Na sako kafa ta a falon kenan zan wuce diningroom don na san duk irin ciwon da nake fama da shi ban isa in ki fita cin abinci ba musamman da yake yau tare da Daddy ne a karshen mako, yana gida don haka tare muke cin three square meal, amma sai na dan dakata ina saurare, iya abinda na ji kenan a kan shirin amma na gama tantance muryar DREAM HUSBAND dina ce. Kawai kuma ba zato ba tsammani na Abba ya kashe rediyon sa domin Wasila ta zo ta tsaya a kan sa tana faman gaya masa "Breakfast. . .
Mashaa Allah