Skip to content
Part 61 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Omar ta koma tsokanata ko ta ina, yana fadin, in je in ci gaba da shan soyayya kawai, shi ba yanzu zai je Najeriya ba, ya kawo matarsa asibiti ne a MEDICANIA tana da matsala ne tun kafin haihuwar first born dinsu.

“Ya Omar kana da Da ashe?” Na fada excitedly, wasu hawaye na son kara tsarto min, ya ce, “Aryan ba, yana nan a gida yanzu haka, a five year old charming boy, kin ce ba kya son jin yadda na hadu da Soulmate dita balle yadda muka samu Aryan da kyar da sidin ludayi ta hanyar artificial insemination”.

Da sauri na dubi Ya Omar kafin na tambaye shi, “Kai ko ita? Wa ke da matsalar infertility?”

Omar ya sadda kansa kasa kamar yana jin kunyar idanuna, a karshe ya ce, “This is not the right time to talk about this Boddo. Amma a takaice matata na da matsalar mahaifa da ake kira endometriosis mun zo Turkiya ne za a yi mata aiki wato (surgery) don ta samu ta dinga iya daukar ciki da kan ta”.

A wannan ‘yan awannin ni da Ya Omar have talked extensively on each other a kan rayuwar kowannen mu da abokin rayuwar sa. Har maganar genotype din mu na kara gaya masa. Omar wasagain shocked, ya ce a kasa irin Amurka aka barku ku ka yi aure kuma? Kodayake Boddo da Dream Husband dinta ne they are meant for each other, bana jin ko an yi test din before, kuma result ya nuna AS-AS za ki qi auren Hamzah a irin jarabar ki a kan sa. Soyayyarku is extraordinary. Yanzu wanne mataki kuka dauka a kan haihuwa?” Nan nake kara labarta masa cikakken abin da ya faru tsakanin Young Abba da Hamzah a kan hakan, wanda shi ne dalilin Hamzah na sato ni nan kada su hana mu haihuwa ko Abba ya raba mu, yace shi yana son ‘ya’yan a duk yadda Allah zai bashi su.”.

Na labarta masa komai har haihuwata ta farko da komawar dan. Da yadda Hamzah ya dauki hukuncin Young Abba da matukar zafi. Wanda nake tunanin kamar ya samu depression a kan hakan, tun daga lokacin shan giyarsa ya karu, wasa da sallah ya karu, Azumi ba ya iyawa idan kuwa na ce ya zauna in koya masa karatun alqur’ani, yanzun nan zai kirkiro abin da zai sa ya bar min gidan. Na ce, “Ya Omar ban daina son sa ba, amma rashin kiyaye addinin kamar yadda na zatar masa ya sanya ya fita kaina. Yet har duniya ta nade he will forever remain apple of my eyes (the one I love most). Amma wallahi na zabi Abba da shi yanzu. Duk hukuncin da Abba ya yanke a kan aure na shi zan bi. Ka taimake ni Ya Omar ka sada ni da Abbana ko na samu farin ciki a karshen rayuwa ta”.

Kuka na ya dawo sabo ina ta rokon Ya Omar don Allah don Annabi ya kai ni ga Abba ko a mace ko a raye.

“Cool down Boddo, take everything easy. In sha Allahu za mu koma gida, amma ba ta hanyar da ki ke nufi ba. Hamzah mai sonki ne, kuma mai kaunar ki ne, duk da zan iya cewa ya so kan sa, sannan rayuwar sa za ta kara jagulewa fiye da yadda ta ke a yanzu idan kika gujeshi a wannan yanayin. Daure ki karasa jihadin ki Boddo. And I promised to stand by you cikin kowanne hawa da sauka, amma daga yanzu “ZA MU GYARA HAMZAH NI DA BODDO NA!”.

Na dubi Ya Omar idanuna cike da hawayen kaunar dan uwana, “my brother like no other”. Ya gyada min kai cikin tabbatar da abinda na ce din, da murmushin kara karfin gwiwa makale a siririyar fatar bakin sa, ya ce, “Now, tell me me ya kawo ku asibiti?”

Na ce, “Na fi danganta zuwana asibiti yau da rabon haduwa da kai. Domin kuwa na kusa shekara cikin Istanbul ko kofar gida Hamzah bai bar ni na taka ba. Amma da yake Allah ya nufa yau zan ga Ya Omar bayan gushewar shekaru takwas ga shi ya fito da ni da kan sa. Awo muka zo Ya Omar, I’m P!”. Na karasa fadar P din da murya can kasa cikin jin kunya. Har da rufe ido da hannaye na.

Ya Omar ya hau dariya, ya ce, “I’m P, means I’m Pregnant. Ku gode wa Allah ku ya ba ku haihuwar ta hanya mai sauki, jinya da abin daukar nauyinta duk na Allah ne, ina tare da Hamzah Mawonmase a nan. Ba na bayan family planning ko adoption ko sau daya, in kin ji wahalar da muka sha da dogon series din asibitoci da muka yi ta bi kafin mu samu a dasa mana Aryan a mahaifa, da abinda muka kashe sai imani da tsoron Allah ya kama ki. Kin yarda dukiya ba ta bada Da, sannan cuta da maganinta duka na Allah ne. Young Abba ya yi kuskure a nan kodayake da ma shi flaws dinsa kenan komai ya fi bada karfi a kan fadar Turawa. Me Doctor da ya duba ki ya ce yanzu?”

“Abin da suka ce shi ne, regarding our genotype ni da miji na, kuma I’m currently pregnant, za su yi amfani da equipments din su su gano shin baby sickler ne ko carrier ko kuma normal? Daga nan za su ba mu option, za mu bari mu haifa and bear all the consequences? Ko kuwa za mu yi terminating pregnancy din?

Sunan test din da suka tura ni in yi yanzu ‘AMNIOCENTESES’ kuma Hamzah ya bai wa likita amsa cewa, ba ya bukatar wannan test din, ko a yaya dan sa ya zo yana godiyar Ubangiji ba zaitabazubar da ciki saboda gudun lalura ba”.

“You see… This is pure love… ki gode wa Allah all the way, even though Hamzah na da flaws, to fa yana da nasa qualities din, babu dan Adam din da ba tara ba ne bai kai goma ba.

Abin da za mu yi tunani yanzu shi ne, hanyoyin gyara dabi’un Hamzah kafin mu kai shi gaban Abbah. Now, take this, ki boye kada ki bari ya gani tunda kin ce ya hana ki rike waya, bana so ya san kin gan ni, hakan zai hana shi kwanciyar hankali ya yi tunanin za mu dauke ki tunda ya riga ya saka wa ransa hakan, ya riga ya saka shakku a ransa a kan kaunar da iyayenki ke masa.

A hankali za mu gyara komai. In ya fita aiki sai ki kira ni ko ki yi flashing sai ni in kira ki, I will be crediting your phone and  I will keep telling you how to carry him along in a very nice and polite way…”. Hawayen da nake tattali na kaunar dan uwa na suka balle min.

Omar ya ce, “Kada ki yi kuka, komai ya faru da sanin Allah we must bear all the consequences of your negligence together, don mu ma mun yi kuskuren fahimtar ki a wancan lokacin, thinking that you are mentally instable ashe… ashe lafiyar ki kalau. ‘Yar baiwa ce mai ganin mijinta cikin mafarkin ta”.

Dariya na kama yi ga hawaye face-face a fuskata.

“Ya Omar so nake in rungume ka ko ya ya ne, in ji cewa ba mafarki nake ba cikin ire-iren mafarkai na da ba sa karewa”.

Hawayen suka kara kwance mini, “I missed you Ya Omar. Had I know abin da na aikata zai sa ka bar gida for good 8 years na rantse da Allah da ban aikata ba. Ba don ina kinka na sha poison ba sai don in samu Abba ya bar ni in tsira da mafarkina which now I realized ba karamar wauta na tafka ba.

Hamzah bai taba betraying soyayya ta ba, amma ya yi min gori Ya Omar, shi da kan sa ya goranta min rashin biyayya ga iyaye, wanda har abada ni ma ba zan yafe wa kaina ba Ya Omar, sai lokacin da Abba ya yanke hukuncin da ya ga dama ga rayuwa ta”.

“You will not do that (rungumar sa) matar aure ce ke, kuma ni ba maharramin ki ba ne tunda akwai aure tsakanin mu. Thank you for the love shown to your brother I thank Allah tunda kin dawo cikin hayyacin ki, for now kin fahimci abin da kowa yake so ki fahimta shi ke nan the game is over sai neman hanyar gyara komai”. In ji Ya Omar.

Ya isa haka daina kuka Boddo, komai zai zama daidai cikin yardar Ubangiji. Now, mu je in maida ke asibitin kada ya koma ba kya nan”.

Na ce, “Ka ajiye ni a gate zan karasa ciki da kafata, don ban sani ba ko ya dawo yanzu, in ya ce bai gan ni ba zan ce na zaga neman abin da zan ci ne, ina jin yunwa”.

Hakan kuwa aka yi, na boye wayar da Ya Omar ya ba ni cikin wayoyinsa guda uku a habar zani na bayan na yi switching dinta off”.

Ya ajiye ni kofar shiga ‘Medicania’ na fita daga motar ina waiwayen sa ina hawaye. Ji nake kamar zai kara bace min, kamar rabuwar kenan again, kamar in ya tafi kara guduwa zai ba zai dawo ba.

Kamar Ya Omar ya san tunanin da nake yi ya ce, “Trust me Boddo, I’m going no where, shaaa, I’m here for you now!”.

Gwiwoyi na na ji sun yi wani irin kwari, na juya da azama da farin ciki na shige asibitin.

Ina shiga waiting lounge na ganin likita na ga Hamzah a zaune ya rafka tagumi, ya rasa inda zai sa ransa. Ya fi sakawa ransa Boddo ta gudu, amma ta gudu ta je ina babu passport? Ya kasa ko da tambayar masu kula da shigar patients ofishin likita saboda tashin hankalin kada ta gaya masa abin da yake tsoron ji, wato fita ta yi.

Ya fi karfin mintuna talatin a wannan halin na zaman shiru da tagumi da tsinkewar zuciya, mai yiwuwa inda likita zai auna jinin sa cikin wannan halin zai tarar ba makawa ya haura 120. cikin wannan halin ya ji kamshin turare na cikin hancin sa, ya kuma ji an dafa kafadar sa.

Idanun sun yi jazir sun kuma kankance ya dago su yana kallo na. Murmushi na yi masa from ear to ear irin wanda na dadae ban yi ba, na ce, “Shaheed ka dawo? Sorry na dan zagaya ne in motsa kafafuna kafin layi ya zo kaina, ka kulle ni for almost a year, kafata har ciwo take min, in kuma nemi pizza in ci don yunwa nake ji Baby sai juyi yake min”.

Wata ajiyar zuciyar ba-zata ce ta kwace wa Hamzah Mawonmase. At least Siyam ba ta gudu ba, duk da abin da ya yi mata wanda ya fi dacewa da a kira shi ‘yaudara zuwa Istanbul’ yaushe rabon da ta kira shi da Shaheed ko Habeeby, yaushe… yaushe?

Ji ya yi kwallar so da tausayin ta ta ciko idanun sa. Da gaske a lokacin bashi da zabi banda yi mata wannan wayon.

“Amma da kin gaya min kina son cin Pizzan ai kin san zan nemo in kawo miki ko? Sai ki bar ni cikin tashin hankali da tunanin kin gudu? Na kusa kamuwa da ciwon zuciya cikin mintuna talatin Habeebty. Don Allah kada ki kara yi min irin wannan zai iya sa wa zuciyata ta buga”.

“Forgive me Shaheed. Ka san abun ka da mai juna biyu in muka so cin abu kamar Da ne ya so fitowa cikin mahaifiyar sa, so na zaga ko ina a asibitin ban ga wajen cin Pizza din ba, shi ne na dawo.

Na san yanzu sai dai kuma mu dawo gobe kuma layin ya wuce kai na”.

Ya mike tare da kama hannuna muka jero zuwa parking lot. Ya bude min murfin mota na shiga ya rufe, ya zagaya ya shiga side dinsa ya kunna motar ya yi reverse muka harba kan titi.

Na dauka gida muka nufa, sai na ga ya nufi wani shahararren Pizza Hut a kan hanya, muka shiga ya yi mana order. Muka samu kujera can nesa da mutane muka zauna muna jira kafin a kawo Hamzah ya kura min ido, ya ce, “Siyam you are looking happier then ever what’s the secret of this sudden happiness?”

Wani murmushi na saki wanda rabona da yin irin sa na manta, na ce, “abu daya nake tunani shi ne, ga shi na haifa mana Baby na kai shi DAAR AL- ULOOM AL-MADANIYYAH tun daga shekarun farko na fara karatun yaro, da yake akwai Nursery a ciki. And ina ganin idan na haihu ka zama Daddy za ka daina abubuwa da yawa albarkacin yaro ko yarinyar mu. Ba za ka so dan ka ya tashi yana ganin ka kullum cikin buguwa (intoxication) ba. Ba za ka so ya gane ba ka son yin sallah ba sai ka ga dama. Ba za ka so ya gane kowa yana azumi kai kana cin abinci ba wani lokacin ba. Ba za ka so ma ya san asali can-can kai ba musulmi ba ne in ya tashi ya gan ka kam-kam cikin addini, ba za ka so ya san ka tashi in chrisitianity ba shi yasa ka ke shan giya. Ba za ka so ya san ba ka wankan janaba ba…sai na matsa maka, all these flaws Hamzah frustrates and irritates me, suna wahalar da ni, suna cutar da zuciyata, Allah me ya kiyaye da zuwa yanzu na kamu da ciwon zuciya ka san cewa son da nake maka daga Allah ne, Shi ya dora min ba ni na sanya wa kaina ba…”

Kuka ya kwace min, na ce, “Mawonmase I’m sorry to say idan na haihu ba ka daina duk wadannan ba zan zabi rabuwa da kai ne ko bana so, ba kuma don in auaari Ya Omar ko wanin sa ba a’ah, zan je ne gaban Abba in raini abin da Allah ya ba ni as a single parenthood don ba zan iya sake aure ba…”.

Hamzah ya sa tafin hannun damansa ya toshe min baki, ya ce, “Da yardar Ubangiji Siyam you will never be a single mother. You will never marry someone because of my flaws. Da yardar Allah yaro ko yarinyata ba za su taso su tarar da ni ina aikata dayan wadannan kazantar ba. Na yi alkawarin fara gyarawa daga yau, na yi alkawari”.

Na kama hannayen sa na rike gamgam ina kuka ina dariya, ya ce, “Insha Allahu, kin daina kuka a kan bakin ciki na. I will endevour to become a good moslem, kuma zan ajiye komai in shiga makarantar musulunci da zarar kin haihu. Yanzun ma don bana son yin nisa da ke ne cikin wannan halin da na nema na tafi…”.

“Hamzah ina zani in goya ka yau? Duk da wai sun ce namiji ba dan goyo ba ne, ni zan goya nawa Hamzahn in nuna wa duniya na yarda da abin da ya ce min yau ko da ba da gaske yake ba, ko da ba abin da ke cikin zuciyar sa kenan ba. Koda ya fada ne kawai don yasa murmushi a kan fuska ta. You made my day… I … I…”.

Na kasa karasawa sabida kukan farin ciki da ya ci karfi na.

“I love you Siyam, ki yafe mini bacin ran da nake saka ki. I love you Habeebty, and will forever love you till my last breath Ina sonki SIYAMAH. (My Damsel S. ZINARIYATA S.)”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 60Sakacin Waye? 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×