Kaico na da sakacin da na yi wa kaina! Kaico na da badawa Abba kasa a ido! Kaico na da zaben soyayya a kan nagarta da nasaba! Kaico na! Kaico na!! Kaico na!! Sakacin ba na kowa ba ne, nawa ne ni SIYAMA!!!”
Na kifa kai a kan dashboard din motar Omar na yi kukan da zai ishe ni. Musamman da na ga Omar ya amsa kiran matarsa a gabana yana mata take care, much love Habeeb-Qalby. Wannan ya tsaya mun a rai, ya tabbatar min Ya Omar ya dade da rufe shafi na a rayuwar sa, ya dade. . .
Sakacin waye