Ni da Ya Omar wata irin mu’amala ce mai kyau kuma mai tsafta a tsakanin mu, ta fi karfin ta Yaya da kanwa don in da akwai alaqar da take sama da ta Yaya da kanwa a karfi da muhimmanci to ni da Ya Omar ce. Bamu da sama da junan mu a komai. Kuma bama hada lamarin da ya shafi dayan mu da komai a muhimmanci.
Ya sanni kamar yadda ya san tafin hannun sa. Na san shi kamar yadda na san farcen hannu na. Omar mutum ne mai martaba iyaye da sanin darajar su, mai wani irin. . .
Very interesting novel
Madallah da Aunty Summynmu