Skip to content
Part 9 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Ba zan iya tantance how I reacted ga maganganun Abba na ba, bayan wucewar sa saman bene, abinda na sani kawai shine Abba da gaske yake yanzu kam, kan hada mu aure ni da Ya Umar, wanda ke garin Calabar a halin yanzu yana kammala hidimar kasa bayan kammala digirin sa da (first class result) kamar yadda Abba ke masa buri. Na tattara warning din Abba na jiye a gefe don ban dauke shi a matsayin abinda zai dame ni har ya hanani kwanciyar hankali ba, yadda nake da tabbacin Abba na so na kamar yadda yake son kan sa, na tabbata ba zai taba yi min auren dole ba.

Idan na kafe akan ra’ayi na nan gaba inada yaqinin Abba zai janye nasa, musamman inna tsaya akan baka na na cewa ba son sa ne bana yi ba, girman sa da nake gani ne yasa bazan iya auren sa ba, ai Ya Omar bai yi kama da mazan da suka rasa matar aure ba, farin jinin sa kamar na Abba yake lokacin da yana jami’ar Jos, su ake cewa ana so ba su suke cewa suna son matan ba sabida kyawun surar da Allah yai mana. 

A gani na Ya Omar ya fi karfin ya auri matar da bata masa so na soyayya, wannan kwaruwa ce a gare shi ba kadan ba. I have ambitions, i have plans, na yin rayuwar soyayya da mijin aure na kamar ba abinda muka zo yi a duniyar sai bautar Allah da kuma SOYAYYAH! Kasancewar Allah ya halicce ni da zuciyar da bata son komai daga mijin auren ta sai soyayyah. 

Shakuwar mu da Omar tayi karfin da ba zan iya rayuwar aure da shi ba, meye bai sani ba nawa? Me zan yi ya burge shi? ‘There’s nothing special’ da zan yi in ja hankalin sa da sunan soyayya, haka shima. (A tunani na).

Mutumin da ya gama goya ni a gadon bayan sa ya kuma gama yi min tsarkin kashi da fitsari! Na fara kirgan dangi da haila akan idanun sa. Ya sanni a sanda nake ‘yar sama tsami tsaka tsami na, wallahi ba zan yi kaffara ba in nace ban iya auren Ya Umar. Idan na yarda na aure shi zan kware shi kuma zan kwari kaina don ba zan iya hada shimfida da shi ba.

A daren yau na yi mafarki da DREAM HUSBAND dina, irin mafarkin da ban taba yin irin sa ba tunda na fara mafarkai na a kansa; na gan mu ne a wata alkarya da tafi kama da korran ciyayin tsaunin Mambilla, cikin wata irin rayuwa ta soyayyahr da ke tsakanin mata da mijin ta kadai, wadda ma’aurata kadai ke tsintar kan su a cikin irin ta.

Lamarin da ya tsorata ni ya firgita ni har ya saukar min da zazzabi-zazzabi. I can hear his voice clearly kuma yau na haddace ta kamar karatun sallah a cikin kai na.

Koda na farka daga barci amon accent din sa wanda ban taba jin mai irin sa ba sakamakon tangardar harshe da yake da shi, kuma kamar harshen Hausa naji yana yi cikin ‘yar sassarfa ta magana da yake fama da ita, amon muryar sa irin na Asians bai bar amsa-kuwwa a kunnuwa na ba, yana maimaita kiran suna na cikin shauki na soyayya wanda miji kadai zai iya yiwa matar sa magana cikin wannan yanayin da na gan mu cikin sa.

Na kasa fita in taya Anty hada breakfast yau kamar yadda na saba a dalilin zazzabin da ya ci karfi na ya rafke ni a kan gado, na koma cikin duvet na cigaba da kwanciya ina kakkarwa. Na kuma tabbata a yanayin dana samu kaina wankan janaba ya kamani, janabar da na san ban aikata ba. Shin ko dai aljani ya aure ni ne wanda nake jin ana cewa haka suke auren bil adama? Sai gani yau ina kuka rurus ina neman agajin Ubangiji a kan wannan Jinnul Aashiq. 

Tsoro mai tsanani ya shige ni. Ina wankan ina jin kunyar hakan kamar na aikata zunubin da gaske. Maimakon in yi addu’ar Allah ya raba ni da shi sai na bige da addu’ar Allah ya bayyana min shi kawai muyi aure, ko aljanin ne INA SON SA HAKA!

Da farko Anti ta kyale ni bata neme ni ba don itama a kule take da ni kan maganganun dana gayawa mahaifi na jiya wadanda ita kadai ta san cewa basu bar shi yayi barci ba.

Yau din ta kasance Lahadi kuma ta kama rana ce ta hutun Ma’aikata (international worker’s day) daga Abba har Anti duk suna gida, data ga shiru – shiru bata ji motsina ba har ta gama hada abin kari sai ta biyo bayana tana tambayar.

“Lafiya dai ko Siyama?” 

Daga kwancen da nake dukunkune cikin Duvet na bata amsa.

“Anti kai na ke ciwo da zazzabi” maimakon ta tausaya min kamar yadda na san ta da tausayi akan ciwo, sai ta kyabe baki ce “sabida an tuna miki maganar da tun haihuwar ki kin san da ita, tuna miki kawai aka yi ba sabuwa bace, shi ne kika sakawa kan naki damuwar data haifar miki da ciwo? To Allah ya sauwake, inda alkawari dai ruwa bazai dafa kifi ba!”

Tasa kai ta yi ficewar ta ta barni da tunanin ma’anar Karin maganar ta.

“In da halacci da amana ba za ki ki dan uwan ki Umar ba!” Ko “in da alkawari Abban ki bai cancanci wannan rashin biyayyar ba?” Dayan biyu, haka Anti take nufi ko me?

To ni na ce ina kin Ya Umar? Ai ina jin bayan wadda ta kawo ni duniya sai Abba sai shi a wadanda nake kauna, sai Ummati sannan kowa ma ya biyo baya.

Ba zasu taba yarda da hujjoji na ba. Ko sun gane din ba zasu basu muhimmancin da ni na basu ba. Ba kowa ya san banbancin kauna ta ‘yan uwantaka da kauna ta soyayyar aure ba. A sani na Namiji zai iya auren wadda baya so, ya zauna da ita for the satisfaction of his sexual desire kadai, mace kuwa ba zata iya auren wanda bata da sha’awa ta aure ko kankani a tare da shi ba, and that’s exactly my point.

Aure da Omar bazan iya ba gaskiya, ko duk duniya zata taru a kaina because i’ve no desire for him. 

A gareni soyayya daban, kaunar ‘yan uwantaka daban. Omar can never be my choice of a husband, ban taba yaudarar Abba ba duk sanda yayi zancen nan ai gaskiya nake fada cewa Yaya na ne, bazan auri biological brother na ba don babu banbanci kona haihuwa a tsakani na da Omar.

Ban taba dai gaya masu ina da wanda zuciya ta ta afu gare shi ba sai jiya dana yi subutar baki. Sabida bani da tabbacin mutum ne ko aljan. Allah kadai ya san nufin sa na sako shi cikin mafarkai na har na saba da shi har haka, na ke jin duk duniya bani da miji sai shi, wanda na tabbata ko bajima ko ba dade mafarkan nan zasu zama gaskiya..

Mutumin nan baki, dogo siriri, mai tarin gargasa a fuska da giran ido, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana don junan mu aka halicce mu…. kuma yana gab da bayyana kan sa gare ni komai daren dadewa.

VOA – HAUSA

Shirin su na safiyar yau Lahadi, wanda ya kasance (live-program) ne daga mita 0900 UTC  (VOA-Muryar Amurka, Hausa). Shi Abba ya kunna a falon kasa ya kure sautin, yayi filo da hannayen sa bisa doguwar kujera yana sauraron labaran duniya daga bakin tauraruwar sa Grace Alheri Abdu. Tun bakwai na safe yake sauraren VOA har zuwa karfe tara lokacin da aka gama, kuma lokacin karya kumallon su yayi shi da iyalin sa.

Grace Alheri Abdu na gama nata shirin, akayi taken VOA mai dadi, har Abba zai kashe rediyon sa shirin “HANTSI LEKA GIDAN KOWA” ya rufawa sallamar Grace baya, wato ya maye gurbin nata shirin. 

“Hantsi Leka Gidan Kowa” Sabon shiri ne daga gidan rediyon VOA wanda ya ta’allaqa kacokam ga zaqulo fitattun mutane na Afrika da suka shahara a fannin su wajen baiwa kasashen Afrika gudunmuwa a kafatanin fannonin rayuwar su ta bangarori daban-daban da suka hada da kiwon lafiya, tattalin arziki, ilmi, rubuce-rubuce (literature), tarihi, wasanni, siyasa ko zamantakewa. 

“A yau shirin mu na “hantsi leka gidan kowa” yana tafe ne tare da tsohon marubucin Najeriya Farfesa (Noble Laureate) Wole Soyinka, wato Shakespearn Najeriya, wanda muka fassara wa masu saurare zuwa harshen Hausa (live) daga gidan rediyon VOA-Amurka Hausa a safiyar yau Lahadi, Ashirin ga watan Aprilu, tare da ni…HAMZAH….ALMUSTAPHA….MAWONMASE……..!!! (Ya fadi sunan nasa dalla-dalla yana sama yana kasa da sautin sa kamar cikin rhyme). Tare da cewa; Ayi saurare lafiya……”

Iyaka abinda ni Aisha-Siyama na ji kenan a safiyar yau, safiya mai dumbin tarihi, safiyar da ta juya ta kuma wulwula rayuwata bakidaya. Muryar ta fito ne kai tsaye daga radiyon Abba ina kokarin fitowa daga daki na don halartar tebirin karin kumallo. A karshe ya yi wa masu sauraren sa bankwana da cewa daga wannan lokacin, daga wannan hirar da zai yi da Soyinka, za’a jima ba’a ji shi ba don zai tafi karo kwas na wasu watanni kafin ya dawo.

Nan take jiki na ya karbi wani irin quick reaction na extreme shock, kafin zuciya ta tayi tsalle ta fado kasa daga cikin kirji na ta karbi wani irin coolness duka a lokaci guda. Tamkar na narke a inda nake tsaye.

Numfashi na yayi sama yana dambarwa a tsakanin kirji da hanci da kuma baki na. Tamkar mai fama da ciwon asthma sakamakon yadda shaqar numfashi ya koma cikin hunhu na ya gagare ni. Domin muryar da na gama ji ce a daren jiya a mafarki na nake jin ta yanzu a rediyon Abba, muryar mutumin da ya haifar min da zazzabi da wankan janaba na babu gaira babu dalili a safiyar yau. Ko ko ince; muryar da na girma na kuma rayu sama da shekaru bakwai ina jin ta cikin kunnuwa na, a cikin yanayin barci (mafarki) da yanayi na ido biyu (imagination) a wasu lokutan. Ta yaddda ta riga ta samu kyakkyawan matsuguni a kwanya ta; a koina na ji ta zan gane ta.

<< Sakacin Waye? 8Sakacin Waye? 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.