Skip to content
Part 10 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Na sako kafa ta a falon kenan zan wuce diningroom don na san duk irin ciwon da nake fama da shi ban isa in ki fita cin abinci ba musamman da yake yau tare da Daddy ne a karshen mako, yana gida don haka tare muke cin three square meal, amma sai na dan dakata ina saurare, iya abinda na ji kenan a kan shirin amma na gama tantance muryar DREAM HUSBAND dina ce. Kawai kuma ba zato ba tsammani na Abba ya kashe rediyon sa domin Wasila ta zo ta tsaya a kan sa tana faman gaya masa “Breakfast is ready!”

Su duka suka juya a tare jin Yiiipp! An fadi a bakin entrance na shigowa falon, Siyama ce dake shigowa ta zame ta fadi kasa, gabadaya suka yi kaina a guje suka daga ni suna faman kiran sunana amma ina! Sun nemi bakin ‘eye balls’ dake cikin idanun kowannne dan adam sun rasa a tare da nawa idon. 

Wasila na fadin Baban Siyama maza dauko mukullin mota” shi kuma yana fadin “ki nutsu, mu fara bata taimakon gaggawa tukunna, kawo min ruwa mai sanyi” kafin ya rufe bakin sa Anti ta fita da gudu neman ruwa Abba kuma ya hau karanta min addu’a yana tofawa, Maryam Jamila ta na gefe tana kuka tana cewa “Anty Siyama!”

Abba na shafa min ruwan da mintuna biyu na yi ajiyar zuciya mai nauyi, kamin in lumshe idanuna bakin kwayar cikin su ya dawo. Hawaye ya gangaromin ta gefen ido, na soma sambatu “…. Abba na gaya maka dama yana raye, mutum ne ba aljani bane. Allah ne ke nufin mu da wani al’amari mai girma da ya shallake tunanin mu”. Abba a kidime ya ce “Waye?” Na ce “Dream Husband dina, na rantse maka da Allah Abba yau na ji maganar shi a zahiri ba’a mafarki ba…… saura ganin sa ya rage min….” nayi – nayi in tuno sunan dana ji ya ambaci kan sa da shi kuma na kasa, tamkar anyi formatting memory dina mai alhakin tuna abubuwa, ko kuma don ban taba jin suna irin sa bane?

Abba sabida takaicin dana ba shi sai ya sakar wa anti Wasila ni yayi tafiyar sa dining ya zauna yayi jugum, sai kuma ya hada shayi amma ya kasa sha. Tsaki yayi can ya tashi ya dau mukullin mota ya bar gidan ya manta jallabiyya ce a jikin sa sai gajeren boxer daga kasan ta. Shi kansa bai san ina zai je ba.”

Anti Wasila ta ciccibe ni ta kai ni dakin ta, ta koma ta hado shayi mai kauri ta kawo min, a baki ta bani duk da zafin sa haka na bude baki na sha sosai don jiya ban ci abincin dare ba na kwanta.

Saida Anti ta tabbatar na samu nutsuwa, barin da jiki na ke ta yi na yunwa da shock ya ragu, sai ta sanya tafukanta cikin nawa ta matsa a hankali. Tace “Yau dai sai an gaya min wanene wannan Lucky din da ke neman sheka min ‘ya barzahu, ya hada ta da fushin mahaifin ta babu gaira babu dalili.”

Wani matsiyacin kuka ya zo min, na ce “Aunty Wasila kin san ba zan miki karya ba ko? Ba zan iya boye miki komai ba ko? To wallahi duk duniya shikadai nake so, Allah ya riga ya nuna min shi tun kafin ya bayyana min shi” cikin mamaki Anti tace “a ina ya nuna miki shi din?””A cikin mafarkai na Anti, rana dai dai ne bana kwana in tashi ban ganshi cikin barci na ba, har ta kai ta kawo zuwa yanzu na haddace kamannin sa da sautin muryar sa”. Idanun Anty was like irin “Siyama ta yi gamo, aljani ya aure ta”. Abinda na gani a cikin idanun Anti tsabaragen tsoro ne zallah. Ta ce “kwanta ki huta, in Abba ya dawo zan masa bayani abin ba na fushi bane Siyama kina bukatar taimako.”

Taimakon da ban gane wane iri take nufi ba.

Da Abba ya dawo daga zagayen da yaje yayi a mota don neman nutsuwar yanke hukunci akan lamarin ‘yar sa Siyama, sai da tayi kokari ya sha tea da chips kadan, sai ta karkace ta soma lallashi.

“Baban Siyama fushi da Siyama ba naka bane, na fahimci gamo tayi”. Abba ya dakata yana kallon matar sa Wasila da kankance ido da sakakken baki, ta ce “kwarai gamo ne, ina kyautata zaton namijin dare (jinnul aashiq) ya aure ta yana zuwa mata cikin mafarki, yau kuma ta ganshi maybe a cikin bangon falo ido da ido”. Jikin Abba yayi sanyi ya ce “kin tabbata ba salon iskancin ta bane?” Anty ta yi rantsuwa akan abunda take zargi ta ce kuma idan aka samo malamai na gaske da suka iya rukiyyah zasu iya raba ni da shi, (a distant cousin of hers) ta yi fama da (similar problem) kuma da iyayen suka dage da neman magani an rabu lafiya yanzu har ta yi aure.

Dole Abba ya yarda da Wasila amma wani bangare na zuciyar sa yana tababar yiwuwar hakan. A tsari da kafin da yasa aka yiwa gidan nan nashi kafin su tare wani shaidanin aljani bai isa ya shigo ba har ya samu matsugunni a jikin iyalin sa. Shima Gidado ne ya bashi wannan laqanin kafin rasuwar sa.

Amma don kore shakku haka ya dauko malamai nagari masu fitar da jinnu daga jikin bil adama suka saka ni a gaba aka banka min turare sannan suka fara karatu. Baka jin komai sai tari na lokaci – lokaci sabida rashin dadin turaren nasu, amma har suka gama Suratul Baqarah ras nake, sai ma kafa danake canzawa position don karatun yana min dadi, na dade ban yi tilawar surah Baqarah ba sabida sakaci irin nawa. Ni na san bani da wani aljani amma na isa in yi jayayya? A je a hakan. Watarana da kan su zasu yarda da ni cewa, na san abinda basu sani ba.

A karshe malaman suka gayawa Abba gaskiya babu shaidani a tare da ni, watakila dai na saka wani saurayi a raina ne shiyasa nake yawan mafarkin sa yake kuma yi min gizo a kunnuwa na.

Abba ya kawo sadaqa ya sallame su. Bai ce komai ba ya bi matattakala zuwa saman bene Anti Wasila ta rufa masa baya.

Tun kafin su karasa daki ya ce “kin ga abin da nake gaya miki ko. Salon iskanci ne kawai irin nata don ta gujewa auren dan uwanta, Omar bai ki Siyama sai ita ce zata ki shi har haka? Na rantse da Allah sai na aura mata Omar sai dai ta mutu da kiyayyar hakan…” Anti bata taba ganin fushin Abba a fili irin na yau ba. Tace “to tunda ta ce yana raye a duniya ka nemi ta kawo shi, in ta kasa sai kayi abinda ya dace” yace “babu wanda zan saurara akan Siyama, ni addini ya baiwa damar zaba mata miji kuma na zabar mata, ya rage nata tayi min biyayya ko ta bada min kasa a ido babu wani shirmen ta da zan kuma saurara.”

A daren ranar Anti ta sameni a daki dauke da indomie da dafaffen kwai guda biyu, ina kwance ne kawai ina fiskantar ceiling tunanin duniya ya addabe ni, kunnuwa na ba abinda suke son sake ji sai muryar sa da sunan sa, takamaimai bansan daga wane gidan radiyo bane don tsakiyar zancen na tsinta babu farkon sa.

“Inaga zaki iya cin wannan tunda baida nauyi” ta fada tana zama a gefe na. “Bana jin yunwa Anti””nikuma bazamu yi magana ta fahimta ba sai kin ci abinci, tashi zaune a baki ma zan baki” ta debo abincin ta nufo bakina da shi, na kauda kai, sai ta hau yimin wakar da take yi wa Shukra-Nadiya idan ta ishe ta da rigima.

“Hayya bina yaa Nadiaa, kam sa’atan laki na’imah!”(Tashi haka ‘ya ta Nadiya, awannin ki nawa kina barci?)

Dariya ta bani sosai don wato nufin ta yau ni da Nadia yar watanni shidda bamu da maraba a wurin ta.

Dole na karbi lomar abincin daga hannun ta, loma uku nayi nace don Allah ta kyale ni kada in yi amai.

Da Anti ta fahimci na dan ware sai tace dani.

“I want to see him!”

Da alamar tambaya na dubeta ina juya hannu wato ina son sanin wa take son gani din?

“I want to see our Dream Guy, in yi magana da shi ta gemu da gemu. Idan na gamsu dashi zanyi kokari in gamsar da Abba duk da na san ba karamin aiki bane mai sauki na daukowa kaina ba.

Amma a matsayi na na ‘yar uwa mace na san illar auren dole don haka zan taimaka miki, ki fada masa gobe ya zo ina son ganin sa a office dina.”

Sai na rasa abinda zan ce mata, anya idan na kara maimaita mata cewa nima ban san shi a zahiri ba, ban taba ganin sa ba, ban kuma san a ina yake ba zata manna min hauka ba? Tunda dai ta ce in kawo shi zata taimaka min to abinda zan yi yanzu shine in nemo shi, a duk inda yake, in kawo mata shi ta rarrasar min Abba ya karbe shi.

Siyama kina da tabbacin shi yana son ki zai kuma iya auren ki? Haka ake soyayyar baka san mutum ba baka san halin sa ba baka san komai akan shi ba? Bai ce yana son ka ba sai ka je ka ce masa zo ka aure ni? Idan ma kin same shin kenan. Ko kuwa shi yace miki yadda kike mafarkin sa shima haka yake naki mafarkin? Lamarin is complicated amma ba’a san maci tuwo ba sai miya ta kare. I vowed to find him, a duka gidajen radiyon jiha dana tarayya. Kuma zan ke ta kasa kunne a duka gidajen radiyo da talbijin ma tunda na fahimci mijin mafarkin nawa Professional Radio Presenter ne. Ba zai min wuyar riska ba. 

Da Aunty ta ga nayi nisa a duniyar tunani sai ta mike tana fadin “sai ya zo. Ki fada masa daga karfe tara na safe zuwa sha biyu na rana zai iya gani na a HumanitarianAffairs”.

Daga haka ta fita, tana kara cewa “kinsan dai WAEC da NECO ne a gaban ki, ki ajiye komai ki fuskance su in kina son gina future din ki yadda ya kamata, idan zaki bari soyayya ta zama priority din ki a rayuwa kin kade har ganyenki.”

Nisawa na yi bayan fitar Anty ina cewa ni kam ai har fadowa kasa warwas na riga na yi daga kan bishiyar karewar kadewar ganye indai a kan sa ne. A yadda nake jin karfin soyayyyar sa a raina zan iya bashi rayuwata, zan iya batawa da kowa in dai har zan tsira da shi. In na ce kowa ina nufin KOWA!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 9Sakacin Waye? 11 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×