Skip to content
Part 8 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Nan gefena ta zauna ta kwafar min aikin da aka yi duka tace in naje gida in tabbata na yi assignment din, wanda na darasin English ne akan darasin letterwriting (rubutun wasika).”

Tun daga ranar muka wani irin kulle ni da Ko’oje, tunda ta fahimci inada rauni take karfafani, idan na  nemi sarewa ta ciccibe ni, tare da taimaka min kullum da rubutu har na fara sabawa da rubutun aji da kai na komin yawan sa da yin assignment. 

Idan na koma gida kuma Ya Umar shi yake zama malami na, duk abinda aka koya min a aji sai ya zauna ya tusa min shi da koyarwa mai nagarta ta juriya da repetition wato ayi ta maimaita karatu kamar ana koyar da karamin yaro mai lalurar LearningDisability, ba zai gaji ba har sai na gane. Ya bani aikin gwaji na yi a gaban sa. Idan ya ga na yi daidai sai ya tafa min sosai har wani lokacin ya bani kit-kat as a gift, shiyasa abin ya shiga raina farat daya na daina tsanar karatun makaranta sam a dalilin Yaya Faruq da Ko’oje. Ina cikin yaran da ke bukatar (special consideration) a yayin koyarwa don ban samu soundbackground wato tushen ilmin boko mai nagarta ba.

Anan falon kasa muke zama a gefen su Abba kullum bayan salllahr isha’i, gefe daya zaka ga Anti bisa kujera da laptop din ta a cinya tana aikin office din ta. Anti ma’aikaciya ce karkashin Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development, Abba kuma yana sauraron labaran harshen Hausa a rediyon sa, ko ka same shi yana kallon labaran Aljazeera ko na CNN, amma ya fi karkata ga sauraron (VOA-Hausa) ban san meyasa ba, sai in ba su da labari wanda ya dauki hankalin sa ne yake murdo wata tashar daga cikin wadancan. Idan goma ta buga duk zamu tashi muyi sallama da juna kowa ya nufi makwancin sa.

Wannan sabuwar rayuwar mai tsari da tarin abubuwan alfanu da abubuwan yi masu muhimmmanci ita ta kara kai ni far away daga mafarkan Dream Husband dina. Anti ta yi mana time – table ta kafe a kitchenkullum akwai abinda zamu dafa, bama taba maimaita abinci a sati sai satin ya zagayo. Aunty na son varities Abba na ganin tana masa almubazzaranci. Dole ta rage don Abba malamin tsimi da tanadi ne har gobe duk da ya bar jami’a.

Sau biyu Ko’oje na zuwa gidan mu, har mun hada kawance tsakanin Maman ta da Anti, nice dai ban taba zuwa gidan su ba don Abba ba zai bar ni ba amma Anti ta san ta sosai yanzu, kuma ta yaba da ita har ma dai ranar da Maman ta ta kawo ta, su a Guzape suke zaune.

Sabida Ko’oje yanzu bana shayin homework ko classwork duk wahalar sa, don sai ta tabbatar na gane na kuma gama nawa kafin ta yi nata, a gida kuma ga babban malami na can na bayan almuru yana jirana wato Professor Omar Faruq Gidado Gembu.

Da ana bada ‘Professorial Chair’ daga matakin karatun dalibai a Jami’a tabbas da na dade da baiwa nawa mallamin; Mallam Omar Faruq Gidado Gembu, sabida koyarwar sa is in style da ko kai kafi kowa daqiqanci dole ka gane karatun da ya ke koya maka, ka kuma rungume shi da hannu bibbiyu sabida saukin koyarwar sa.

*****

Yau Asabar a gidan iyayen Anti muka wuni, dake a unguwar Apo, Hajiyar su Anti mace karimiya mai son mutane, nan na tabbatar wa kaina Anti ba a kasa ta dauka ba, ita din ‘yar na gada ce ba ‘yar na koya ba a karrama ‘yan adam kuma ‘yar babban gida na tarbiyya da arziki sosai. Yau har Daddyn su Anti na gani, na kuma yi hira da shi inda ya tambaye ni abubuwa game da makaranta, don yana gida a yinin ranar bakidaya.

Yadda kullum nake dada canzawa haka ma Omar ke girma yana dada murjewa, wani abin mamaki kwanannan na dade ban kara mafarkin ‘Dream Husband’ dina ba, sakamakon yadda na zama busy da karatu da ayyukan gida bani da lokacin kaina sam, balle in samu nutsuwar da zan yi mafarki ya zauna a cikin kai na.

Koda muka samu hutu Abba yace ba zani Mambila ba sabida Tahfiz dana ke zuwa a nan kasan Estate dinmu kullum karfe hudu zuwa shidda, ba’a yi nasu hutun ba. Ya ce mu bari sai ya dauki annual leave (hutunkarshen shekara)Anti ma ta dauki nata in yasodukkan mu sai mu tattara mu tafi Gembun. Ummati dai kullum muna waya ko tuntube na yi a rana sai Ummati dake Mambila ta ji labarin sa. Shiyasa ban damu sosai da rashin zuwa na hutun ba kamar yadda aka riga aka yimin alkawari cewa duk hutun makaranta a Mambila zanyi.

Nutsuwa ta shige ni sosai, ilmin addini dana zamani ya soma ratsa ni, ta ko’ina na zama cikakkar AISHATU-SIYAMA MAMMAN GEMBU na tashi daga (Boddon nan ta Mambila). Bani da abunda zan ce da Aunty Wasila sai Allah ya ja girman ta, ya kara hasken tauraruwar ta a zuciyar Dr. Mamman Dalhatu Gembu.  Ya kuma sauke ta lafiya da abinda ke cikin ta, yasa ayi wa abinda zata haifa duk irin abinda ta yi min a bayan ran ta.

Da ace duka matan uba irin Wasila ne tabbas da ‘ya’yan da wani dalili yasa suka rasa iyayen su bazasu taba koka maraicin uwa ba. She is really a MODEL!

*****

Haka kwanaki suka yi ta shudewa a hankali suna mirginawa suna komawa watanni, har muka gangara wata na tara da komawa FCT, dukkan mu sai muka samu hutun kirsimeti Anti da Abba kuma suka dauki (Annual Leave) a lokaci daya don haka muka tattaro zuwa Mambila don yin hutun mu, dauke da tsarabar Ummati niki-niki iri-iri. 

Irin sukuwar dokin da na yi a jikin Ummati da shigar mu gidan sai da Abba ya daka min tsawa, “karasa min uwar zaki yi? Wannan wane irin rashin hankali ne? Ummatin kwari gareta har haka?”

A can ne muka tarar dasu Young Abba (Adamu) da matarsa Anti Nasara suma sun zo hutun kirsimeti daga Lagos, familyn Ummati ya hadu ya batse waje daya abin sai masha Allah. A washegari aka yi (Get-together Party) na family, aka yi hotuna da vedio don tarihi aka yiwa mamatan mu Addua; Kakan mu Malam Dalhatu, Baba Gidado, iyayen mu Hassu da Asshe. Abba na yi wa Young Abba korafin bai taba zuwa gidan mu ba, in shi ba zai je ba ya dinga kai mana Nasara, Young Abba ya ce aikin shi sam bashi da lokacin tafiye tafiye amma ita Nasaran zai iya sako ta a jirgi ta zo insha Allahu idan sun koma sun samu dama.

Young Abba dai dama rayuwar shi duka ta bakaken turawa ce, sai kuma ya zo ya samu aiki da US Diplomatic Mission tunanin sa ya kara sauyawa ya karkata kacokam kan rayuwar malam bature, bai wani damu da dangi ba, rayuwar sa ta ‘yanci kawai yake yi da matar sa, yana dadewa bai zo gida ba. Kuma in ya zo ba ya jimawa. Hana rantsuwa ya san shi cikakken musulmi ne.

Wato kowa ya bar gida gida ya bar shi kuma gaskiyar bature da ya ce “no place like home”. Mun ji dadin hutun mu a Mambila domin daga can mun je Gashaka ni da Ya Umar wajen dangin mahaifan mu na Uwa, Kakanmu Malam Muhammadu Jauro ya jima da rasuwa Amma akwai kanwar sa Goggo Halima da sauran dangin mu duk suna raye ba inda Goggo Halima bata sa a n kaimu ba, aka kuma rako mu da tsaraba rankatakaf ta fruits (Piya) kwan Zabbi da kwaryar Zuma, muka baro Gashaka cike da kaunar ‘yan uwa.

Satin mu hudu cur a Mambila muka koma FCT don fara shirin komawa makaranta.

Shekaru Uku A Gaba

Awannan lokacin ‘ya’yan Anti Wasila biyu; Maryam-Jamila yar shekara biyu da goyon Shukra-Nadiya ‘yar watanni shidda. Anti haifar ‘ya’yan kawai take amma ni ce komai din su, ma’ana ni nake musu komai amma dole dagabaya ta dauki Nanny sabida bana wuni a gida kullum ina makaranta har a Asabar da Lahadi muna yin Tahfiz. Ita kuma ga zuwa aikin ta.Ni da kaina “Azumi-Siyama” idan na dubi kaina a mudubi a wannan shekarar dana ke cika shekaru goma sha tara da haihuwa, ajin karshe na sakandire, bana saurin yarda cewa nice. Sabida girman da na kara da samun cigaban rayuwa ta kowannne fanni. 

Nafi yarda in aka ce wata bakuwar balarabiya ce daga UAE ba Boddo-Siyaman Ummati ba. Wannan Budurwa ce mai aji daidai nata, ba wannan kazamar Boddon ba. Kuma rainon ‘Regent College’.  Ga nonuwa sun cika tantsan a kirjina har rinjaya ta suke yi. Wayewa ta, girman jiki na da exposure dina sun fi kama da na matakin ‘yan Jami’a bana ‘secondary school level’ ba.

A wannan shekarar da muke ciki zamu zana WAEC nan da watanni uku masu zuwa, kuma a cikin wannan shekarar ne abinda nake tunanin ya tafi har abada ya dawo min sabo; na koma mafarkan DREAM MAN dina.

“Dream Man, ina murna ka tafi ka bani sarari ina karatu na yadda ya kamata don ginawa kaina future, sai gashi rana daya ka dawo, me yasa?”

Na yi tambayar tamkar yana ji na, kodayake na tabbata yadda nake jin sa a ruhi da zuciyata shima yana jin hakan. Kamar dama yayi dan balaguro ne jira yake in gama da muhimman abubuwan da ke gabana, in mallaki hankali na sannan ya dawo ya cigaba da yi min babakere a zuciya.

Burin Abba na shine in kammala sakandire lafiya, ya cika dadadden burin sa akan mu ni da Ya Umar. Hatta gidan da zamu zauna yasa Archititects sun zana masa an saka harsashin ginin a sabuwar unguwar Katampe. 

Tunda Abba ya fahimci bana so ana alakanta maganar aure tsakani na da Ya Umar ya shiga wani irin rudani, tsoron sa Allah tsoron sa abinda zai tada wannan alkawarin nasa, wanda yake son tabbatar da shi koda shine abu na karshe da zai aiwatar kafin Allah ya dau ran sa, don haka Abba ya dage wajen kyautata mini a dan tsukin nan da na ke gab da kammala makaranta, don samun damar cika kudurin sa a lokaci mafi dacewa, yana ja na a jiki sosai yana tambaya ta abubuwan da nake so ya saka min a gidan mu da yake gina mana. Yace hatta penti sai kalar dana zaba za’ayi. 

Rannan da abin ya ishe ni don na fara yarda Abba dai da gaske yake Ya Umar zai aura mini nan ba da jimawa ba, domin ya kawo taswirar zanen gidan da yake gina mana yana nuna min komai yana bayanin kowanne lungu da kowannne sako na gidan, ya ja layi a kan wani daki ya ce yana murmushi.

“Ga nan dakin Grand-children dina, ba abinda baza’a saka a ciki ba tun daga kan feeder har keken koyon zama.”

Hankali na ya fara tashi kan maganganun Abba, don babu wasa yau a fuskar sa sabanin sauran lokuta da yake fadi cikin raha, idan ya ga na bata rai ya bar zancen, na yau din sounds extremely serious. 

Na sunkuyar da idanuna kasa daga barin kallon cikin idanun Abba na wadanda ke cike taf da kauna ta da fargaba as well; wato tsoro da fargabar kada na ce masa “a’ah”, bazai yimin dole ba amma kuma ba zai iya tada alkawarin sa ba, nace,

“Shin Abba da gaske kake wai? Ni fa duk maganar auren Ya Omar da kake yi min tun ina karama na dauka wasa kake yi. Abba ba zan iya auren Yayan da na tashi a hannun sa kamar shi ya haife ni ba. Wallahi Abba ba zan iya ba (because i respect him). Kayi hakuri don Allah Abba inada wanda nake so tun ban san so ba!”

Daga Abba har Anti Wasila, zaro ido suka yi cikin kidima suna kallo na, Abba harda waiwayawa yana addu’ar Allah ya sa Omar baya falon, yayi ajiyar zuciya da ya tabbatar Omar bai ji ni ba. A wannan karon Abba ya nuna ni da dan yatsa idanun sa sun kada sun yi jajir ya ce.

“Boddo kike ko Azumi ko Siyama ki kiyaye ni, mugun kiyayewa, wallahi bani da kyau, a fuska ne na ke da kyau, ban taba nuna miki other side dina ba sai na Uban da ke son ‘yar sa, sai dai ki sani wannan uban ” ya fi son zumunci fiye da ‘ya’yan sa.” 

Ni da dan uwa na Gidado bayan kasancewar mu ciki daya iyayen ku mata ma cikin su daya, ki gayamin akwai wanda zaki aura ya rike ki da daraja da ya kai Omar? Don haka ki duba wannan kusancin ya wuce duk yadda kike tunani, babu inda zan kai ki sai hannun Omar sai idan bana raye, zan tabbatar kuma kafin na mutu na barwa Ummati wasiyyar ko kin mutu a fara kai gawar ki gidan Omar kafin a zarce da ita makwancin gaskiya.”

Daga haka ya tashi ya bar falon yana jin wani irin bakin ciki a ran sa, sakayyar da Siyama zata yi musu shi da Omar kenan? Lallai dan yau ba’a taba ci masa alwashi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 7Sakacin Waye? 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×