan wallahi…kamar Iman sai abinda take so ne dole za a yi.”

Ƙarasawa inda Labeeb yake Zulfa ta yi ta karɓi Iman daga hannunshi. 

“Bari mu je mu dubo wani ko?”

Sumbatar Zulfa Iman ta yi a kuncinta. 

“I love my Ammu.”

Ta faɗi, mayar mata da sumbar Ateefa ta yi. 

“Ammu love Iman da yawa…”

Binsu da kallo Labeeb ya yi, cikin da ke jikin Zulfa ya sa ta ƙara wani irin kyau, ta yi ƙiba. Sai da ya ga sun hau benen tukunna ya taka inda Ateefa take tsaye. Mintsinin ta ya yi a kunci ta ture mishi hannu tana yamutsa fuska

“Da zafi fa…”

“Kin bi min yarinya da faɗan ki ko?”

Cikin idanuwan shi ta kalla. 

“Ba kwa son laifin Iman.. Musamman zulfa. Duk kun shagwaɓata.”

Buɗe baki ta yi ta ji ƙarar fadowar wani abu, da gudu ta tura ɗakin tana shiga. Labeeb ya bi bayanta. Arif ne tsaye da robar ruwa a hannunshi da ya sadda kanta ƙasa tana zuba, ya buɗe bakin shi yana kallon wayar Ateefa da take a ƙasa. 

Da gudu ta ƙarasa ta fara ƙwace robar ruwan ta ajiye, ta ɗauke shi tai gefe da shi tukunna ta tsugunna ta ɗauki wayarta da screen ɗin tuni ya tashi aiki ga ruwa da ta sha tana hurewa. Dariya Arif ya ƙyalƙyale da ita. 

“Abin dariya ya ba ka ko? Ka fasa min waya abin dariya ya ba ka?”

Wannan karon Labeeb ne yake dariyar. Hararar shi ta yi. 

“Kaima abin dariya ya ba ka kenan?”

“Yi haƙuri… Arif zo mu tafi kafin Ummi ta mana duka.”

Labeeb ya ƙarasa yana ɗaukar Arif ɗin. Wayarshi ta soma ringing ya zaro daga aljihunshi yana dannawa ya kara a kunne. 

“Zee Zee.”

“Yaya kuna wajen meeting ɗin?”

Ta tambaya. Don ita ma tana garin, jiya suka zo wajen family meeting ɗin da sukan yi duk bayan wata shida. 

“A’a, yanzun dai zamu fita. Ya akai?”

Tana dariya ta amsa da, 

“Bakomai… Dama kira na yi in ji ko mu kaɗai muka makara… Kuma bamu kaɗai ba ne. Sai kun taho…”

Ba ta jira amsarshi ba ta kashe wayar.

“Tee yi sauri…kin ji Zainab fa… Wai ta ji daɗi ba su kaɗai suka makara ba.”

Dariya Ateefa ta yi. 

“Sai mun riga su zuwa ai… Bari in sako kaya in fito.”

Kai ya ɗaga mata yana fita shi da Arif. A mota Iman da Zulfa suka same shi. Gaban motar Zulfa ta buɗe ta saka mishi Iman tana komawa baya ta zauna, Ateefa ma na fitowa ta buɗe bayan ta shiga. 

“Me kuke nufi? Waye za ku hakimce wa a bayan motar ya ja muku?”

“Mijin hajiyoyi.”

Ateefa ta faɗi, sosai abin ya ba Zulfa dariya. Shi kanshi Labeeb duk yadda ya so kar ya yi dariya sai da ta kubce mishi. Ƙaunar su a jininsa take. 

***** 

Kayanta tagama sawa tana zaune a bakin mirror tana shafa powder a fuskarta, sauri-sauri take yin komai kafin Khadija ta tashi daga baccin da ta samu ta lallaɓata ta yi. Ganin an murza handle ɗin ƙofar ya sa ta cilli da soson powder ɗin da take shafawa tana rugawa ta buɗe ƙofar a hankali. 

Ishaq ne sanye da farin yadi, aikin jiki light blue haka ma hular kanshi da agogon da ke hannunshi. Sumbatar ta ya yi ta janyo hannunshi tana shigo da shi ɗakin tare da tura ƙofar a hankali. 

“Kar ka tashimmun Khadee. Ka ga abinda ya sa nace ka barni in kwana a gida rikicin ka ya hana ko? Har goma ta kusa.”

Ta karasa tana hararar shi. Dariya ma ya yi yana faɗin, 

“Na fi son ganin ku a kusa da ni?”

“Don Allah ka daina min wannan fatan. Sai ka ce wata kaza?”

“In ma kazar ce ai tawa ce ko? My kaza.”

Girgiza kai kawai Zainab ta yi tana ƙoƙarin ɓoye dariyarta. Ishaq ba zai tgaji da burgeta a kowace rana ba. Ba ya gajiya da sa ta dariya. Soson powder ɗinta ta ɗauko can gefen gado, ba ta koma ta zauna ba aka bankaɗo ƙofar da ƙarfi. 

Yasir ne ya shigo Yassar na biye da shi, yaranta na farko kenan. ‘Yan biyun su ita da Ishaq. Kamar da suke ne ya sa dole suke musu aski kala daban-daban don su dinga gane su. Kallon da Zainab ke musu ne ya sa su faɗin, 

“Sorry…”

Lokaci ɗaya sujs koma da gudu suka ja ƙofar suna yin sallama. Ishaq ne ya amsa musu tukunna suka shigo. Khadeeja ta farka ta soma kuka. Tashi Zainab ta yi ta ɗauketa tana saɓe ta a kafaɗa tare da rocking dɗinta. 

Su Yasir ba su yi mata rigimar nan ba. Barsu da ƙiriniya har ba ta son ta fita unguwa da su. Amma Khadee rigimarta sai addu’a. Ishaq ne ya ƙarasa yana karɓarta. 

“Kawo ta in riƙe ta ki ƙarasa shiryawa.”

Bai rufe bakin shi ba ji kake tas. Yasir ya ɗauke Yassar da mari. Sai faɗa ya kacame, duk haƙurin Yassar lokuta irin hakan sai Yasir ya ƙule shi. Ko musayar magana yanzun zaikai hannu kuma shi ne ƙarami. 

Da ƙyar Zainab ta ɓanɓare su tana ce ma Yasir, 

“Me ya sa ba ka da kunya ne? Ban hana ka saurin hannu ba? Je ka zauna a can ba inda zan je da kai. Dama na faɗa maka ai.. Mun ɓata.”

Yassar ne ya riƙo hannu Yasir da yai rau-rau da idanuwa zaiyi kuka. 

“Mummy yi hakuri. Mun daina fada ko Yasir?”

Kai Yasir ya daga yana kallon Yassar

“Am sorry”

“Ya bani haƙuri ma… Daddy ka ce Mummy ta je da Yasir.”

Kallon su Ishaq yai yana murmushi tare da jijjiga Khadee da ta yi luf a jikinshi. Ko ya za su yi faɗa kamar za su cinye juna kai ba ka isa ka ce za kai wa ɗaya faɗa ba yanzun za su haɗe maka kai. 

“Mummy ki je da su duka tunda sun daina faɗan.”

“Ku ɗaukar min jaka ku kai mota to.”

Da gudu suka ƙarasa kan gadon suka sa hannu kan Jakar. Yassar ne ya sakar wa Yasir don yasan rigima zai sa suka fita tare. 

“A haka kake min fatan wani cikin? Su ukun nan kamar in kai ajiya in ɗan huta nake ji.”

Dariya Ishaq ya yi. 

“Na ce ki samo me raino.”

Da sauri ta girgiza mishi kai. 

“Me yasa takarduna suke ɗaukar ƙura a ɗaki? Bazan bar yarana a hannun kowa ba. Zan kula da su da kaina…”

A gurguje ta ƙarasa shafa hodar ta mike tana ɗaukar ɗankwalinta ta ɗaura. Wayarta da ke ajiye ta ɗauka ta ga goma har ta wuce. 

“Bari in kira yaya inji…Allah yasa bamu kaɗai muka makara ba.”

Labeeb din ta kira tukunna ta sa takalminta tana faɗin, 

“Su ma basu fita ba.”

Dariya Ishaq ya yi yana wucewa gaba ta bi bayanshi suka fice daga gidan suma. 

**** 

Mami na kitchen ta ji sallamar su Dawud. Amsawa ta yi tana fitowa, da gudu Ahmad ya ƙwace daga hannun Yumna yana rugawa jikin Mami.

“Babban maigida…”

Mami ta faɗi.

“Ina kwana.”

Ahmad ya gaishe da Mami ta amsa tana maida hankalinta kan su Yumna. Gaishe da ita suka yi suma. Ta kalli Aliyu da ke kafaɗar Dawud ɗin. 

“Sarkin bacci sana’ar ake kenan?”

Dariya Dawud ya yi. 

“Kai Mami har ya koma sarkin baccin gaba ɗaya ma.”

“Yaushe kuka taɓa zuwa min da shi ido biyu?”

“Yau zai ba ki mamaki Mami. Ali ka buɗe ido yau.”

Tayyab da ya fito daga ɗakin shi zuwa falon ya faɗi. 

“Gwauraye an tashi kenan.”

Dawud ya faɗi. 

“Nan da wata uku za ku daina yi wa ɗana tsiya in sha Allah…”

Mami ta faɗi tana murmushi. Gaishe da su Tayyab ya yi suka amsa da fara’a.

“Shi da Anees ai da za mu raba hotunan su a masallacin Juma’a ko za a samu mai so.”

Dariya Tayyab yake yi.

“Kai jama’a wai mun kawo matan ma ba mu huta da surutunku ba.”

Tayyab ya faɗi. Taɓe baki Dawud ya yi. 

“‘Yan mata dai. Sai an ɗaura tukunna.”

Wucewa Tayyab ya yi ya karɓi Aliyu daga hannun Dawud da ke baccin shi, duka watan shi uku kenan, su zulfa har tsokanar Yumna suke wai matar Doc an yi tsarin iyali. Duk da sun san babu wani tsarin iyalin da ta yi. Allah ne ya tsara mata abinta. 

“Ina Khateeb?”

Dawud ya tambaya. 

“Ya je Islamiyya tun ƙarfe bakwai. Wai gara kar ya yi asarar lokacin kafin duk ku zo.”

Jinjina kai Dawud ya yi. Nacin makarantar Khateeb na tuna mishi Sajda. Ita dai ko me za a yi kar a ce ba za ta je makaranta ba. Waje Yumna da su Tayyab suka samu suka zauna . Dawud kam Mamin shi yabi kitchen yana tayata aiki suna hira. 

**** 

Fitowar da suka yi ba su ci komai ba ya sa Mamdud fita da Junior daga asibitin ya bar Fatima don ya samo mishi wani abin da zai ci. Yoghurt kawai Junior ya ɗauka da faɗin, 

“Wannan ma zai yi Papi… I am not that hungry.”

Kuɗin Mamdud ya biya suka kamo hanya suka dawo. Da wuri suka shirya sanin meeting ɗin da suke da shi karfe goma. Breakfast za su yi, da Mamdud ba ya tsaye da Fatima tai mummunar faɗuwa saboda jirin da ya kwashe ta. 

Karin da ba su yi ba kenan suka taho Asibiti, hango ta ya yi ta taho da takarda a hannu tana sa hannu tana goge fuskarta. Da sauri suka ƙarasa shi da Junior.

“Mine…”

Mamdud ya faɗi yana nazarin fuskarta, kallon shi ta yi hawaye na zubo mata. A rikice ya riƙo hannunta, yasan ta sarai, ba ya zaton bayan Labeeb a rayuwar shi ya taɓa ganin mai haƙuri irin na Fatima. 

Ko tsakanin harshe da haƙori ana samun saɓani amma shekaru huɗun nan da suka yi tare ba ta taɓa ɗaga mishi murya ba. Ko da za ta ɓata mishi rai ya yi faɗanshi sai dai tai shiru in ya gama ta ba shi haƙuri. 

Wannan ne karo na biyu da ya taɓa ganin hawayenta na zuba haka. Tun daren auren su, sai kuma yanzun. Shi ya sa ba ƙaramin ɗaga mishi hankali ta yi ba. Har ya rasa kalaman da zai mata magana da su. 

Takardar da ke hannunta ta miƙa mishi tana riƙe fuskarta da dukka hannayenta tana kuka har jikinta ke ɓari. Sam ya kasa buɗe takardar. Junior ne ya riƙo hannunta yana ƙoƙarin ganin ta daina kukan da take yi. 

Tsugunnawa ta yi ta kasa daina kukan, hannu Junior ya sa yana goge mata fuskarta tare da girgiza mata kai shi ma idanuwanshi cike da hawaye duk da baisan kukan me take ba. 

Ɗago ta Mamdud ya yi ya kasa samun nutsuwar buɗe takardar saboda kukan da take ya karya mishi zuciya. Da tsoro ƙarara a muryarshi ya ce, 

“Mine… Me suka ce ya same ki? Mene ne?”

Ya ƙarasa yana haɗiye wani abu da ya tsaya mishi a wuya. Jikinshi na ɗaukar ɗumi da wani zazzaɓin tashin hankali. Ba zai iya jure wani abu ya sameta ba, cikin ƙarfin halin da ba ya jin shi ya riƙo ta yana haɗa goshin shi da nata ba tare da damuwa da inda suke a tsaye ba. 

“Ki faɗa min don Allah mene ne?”

Kasa magana ta yi sai hannunshi da ta kamo ta ɗora akan cikinta. In da har zuciyar shi na iya barin ƙirjinshi zai ce ita ce yake ji tana yawo a ko ina na jikinshi cikin sauri ta kewaye ko ina kafin ta koma mazauninta ta nutsu tana son fahimtar abinda Fatima take nufi. 

Cikin kuka take danna hannunshi akan cikinta. 

“Wata…wata biyu…”

Ko da tai missing period ɗinta ba ta ɗauke shi komai ba. Don takan yi har na wata uku wani lokacin. Miyau ya nema a bakinshi ya rasa. Kai yake girgiza mata yana son ya ce mata in wasa take ta bari. 

In zolayarshi take son yi ta zaɓi wani abin daban banda maganar ciki amma ya kasa saboda idanuwanta da yake kallo yana ganin gaskiyar maganar da ta faɗa. 

“Ciki… Ciki gare ki?”

Mamdud ya tambaya yana jin kalaman na zame mishi baƙi a cikin bakin shi. Kai ta ɗaga mishi hawaye na zubo mata. Runtsa idanuwanshi Mamdud yayi. 

“Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ke da Iko akan komai da kowa. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yake kyauta ga wanda Ya so. Tsarki ya tabbata ga Ubangiji…”

Mamdud ke faɗi karfin abinda yake ji a zuciyarshi na zubo da hawaye daga idanuwan shi. Baisan abinda ya kamata ya yi ba. Sakin Fatima yayi yana zubewa ƙasa da yin sujada kafin ya ɗago ya rungumeta a jikinshi. 

“Papi mene ne?”

Junior yake tambaya yana kallansu cike da rashin fahimta. 

“Mummyn ka za ta yi maka ƙani ko ƙanwa Junior.”

Ware idanuwa Junior ya yi don ya sha tambayar su shi ma yaushe zai samu ƙannai? Don baya son in Iman ta zo musu weekend ta tafi. Sai dai su ce mishi yaita addu’a. Tunda yana da su Iman zai ƙara samun wasu in yana addu’a sosai. 

Rungume su ya yi shi ma. 

“Sallah na yi jiya Papi… Banyi bacci ba ina ta addu’a… Allah ya amsa ko?”

Kai Mamdud yake ɗaga wa Junior yana jin kamar ya mayar da shi da Fatima cikinshi saboda ƙaunar su da yake ji. Sun kai mintina goma suna tsaye kafin ya saketa ya kama hannuwansu ita da Junior suka fice daga asibitin. 

***** 

Ta cikin mudubin motar Mardiyya ke kallon fuskarta tana ganin yadda hancinta ya baje. 

“Kowa yayi kyau nasan sai ni nake fama da ƙaton hanci.”

Ta faɗi tana turo baki, ɗan kallon ta Asad ya yi yana mayar da hankalin shi kan tuƙin da yake yi, watan cikinta biyar amma ya yi wani irin girma. Gaba ɗaya ta sauya kamanni. Fuskarta cike take da pimples, ga hancinta da ya yi wani irin girma. 

Dariya Asad yake yi, ƙwalla ta ciko idanuwan Mardiyya. 

“Abin ma dariya yake ba ka ko?”

Haɗiye dariyarshi yayi. Mood swings ɗinta ko ba ciki zuwa yake balle yanzun da ta samu dalili. Hawayen da ke idanuwanta suka zubo. 

“Ka ci gaba… Tun da ba a jikinka yara uku suke girma ba… Ba hancinka bane yake kamar an taka tomato.”

Sake bushewa da dariya Asad ya yi, komin girman hancinta, komin yadda ta koma inya kalleta babu abinda ke cika zuciyarshi sai wani sonta da ya fi na da. In ya kalli cikinta ya tuna ba ɗanshi ɗaya bane a jikinta. Yara ne har uku ji yake kamar ya ɗauketa ya goya ta. 

Parking ya yi a gefen hanya ya juya yana kamo hannunta. Fuskarshi babu alamun wasa ya sumbaci hannunta. 

“Mardi yarana ne har uku suke girma a jikinki… Yeah ba a jikina suke ba. Bazan taɓa sanin yadda kike jin nauyin su ko wahala da su ba… Ba a fuskata ƙurajen nan suke ba. 

Hancina na nan yadda yake. Kin san me ya canza a jikina?”

Kai ta girgiza mishi. Matsawa ya ƙara yi yana ɗora hannunta akan ƙirjinshi. 

“Da duk wani canji da jikinki yake saboda yarana zuciya take ƙara canzawa da ƙaunarki. Da babban hanci.. Da ƙurajen.. Da cikin ki da ke ƙara girma… Duka ƙaunarki ba ta canza ba sai ƙaruwa da ta yi…”

Dayan hannunta ta sa tana shafar cikinta. 

“Ina ƙaunar su sosai tun kafin in gansu.”

Sumbatar hannunta ya sake yi.

“Ina ƙaunar ku huɗun dukkanku.”

Dariya ta yi. Sannan ya saki hannunta ya ja motar suka tafi. 

***** 

Hotuna kawai suke ɗauka, ba wani abu suka tattauna a wajen meeting ɗin ba. Wasu kan yi family meeting don a tatattauna matsalolin family. Wanda yake da matsala da wani a sulhunta. 

Sukan yi nasu ne don su kalli junansu cike da ƙauna. Don su ga ci gaban da yake faruwa a rayuwar junan su, don su ga da duk yadda kowa yake tsaye da ƙafafuwan shi, da yadda kowa yake da gidanshi da iyalanshi. 

Da yaransu dukkan su, ƙaunar su ba ta canza ba. Kusancin su bai samu rauni ba sai ma ƙarfi da kusancin da yaran su suke samu. Hira suke su ci su sha su ɗauki hotuna. Shi ne kawai abinda suke yi a nasu family meeting ɗin. 

Yanzun ma hotunan suke yi Mamdud ya yi ƙasa da muryarshi saitin kunnen Labeeb. 

“Fatima ciki take da… Wata biyu.”

Su da basu san me ya faru ba wani irin tsalle suka ga Labeeb ya yi yana rungume ɗin Mamdud. Duka hankalin su komawa ya yi kan Mamdud da Labeeb ɗin. Ba tare da ya saki Mamdud ba yana wata dariya ya ce, 

“Fatima ciki take da shi.”

“Ba wasa kake ba ko? Wallahi Yaya in wasa kake ka sa zuciyata tsalle haka kuka zan yi.”

Zainab ta faɗi tana jin hawayen da ya cika mata idanuwa. Kai Labeeb yake ɗaga mata yana wata irin dariya. Da gudu ta ruga ta ruƙunƙume Fatima. Suma su Asad din Labeeb da Mamdud suka riƙe, basu damu da hug ɗin bai kaiwa kan Mamdud ba, duk wanda ya samu wani akanshi yake ɗora hannuwan shi. 

Ƙaunar su mai girma ce. Basu fara ta da sauƙi ba sai dai sun ƙareta cikin nutsuwa. 

<< Rayuwarmu 50

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.