Skip to content
Part 4 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

HERE COMES “WASILAH”

(MY LIFESTYLE  INFLUENCER)

Masu iya magana kan ce “Rai dai… ba ya rabuwa da rabo sai dai idan ya kare.” Ko su  ce “komai lokaci ne” musamman aure lokaci gare shi kuma kamar habo ya ke idan lokacin da aka kaddara ma dan adam yin sa ya zo. Abin mamaki a wannan zuwan da Abba ya yi Mambila ya zo ne da zancen da ya bai wa kowa mamaki, wato ya samu matar da zai aura a can Abuja, diyar shugaban wajen aikin su.

Ummati ta bantari goro ta tauna kafin ta kura masa ido da son gane yana ciki hayyacin sa? Ko kuwa wannan matar asiri ta yi masa? Don an ce abinda matan barikin suka fi kwarewa a kai kenan in sun ga mazan da suka yi musu. Bata ga komai a tare da shi ba sai wata irin nutsuwa, da murmushi mai kwantar da rai, wanda ya nuna bayan cikin hayyacin sa yana cikin tantagaryar soyayyah kuma.

“Matan Gembu da na kabilar Mambila sun kare ne?” Cikin izgili da tauna goro Ummati ta tambaya. 

Cikin lallashi da kwantar da murya Abba ya amsa mata da cewa.

“Basu kare ba Ummatin Mambila, kuma har abada bazasu kare ba, wannan din ce dai kawai hankali na ya kwanta da ita. Ba ita ta ce tana so na ba ni na gan ta da kaina a gidan mahaifin ta, na yaba da hankalin ta, tarbiyyar ta da gidan da ta fito, na roki mahaifin ta cikin alfarma da ya bani ya kuma amince sabida kaunar da yake yi mun, ya ce in zo in turo magabata na.”

Ko ba komai bayanan da yayin abun a duba ne, don haka Ummati ta rasa abin cewa, can kuma ta ce.

“Ka ba ni kwanaki uku in yi istikhara.”

Jiran kwanaki ukun a garin Mambilan da suka zamarwa Abba tamkar jiran shekaru uku, don hakika yana son Wasila.

Bayan kwana ukun kuwa Ummati ta ce da Abba ya je ya samu waliyyan su wato aminan mahaifin su marigayi Malam Dalhatu su je su nema masa auren. Bata ga komai a tare da yarinyar ba sai alkhairi mai tarin yawa tattare da ita. Ta tambaye shi ko ‘yan asalin ina ne? Ya ce “Katsinawan Dikko ne. Aiki ne kawai ya kai mahaifin ta Abuja kamar yadda ya kai kowannen mu.”

Ummati ta yi murmushi tana ta karantar farin cikin da yake ciki duk da yana kokarin dannewa ta ce, “kai da dan uwan ka duk Katsinan kuka gudu? Ina nan zaune kan shimfida ta zaku zo neman karin ta bibbiyu a Mambila, don matan mu basu da maraba da Hurul eenin aljannah”. Abba ya yi dariya sosai ya ce, “to babu laifi Ummati, bari sai mun karasa Aljannahr gaske, sai na kara da su.”

Kowa ya na ta murna Abba zai yi aure ban da ni, karewa ma, bakin ciki nake yi sosai, ni bana son matar duk da zata auri Abba gaskiya haka kawai ta raba mu da shi. Ranar da na yi kuskuren fadin wannan maganar Ya Omar sai da ya buge min baki da tafin hannun sa, Ummati kuwa ta ce “irin ki kam, kishi zakuyi, har dana balbal wanda bai dace ba. Allah ya shirya masu kishin iyayen su, matar sa ai uwar ki ce in da tunani, kada in kara jin wannan maganar a bakin ki Azumi, shima in ya ji baki so ko bai fasa ba zaki sanyaya masa gwuiwa.

Ke daban a wajen sa, matarsa ma daban, da wannan zaman da yayi shekara goma sha biyar cikin gwaurantaka ba gara masa auren ba koma wacece zai aura ai ta rufa masa asiri ta kuma taimake shi.”

Wannan Magana ko kadan bata sanya na ji ina farin ciki da auren Abba ba, damuwa sosai na dauka na sakawa raina a kai babu gaira babu dalili har da kin cin abinci wuni guda, har Ya Omar ya gane fushi nake yi da dukkan su, tunda babu wanda ya bi bayan ra’ayi na.

Na zo wucewa cikin gida daga islamiyya na gan shi zaune akan dakalin kofar gidan mu yana karatun jarida, wucewa nayi ba tare dana yi masa magana ba don har zuwa lokaci ina jin haushin buge min bakin da ya yi a kan matar Abba da bata kai ga zuwa bama. Omar ya bi ni da kallo ta kasan idanun sa har na wuce ciki ya ce,

“Boddo am, kawomin buta a cikin gida zan yi alwallahr sallah, magriba ta yi” na zumbura baki na yi cikin gida ina cewa a raina zaka ga buta, tunda kana bayan auren Abba, kai ma idan ta zo raba mu zata yi don na fahimci ta fi ni farin jini yanzu a wurin ku, don ba abinda suke yi duk gidan yanzu sai shirye-shiryen tarbar matar Abba, an yi renovating gidan mu sosai ya koma na zamani, sabida a nan gidan mu zata fara zama na tsayin sati hudu. Na ji Ummati na fadin saura kwana uku daurin aure.

Ya Omar ya na can yana ta jiran buta, har aka kira sallah, dole ya shigo cikin gidan ya dauka da kan sa yana mamakin share shin da na yi, sanda ya shigo nima alwallah nake yi a gindin famfo ya ce.

“Boddo kin kyauta, ni kika share ko?” Kasa-kasa yadda Ummati bazata jiyo ni ba na ce “amaryar Abba ta dauko maka, tunda har zaka iya bugun baki na a kan ta” dariya yayi ya ce “to ni meye gami na da amaryar Abba? Ban san ta ba bata sanni ba, rashin kunya kika yi na hukunta ki, shin ma wai ke meye matsalar ki da auren Abba ne? Kada dai kina nufin kishin Baban ki kike yi?”

Zaro ido na yi ina kallon Ya Omar, amma can a karkashin kasan idanun tabbacin hakan ke bayyana kansa baro-baro, wato tawa mahaifiyar na ke tayawa kishi wadda ke karkashin kasa har ta zama turbaya, a fili kuma nace.

“Ba haka bane, zan gaya maka dalili na Ya Omar bayan sallahr isha.”

Ana idar da sallahr isha kuwa Ya Omar ya shigo gidan kamar yadda ya saba, Ummati na lazumi har zuwa lokacin, ban taba ganin mutum mai yawan jan tazbaha irin Ummati ba, abincin daren sa na fara dakko masa, gudun kurna ne da miyar taushe Ummati ta yi mana, yana budewa ya yamutsa fuska ya ce “Ummati, kin san bana son wannan abun” ta harare shi ta cikin hasken kwan lantarki da ya haske fararen fuskokin mu bata ce masa komai ba don bata gama lazimin ta ba. 

Ya mike tsaye yana karkade jikin sa yana fadin “da in ci wannan kulakulan naki ya sa ni bacin ciki gara na yi birki a teburin mai shayi an soya min lafcecen kwai da zazzafan shayi da ya ji madara creamler” ai jin haka yawu na ya tsinke na mike ina cewa “sai dai mu je tare baza ka ci kai kadai ba” wata harara ya sakar min ya ce “tebirin mai shayin zaki je? Kiyi zaman ki zan kullo miki” na ce,

“Ni ba teburin mai shayi zan hau na zauna ba, raka ka kawai zan yi muna tafe muna hirar mu kan abinda ya dame ni, na gaya maka Ya Omar ina da damuwa.”

Da wannan Ya Omar ya yarda muka tafi tare, don ya sanni wajen kafiya ko ya kara turzawa ba hakura zan yi ba. Ummati ko kula mu bata yi ba. 

Sararin samaniya yayi haske da hasken farin wata, babu wadatar haske a layin, muna tafe gefen hanya ni da Ya Omar a cikin layin mu, na ke gaya masa damuwa ta a kan auren Abba ba kishi bane na ke yi, na san in kowa bai fahimce ni ba shi Omar zai fahimce ni, mun yi nisa na ce da shi cikin sanyin murya,

“Ya Omar ka san yadda nake son Abba na, na kuma ji an ce matan birni irin wadannan da Abba ya dauko zai aura azabtar da ‘ya’yan miji suke yi, su raba shi da mahaifiyar shi da ‘yan uwan shi, su cinye halayen sa na kirki ya koma wani sabon mutum mai sababbin halaye marassa kyau.

Yau da a ce a nan Mambila Abba ya samu mata zai yi aure ba zan damu ba, kuma hankali na ba zai tashi ba.”

Na karasa maganata cikin damuwa tsantsa. Ganin haka Omar ya dube ni ciki mamaki ya ce “what is your business with this? Kina nan Mambila hannun Ummati suna can Abujan su me zai hada ki da su? Wannan rashin adalci ne ki ce duka matan birni haka suke, kina ina ta kauyen ta nemi kashe Baba Gidado? Boddo ki bari ta zo ki ga irin kamun ludayin ta kafin ki yanke mata hukunci. 

Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya Boddo na. Na hore ki da rashin daurawa kan ki matsalar wasu, abu ne da ba zai amfane ki ba.”

Daidai lokacin da muka iso wajen Garba mai shayi, ya biya aka soya mana Kwan, ina can gefe harde da hannaye a kirji aka zuba mishi a leda muka kamo hanyar gida Ya Omar ya ce.

“Boddo abin kunya ne ace kina mace amma ko kwai baki iya soyawa ba, bana son wannan goyon jaki da kaya a kan da Ummati ke miki, don ke mace ce, uwa kuma matar aure, kika yi aure a gidan mijin da ke son abinci, na rantse wahala zaki sha a hnnun sa don ba zai jure ba”.        Na tura baki na yi gaba na bar shi ina kunkunin cewa “Ya Omar wa ya gaya maka zan yi aure? Ai sai Mutumin Mafarki na ya zo. Kuma har yanzu bai zo ba tukunna.

Ai wato ni miji na duk duniya babu irin sa a halayya da dabi’a he’s simply special (na musamman ne) halin sa ba irin na sauran maza bane, ni na gaya maka bazai taba damuwa ba wai don ban iya girki ba, ni yake so ba girki na ba, ni kadai na san shi…

A mafarki na kawai nake ganin sa….!!

Shi ba fari ba shi ba baki ba, gashinan dai Bakin dan Najeriya mai tsayi da cikar zati, dogo haka siriri, mai cikar gargasa da wadatar saje a zagayen fuskar shi, kullum sai na yi mafarkin sa Ya Omar ya na murmushin sa mai ratsa ni, yana gaya min cewa yana nan tafe, nan bada jimawa ba, na duba na hanga anan garin baki daya babu shi babu mai kamar sa….

Ledar kwai da biredin hannun Ya Omar ta subuce ta fadi kasa, a lokacin he was like (ko Boddo ta yi gamo ne?) Ya sunkuya nima na sunkuya at the same time don daukar ledar da ta fadi, sai kawai hannnu na ya sauka a kan nasa.

Ba zan taba mantawa da wannan glimpse din ba da ya faru cikin hasken farin wata. Hasken farin watan ya haska min cikin kwayan idanun Umar, sai na ga sun koma reddish-brown ba ainahin kalar su ta zahiri ba, kunshe da wani bakon al’amari da ya fi kama da kishi da ban taba gani cikin idanun sa ba, sakar min ledar yayi na dauka muka cigaba da tafiya bai tanka komai a kan shirmen da na fada ba.

Ni kuma da gaske nake har ga Allah kullum sai na yi mafarki mijin Boddo, exactly yadda na suffantawa Ya Omar shi. Tun bana rike kamannin sa har na zo na rike, a da can bana iya rike kamannin sa banda cewa baki ne dogo mai cikar gargasa a fuska kuma ba dan Mambillah ba.

Kwatakwata Ummati bata saka ni girki, ko tace in zo in gani in tana yi wai bata so in sha wahala, jikin nawa bashi da auki, don haka ni dinnan ko dafa indomie ban iya ba a shekaru na goma sha biyar a duniya, aji uku na karamar sakandire.

Ga kiwa, ga son jiki kamar ‘yar mussa, inda duk wadannn abubuwan guda biyu suka hadu a waje guda ga mace to fa za’a samu boyayyar kazanta a tare da ita, bana son aiki ko kankani don tun farko ba’a sabar min da shi ba.

Gashin kaina bai yi kama da na ‘yammata tsararraki na ba wadanda kullun cikin gyaran shi da yin ado da shi suke yana reto akan fararen fuskokin su, ni nawa kullum cunkushe ya ke cikin bakin dankwali babu wanki babu taza babu retouching, ga kwarkwata wadda na tabbata rashin kula irin nawa ne ta sabbaba zaman ta a kai na.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 3Sakacin Waye? 5 >>

11 thoughts on “Sakacin Waye? 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×