Iyaye da sauran ‘yan’uwa duk sun sawa Mujahida da Binta ido, suna ganin abinda ke wanzuwa a tsakaninsu, lokacin da Binta ke cikin tsananin kuka da damuwa, lokacin shi kuma Mujahid ke nuna babu komai, daga son Binta har baqin cikin auren.
Kowa na lura da su, dangantaka tsakaninsu ba tsami ta yi ba, amma dai ana zaman marina, Binta tana iya wucewa Mujahid ya wuce ba tare da ko sannu ta hada su ba, ba a ganin komai a idon Mujahid sai babu komai, duk wata halittar sonta ya sake binne ta cikin ransa kamar yadda yayi da farko kafin ta san yana sonta, ko ma fiye da haka, illa a idon Binta ake gano tsananin adawa da qiyayya.
Hikimar Iyayen shi ne ba su damar su sasanta kansu kafin a kaisu gida su kadai a kulle, amma da ba su hango alamar hakan ba sai suka kira mai nuna babu komai din suka titsiye.
Alhaji ne da wannan aikin,
“Mujahid wai me kake jira ne?”
A ladabce ya ce,
“Alhaji da me fa?”
Alhaji ya masa,
“Da bikinku mana”.
Muhajid yayi murmushi ya muskuta,
“Wai da bata lokaci na yi ta dan dada hutawa, na ga har yanzu tana cikin damuwa”.
Alhaji ya tsura masa ido, kuma bai rufe shi ba ya fada masa abinda ya fahimta,
“Da wannan zaman gabar da kuke kake jiran ta huce?”
Mujahid yayi dariya kuma ya fadi gaskiyar zuciyarsa shi ma,
“Alhaji Binta ce fa, in ba haka na yi mata ba raina ni zata yi, so take kullum na yi ta shan kanta tana yi min rashin kunya.”
Alhaji ya fahimce shi, ya dan jima shiru sannan ya fadi maganar da tun tuni take yi masa shawagi take damunsa a qirji,
“To amma dai kai ba ka da matsala da wannan auren hadin da muka yi muku, zaka iya karrama mu ka riqe Binta a matsayin matarka tsakani da Allah?”.
Nan ma kai tsaye ya amsa,
“Ban taba son wata mace ba sai Binta Alhaji, ita ta san haka tun kafin Allah yayi hukuncinsa a kanmu, ban san burinta ba kuma tun wancan lokacin, da na karramata wallahi na bar ta ta cika burin, ni na janye son da nake mata, to sai na fahmci ma kamar ba ta da burin, don haka na qi janye mata sona”.
Alhaji ya ji ya cika da haushin Binta,
“Manta da ita, ai ba ma ta da wani buri, sai dai ta mutu qarqashin iyaye ba qarqashin inuwar aure ba”.
Mujahid yayi dariya kawai.
Alhaji ya nisa ya ce,
“Me kake shiryawa bikin naku, kuma yaushe?”
Mujahid ya dan yi kasaqe, sannan ya dubi Alhaji,
“To zata yarda da wani biki ne ma? Zamu tara mutane ne ta yi ta ihun fada musu auren dole aka yi mata.”
“Haka ne, to sai ka dan kikkintsa ka sa muku ranar tarewar, kuma wannan gabar a rage ta don Allah”.
A ladabce Mujahid ya ce,
“In sha Allah”.
A ranar da dare ya kira Nabila,
“Amma dai yarinyar nan ko shekara guda ne yakamata ki sanya bikin nan mu jira shekarar ta qare”.
Da qalubalen da ya tari Nabila kenan.
Nabila ta jima kafin ta amsa saboda mamaki, sai can ta nisa,
‘Yaya Mujahid wai menene hikimar in sa muku biki?”
“Au maimaita miki dalilin zan yi?”
Cikin yanayin gatse ya ce,
“Amma tun farko da kin san ba zaki sanya ba yakamata kawai ki fito fili ki ce ba zaki sa din ba”.
Tana dariya da yanayin Nadama ta ce,
“Allah ba ka haquri, sati biyu yayi?”
“In yayi miki yayi min, amma fa ki tabbatar kina cikin yanayin farin ciki daidai lokacin, ma’ana babu abinda zai iya sumar da ke”
Tana dariyar qarfin hali da son a basar da maganar ta ce,
“Ko a wanne hali zan zama mai tawakkali, babu abinda zai sake sumar da ni”.
Yayi daria,
“Ashe kin fahimci manufata, ba zaki zama cikakkiyar qanwa a wajen Binta ba sai kin watsar da suma wajen taya ta damuwa ko kuma hada damuwa da ita lokaci daya”.
“Na ji.”
Ta fada da dariyar, wannan bahagon mutum din dole sai ana yi ana boye masa fuskoki.
Ya fahimci hakan, amma abinda yake so kenan, don haka ya biye mata suna ta dariya, ya ce,
“To ko ke fa? Ki ba ni akawun numba zan turo miki kudin kayan lefen nawa, ya zama kayan ya samu cikin satin nan don za’a kai boto su gani, na zabi ki siyo min ne don ke zaki iya dabarar ki ji abubuwan da Binta ta fi so.”
Tsakaninta da Allah ta ce,
“Wallahi Yaya Mujahid ba zan iya ce mata ni zan siyo mata kayan lefe ba, sannan ba ma zan so ta san ni na siyo ba in ma na siyo din…”
“In ba ki siyo ba kin saba min, zan kuma yi godiya da wannan koma bayan”.
A sanyaye ta ce,
“Ai zan siyo”.
“To kin kyauta”
Suka yi shiru kafin ya nisa,
“Gobe zan cika miki alqawarinki, zan je na wanke ki wajen Binta”.
Cike da zumudi ta ce,
“Allah da gaske? In ka yi hakan ka cece ni wallahi, wannan ne dalilin da ya sa har yau na kasa komawa gidan na hada ido da ita, ko kiranta a waya ba na iyawa, ita kan kira ni cikin yanayin zargi ta gaishe ni”.
Da yanayin ba ta muhimmanci ya ce,
“Wanne irin zargi?”
Ta ce,
“In ka yi doguwar magana da ita zata yi maka shi”
“Ko?”
Ya ce mata.
“Haka ne.”
Ta tabbatar masa.
Suka dan yi shiru na wani dogon lokaci sannan shi ma ya bijiro da nasa zargin,
“dazu da wa kike waya har tsawon kusan awa daya na yi ta kira ana cewa kina Busy?”
Ta kebe fuska ta amsa alamun labarin babu dadi,
“Yaks ne”
Ya ji wani haushi cikin ransa, ya ce,
“Har yanzu ku na tare kenan?”.
Ta ji qwalla na son cika mata ido,
“Tunda Anti Binta ta jona mu dalilin ka ai ya zame min qarfen qafa, ni da na san ma daga can gida zasu sa qarfi su dauro muku aure ai da ban shiga wannan cacar tata ba, gashi nan na shiga damuwa ina hira da mutum tamkar ina cikin wuta, Allah in an ga na mutu haka siddan to hira da shi ne ya sa zuciyata ta buga.”
Dariya da takaici suka ishi Mujahid lokaci guda, ya katse su duka ya ce mata,
“Lallai kam Caca, tunda Binta ta ci qasa, ai gara ke ma ki yi fuska ki share, bai kamata ki cigaba da zama da abinda zai cutar da ke ba”.
Ta ce,
“Zan yi dabara mu rabu ta ruwan sanyi ba tare da Anti Binta ta ji cewar na saba mata alqawari ba”.
A ransa ya ce,
“Sai ka ce wata Bintan arziqi.”
*****
Babu zato babu tsammani Binta ta ji muryar Mujahid a samanta yana tayar da ita bacci ta hanyar dukan qafarta,
“Ke Malalaciya tashi don Allah”.
Ta zabura a firgice ta tashi zaune, ta shiga ja da baya har ta qure da bangon gado tana kallon yadda yayi mata tsaye a ka, amma fuskarsa babu walwala sosai, da sauri ta shiga hada kanta tana lullube jiki da bargo.
Ya sake bata rai yana sa mata ido,
“Na ce miki jikinki na zo in kalla ne kike ta wani gargajigar rufewa?”
Bata gama dawowa kan doka da oda ba, don haka ba ta iya hada amsa ta bashi ba.
“Taso zamu yi magana.”
Ya wuce kan Sofa ya zauna.
Ta hada duk wani mugun kallo da ta iya a duniya tana binsa da shi ba tare da ta sake motsawa daga inda take ba har ya je ya zauna ya tattaro hankali kanta,
Ya sake bata rai,
“Ni fa baqon sauqi ne, in kina jin wahalar tashi ina iya zuwa nan na same ki”.
Ta yi magana bakinta na rawa,
“Ka zo magana da ni ne ko kuma ka zo ka saurari kukana da ashariyar da zan maka?”
Tana rufe baki ya amsa mata cikin gintse ido,
“In na baki dama ki yi ko daya a cikinsu ko? Zaki yi kuka ko ki zage ni ne a lokacin da ban zo hada shirgi da ke ba, amma in dai na zo dole ne ki saurare ni.”
Ta fara qoqarin sakkowa daga gadon cikin rauni da son fashewa da kuka, tana cewa,
“Allah wadaran auren hadi da za’a zabawa mutum abinda bai taba so ba, sannan abinda bai san tausasawa da kyautatawa mace ba sai dai ya sa mata qarfi.”
“Mace ma ai suna ta tara Binta, duk wanda ya lallaba wadda ba ta cancanta ai ya zama sakarai kamar ita.”
Bata tanka masa kawai sai ta doshi qofar fita daga dakin amma sai ta ji ta a rufe, da sauri ta wawuri qofar bandaki, nan ma a garqame ta juyo ta kalle shi a fusace, sai kawai ta gan shi ya zuba tagumi hannu bibiyu yana kallonta, kallo irin wanda bata taba ganin me kaifi irinsa a idonsa ko na waninsa ba.
Ta yi yunqurin ta yi magana ta kasa, fuskarta kawai da ke nuna tsabar azabar fishi da qiyayya, sai kawai ta cigaba da tsaiwa a wajen.
Suka jima cikin shiru babu wanda ya tanka, yanayin fuskarsa ya nuna mata lallai ma ba shi da niyyar tankawa, sai cikin fishi ta ce,
“Kai ba ka da asara ko? Ba gidanku ba ne kuma ba mahaifanka ba ne, shiyasa ka zo ka kulle mu a daki?”.
Kawai sai ya tashi ya doshi qofar ya bude ta, haka qofar bandakin, ya koma muhallinsa ya zauna yana ce mata,
“Na bude qofofin tunda yanzu kin san kunya, abin kunya ne ki kulle kai da mijinki a daki, amma ba abin kunya ba ne a tsakiya gida a ganki rungume da saurayi kina tsotsar bakinsa”.
Ta yunquro da niyyar turin haushi amma ya tare ta ta hanyar tashi tsaye ya fuskance ta,
“Binta duk wannan tsawon lokacin da na ba ki sama da wata guda ba ki yi abinda na baki lokacin dominsa ba? Kuka don ki rage takaici kuma ki rage tsanata? Zagi don ki qarar da dukkan zagin da kike da shi a maqoshi yadda zan ci arzikin ki daina duban qwayar idona kina zagi. Qin rabarki don ki san son gaskiya ba sai ka nane wa masoyi yake dorewa ba… Binta ke wacce irin mutum ce mara imani kuma wadda ba ta san darajar so da me son ba? Yaushe kike tunanin na fari son ki? Shekara daya? Biyu, uku ko biyar? Na fara sonki ne tun da na bude ido na gan ki a duniyata, ban taba jin fashi ba haka kuma na cigaba da mu’amala da ke ina boyewa, duk wannan kin hana ni in bayyana miki su, kin tsane ni tsanar da sam ban cancance ta ba. Kin tashi wani wasa a tsakaninmu inda kika qirqiri Yaks da gangan don ki kori sona daga gareki, ko na fahimci gaske ne ba fasa sonki zan yi ba Binta, don ba wani dalili ne ya aza min sonki ba bare wani dalili ya cire min.”
Yayi shiru yana jan numfashi da kuma nazarin fuskarta don ganin yadda fuskar ke karbar maganganunsa, amma bai ga komai ba sai zallar fishi da wannan qiyayyar tata gare shi. Wannan yasa karo na farko ya ji wata ‘yar karaya, yayi magana cikin raunin murya,
Na taya ki da wasan da kika zo min da shi inda na samar da Nabila, gaskiyar magana babu so irin wanda kika zata a tsakanina da ita, ni na roqe ta ta taimaka min don na rama abinda kika yi min ke da Yaks duk da ban fito fili na fada mata maqasudi ba, ta karbi tayina don tana da kirki kuma ita mutum ce me karamci kuma me taya mutum neman abinda yake so…”
A fusace ta tare shi,
“Wannan dalili ne ya sanya ta rikice har ta suma ranar da ta ji ka fara aurena kafin ita ko?”.
Babu abinda ya zo ransa sai maganar zargi da Nabila ta ce Binta na yi musu, zargin yayi masa dadi sai dai fuskarsa ba ta nuna ba.
“Amma dai ai gabanki likita ya bayar da rahoton matsalarta ko?…”
Ta tare shi,
“A gabanka dai, ka kawo mana labari yadda ka so”.
Ya yi shiru don ya rasa abin cewa, sai kallonta kawai ya ke.
Tana sabunta fishinta ta isa bakin gado ta zauna, kuma ta dubi tsabar idonsa ta ce,
“Ka samar da dalili na biyu da zan cigaba da gudunka har abada Yaya Mujahid”.
Duk da ba shi da wani qarfin gwiwa ya tambaye ta,
“Lissafa min dalilan”.
Kai tsaye ta amsa,
“Na farko shi ne, ni tun fil azal babu son aure a tsakanina da kai, da gaske nake ba na sonka a matsayin miji wallahi kuma har abada zan cigaba da nuna qiyayyar, dalili na biyu kuma shi ne, ka fada son qanwata, ko kuma ka janyo dalilin da ta fada sonka, salihar yarinya ka shiga rayuwarta zaka lalata mata da so, alhalin ba aurarta zaka yi ba, sannan in ma zaka aure ta ni ba zan iya hada miji da ita ba, wannan shi ne dalili na biyu da zai sa lallai ko ta halin qaqa na yi abinda zaka rabu da aurena, ko ka je ka aure ta ko ma ka je ka yi duk abinda ka so kai ka sani”.
Mujahid ya jima tsaye a wajen gabadaya kwanyarsa ta hargitse, gaskiya ba haka ya zaci Binta ba, bai zaci hargitsewarta ta kai haka don haka yake diban abinda sauqi, ashe ita ba sassauqa ba ce.
Karo na farko da ya ji babu laifi in ya sa qarfi a rayuwar Binta don ita ba ta da sauqi kuma ba ta da digon tausayin mutum bare ta fahimce shi.
Ya yi fuskar fishi kamar yadda ta yi, ya dan dinga safa da marwa kafin ya tsayar ya fuskance ta,
“Wannan ce matsayarki?”
Ta yi saurin kada kafada da alamun turin haushi,
“Qwarai ita ce, idan murnarka ita ce iyaye sun je sun qudira mana aure shikenan sun cika maka buri to gaskiya ka yi kuskure don ba su zasu je gidanka su zauna ba, ni ce zan je, kuma ba zaka same ni yadda kake so ba, ba zaka taba farin ciki da zamowa ta matarka ba…”
Wata zazzafar qwalla tana qoqarin bullo masa a ido yana mayar da ita da jarumta ya ce,
“Don na taba yi miki wanne laifin duk na sami wannan sakamakon?”
Da azama ta amsa,
“Kai da ka fara sona babu dalili sai kake jiran ni na fara qin ka da dalili? Ni kawai sonka ne bana yi… in kana da mataki kawai sai ka dauka”.
Ya yi ta maza ya kada kafada yana murmushin yaqe,
“Gaskiya ba ni da shi, abinda ya rage kawai na yi saurin kai ki gidan nawa ki je duk ki sauke abinda kika yi niyya, in ma kina da wanda ya fi shi don Allah duk ki yi guzirinsa ina jiranki”.
Ya murza yatsu,
“Na san ba ki da abinda zaki yi wa biki a aurenmu, saboda haka ki shirya zaki tare a gidana nan da kwana sha biyu, asabar ta sama kenan”.
Bai saurari cewarta ba kawai ya doshi qofar fita ya fice.
Ta bishi da kallo lokacin da wasu kibiyoyin tsanarsa suka qara yawa suna huda mata zuciya.