Ta janye hannunsa daga kafadarta tana murmushin yaqe,
“Kar ka damu, ko me zan zama dai ai kai buqatarka Nabila ta yi farin ciki, Alhamdulillahi kuma tana farin cikin.”
Ta nufi daki, shi kuma kawai sai ya bi bayanta.
“Eh to, amma fa ba ta san da wannan sharadin naki ba.”
Ta ji ranta yana dan baci, shiyasa ta jima ba ta tanka ba har ta murza qofar Toilet tana qoqarin shiga tana amsawa,
“To wannan ai ya rage naka, sai ka duba ka gani, idan sanin zai ba ta farin ciki sai a sanar da ita, in kuma ba. . .