Skip to content
Part 45 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Mujahid bai halarci wajen daurin aure ba, su kuma ba su fasa daurawa da shi ba, ya kuma ja wayarsa ya kashe gaba daya ya shiga jiran tsammanin ganin za’a yi ko za’a fasa? Ya san dai babu mai gangacin da zai daura masa aure ba tare da yardarsa ba.

Binta na can a daki zarginta ya qara daduwa, Mujahid a cikin tashin hankali yake don haka ne ma ya kulle kansa a daki ya hana kansa sukuni, kuka yake, me yake? Sai ta ji ta matsu ta sani, a nan ne ma ta sidada ta hau Benen don ta je ta sato ganin abinda yake yi, kuma cikin rashin sa’a ta tarar da qofar a kulle.

Dole ta sakko ta cigaba da sabunta damuwa da tashin hankali.

Ta yi wanka ta shirya, ta zauna zaman jiran tsammanin ya fito ya kai ta dubo Nabila daga nan kuma ta wuce gidan daurin aure ko da kuwa ba ya so, to amma har sha biyun rana shiru. Sai ta ji gabanta ya fara faduwa, wannan Man din rataye kansa yayi a dakin ko kuma me? Tana ta shawarwarin ta je ta buga masa qofa amma ta rasa qarfin gwiwa, kar a yi katarin kwanyarsa ta tabu ya dauke ta ya cillo daga Bene.

Ta kirayi wayoyin mutane da dama musamman guda uku, Nabila da Hajiyarta da kuma Alhaji. Wayar Nabila a kashe, wayar Iyayenta kuma ta tabbatar suna ganin kiranta fushin da suke da ita ne ya hana su dagawa.

Nan ma ta sake wani kukan zucin da Allah Allahn Mujahid ya fito ya kai ta, har gidansu zata je da hawayen neman a yafe mata, in Mujahid din ne su sha kuruminsu, zata karba a maneji.

Karfe daya ta yi babu labari, dole ta miqe ta yi dan sassauqan abincin rana ta koma ta zauna ta cigaba da jira.Karfe biyu ta yanke shawarar hawa benen ta qwanqwasa qofar in yaso duk abinda zai yi ya yi, baqar magana ce dai ta san zata sha ta, to babu komai ba yau farau ba, ai yau ma damar ta ce, ita zai sha baqar maganar a wajenta tunda an aure nabila yana neman kashe kansa.

Zata fita daga falon kenan sai ga kira, ta duba cikin doki sai ta tarar Yaks ne, cike da murna ta dauki wayar tana yi masa kirari, kawai sai ta ji ya rusa mata ashar, a gigice ta ce,

“Kai Yaks kana da hankali kuwa? A ranar farin ciki irin wannan kai kuma zaka fara shan giya?”

Ya sake lalilayo wata ashar din ya quga mata, sai ta yi saroro zuciyarta na bugawa, cikin hanzari ta sake duba lambar mai kiran dan ta tabbatar ma Yaks din ne? sunansa dai ta gani, jiki na bari ta sake kara wayar a kunne tana salati.

A haukace ta ji yaks ya tuhume ta,

“Binta da ke za’a hada kai a cuce ni? Daga jiya zuwa yau me ya hana ki sanar min Mujahid ne zai auri Nabila ba wani ba? In da kin sanar min wallahi da sai na kashe shi kafin ranar yau…”

Binta ta zaci ba taji da kyau ba ne, da sauri da gigita ta ce,

“Mujahid ka ce ko me? Mujahid kuma wanne?

Ya zaci raina masa hankali zata yi ya sake lailayo wasu iyayen ashar din ya auna mata, idanunsa da zuciyarsa a rufe suke, kowa ba shi da mutunci a idonsa.

“Binta ta fara son fashewa da Kuka,

“Yaks ka fada min don Allah, wai Mujahid nawa aka aurawa Nabila?”.

Ya ja tsaki ya ajiye wayar yana ta zabga bala’I da hayaniyar hankali ma take son raina masa.

Tun daga nan ta tabbatar Mujahid dinta ne ya auri Nabila, ashe da gaske yake zai yi kwanan tsallen murna ne shiyasa jiya ya ci mutuncinta ya koro ta kamar karya? Ashe ma da take zaton yana kulle cikin daki shi asubancin ficewa wajen daurin aurensa yayi babu ko sallamar fita?

Sai ta ji zuciyarta na neman ta kekkece, ta yi qoaqarin ta yi kuka shi ma ya gagara, abu daya take maimaitawa a fili tamkar wata zararriya,

“Yaks in zaka yi kisa ni zaka kashe, ni na cancanci barin duniya don ban zo cikinta a sa’a ba.”

Ta birkice iyakar birkicewa, har ta fara zaton ma ko haukacewa ta yi ne?  in tashin hankali na zoza hauka tabbas ita ma ya zoza mata, sai dai abin kunyar shi ne, in an biciki dalilin haukanta ba zai zama abin kunya ba in dalilin ya zama tashin hankalin Mujahid ne yayi mata kishiya? Ba ta sonsa fa, ya sani duniya ma ta sani, sanin da kowa ma zai yi tsammanin in zai auro matan duniya ba zata damu ba.

Abin haushi ta damun, har tana jin zabar mutuwa da cigaba da rayuwa.

Ta ja jiki ta shige daki ta kife a gado ta dinga rasgar kuka har tsawon awa daya.

Ba ta da wani zabi bayan kukan, domin damuwoyinta sun wuce daya biyu uku zuwa abinda za’a qirga, in damuwa da auren mijin da ba’a so sunanta damuwa, to shi kansa mijin ma irin Mujahid damuwa ne, me so a baki kawai ban da aiki, damuwa ta gaba kuma shine sanin halin da take ciki wanda iyayenta suka yi, ko ta qi ko ta so sai sanin nasu ya taka rawar hana ta daukar mummunan mataki akan wannan banzan mara amfanin mutumin Mujahid.

Can cikin rashi hayyacinta ta ji kamar idonta ne ke gizo Mujahid ne ke sakkowa daga bene. Ta zabura cikin barin jiki ta leqa ta windo sai kuwa idonta yayi arba da shi yana sakkowa daga Bene cikin rangaji da galabaita, duk da a fizge ta kalle shi saboda duhunsa da take gani sai da ta lura da cewa ya yi muguwar rama.

Da sauri ta saki labulen ta fada gado ta balle sabon kuka, ba ta san tsawon lokacin da ta dauka ba sai muryar Mujahid din ta ji a kanta babu zato ba tare da ta san lokacin da ya shigo ba,

“Don Allah taimaka ki dan dauki hutun kukan nan ko na minti goma ne ki ba ni abinci, in na kauce Allah basshi sai ki dora daga inda kika tsaya.”

Ta jima kafin ta gama tattara kanta da hankalinta ta dago da hawayenta shabe shabe ta dube shi,

“Yaya ake daukar hutun kukan zuci na gwada ko zan iya? Don Allah koya min, In na bar kuka a sarari na zuci nake don bana hutawa da kuka ina tsammanin sai ranar da qasa ta danne idona matuqar ka hada jinsi da mayu bare ka iya sakina na sarara”.

“Babu laifi, rakici kanki da dukkan Kukayen naki ki je ki ba ni abinci, bai kamata a ce ni kuma taki damuwar ce zata kashe ni ba… ta ina kukanki ya shafe ni da zan nemi abinci na rasa?”

Cikin tsawa da kuka ta ce,

“Ai wallahi sai dai ka jira Nabila ta shigo ta baka, ita ta aure ka don son, ni da zan iya ma, kashe ka zan yi na huta da ganinka…”

Daga kalmar ita ta aure ka don so bai qara jin wata kalmar a kunnensa da hankalinsa ba, ya dafe kai yana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un.

Damuwarsa ta kai maqura a bayyana yadda har ta ja hankalin Binta mara hayyaci ta yi sagwal tana kallonsa da son ta fahimci inda ya dosa, cikin minti daya idanuwansa suka yi jawur, alamar damuwa ta cika su, amma hawaye ya qi rage ta.

Yana ta maimaita hirji har ya fara dawowa kan doka da oda da tuna alqawarin da yayi wa kansa na cewa har abada ba zai wulaqanta Nabila ba, kuma ba zai buda qofar da kowa zai wulaqantata ba.

Kawai sai ya juya ya fice yana cewa,

“In an ce kina sona ki ce ba kya sona, to in ba so ba menene dalilin baqin cikin na auri wata da na fara so, son ma irin wanda nake miki? Ki je ki ji da qiyayyarki, ina da tabbacin in ta zo har gaba da abinci zata ba ni.”

Kafin ta gama mayar da numfashi tare da tattaro kukanta tuni ya fice daga dakin, kukan nata ya koma inda ya fito lokacin da ta yanki jiki ta fada kan gado duniyar na mata nisa.

Da qoqarin riqe kai Mujahid ya sallaci sallar la’asar sannan ya rarumi mota ya dauki turbar boto, amma maimakon haka sai ya yanke hanya ya shiga daji mai qarancin shige da ficen jama’a yayi kwance a mota yana ta faman tsotsar tsamiya.

Hankalin Mujahid da hangen nesansa shi ya fara nuna masa abinda zai duba, shi ne, Nabila dai an riga an aura masa, duk hukuncin da zai yanke nan gaba yana da alaqa da mutuntakarsa da kuma nuna hankalinsa, kuma zai iya zubar masa da qima ko kuma ya samar masa. Yanzu maganar barin halak don kunya ta wuce tunda an riga an daura, ragowar yanzu hakkin Allah ne wanda ba a yi masa hanzari ko uzuri, dangantaka ba zata zama hujja ba, son Binta ba zai zama hujja ba, rashin son riqe mace biyu duk da ba zai zame masa hujjar wasarere da haqqin Allah wajen riqe ta ba in dai kunyar duniya ta iya hana shi sakinta.

A qarshen tunaninsa ya ji wani hawayen tsoron Allah ya shiga fadowa fuskarsa, ya ji girman Nabila ya qaru a idonsa, wadda ta take so domin Allah sannan ta mayar da lamarinta ga Allah, sai ga shi cikin ruwan sanyi ya bata abinda take so ba tare da ta zubar da qimarta ko duniya ma ta san tana son ba.

A nan wajen ya gabatar da sallar magariba da ta isha  cikin rashin qarfin jiki, qarfe goma ya taso motarsa zuwa gida cike da tararradin yadda zai tunkari wannan rayuwar, ta ina zai bi ya kubuta, ta ina zai bi bai ci haqqin kowa ba, ta ina zai bi ya guje wa kansa raini daga waje har cikin gida?

Bai samo amsoshin ba, amma ya shiryawa rayuwar, don haka ya kunna wayoyinsa ya kuma fara samarwa zuciyarsa sarari ta hanyar rage damuwa.

Yana qoqarin fitowa daga motarsa kira na farko da ya shigo wayarsa na Nabila ne, ya ji kansa ya fara juyawa saboda fargabar dalilin kiran, dole ya rabe cikin motar ya daga wayar,

“Nabila.”

Abinda ya iya ce mata kenan, sai ya ji ta cikin tsananin kuka, yadda har muryarta ta dashe. Tana ta qoqarin ta yi magana amma ta kasa.

Ya ji wani matsanancin tausayinta ya baibaye shi, yana taba duk wani kafar jin shaqi a tattare da shi, nan da nan ya ji ya tare ta cikin sarqewar murya,

“Nabila me yake sa ki kuka?”

Ta sake kecewa da kuka,

“Ka yi haquri Yaya Mujahid, ka ba wa Anti Binta haquri, ina ta kiran wayarta ta qi dagawa tun da rana.”

Ya sake jin wani sabon tausayinta, cikin tausasawa ya ce mata,

“Na tambaye ki abinda ke saki kuka kina rakito haquri kina ba mu, mu da muka fi ki farin ciki kuma ba ma kuka?”

Ta qara tsananta kukan,

“Kararku ce kawai, na fi kowa saninku Yaya Mujahid saboda haka na san ba kwa farin ciki, don Allah ku gafarce ni, ban so na rayu don na zame muku abinda zaku yi kuka  ba, wallahi tallahi ban taba zabar haka ba Yaya Mujahid, ka fahimce ni ka fahimtar da Anti Binta, abinda ya faru ba ni na zaba ba, kuma ba da sanina aka zaba ba, da zan yi iyakar qoqarina na hana”

Sai Mujahid ya sallamawa lamarinta, wannan wacce irin macace mai dan banzan kawaici da sadaukarwa?

Ya tattara qarfin halinsa  ya shiga rarrashin da yake jin kamar bai saba da shi ba,

“Mu kika ji muna kuka dan zamu rayu tare da ke ko ke muka ji kina kuka don zaki rayu tare da mu? In takura ce wanene ya nuna takura tsakanin mu da ke? Haba Nabila?”

Ta sake sabunta kukanta sosai,

“Na sani Yaya Mujahid, na san irin son da kake wa Anti Binta, na san ba zaka so ni a tsakiya ba, nima ban kyauta ba in na shigo tsakiyarku, don Allah ka yi haquri Yaya Mujahid… in da yadda zaka yi da ni ka gwada, zan fahimce ka wallahi, zan kuma fahimtar da kowa ma, ka yi…”

“Hush!!!”

Ya fada cikin tsawa.

Ta tsagaita magana sai dai kuka.

Ya nisa ya ce,

“Nabila ke ma haka zaki yi min? wata da watanni Binta na fada min kalmar in sake ta ke ma ita zaki dinga fada min? To wai meye aibuna da ba a so?”.

Da sauri Nabila ta canja fasalin kuka, yanzu na raunin so ne ke yawo a qirjinta, tare da na rashin sanin tabbaci, cikin raunin murya ta ce,

“Ka gafarce ni, ni ba manufata kenan ba, na fada maka dalilina, na san Anti Binta kake so irin son da ba kwa buqatar kowa ban da kanku…”

Ya tare ta cikin tausasawa,

“Ke ma na fara yi miki irin son da nake mata daga yau, ko ma fiye da nata, in wannan ne fargabarki to ki janye, don Allah ki yi farin ciki, ki dena damuwa kin ji? Ina sa ran farin ciki tare da ke, ina sa ran haihuwar iyali tare da ke, ina sa ran mu rayu tare mu tashi a aljanna tare, ni na yi miki alqawarin iyakar iyawata zan ba ki farin ciki, zan hana ki zubar da hawaye, zan kyautata miki… amma ina roqon ki janye damuwa”.

Yanzu ta sauya kukanta zuwa na farin ciki, sai dai ta boye shi a sigar alhini, cewa take,

“Yaya Mujahid Anti Binta…”

Ta maimaita ya kai sau biyar kafin ya tare ta,

“Wai kukan ne ba zaki daina ba? kin fi damuwa da damuwar Binta akan tawa da taki, Nabila su Alhaji fa ba Binta suka aurawa ke ba, don suna sa ran zamu ba su farin cikin da zasu yi alfahari da mu, kar ki ba ni kunya mana”.

Ta fara qoqarin gintse kukanta zata yi magana, ya yi saurin tare ta,

“Ki kwantar da hankalinki, ki kori damuwa kin ji? Ki kwanta ki yi bacci mai dadi a cikinsa ki dan buda min waje kadan a zuciyarki da nuna so na samu na shigo, ta haka ne zamu samarwa iyayenmu farin cikin da suka zata daga gare mu, kin ji? Ki yi haquri ko wani aka aura miki na san zaki runguma ki haqura bare ni Amininki don Allah kar ya zamana nine ba zaki so ba.”

Ganin yana neman canja mata akalar dalilin damuwarta ya sa ta jan bakinta ta yi shiru, ko komai zai zama na munafunci da boyewa a zuci a fitar da akasinsa to ba zata yarda son Mujahid ya zama haka ba, tana sonsa ba zata iya yafewa kanta ba in ta bar shi ya tafi a zaton ba ta sonsa.

Ya jajirce ya dinga rarrashinta yana fada mata kalaman da dole ma zuciyarta ta narke ta manta da tuna wata Binta, har sai da kudin wayarta suka qare kiran ya katse.

Ta koma gado ta zube tana ta faman rusa kukan da ba na komai ba ne face na farin ciki, ta sha zaton in an sami Mujahid a matsayin miji abinda za’a samu kenan wato farin ciki da kulawarsa, amma a yau da tana cikin mawuyacin hali a gadon asibitinta aka bata albishir din Mujahid aka aura mata, duk hasashe hasashenta ba ta taba kawo cewa Mujahid zai karbe ta ya so ba, ta sha fargabar kar ta shiga hannun masoyinta kuma mutumin da ta fi amincewa duk duniya ya zalince ta yadda zai gamu da sakamakon zalintar aminin da ya yarda da shi.

Ana cikin haka ta ji qarar shigowar saqo wayarta, tana dubawa sai ta tarar Mujahid ne ya turo mata da qwayoyin kalmoni biyu kacal, amma masu nauyi a ma’ani, wato,

“Ina sonki.”

Tunda ta wayi gari a matsayin budurwa ake mata kyautar kalmomin nan, amma bata taba ganin darajarsu ba sai da suka fito daga taskar Mujahid.

<< Rigar Siliki 44Rigar Siliki 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.