Skip to content
Part 5 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Ni da Ya Omar wata irin mu’amala ce mai kyau kuma mai tsafta a tsakanin mu, ta fi karfin ta Yaya da kanwa don in da akwai alaqar da take sama da ta Yaya da kanwa a karfi da muhimmanci to ni da Ya Omar ce. Bamu da sama da junan mu a komai. Kuma bama hada lamarin da ya shafi dayan mu da komai a muhimmanci.

Ya sanni kamar yadda ya san tafin hannun sa. Na san shi kamar yadda na san farcen hannu na. Omar mutum ne mai martaba iyaye da sanin darajar su, mai wani irin kawaici da alkunya, ma’abocin maida kai a kan duk abinda ya sa gaba tun a lokacin kuruciyar sa. Mai fifita ra’ayin wani sama da nasa. A fannnin karatu kuwa na rantse na sake rantsewa; ban taba katari da hazikin mutum a karatun boko dana addini irin Omar Faruq Gidado Gembu ba. Dalili na na fadin haka shine; Ya rubuce Al’qurani da hannun sa ya kai sau bakwai ya kuma haddace shi. Abba kan ce ko Alhuda-huda ba zai so hada gasar karatu da Omar ba.

Wadannan qualities din ne Abba ke hange har yake ikirari shan alwashin hada mu aure, a tunanin Abba babu namijin da ya dace da auren Siyamar sa sai Dan sa Omar, Omar din da ya raina da kan sa, yake kuma fatan aure tsakanin mu ya dawwamar da zumuncin sa da marigayin dan uwan sa a bayan ran sa, ya kara yawan zuri’ar Ummati a igiya guda su zamo tamkar tsintsiya guda. Har ila yau, yake kuma fatan Ubangiji ya cika masa wannan burin nasa da ran sa da lafiyar sa. 

Abba kan ce “ba’a shaidar dan yau, amma ni na shaidi Da na Omar, shikadai zai rike min Boddo da irin rikon da nake so ta samu a gidan aure.”

Amma kuma ni Siyaman, ina girma ne tare da mafarkai na da burika na (fantasies) wadanda daga ni sai Allah muka san su. Wato tunda ni fara ce farin da babu surki to miji baki (black) zan aura wannan na cikin mafarki na, har na kan hango ‘ya’yan da zamu haifa masu duhun kala da kyakkyawar suffa, idan ni suka dauko ko baban su wato mijin mafarki na zasu zama ne tamkar ruwa biyu.

Ba ruwa na da abinda Abba ke hange, ba ruwa na da mafarkan Abba sai nawa mafarkan, ba ruwana da burin Abba, duk da ya dade yana fada yana maimaitawa a gaban mu ni da Omar din. Iyakaci Omar ya sunkuyar da kai amma bai taba tankawa a kan hakan ba, ni kuwa a duk lokacin da ya fada na kan zumbura baki ne in ce.

“Abba! A ina ka taba ganin Yaya da kanwa sun yi aure?” Abba sai ya ce “daga kan ku za’a fara!”. Kuma daga wannan amsar da ya ke bani, ba na daukan zancen da nisa.

A haka muke girma hankali na kara shigar mu, amma mafarki na da buri na na auren bakin mutumin cikin mafarki na bai taba canzawa ba, ta kai ta kawo har ina imagining din sa a idanu na na zahiri, I can feel his eyes all over me, da lamarin yayi gaba sai na fara jin muryar sa all over my earsyana kiran sunana in a unique way. A cikin mafarkin na kan gan shi tarr, ganin ido na, in ji shi sarai jin kunne na, in kuma rike kamannin sa amma da zarar na farka sai a shafe komai daga kwakwalwa ta.

A wannan shekarar Ya Omar ya kammala karatun sakandire, da sakamakon su ya fito Abba ya ce ya cike jami’ar Abuja a JAMB form din sa don burin Abba kullum shine ya bude ido ya gan shi tare da Omar. Duk da ya san ba karamin yaki zai yi da Ummati ba kafin ta yarda Ni ko Omar wani ya bar gaban ta. Amma dole ne Omar ya shiga jami’a.

*****

An daura auren Abba da Anti Wasila a wata ranar Lahadi. Abba ya yi furnishing bangarensa na nan gidan mu ya tashi a matsayin apartment na zamani, ba can kadai ba har bangaren Ummati ya gyare tas babu maraba da nasa bangaren, ya min daki na mai kyau ya zuba min duk abin bukata. Duk garin Gembu yanzu babu gida kamar namu har wani lakabi akewa gidan wai gidan gilashi, sakamakon duk ta inda ka bi a gidan mu gilashin tagogin da na kofofin ke daukar idanun ka. 

Anti Wasila ta tare a gidan da tarin dukiya wadda ta kara kawata sassan nata kwarai. Ta tabbata ‘yar Ogan su Abba domin kuwa ni dai ban taba ganin duniya irin ta dakin Anti Wasila ba, ko kuwa don bani da exposure?  Amma da na tuna Abba ya ce diyar shugaban sa ce sai ban yi mamaki ba. 

Anti Wasila na yawan gayamin cewa wai kira ta da suffata ta matan manya ne, wannan ya na kumbura kaina ya kara min burin auren mijin mafarki na, domin kuwa babban mutum ne ba yaro ba. Maganar da Abba na ke yi ba tun yau ba wai zaman Ya Umar nake ban taba daukan ta da wani muhimmanci ba. 

Can nake hango miji na bakin dan Najeriya, dan sardidi da shi na burgewa, ban taba addu’ar Allah ya bani miji nagari ba, nidai kullum addu’a ta Allah ya bani mijin cikin mafarki na, ya sada fuskokin mu nan ba da jimawa ba, domin jiki na ya gama bani yana raye cikin duniya, amma ba a Mambilah ba; shi ba fari bane yafi zama a rukunin bakake, dogo siriri mai yawan gargasa a fuska, mai wani kasaitaccen aji na musamman. 

Ranar da Ummati ta ji na furta wannan addu’ar bayan na idar da sallah taji nace Allah ya bayyana min mijin mafarki na haka, sai ta yi tsam, ta nutsu, tana sauraro na har na gama. Cikin nutsuwa Ummati ta ce.

“Azumi, me na ji kin ce? A kul! Na kara jin wannan bahaguwar addu’a a bakin ki. Yau nake jin lalacewa wace irin addu’ar banza ce wannan?” 

Na kuwa cunno mata baki ina kunkunin cewa “ina ruwan ki da addu’a ta? Daga ranar sai nake addu’a ta a zuci kada wani ya kara ji ya yi min fatan rashin karbuwar ta. 

Ko sati biyu Anty Wasila bata rufa ba a gidan mu kasancewar ta caring a kan lamarin kowa na gidan ta gano wacece real Siyama; irin rayuwar tabarar da nake yi a gaban Kaka ta ta babu shan rana babu hantara sannan babu aikin wahala, domin ko firar dankali ta bani in yi mata zan fara amma tana kaucewa zan aje mata abinta in zura in gudu sassan Ummati. Gashi bata zo da mai aiki ba ayyuka suna mata yawa don bata rabo da girke girke kai kace (food and nutrition) ta karanta.  

Amma sam ko wankin cokali bana taya ta, ta lura ba ita kadai ba ko Ummatin ma bana tayawa kuma Ummatin bata damuwa, sannan bana son karatu ko kadan bana assignment bana homework iyakaci a dake ni in ban yi ba to jikina kam zuwa yanzu ya saba da dukan malaman makaranta har bana jin zafin sa, ya fi min sauki a kan wahalar karatu.

Yadda nake ta munanawa Anti Wasila zato sai na samu akasin haka a dan zaman da tayi tare damu, bilhaqqi take son Abba da duk wanda ya dangance shi. Kullum sai ta zo ta sharewa Ummati daki ta wanke mata hijabanta ta shanya da yake Ummatin bata barin ayyuka su tarar mata kullum cikin aiki take shiyasa babu ayyuka da yawa a dakin nata. 

Da ta shiga daki na kuwa sai da ta toshe hanci, panties dina masu menses a jiki tun na wancan watan na cukuikuiye su na saka a wardrobe kana budewa wani hamami zai buge ka, babu shara babu mopping a dakin kaca-kaca da shi, ko ‘yar aikin gida bazata bar dakin ta haka ba, undies dina kamar tsummokara dukundukun dasu sai ‘yan dukununun uniform dina na boko da islamiyya duk sun ji jiki kasancewar bana goge su, littattafaina na makaranta kuwa da ta buda sai da ta kusa kuka. Shin ko wannan shine maraici na UWA-MAHAIFIYA A TARE DA DIYA MACEN DA TA BALAGA? Take neman uwar da zata ja ta a jiki ta nuna mata komai na tsaftar jikin ‘ya’ya mataat puberty stage? Wasila ta tambayi kan ta cikin tausayin Siyama. Amma kuma bata cewa Ummati komai ba kan abubuwan data gani don ta lura da wani abu; ba’a fadar laifi na a gaban Ummati. Saidai daga wannan ranar Wasila ta dauki aniyar canza rayuwar diyar mijin ta Siyama.

Rannan da gangan ta saka ni girki wai kanta ciwo yake. Ta shige daki kamar mai ciwon gaske ni kuma kamar abin arziki na tafasa ruwa daganan kuma na rasa me zan yi? Don wallahi ko dafa kwai ya dahu daidai ban iya ba sai ka samu ruwa-ruwa a cikin sa wato bai dahu gabadaya ba.

Sai na ce tunda ta shige daki bari kawai in gudu iyakaci gobe ta ki kula ni, to sai me in ta ki kula nin? Na zo ficewa ashe-ashe ta kulle sassan da mukulli ta kuma zare mukullin ta tafi da shi dakin ta. Na rasa inda zan sa kaina don takaici na koma kicin na hau safah da marwah, a karshe nace bari kawai in mata wake da shinkafa ta ci da mai da yaji tunda shi ba sai an yi miya ba.

Na hada waken da shinkafar na zuba a tukunya na antaya ruwan zafi a kai. Suna tsotsewa na kashe na hau kwashewa a sabuwar warmer dana taka island din kicin din na daukoa cikin kwalin ta, ni da kaina daga ganin abincin a ido na san tsoro kawai na bashi wato bai dahu ba. To amma yafi ta zo ta ga ban yi komai ba ta dauke ni wata bi ta can, in yaso in bai mata ba sai ta kara dafawa da kanta. 

Anti Wasila ta shigo tana hamma wai ta tashi daga baccin data samu, ta ce “Siyama na ji dadin kan nawa yanzu dana yi bacci kadan na sha paracetamol, zubo mana abincin nan muci a kan leda bana jin hawa tebir din nan ga shi yunwa nake ji sosai.”

Iyakacin takurawa Anti Wasila ta takura min yau na rasa dalili, buri na kawai ta bude kofa in fece wajen Kakata amma ta ki, na zubo abincin a faranti mai fadi sai cin magani nake yi tayi kamar bata ganni ba, don kuwa cewa ta yi “sako cokula biyu yau tare zamu ci”, na bi umarnin ta, bayan na antaya mai da maggi da uban yaji na kawo kan ledar data shimfida, ta hau juya abincin da cokali amma ta ki kaiwa bakin ta, tana jira ni in fara kai loma. 

In kaga fuska ta a lokacin yadda ta yankwane kamar zan fashe da kuka don na gane Anti Wasila kamun kazar kuku tayi min yau, na dade ina guduwa in ta saka ni wani abu da ya shafi aikin gida ko na abinci. Ni kuma ba zan iya ce mata ban iya ba, na san a shekaru na goma sha biyar ba karamin abin kunya hakan zai haifar ba ko kuma ma ta raina ni.

Dana ga ba sarki sai Allah dole na kai abincin baki na, na kuwa runtse ido na ki hadiyewa. Tsahon mintuna biyar Anti na bin karatun Qur’ani a wayar ta tana jujjuya cokali a abinci, cikin ginshira tace.

“Yau sai kin cinye abincin nan Siyama, don ki tabbatarwa kan ki irin sa zaki dinga baiwa mijin ki Umar nan da shekaru biyu ko uku”. 

Ido na fal hawaye na furzo na baki na nace “Anti ki yiwa Allah da Annabi ki kyale ni haka” ta yi dariya ta ce “zan kyale ki ki fita in kin cinye, ko babu dadi ne?” Na fara hawaye na ce “wallahi Anti bai dahu ba, zai bata min ciki, ko taunuwa ba ya yi” “shi mijin ki da zaki dinga baiwa wannan ba zai bata masa ciki ba?” “Anti ai banda mijin tukunna ki bari sai nayi auren sai ki koya min” Anti ta ce “don tuwon gobe ake wanke tukunya ba sai an zo amfani da ita ba, zan kyale ki only in kin nuna min hammatar ki da cikin wandon ki don ban yarda bama kina yin shaving dasu wanke baki. Look at your teeth (kalli hakoran ki) yadda suka koma yellow kamar kin shekara baki basu maikilin ba”. 

Jin abinda tace wai in nuna mata hammata ta da cikin wando na na soma tababar ko matar nan bata da hankali ne? Ko kuma shaye shaye take yi? Ban furta ba amma kwayar idanuna  sun gaya mata abinda nake tunani a kanta. Ko a jikin ta sai ma dora kafa daya da tayi kan daya, tana jiran in cika umarnin ta ko in kwana nan a dakin ta.

Jin Anty Wasila ta yi rantsuwa sai na nuna mata hammata ta zata bude min kofa, na dinga kuka ina kankame jiki na. 

“Ummati ki zo ki cece ni, na shiga uku, kina ina ne za’a tube ni yau, Ummati!?”

Anti na gintse dariyarta ta ce “tara kika shiga ba uku ba, sama tsami tsaka tsami matar Umar” sai na bar kiran Ummati don na tabbatar ta yi nisa bazata ji ni ba, na hau kiran Ya Umar shima, ta ce “ai gara ya zo don ya ganewa idon sa irin kazamar matar da Abban sa ke masa tanadi.”

Ba shiri na yi shiru. Har da toshe bakin. Na hadiye gunjin kuka na don nima ba zan so ko kusa Ya Umar ya ga kasan hammata ta ba. 

Haka Anti ta tasa ni a gaba muka shiga toilet dinta ta aske ni tas da (shaving cream) mai santsi, ta ce kuma kaina ma askewa zata yi  kwalkwal zata min idan har ban yarda ta wanke min shi da kanta da sheltox da kalkashi ba. Yau ni Siyama na ga ta kaina, har tara na shiga a wurin Anti Wasila hatta baki na sai da ta wanke min shi tas da maclean dinta mai karfi na Longrich sannan ta kyale ni. Na kuwa fice da gudu sai dakin Ummati ina nishi kamar wadda tayi gudun famfalaki.

<< Sakacin Waye? 4Sakacin Waye? 6 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.