Cikin haka Nabila ta fara rankwasar qofar dakin. Ya dan jima bai kai hankalinsa kan azancin cewa zai yi a bude a shigo ba, sai daga can zuciyarsa ta tuno ta ba shi dama.
Bismillah.
Babu zato Nabila ta turo qofa ita da nutsuwarta suka shiga, bayan kunya da ta ke musu jagora.
Ya yi kasaqe cikin qoqarin dauke numfashi da cokalin shayi a hannu yana kallonta.
Da qyar ya iya sarrafa kansa ya nuna mata gurin zama.
Shigo-shigo, ga guri zauna.
Ba za ta iya haqiqance yadda ta kai kanta kujerar ta zauna ba, ita dai ta ganta zaune tana gaishe shi a kunyace yana amsawa da fuskar nan tasa wacca ta saba gani, wadda kuma ba ta taba kwatanta mata tatsuniyar da Anti Binta ke shan labarta mata ba wato Yaya Mujahid na sonta.
Yanzu gabadayanta a muzance ta ke, don yadda ya karbi gaisuwarta ya tabbatar mata lallai Binta tatsuniyar ta ke.
Bayan gaisuwar duk sun yi jugum-jugum, ita kai a qasa tana jin ina ma ta yi girgiza ta zama ba ita ba, shi kuma da ya gaji da zaman shiru da kuma rashin abin fada kawai sai ya yi fuska ya ci gaba da shan shayinsa.
Wannan matakin nasa ya sanya Nabila ta ji tana son barkewa da kuka, da qyar ita da jarumtarta suka taru suka hana ta.
Can ta dago kai a sanyaye ta dube shi, ba tare da ta shirya ba ta ji tana ce masa.
Anti Binta ta ce kana kirana akwai wani saqo da za ka ba ni.
Ya dago sosai ya tsayar da ganinsa a qwayar idonta suka yi wa juna kallon ido cikin ido sama da sakanni talatin, Nabila ce ta fara kawar da kai bayan ta gama dahuwa a zafin so har tana shirin fara narkewa, ta san tuni tana son Yaya Mujahid duk da tana qaryata kanta, amma cikin sakannin nan ta gaskata kanta ta qara har da jin son da ta ke masa ba a taba irinsa ba a duniya shi ya sa ta yi saurin dauke kai don ta san tana gab da bayar da kai a fatar baki ko ta ido ko kuma ta hanyar fashewa da kukan da shi ne qarshen bayyana so.
Duk abin da ta ji a ranta Mujahid ya hango a qwayar idonta, don haka ya dinga jin wasu abubuwa masu kaushi na yakushinsa a qirji, tausayinta da kuma neman dalilin ma da za ta so shi.
Daga qarshe sai abin da ya fi su kaushi ya zo ya danne su, wato son Binta. Bai ga dalilin da wani tausayi ko neman dalili za su kawo masa waigi har da neman yin nasara a kansa ba, Binta ya ke so, kuma wannan ce gabar da zai nuna mata ya nuna wa duniya, ya kuma katange kansa daga wannan banzar alaqar soyayyar da ta qirqirar masa ba tare da ta dace da shi ba.
Nan da nan ya yi fuska ya miqe yana ce mata.
Ashe ba ta manta ba, dan jira ni kadan Nabila.
Ta yi mutuwar zaune zuciyarta na faman lugude tana bin qofar dakin da ya shige da kallo. Tana da yaqinin da Allah ya hukunto ajalinta da tashin hankali, haqiqa wanda ta ke ciki yanzu ya isa kashe ta kafin Mujahid ya fito da saqon da zai ba ta, idonsa da yanayin maganar da ya yi mata ba su nuna alkhairi suke nufi da ita ba, saboda haka ko kadan ba ta sanya rai alkhairi zai fito mata ba.
Tana can duniyar rudaninta ba ta iya qiyasta tsawon lokacin da ya dauka ba, ya fito hannunsa dauke da wata farar siririyar ambulan mai adon furanni, dayan hannun kuma yana dauke da fure (bouquet).
Maimakon zuciyarta ta sami nutsuwar hango shi da alamun bayyana so, musamman bisa duban annurin fuskarsa ya qaru kuma ya qara masa kyau, sai fargabarta ta qaru tare fa kabbama mata zargin Mujahid ya fi qarfinta.
Ya qaraso gabanta ya same ta cikin rashin hayyacinta, amma ya tattara dukkan raunin da zai sanya shi tausayinta, ya watsar cikin karsashinsa ya miqa mata furen.
Ba hannunta kawai ba, ita da illahirinta bari suke ta miqa hannu ta karbi furen tana duban tsakiyar idonsa tamkar in ta dauke za ta juyo ta ga babu shi.
Bai yi qasa a gwiwa ba, ya sake miqa mata takardar. Nan ma jikinta na rawa ta karba tana binsa da kallon rashin fahinta wanda a zahiri qarfi ta sanya ta mayar da shi na rashin fahimtar alhalin ya fito zuciyarta kai tsaye a matsayin mai mayen so.
Ya yi taku uku daga gabanta bayan ya juya mata baya yana soke da hannu a aljihu.
Allah ya ba ki ladan qulla harkar alkhairi irin wannan.
Tana jiran zubar ruwan kalmomin so daga bakinsa kamar zubar ruwan sama, amma sai ta ji wadannan qwayoyin kalmomin nasa sun fado kunnuwanta, dole ta zarce da yi masa kallon rashin fahinta a gaske.
Ba ya dubanta saboda haka bai san waqiar da ta ke ciki ba ya juyo yana fuskantarta cikin taushin lafazi ya ce mata.
Ki kai wa Binta wannan saqon, ba sai kin ce mata komai ba, in ta karanta za ta fahince mu.
Nabila da zuciyarta gabadaya suka taru suka rude ta sauke kai a kasalce ta kalli fure da ambulan din hannunta wadanda a sakannin da suka wuce ta ke ganinsu zuciyarta na bugawa da shauqin su ne mabudin tarihin soyayyarta mai razana zuciya, ashe ba za su dade suna shan wannan sharafin ba za su dawo baqaqe a idanunta, kuma makullan kulle tarihin soyayyarta da kullewar ba za ta hana ranta so ba, sai ta ji tana son xora hannu a ka ta kece da kuka, amma ta yi ta mazan shanyewa, ta zaga kai tana binsa da kallo cikin kada kan da ya kasa boye rashin hayyacinta.
Ta miqe da barin jikinta tana cewa.
To bari na yi sauri na kai mata Yaya Mujahid.
Duk dauriyar Mujahid da yadda qaunar Binta ke buga masa guduma a qirji sai ya kasa ci gaba da waske lurar da ya yi Nabila a cikin milyoyin sonsa ta ke, ya ji tausayinta ya karci ransa, har ya dan ji nadamar danyen hukuncin da ya yanke mata alhalin duk inda masoyi ya ke ko a bisa dole ne ya cancanci a kiyaye abin da zai sosa masa rai.
Nabila.
Ya yi saurin kiranta da cusasshiyar murya lokacin da ta kama mariqin qofar za ta murza.
Cika umarnin so ya sanya ta juyowa da sauri tana amsa kiran nasa ba tare da ta tuna qwallar idonta tuni ta sauko ta zama hawaye ba.
Suka yi cirko-cirko suna kallon juna, amma shi ya fi nacewa kallon hawayen fuskarta, kimanin sakanni arbain sannan ya fizgo magana da qyar.
Nabila me ke damun zuciyarki?
Nan da nan ta dan shiga rudu ta hau caje jikinta tamkar zuciyar tata ta ke nema ta tuhuma. Ta yi dabarar goge hawayenta, sannan ta kalle shi tana qirqiro murmushin qarfin hali, ta dora yatsa a qirjinta.
Ni? Me ka gani?
Ya tafi da baya a hankali ya zauna kujerar kusa da shi ba tare da ya dauke ido daga kanta ba, fuskarsa babu walwala ya ce mata.
Ke! Na ga abubuwa da yawa a zuciyarki da fuskarki, kar ki boye min wataqila ina da taimakon da zan iya yi miki.
Wannan karon ma ji ta yi tana son tsinkewa da kuka, furucin Mujahid da idanuwansa ba su nuna canci-canki ya ke ba, ya fahinci komai game da ita, ta barar da yaya mata, ta yi abin da matan kirki ba su saba yi ba, Allah ya sa su yafe mata.
Tararradi kawai suke ita da zuciyarta sun kasa ba wa Mujahid amsa duk da jiran da ya ke musu har sai da ya jaddada mata cikin taushin murya.
Nabila ba ki ji ni ba?
Ta girgiza kai da sauri.
Ai ban fahince ka ba Yaya Mujahid.
Tana rufe baki ya amsa.
Me ke sanya mutum qwalla?
Kai tsaye ita ma ta amsa.
Ciwo mana.
Ya murza yatsu.
Ciwo kala-kala ne
Ta tare shi.
Na zuci ko na gangar jiki
Nan take shi ma ya tare ta cikin murmushin samun nasara.
Hawayen da ki ka goge yanzu na mene ne?
Ta dan yi dum! Amma jarumar zuciyarta da ta yunquro tun dazu bayan ta hango mata na yi mata tur saboda ta bayar da su, ta yi saurin qarfafarta tare da bata satar amsa, da qumajinta ta amsa masa,
Mura na ke.
Ya yi kasaqe yana kallonta cikin murmushi da qaryatawa, ita kuma ta ci gaba da kallonsa cikin fargaba sai can ya rausaya mata kai.
Ban yarda ba.
Ta dan fiddo idanuwa tana dubansa, bai bari ta yi magana ba ya tare ta.
Amma ba nufina in ci gaba da jayayya ba, na dai so ki fada min gaskiya ko taimakon nasiha ne na yi miki saboda na san irin abin da ki ke ji a qirjinki, don na dandani irinsa, amma ina da yaqinin ke mace ce kina da rauni, saboda haka za ki iya mantawa.
Yanzu rudunta ya wuce yadda za ta iya sarrafa kanta, can maqerar maganarta aka dinga qero mata tambayoyi da amsoshi har da qalubalen da za ta yi wa Mujahid, amma da ya ke shi shuumi ne tuni ya fahinci hakan qila, ga mamakinta sai ya nuna mata qofa cikin murmushin da ta dauka na qeta ne yana ce mata.
Ah, ai tuhume-tuhume sun wuce ki shiga ciki ki kai wa Binta saqona, ki fada mata ina sonta, kuma zan ci gaba da sonta a kowanne hali za mu sami kai.
A qulliyar dabiun Nabila babu fushi, amma juyawar da ta yi cikin zafin nama ta fice ta tabbatar nauI ne na fushi, kuma ba ta yarda ita da kanta ta gayyato shi ba, face wani daban ne ya aro mata don ya ceci zuciyarta daga bugawa ta fashe saboda sauraron maganganun Mujahid wanda da sauke mata kwandon ashariya ya yi zai fi mata mutunci.
Yadda ta buga masa qofa vam! Haka ya yi tsalle a guje ya shige dakinsa ya dire gaban windo ya dan ja labule ya fara hangenta a kusurwar da ya ke zargin in dai ta so kuka a nan za ta tsaya ta yi.
Can sai ga ta ta iso gurin da ya za ta, hankalinta a matuqar tashe, babu alamun hawaye a fuskarta, amma abin da fuskar tata ke nunawa kukan ya fi shi sauqi.
Tsawon lokaci tana sambatun da nisan da ke tsakaninsu bai barshi ji ba, har inda ta kai gangara a illahirinta ya hango haquri da tawakkali, ya ganta cikin sanyin jiki tana goge fuska, cikin saa kuma ta iso windon da ya ke tsaye kasancewarsa madubi sai dai a ga kai ba a hango na ciki domin ta gyara xaurin dankwalinta. A hankali ta sunkuya ta ajiye furensa da takardarsa tamkar mai ajiyar qwai, ta miqe ta fuskanci madubi tana goge fuska, sannan ta hau gyara daurin dankwalinta, yana tsaye ko motsin kirki ba ya iyawa sai ka ce idan ya yi za ta hango shi.
Ta dubi kanta sosai a madubi, cikin rarraunar murya ta ce.
Ubangiji ka yalwata qirjina da farin ciki tare da yi maka daa, ka sanya wautar da na yi ta son wancan bawan naka ba tare da neman zabinka ba ta zama mafarkin da tuna shi ba zai cutar da numfashina ba, lafiyata rayuwata da addinina ba, Allah Ka zamo gatana kar Ka yanke ni daga alkhairan da Ka azurta ni da su, na game da kyan hali tare da dogaro da kai
Mujahid bai gama jinta ba, da sauri ya saki labulen ya fada gado a wahalce dakin na hajijiya da shi, wasu abubuwa masu kaifi suna huda zuciyarsa suna hukuntata da zummar ita ba ta gari ba ce, ba ta san tawakkali ba, ba ta san ba wa Allah zabi ba, ba ta san nadama ba, ba ta san sauya abin da bai yarda ya dace da ita ba, wato Binta. Shi da zuciyarsa komai ba su sani ba, ba su iya ba? Sai kawai ya ji shi cikin wani mitsitsin hawaye kasancewar shi ba gwanin kuka ba ne, mitsitsin hawayen ma ba ya iya ko kamarsa sai ta kacame.
Ya dinga birgima a gado yana tambayar kansa.
Ni ne namiji, me ya sa ba ni da jarumta kamar Nabila? Me ya sa ba zan so abin da ya ke sona ba? Me ya sa kuma ba zan yi tawakkali ba? Tambayoyi kawai ya ke jero wa kansa ba ya wahalar da kansa nemo amsa don ya san babu abin da zai samo sai son Bintu da mutuwa a son nata, don haka ya ci gaba da jero tambayoyin tamkar yana sanya su a layin debe masa kewa da radadin zuciya duk da zuciyar tasa ta ja wa kanta bisa kafiya da jin ita ta fi kowa iya zabi ko kuma kokawar cika buri.