Skip to content
Part 29 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Tana kaiwa nan ta share hawayenta ta dubesu, sannan ta ɗora. 

An karɓeni hannu bibbiyu a dangin Haisam, ban samu wata gagarumar matsala daga iyayensa har ƴan uwansa ba face matarsa Salma wacce nan duniya babu wacce ta tsana sama da ni. Har dakina ta shigo bayan kwana biyu da zuwana gidan ta tabbatarmin kada na saki jiki ma a gidan domin kuwa kwanakin da zan yi na lokaci kankani ne. Babu wanda ya isa ya haifawa Haisam magaji sai ita. Ita kadai ce mai ɗa, kuma har abada ya gama haihuwa. 

Duk da karancin shekaruna, don kuwa a kan Salma ni yarinya ce. Na so na fahimci inda zancenta suka sa gaba. Sai ya zamana tsoro sosai ya shige ni, na kasa faɗawa kowa maganar na bar wa cikina. Babban abin daure kai duk wani abu da za ta nunamin ko ta yimin, ba ta yi a gaban Haisam. Asalima wani kulawa da nuna kauna take yi gareni idan yana nan, wannan kan faranta ransa sosai don a ganinsa mun hada kai ba kamar yanda ya zata daga Salmar ba. Ta silarta aka kawomin ƴar aiki mai suna HALIMA.  Babba ce a kaina don a lokacin za ta iya samun shekaru talatin da kusan uku ma. Acewar Salma, bai dace ace nima a nawa bangaren ba ni da mai tayani hidima ba. Da wannan ta kara siye zuciyar Haisam. Allah Ya jarabceshi da wani irin sona, yanda ba ya iya ɓoyewa ko gaban waye, wannan ta duk wani da zai nunan kauna to yana sonsa. Salma kan jefamishi magana cike da zolaya. Wai toh idan ni ce mahaifiyar Fu’ad ya kenan? Nidai bana tankawa sanin da nayi yaron ko bangarena ba’a yarda ya zo, acewarta ni mayya ce, zan iya cinye kurwar ɗanta. 

Bangaren Haisam kuwa, zama muke mai dadi da kwanciyar hankali, sai dai kawai saɓani irin na harshe da hakori da kan faru. Na ci gaba da zuwa makaranta inda nake karantar fannin malaman jinya (nursing) a makarantar koyo na Malam Aminu Kano. Mujahid yakan zo mu gaisa sai dai bai cika zuwa gidan ba, tun a farkon zuwansa da ya ga Halima ya nunamin shi sam ba ta kwanta mishi a rai matsayin ƴar aikina ba, ban nemi ba’asi ba na share maganar na nunamishi ba ta da wata matsala. 

Sau biyu ina daukar ciki ya zube a shekara guda da aurenmu, wannan abu ba karamin taɓa zuciyar Haisam ya yi ba, a karshe ya kaini asibiti. Duk iyakar binciken likita an tabbatar da lafiyata kalau. Kulawarsa da takatsantsan sai ta karu, ya tabbatarmin muddin Allah Ya kara bani wani cikin to fa ko tsinke na bar dauka. Hakanan daga Hajiyarsa, takanas take aiko wata dattijuwa ta zauna har sai na warware sannan ta koma. Abu daya kuma dana lura da shi, jininsu bai haɗu da Salma ba. Basu kaunarta asalima ko Hajiyar ta zo gidan ba ta shiga sashin Salma sai dai Salmar ta zo bangarena su gaisa, nan ma Hajiyar ciki-ciki take amsawa.

Halima ta tsiri zance da samari kala-kala, na nunamata bana kaunar hakan ko kuwa na fadawa Mai gidan, ta ban hakuri gami da yimin nuni ba za ta kara ba. Tun daga lokacin ta sauya, sai na sanyata aiki ko kuwa nake makaranta na dawo na tarar da wuri babu gyara, mafi yawan lokuta kuwa tana sashin Salma. Wannan abu ya soma damuna sai dai ban nunamata komai ba. Haka nake zagewa nayi aikina ko idan ta shigo tana ban hakuri nakan nuna ba komai bane.

Sai da na cinye shekara sannan su Anna suka ziyarcemu, sun ji dadin ganin yanda na kara haske sai da na rame  na zama kamar ba ni ba na basu uzurin cewa zirga-zirgar makaranta ce. Anan nake jin labarin auren Abba da za’a yi a bayan karamar Sallah. Nayi murna kwarai na kuma yi fatan zuwa muddin lokacin muna hutu, Mujahid ma ya koma Maiduguri wannan ya sanya koda zasu juya naji kamar na bi bayansu. Sun tafi su na masu yabon halayyar Salma, ta karɓesu hannu bibbiyu tamkar dama can ta sansu. Duk wani mugun halayyarta ɓoyesu ta yi, wannan ne dalilin da ya sanya basu fahimci komai ba illa yabo da take sha daga bakunansu nidai ban ce uffan ba. 

A watarana ce ta Alhamis, cikin watan Ramadan, an sha ruwa ina zaune ina jiran lokacin sallar isha’i ya buga don na yi sakamakon nauyin da jikina ya yi. Haisam ya shigo ransa a dagule, tambayar duniya nayi ya nunan ba komai wannan ta sanya na lallaɓa ya sha ruwa kadan. Sai bayan mun idar da sallar isha’i ne lokacin ya wuce masallaci, Halima ta shigo a ɗan firgice take sanarmin cewa ya rabu da Salma. Ya kuma ce ta tafi har da Fu’ad ba ya kaunar ƙara ganinsu. Duk da cewa ba zaman mutunci muke da ita ba sai da naji duk na sukurkurce. Hanjin cikina suka kaɗa, na tambayi dalili ta nunan ba ta da masaniya. Fu’ad kawai ya fi faɗomin a rai, duk da cewar yaron bai yi sabo da ni ba, asalima ba ya kaunar ganina ko ji daga gareni. Sai mu fi sati muna gida ɗaya amman ba zan sanyashi a idanuna ba, amman na tausayawa Haisam na rabuwa da shi na kuma yi mamaki matuka da har ya iya barin Salma ta tafi da shi. 

A daren nayi kukan da bansan dalili ba. Har watan azumi ya shuɗe, sallah ta zo, Haisam ya kaini Maiduguri, bai fadi dalilin rabuwa da Matarsa ba hakanan hatta da Hajiyarsa ta yi mamaki kuma ita kanta bai sanar da ita ba. Ta yi faɗa akan bar wa Salma Fu’ad sai dai ya nemi gafararta kawai gami da alkawarin da zarar ya dawo daga tafiyar da zai yi zuwa Lagos zai sanarmata komai. Da wannan ta kwanyarta hankalinta. 

A bangarena koda na je Maiduguri bani da wata nutsuwa sai da na zayyanewa iyayena rabuwar Haisam da Salma. Su kansu sun yi mamaki sai sai an tsawatarmin akan kada na kara tambayarsa dalilin rabuwar tunda har bai faɗa ba kuma ya nunan bai kaunar maganar. Aka yi bikin Abba da Hauwa, haifaffiyar yar Maiduguri, suka dunguma zuwa Jigawa inda yake aiki.  

Sati daya na ƙara bayan biki, na tattara na dawo Kano. Bana mantawa ina kuka, kukan da bansan dalili ba har Mujahid na zolayata kan cewa idan auren ne bana so to na yi zamana kawai shi zai fadawa Haisam. Wannan ya sa na harareshi muka yi dariya. 

Anna kuwa ƙuramin idanu ta yi kamar a ranar ta soma ganina har sai da naji jikina ya yi sanyi. Kirjina na dukan tara-tara, na karasa na rungumeta na ƴan sakanni itama ta rungumeni, karshe na saketa ta yimin murmushi da fatan alheri. 

Komawata Kano na tarar Halima ba ta dawo ba, asalima kaf kayanta da ke gidan babu ta kwashe a ɗakinta wannan ne ya tabbatarmin ta tafi kenan, ban yi  wani dogon mamaki ba duba da nayi cewa wacce ta kawota ma ba ta gidan, ina da tabbacin wannan ne silar tafiyarta. 

Kwanaki uku nayi da dawowa Haisam ya dawo, ranar kamar mu hadiye juna tsabar farin ciki da murna. 

Watanninmu biyu a wannan rayuwa na kara samun juna biyu sai dai wannan karon shiru nayi ban sanarwa Haisam ba don ina tsoron sai ya gama murnarsa kuma a zo ya zube. Haka na ci gaba da rainon cikina har sai da ya kai watanni uku a duniya. A wani zuwa da Hajiya don titse Haisam ya faɗamata dalilin rabuwa da Salma,  ta gane ina da juna biyu. Wannan murna ya mantar da ita abinda ya kawota, ita ta sanya ya kai ni asibiti aka tabbatar da hakan ne ina da ciki har na wata uku. Ban manta irin murnar da Haisam ya yi ba. 

Yana yawan cemin idan namiji ne to fa sunan yaron Muhammad idan kuwa mace na haifa zai sanyamata Aisha Humaira. Nakan yi murmushi da fatan Allah Ya saukeni lafiya. 

Cikina nada watanni huɗu, aka aikomin Sadik  daga gidan su Hajiya kan cewa na bishi muje. Daga yanayin rabuwar da mukai da Haisam da safe inda har ya fita ya kuma dawowa ya rungumeni ya tabbatarmin da cewa yana sona, ya kuma bani amanar abinda zan haifa. Kuka na sanya alokacin na nunamishi ban son haka, yau ya saba fita ofis da har zai dinga maganganu kamar wanda ke min sallama. Murmushi ya yi gami da daukar wani dan kundin sirrinsa karami ya damƙamin a hannun dama.

“Wannan sirrina ne a yau na damƙamaki Maryam, saboda kafa a duniya ke ce mafi kusa da ni, karki sake ki ba kowa, kar kuma ki nunashi ga kowane bawa har zuwa sadda za ki haihu. Na miki iznin ki karanta a sadda ki ka ji labarin mutuwata saboda a kowane dakika ina jin kamshinta na kara kusantoni. Ki yafemin domin Allah.”

Wannan shine kalamansa na karshe da na saurara, ganin Sadik kawai sai na fashe da kuka, ya nunan ba abinda nake zargi bane sai dai kuma jinsa kawai nake. Na dauki mayafi muka wuce gidan Hajiya. Ina cin karo da gawar Haisam na fadi a wurin na suma.

*****

Maryam ta dakata tana mai sheshsheƙa, babu wanda bai zuba hawaye ba a wurin. Ta daure ta ɗora.

*****

Haisam ya rasu, ya bar ni da cikinsa dake jikina. Salma har gidan ta zo gaisuwar mutuwa tana kuka, ganin Fu’ad, Hajiya ta rungumeshi tana jin kamar Haisam ta runguma. Mun sha kukan ganin tsatson Haisam, muka ji kamar shi ne a wurin ya dawo. 

Sai da aka yi sadakar bakwai ne labari ya je ga Salma ina da juna biyu. Ta kasa yarda ta tarfani ni ɗaya a ɗakin Hajiya a kwance. 

“Maryam dagaske ciki gareki?”

Takaicinta ya kamani, ban ko kalleta ba balle ta sa ran amsa. Ba zato na ji ta yayemin hijabi, ta kuwa doka wani uban ashar wanda ya dauremin kai na tashi zaune ina neman tsari daga shaidan. Ban iya furta komai a fili ba, ta ci gaba da kallon cikina kafin kuma ta yi kwafa ta fice daga dakin. 

Na ci gaba da neman tsari daga dukkan masu sharri sannan na koma na kwanta sai dai hankalina na kan kundin sirrin Haisam wanda ya damƙamin. 

*****

Anti Amarya, Mujahid da Abba ne suka zo min gaisuwa, Anna a sannan tana jinyar Baba wanda ya samu gocewar ƙashi a ƙafa, a sanadin haka ba za su zo ba sai daga baya. Anti Amarya kallo daya ta yimin ta san ba lafiya nake ba, ta nemi sanin kodai bayan mutuwar Haisam akwai wani abun? Ban ɓoyemata yanda mukai da Salma ba, ta bani shawara akan kada na kawo komai a raina, kuma babu bawan da Ya isa yimin abinda Allah bai nufa a kaina ba. Da wannan na samu jin nutsuwar zuciya har ya kai ga na kara jin kwarin gwuiwa. Babu wanda na faɗawa batun kundin sirrin da Haisam ya bar min, na yi shiru da bakina. 

Hajiya kuma, lura da ta yi da cewar bana sakewa sosai da ita ne ya sanya ta ce na koma can gidana mu zauna da Zulai, dattijuwar da ta yi zaman jinyata sadda nayi ɓari. 

Ban iya shiga ɗakin da muke kwana da Haisam ba har sai da ya cika kwanaki talatin cif da rasuwa, lokacin cikina nada watanni tara, inda na adana kundin sirrin da ya bani na dauka na karanta. Anan ne na karanta abubuwan ban mamaki da ɗora kai, na kuma gane wadanda suke da hannu a kashemin mijina. Nayi kuka iyakar kuka, na kuma ga abin ba zan iya kyalewa ba. Wannan ta sanya a birkice na zura hijabi bayan na maida kundin sirrin dakina na ɓoyeshi cikin kayana na fita daga gidan kai tsaye da zummar zuwa gidan Hajiya. Zulai na banɗaki, na ji ba zan iya koda minti biyar na ban je na sanar da yan uwa Haisam wannan lamari ba. Jikina na rawa na fito, nan ma cikin rashin sa’a babu direba, sai Maigadi. Shi ya tambayeni inda na nufa na sanar mishi cewar ba nisa zan yi ba. A hanya kuwa ina tafe ina share hawaye, fatana na karasa titi na samu mai tasi ko acaɓa.  Sai dai bansan ya akai ba naji an shaƙamin abu a hanci an yi awan gaba da ni. 

Koda na farfaɗo, na ganni a wani tafkeken gida da ba zan ce ga yanda yake ba. Na shiga salati ina neman tsari daga sharrin mutanen cikinsa, na yi mamakin ganinsu, fuskokinsu bana jin zan manta domin daga labarin da Haisam ya bani, naga zahirin ɗaya a ciki, na cewar su ne silar mutuwarsa.

“Yanda Haisam ya mutu, wallahi kema sai kin mutu Maryam! Ba za ki zamemin cikas a rayuwa ba! Ba za ki taɓa haifar abinda ke cikinki ba. Daga ke har abinda ke cikin naki sai kun bar duniya.”

Shi ne abinda ta fadi da kakkausar murya, na maida mata martani.

“Ku yi iya yinku, sai dai ku sani Allah Shi ke rayawa kuma Yake kashewa. Idan Allah bai ƙaddaramin mutuwa a wannan lokaci ba, babu waninku da ya isa ya kasheni. Ina tare da Allah.”

Wannan furucin ya janyo min kyakkyawan mari, a karshe namijin ya sanya wani da ya ambata da GWASKA ya tafi da ni ya ƙulle har sai sun kammala yanke abinda suka tsara. Ina ji aka kara sheƙamin abu a hanci aka fice da ni zuwa inda bansani ba. Bayan kwana biyu wata gabjejiyar mace ta shigo dakin da aka bani wanda daga gani kasan wurin kiwon dabbobi ne inda ya tabbatarmin koma ina ne to gida gona nake, ta yimin zirr sannan ta wullamin wata doguwar riga na jan yadi sai dankwali. Ta kwashi kayana har da takalmina ta fice, da sauri na suturta jikina na karasa jikin kofar sai da duk iyakar yi na bai buɗu ba. Wannan ta sa na koma na zauna na shiga rera kuka. 

Sama-sama na dinga jin maganarsu wannan ya sanya na ja jiki dakyar na karasa jikin kofar dakin. Naji suna fadin an kai dukkan wani shaidu da ke nuna cewar mutuwa nayi a gobara a wata tasi. An nuna konannun kayana sai kuwa hijab da takalmina. Wannan ya sa naji gabana ya faɗi, kenan babu wanda zai yi cigiyata. Ina jin sadda suke cewa babu abinda za’a yimin har sai an damƙawa Fu’ad gadon mahaifinsa. Nayi kuka sai dai nasan ba amfanin da zai min don haka na yi amfani da sauran ruwan da aka ban na cin abinci nayi alwala na shiga gayawa Allah. 

Sai da nayi kwanaki ashirin a wannan yanayi kafin na kuɓuta. Shima Allah ne Ya taimakeni yaron ogansu wanda ake kira da Shanu ya shigo a wani dare da zummar yin lalata da ni, kasancewar a buge yake ya sanya na kwala mishi kwalbar da ya ajiye na mayensa a kai, sannan na fita ina sanɗa, da taimakon Allah na kuɓuta daga gidan don ba zan ce wayona ba don kuwa wuri ne marar tsaro. Ina jin hayaniyar  Gwaska da yaransa suna shaye-shayensu sun ware kiɗa. Sai dai me? Ina fita naga ashe ba gida gaba babu a baya, na rasa ya zan yi, a dole na  ci gaba da gudu ga walƙiya da ake da kuma iska wanda ke nuna cewa ruwa kan iya sauka a kowane daƙiƙa.

Ina zuba sauri ba tare da na fasa ba na ga mota ta haskeni tana kuma bibiyarta gami da yimin hon. Duk a zatona Allah ne Ya jefomin mataimaki wannan ya sanya na tsaya ina jiran motar ta ƙaraso, sai dai irin hayaniyar da na jiyo daga masu motar su na kiran kasheta zasu yi, ya ankarar da ni ko su waye.  Na miƙa dajin dake ta gabas ɗina na ci gaba da gudu suna biye da ni bayan sun faka motar.

*****

Maryam ta share hawayenta, idanunta kamar an watsa barkono ta dubi Inno da  Malam Zakari.”Wannan ne silar faɗawata Ƙauyen Cinnaku hannun Sarkin Dawa, daga karshe kuma zuwa hannun Malam. Wannan shi ne tarihina. Abinda yasa ban ambaci sunan wadanda suka kashe mijina ba, saboda ina son da kaina naje na tona asirinsu a idon duniya. Ina son naga an kamasu an musu hukunci daidai da abinda suka yi ga mijina.”

<< Rumfar Kara 28Rumfar Kara 30 >>

1 thought on “Rumfar Kara 29”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×