Skip to content
Part 60 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Kaico na da sakacin da na yi wa kaina! Kaico na da badawa Abba kasa a ido! Kaico na da zaben soyayya a kan nagarta da nasaba! Kaico na! Kaico na!! Kaico na!! Sakacin ba na kowa ba ne, nawa ne ni SIYAMA!!!”

Na kifa kai a kan dashboard din motar Omar na yi kukan da zai ishe ni. Musamman da na ga Omar ya amsa kiran matarsa a gabana yana mata take care, much love Habeeb-Qalby. Wannan ya tsaya mun a rai, ya tabbatar min Ya Omar ya dade da rufe shafi na a rayuwar sa, ya dade da gina sabuwar rayuwa wadda babu ni Boddo a cikin ta.

“Allah sarki rayuwa!”.

Na fada cikin tausaya wa kai. Ina jijjiga kai na da karfi ina hawaye cikin wani hali na kaka-nikayi.

Omar bai katse ni ba, ya bar ni na yi ta sambatuna da kaico-kaicona. Wasu in gyada kai, wasu in share hawaye, wasu in ciji yatsa. A karshe na koma sauke ajiyar zuciya a jejjere irin ta wanda ya ci kuka har ya gode wa Allah.

Farin hankicin sa ya zaro daga aljihunsa ya miko min, “Amshi goge hawayen, ki bar kukan haka Boddo tunda har Allah ya hada mu a inda dukkanin mu ba mu zata ba, to yana nufin kawo karshen matsalolin mu, gyara tsakanin mu da iyayen mu da gyara lahirar mu, ba sai kin fada ba, “labarin zuciya a tambayi fuska”.

“How is he? Where is he now?”

“Ya kulle ni a gida wata tara, ko kofar gida ban taka ba tun zuwa na Istanbul. Ko waya bai bar ni na I da su Young Abba ba. Hamzah da na sani a baya mai gudun bacin raina, yanzu ba shi ba ne, burin wannan Hamzan na yanzu shine kawai in cika masa gida da‘ya’ya, ni da ganin nawa iyayen kuwa ko oho. Auren mu ya zo da obstacles da dama, muhimmi shi ne, Hamzah ba a haife shi cikin addinin musulunci ba”.

(Ina ganin yadda idanun Ya Omar suka kara girma suka firfito waje).

Na gyada masa kai in affirmation, “Daga baya ya karbi shahada a hannun su Young Abba, ya musulunta sannan muka yi aure. Na saka a raina wannan shi ne jihadin da Ubangiji ke so in yi da Ya sallado shi cikin mafarkai na shi ya sa har kullum nake godiya da kaddara ta, domin alkawarin da Ubangiji ya yi ta hanya ta Hamzah zai musulunta ya cika. Duk da cewa ya kasa coping da komai na musulunci yadda ya kamata, har gobe har kuma jibi Hamza na shan giya Ya Omar, har in ta kai masa karo ya doke ni ko ya mare ni”.

Tsigar jikin Omar ta shiga tashi, idanun sa suka kankance daga girman su, ya ce, “Duka? Wane irin duka?”

Na ce, “Dukan mai sauki ne ai Ya Omar, babbar damuwar ita ce, ya raba ni da kowa yanzu, ya ce ni da iyaye na sai na haifa masa yara biyar. Don wai Young Abba ba ya so mu haihu tare kasancewar sa AS ni ma AS, Hamzah ya kawo ni nan kasar ne don kada iyaye na su raba mu. Sallah, azumi duka ba ya iya su, shan barasa kamar shan ruwan famfo, na rasa yadda zan yi Ya Omar. Ba ni da wanda zan gaya wa ya taimaka min ko da da shawara ce, Anty Nasara ce kawai to itama yanzu bama communicating don hatta wayar hannuna ya kwace. Rabo na da rike waya yanzu watanni tara kenan cif”.

“Wannan selfishness ne, kuma mugunta ne. Huhh! Koda yake zabin ki ne, shi kuma irin nasa salon soyayyar kenan? Anya Boddo mai son ka zai iya raba ka da iyayen ka for his own benefits? Sai ya hana ki samun albarkar iyaye ne za ki haihu? Ana hana masu wannan genotype din yin aure ku me ya kai ku yin aure babu bincike kamar wadanda basu je makaranta ba?”

Ina girgiza kai na ce, “Kaddarar mu ce ta zo a haka Ya Omar, na kuma karbe ta hannu bibbiyu idan jarrabawa ce ina rokon Allah ya ba ni ikon cinye ta”.

“Babu ruwan kaddara, ke ki ka kai kan ki sabida kafiya, taurin kai da nacinki a kan abin da ki ke so maimakon ki yi addu’ar zabin alkhairi. A irin kafiya da rashin biyayyar da ki ka gwada mana na tabbata wata babbar jarrabawa ke kiranki. That’s why I stepped away from your life, na barki ki je duniya ta koya miki hankali, ba kuma baki ko mugun fata na yi miki ba, a’a, as long as za mu bar zuciya tana driving and controlling emotions dinmu, a reality irin na rayuwa, we must bear the consequences.

Na taba jin lokacin da Ummati ta buge miki baki da ki ke addu’ar Allah ya ba ki zabinki ko ta halin kaka. Ta ce, Boddo wace irin addu’ar wofi ce wannan? Kada in kara jin kin yi irinta… bana jin a lokacin kin saurare ta ko kin dauki gyaran da ta yi miki da muhimmanci.

Boddo kin yi wauta mai yawa, kin kuma zalunci kanki domin ni da Abba ba ki zalunce mu da komai ba, ban da raba mu da Boddon mu sanyin idaniyar mu da ki ka yi. Amma a gare ni Allah ya yi min sauyi da mafi alkhairi a gare ni, tunda ya ba ni KAUSAR a lokacin da nake matukar bukatar ganin wanda zai so ni a duniya tunda Boddo ta kasa so na… har guba ta sha don kar ta aure ni… Let me confess, kin karya min zuciya a wannan lokacin har nake tunanin duk duniya ba macen da za ta so ni saboda kawai ni fari ne ba baki ba?

Ko shekara ba a rufa ba na samu wadda ke sona fiye da son da ta ke yi wa nata ran.

She made me who I’m today! A successful Omar, ba ni da abin da zan ce wa Kausar sai Allah ya bar mu tare cikin alherinSa har zuwa ranar da muka daina numfashi”.

Wani abu mai kama da makwallato ya zo ya tokare ni, amma on which ground zan ji haushin matar da ta so Ya Omar ta tallafe shi a sanda ni na ce da aurensa gara shekawa lahira? Kai na tafka babban kuskure wauta da asara irin wanda ba zan taba iya gyarawa ba.

Kuka na ci gaba da sheka masa ina fadin, “Ya Omar, ka yarda ban yi don kiyayyah ba, na yi ne karkashin kuruciya, ajizanci da kaddarori na da ke jana zuwa ga gidan radiyon VOA, wadanda ba zan iya tsallake su ba tunda Allah ya riga ya rubuta min su, ya rubuta cewa Hamzah zai yi shahadah, amma a hannu na. This is my fate, my unvoidable destiny Ya Omar, yanzu dai ka ba ni mafita, ka kuma tafi da ni gidanka har mu samu hanyar komawa gida”.

“Haram alaini! In dauki matar mutum in kai gida na in boye, wallahi in ya kai karata a kasar nan sai buzu na. In kuwa ni aka yi wa haka Allah kadai ya san hukuncin da zan yi wa amutum. Now, tell me, what are your major problems mu yi tunanin hanyar gyara su, mu kuma bi shi a hankali har ya yarda mu tafi gidan bakidayanmu har da shi mu je mu fuskanci hukuncin Abba bakidayan mu?

Ba ke kadai ki ka yi wa Abba laifi ba, duk da cewa ina masa email ina gaya masa cewa ina nan lafiya, but ina yi ne ta hanyar da ba zai iya maido min reply ba (noreplay email). Na yi alkawarin komawa gida only when you meet your Dream Husband, marry him and fulfil your dreams, and…quench the  love that’s burning inside you!”

Ban san sanda na  fada masa ba, ina fadi cikin kuka na garari da nadama.

“Ya Omar, na yarda a duniya babu mai kaunata, babu kuna wanda ya san ciwo na kamar ka. Idan haka ne ka yi hakuri mu yi bearing consequences din SAKACI na tare mu gudu gida…ko me Hamzah zai mana”.

“Boddo am, daga ni ke matar aure ce fa, da da yanzu ba daya ba ne, sakaltacciyar Ummati kawai”.

Na janye jikina na koma gefe ina ta girza kuka, “Wallahi ba zan bar motar ka ba Ya Omar. Daga nan sai inda mai ya kare min, don ko a fiffike gida zan tafi, ya yi ta rikon passport dina har ranar busa kaho”.

“Take it easy Boddo na, da yardan Allah za mu je gida, amma da yardar mijin ki kuma tare da shi, tunda ba sakin ki ya yi ba…”

“Ya Omar ba za ka gane ya ya zama da wanda ya kasa kiyaye addini yake ba. Ba ya sallah kullum, ba ya iya azumi yadda ya kamata, ba ya wankan janaba sai sai ya ga dama, ga shan barasa… wannan shi ne Dream Husband dina ni Siyama!”. Na kifa kai a kan tafukana ina kuka mai tsanani.

Kuka na ya soma karya zuciyar Omar ya ce, “Boddo saurare ni tunda har Hamzah ya yi mai wuyar ya karbi shahada we will all over come it, a hankali za mu gyara shi, sai ko idan kin daina son Hamzahn VOA. A yadda na samu labari ke da shi kun gina wonderful love affair mai ban sha’awa, na kuma samu labarin cewa, he’s a very nice guy and kindhearted gentleman, so in har ba kin tabbatar wa kanki kin daina son mijin ki ba ne Boddo, wanda na san ya fi kana da (impossible) a ce hakan ta faru. To ki jure, ki kuma taimaka masa ya gyara lahirar sa.

Wanda zai iya barin addinin sa na iyaye da kakanni don ya same ki ya rayu da ke, shi ma masoyi ne na hakika Boddo. Amma kuma dan Adam ne shi ma wanda bai fi karfin shaidan da jarrabawar imani ba.

Da yardar Allah nan ba da jimawa ba ZA MU GYARA HAMZAH NI DA BODDO NA!”

Omar ya fadi cikin murmushin tausayin Boddon sa, duk wani haushinta da rike ta a rai da ya yi a baya ya samu yana melting. Ya yarda kaddarar ta da Hamzah babba ce. Ya dubi yadda nake share hawaye da gefen gyale na a zaman nan da na yi a gaban sa na zubda hawaye ya kai cikin bokiti, wanda ke nuna Boddo ta yi nadama, ta kuma yi dakacen biyewa mafarkai da burikan ta.

Omar ya dade yana lallashina, yana gaya min kalamansa da na yi missing shekara da shekaru, wato gabanin ko me zai ce sai ya ce, “Boddo am, Boddo na”, hakika my heart is melting da wannan salon kulawar tasa da ya ke min tun ina karama wadda na rasa gardin cikin ta for so long sai yau.

Wayar Omar ta yi kara, da tune din dazu wanda zuwa yanzu na tabbatar na matar sa ne. Wani malolon bakin ciki da kishi ya zo ya kara tokare ni a makoshi, musamman da ya daga ya ke amsawa da dukkan attention da kuma dukkan kulawar duniyar nan (kada dai Boddo yau kishin Omar ki ke), zuciyata ta tambaya, na yi hamzarin kwabarta da cewa, “Eh, kishi ne, amma irin na wata banza ta kwace min kulawar Yaya na, ba kishi na soyayya ba. So guda daya ne tak! Kuma na tabbata yana can inda yake.

Ya Omar ya rufe wayar yana cewa, “Ba ki tambaye ni inda na hadu da sanyin idaniya ta Kausar ba”. Da sauri na ce, “Ba damuwa ta ba ne wannan, damuwa ta ita ce in ga dan uwana a raye, kuma lafiya kalau. Alhamdu lillahi tunda na same shi a raye, healthy and vibrant”.

Omar ya hau  dariya yana fadin, “Ba ki da wannan hujjar, kamata ya yi ki gode mata ta tallafe ni a sanda ki ka yasar da ni a kwalbati. Ta ba ni mafaka inda na yi mourning kaddara ta ta Boddo ba ta sona. A karshe kuma ta aure ni a cikin girma da daukaka ba tare da kowa nawa ya bayyana gare ta ba. Ni shege ne ko ban da asali ba ta sani ba. Ba ta san komi a kaina ba sai kwalayen karatuna da nake tare da su.

So in ba ki gode mata ba Boddo, ba ki da hujjar kishi da ita. Kishin naki wanda bai da madafa…bai da alqibla”.

Yakarasa da dariya, ni kuma na tamke fuska, na ce, “One thing da ba zan tambaye ka ba bayan rabuwarmu shi ne, yadda ka gamu da ita. Bayan wannan zan so sanin komai da ya faru a dalilin barin ka gida da yadda aka yi ka samu kan ka a Amurka da nan Istanbul kuma”.

Cikin mamaki Ya Omar ya ce, “Who told you na taba zaman Amurka?”

Na ce, “Yadda ka yi ka binciko nawa labarin har ka san sunan Hamzah da inda yake, haka ni ma na yi na sani”.

Ya Omar ya bugi sitiyarin sa cikin dariya ya ce, “This is amazing. Da gaske na zauna a Wishington for long, na yi aiki da babban bankin JP Morgan, amma wallahi na zabi zaman kasar ne sabida na san a can ki ke.

Na zauna a Amurka ina monitaring duk wani takun rayuwar ki ta hanyar Antin ki. Amma wallahi har inda nan ke motsi ba ta san ina Hamzah ya gudu da ke ba, kuma ba ta taba gaya min matsalolin sa ba. Wanda na san ba za ki kasa gaya mata ba. Ta yi keeping secret din auren ki”.

Na ce, “Lallai ma Anti Nasara, wato all these while ta san inda ka ke amma shi ne ta yi min badda kama. Har da ita fa muka je nemanka a bankin da ka ke aiki din”.

Dariya ya yi, ya ce, “Ita ta gaya min za ku zo, kuma ni na sa abokina ya gaya muku hakan. Cewa na koma UK. Daga ni har ita har Young Abba muna bayan ki rayu da wanda ki ke so, in ya so ki yi bearing all the consequences ta haka ne kawai za ki bambance aya da tsakuwa na abinda in za a shekara dubu ana nusar da ke ba za ki taba ganewa ba”.

Na yi kuka na gaji na koma hadiyar zuciya, na ce, “Wato, you people have been fooling and playing with my senses for all this while. Har Young Abba ya san inda ka ke? Kun yi wasa da zuciya ta, kun wahalar da ni”.

Na ci gaba da kuka, ina cewa, “Ban taba regretting auren Hamzah ba, kuma har abada ba zan yi ba, domin na yarda shi din kaddarar rayuwata ne. Kuma zanannen abu ne daga Ubangijin mu. Amma na yi nadamar abin da na yi wa Abba, na yi kewar sa yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba. Na tuba na bi Allah na bi ku, ku kai ni gare shi ya yanke min duk hukuncin da ya ga dama, rayuwa makaranta mai azuzuwa iri daban-daban ta koya min hankali mai yawa. Yau idan Abba ya ce in bar Hamzah, wallahi zan bar shi. Idan ya ce in ci gaba da zama da shi, to kuwa ba dai a yadda yake yanzu ba.

I have learned my lessons, I’ve learned a lot; ba ka isa shiryar da wanda Allah bai shiryar ba sai dai ka dora shi a hanya. Ruwan sa ne ya bi, ko ya ki bi as well. Shiriya tana hannun Allah”.

Ya Omar na ta dariya ya ce, “Shaikhana Boddo na, Boddon Hamzah, Azumin Ummati, Siyaman VOA, wato utaziya kika koma ke a Amurkan. Allah ya kara hasken makaranta”.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 59Sakacin Waye? 61 >>

1 thought on “Sakacin Waye? 60”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×