Skip to content
Part 59 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Idan yau ya yi azumi ya kai da kyar, ya yi buda baki da barasa, gobe sai ya ce hutawa zai yi, har da cewa, sanda yake Christianity ma ba ya iya nasu azumin na kwana hudu ko na daga safe zuwa hantsi da suke yi.

“Siyam, I cannot kill myself with hunger, inakokari fa, ke ce ba kya ganin kokarin nawa”. Ya fada, yau da na kama shi ya buya a kitchen yana daddakar ruwa. Rasa me zan ce masa na yi, sai kawai na juya na bar kitchen din.

Hamza ya biyo bayana da sassarfa yana cewa.

“In ki ka dau fushi da ni shi zai sa gobe in kasa. In ba ki yi fushi ba na yi miki alkawarin gobe zan yi.

Wallahi sau dubu gara sallah a kan azumi. Na miki alkawarin zan dinga sallah daga yau in ban manta ba, amma azumi ina yi ina hutawa kada ulcer ta kama ni. Ba zan iya hora kaina da yunwa ba. I’m not that jarumi at all, amma na miki alkawarin zan daure in dinga sallah a madadin sa tunda ayyukan ibadar kala-kala ne babu laifi in ka yi wani ka bar wani”.

“A wace ruwayar aka gaya maka haka? Kuma wane malamin ne ya gaya maka wannan fatawar? Ni kam na gaji da cewa ka koma islamiyyah, na yi kadan in zama malamar da ake tunanin zan iya zama a kan ka, saboda you are not keeping your promises”.

Ya ce, “Sai ki min uzuri da ajizanci irin na dan Adam, amma wallahi ina kokari, kawai ke ce ba kya ganin kokari na kullum sai weakness dina ki ke iya hangowa”.

Daga ranar na koma kunna masa wa’azi na koyarwar musulunci wanda balaraben malamin nan mai farin jini wato “Mufty Ismael Menk” ke yi a tasoshin kasashen duniya da harshen turanci, muddin na gan shi a zaune a falo ko da aiki yake a system din sa, zan kunna masa karatun Alkur’ani na kira’ar Mahir SALAH BUKARTI ko wa’azin Shekh Mufty, wanda yake yi a kan darussa daban-daban na addinin musulunci, tun daga kan tsarki, wajibcin sallah da azumi da zakkah ga musulmi da sauran su. Kuma idan na kunna sai na nemi kujera in yi zamana don ta tabbatar yana sauraron wa’azin ko a’ah?

A wasu lokutan ya kan ce, “Siyam, canza tasha mana. Kullum Mufty Menky? In don ni ki ke kunna wa’azin nan na ce miki zan daure in dinga sallah, azumi ne sai a hankali zan koya”.

Na ce, “Ba ka da uzuri a wurin Ubangiji, tunda an gaya maka wajibcinsu kafin a ba ka shahada kuma ka ce ka ji ka gani za ka jure. Ba fa takura maka nake yi ba Hamzah, kawai ina so ne mu tsira tare, mu tashi tare ranar alqiyamah matsayin mata da miji, kada Allah ya kwace ni a aljanna ya ba ni ‘Zaujil Eeni’, kai kuma ka hadu da fushinSa da matar ka a wutar Sa’irah”.

Ya dan yi kasake, daga aikin da yake yi a kwamfutar laptop din sa yana sauraro na, daidai lokacin da Mufty Menk ke fadin hukuncin masu shan azumi da gangan, da masu dauka suna karyawa da gangan, da kuma wadanda ba sa yi ma kwata-kwata sabida raki.

Hamzah ya dade cikin halin shiru yana sauraron shaihin malamin, wanda ke yin laccarshi cikin tsaftataccen turanci.

Daga ranar na samu ya ci gaba da yin azumin, amma na rasa sunan da zan kira azumin Hamzah, ka yi azumi lafiya har faduwar rana, amma kuma ka bude baki da barasa? Ga kara’in salloli don sai ya dawo ofis yake hada su bakidaya ya yi su at once.

Tun matsalolin sa na damuna har sun zame min jiki. Tun ina hora shi ta hanyar hana shi kaina wai don ya tsaida sallah da sauran ibadodin da suka hau kan sa, har na gaji na bari, na yarda wanda Allah ya shiryar, idan duk duniya za ta taru don batar da shi ba za ta yi nasara ba, haka wanda Allah ya batar, ba mai shirya shi sai Allah, addu’a na koma yi kullum a kan sa, dare da rana ina rokon Allah ya tsayar da zuciyar sa da hankalinsa a kan addinin sa na yanzu.

Wa’azin Shekh Mufty Ismael Menk ban fasa kunnawa ba, in ya dau wani zai bar wani, haka tashar talbijin na daina kunna kowacce sai ta Saudiyyah da ta wa’azozin malamai daban-daban da suke yi da harshen da na tabbata ya fi fahimtar sa fiye da kowanne, wato Hausa da Turanci.

Mun kwashi watanni takwas a kasar Turkiyya ba tare da na ji duriyar kowa nawa ba. Haka sakaci da addini irin na Hamzah sai abin da ya yi gaba, don ba zan ce ya ragu ba. A hakan Allah ya ba ni wani cikin, mai dankaren laulayin tsiya. Hamzah tun yana kulle ni in zai fita aiki ta baya, har ya gaji ya daina don ya lura in ma ya bar gidan a buden ba wani sha’awar fita nake ba.

Na maida hankali na a kan ibada da nema masa shiriya wajen Ubangiji. Lokacin da na gane ina da shigar ciki ta hanyar daukewar al’ada wajen watanni biyu kenan, da yawan kasala daga kwanciya sai kwanciya, ga wani tsinkakken yawu da yake tsirgo min a baki yanzu.

Gane hakan da na yi sai na ja bakina na tsuke, ban gaya masa ina da shi ba, don na san muddin ya sani ba zai kara bari na zaman lafiya ba.

Amma abin ki da mutum mai tsananin kula a kan matar sa, da duk wani motsi nata. Ciki na da watanni hudu ya gano, don tun a lokacin ya fara nuna kan sa.

Ranar da Hamzah ya gane ina da ciki har da kukan sa, wai a cewar sa in bai yi kuka ba ba zai gane yawan farin cikin sa ba. Ya ce, kuma yau ce ranar da zan soma fita cikin birnin Istanbul don tun zuwan mu kulle ni yake yi idan zai fita, ko kofar Estate dinmu da ke cikin TAKSIM SQUARE a ULUS ban taba takawa ba.

Washegari da zai tafi TRT World ya ce in shirya sai ya fara kai ni asibiti an tabbatar masa da lafiya ta data jaririn sa sannan zai wuce aiki, yau da na tako kafa ta a waje bayan kullen sama da watanni tara sai na ji kwallar kewar gida da kowa nawa ta cika idanu na.

Allah kadai ya san halin da suke ciki a kan batar da mu din da Hamzah ya yi, wanda bacin rai ya fi yawa a zaman namu fiye da soyayyar da yake ikirari, idan ma akwai, to ba ta fi cikin cokali ba, saboda duk lokacin da ya ki yin sallah ko ya sha barasa cikin bakin ciki da bacin rai na ke kwana, shima kuma ba zai samu yadda yake so daga gare ni ba, don haka zaman mu a nan bakidaya ba zan karar da soyayya mai dadi a cikin sa ba.

Soyayya da kwanciyar hankali kam mun baro su tun a Miami Resort na birnin Florida dake kasar America, inda duk motsin da na yi zan ji muryar Young Abba da Anti Nasara ko da kuwa a waya ne.

Na fara awo yau a asibitin ‘MEDICANIA’, inda kwararru suka duba ni yadda ya kamata. Aka rubuta min tasa-tasai da zan fara da su, wato (test-test) irin na awon ciki. Hamzah ya kai ni inda zan yi awon jini, ya ce zai je office ya yi reporting ya dawo ya maida ni gida.

Bai zaci haka za mu dade ba da office din zai fara zuwa ya dauko excuse sannan mu zo mu gama duka tests din a tsanake.

Mata guda biyu na tarar a inda aka tanada don jiran kiran likita, ta biyun ita ta fi daukar hankali na don da gani babu tambaya Bahaushiya ko Kanuri ce ‘yar kasar Najeriya.

Ba kasancewarta Bahaushiya ne kadai ya dauki hankali na ba. Wani irin sassanyan kyau ne da ita na bugawa a jarida, wanda cikin mata dubu kafin ka samu goma masu irin sa sai an tona, fatar ta mai tsananin taushin gani a ido, wata irin kyakkyawar choculate colour skin Allah ya hore mata kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, da gayu da aji da kasaita na musamman, a ido ba zata wuce tsarata a shekaru ba, amma nesa ba kusa ba ka kalle ta ka san ta fi ni class irin na ‘ya’yan hutu, in ka kalle ta sau daya sai ka so karawa, ta fi ni samun kwanciyar hankalin rayuwa a ido, sannan ta fi ni gayu da kwalisa.

Tana waya sanda na zauna kusa da ita, amma duk kwakwarka ba za ka ji me ta ke fadi ba saboda yadda ta ke kalmasa harshe tana walainiya da fararen idanunta kadai zai tabbatar maka da masoyinta ta ke wayar nan ko kuwa mijin da babu kamarsa. Na bude hanci sosai ina zuqar wani daddadan turare da ban taba jin turaren mata ma dadi da sanyi da sanyaya ran sa ba.

Nurse ta kira sunanta, KAUSAR SHETTIMA! Ta mike da sauri.

Na bi ta da kallo, hatta takunta mai daukar hankali ne sabida yadda ta ke takawa cikin kasaita tamkar basarakiya. Ga kira da zati na matan manya a tare da ita. Doguwa sambaleliya irin matan Kanuri.

Ba dabi’a ta ba ce bin mutane da kallo, amma matar nan ta tafi da ni da yawa, ta bar ni cikin dakacen “ina ma ni ce ita!”

Kamar an ce in kalli kofar shigowa na juya kai, sai na hango shi yana shigowa reception, yana tafe yana magana cikin wayar hannunsa, sanye da kaftan na danyar shadda Getzner ruwan madara, wadda ta haska jar fatarsa ta fiddo ilhama da cikar zatin sa na bafillacen usuli. Bafillacen ma na Mambilah fulanin da babu irin su duk fadin Najeriya.

Inda nake zaune yake tahowa, ko mutuwa na yi na dawo ba zan kasa shaida Yayana OMAR ba, balle cikin kyakkyawan yanayin da hutu da kwanciyar hankali dana gan shi a ciki. Ta gaba na ya wuce ba tare da ya ankara da ni ba zai shiga ofishin likita.

Da wani irin zafin nama, wanda ban san ina da shi ba na saka hannu na damke gefen rigarsa.

Wanda hakan ya sanya shi wani irin juyowa cikin slow motion. Cikin kowanne hali OMAR GIDADO DALHATU GEMBU ba zai kasa gane BODDON sa ba. Duk da ta yi wani irin zuru-zuru irin na rashin kwanciyar hankali, ta rame idanunta da kusan kullum sai sun yi kuka sun zurma ciki, sun yi zuru-zuru da su a loko.

“YA OMAR!”

Na fada da wata irin murya tamkar an fisgo ta daga makoshi na, sabida da kyar sautin ya iya fitowa, a wani yanayi da yafi gaban farin ciki da mamaki ya zarta excitedness. Yau wace irin ranar sa’a ce a gare ni? Ko ko in ce ranar da ta fi kowacce rana muhimmanci a gare ni tun barowa ta gida? Watanni tara ina cikin gida a kulle, kamar yar fursuna, sai yau na fito, kuma fitowar ta yi min irin wannan sanadin alherin?

Omar ya juyo don ganin wadda ta rike masa riga tamau haka, sai idanunsa cikin na Boddon sa. Wayar hannun sa ta subuce ta fadi ta tarwatse a kasa, ya ce (in exclamation)

“BODDO!”

Iya abin da na ji kenan na yi baya luu! Zan fadi cikin wani hali na uncosciousness. Allah ya so ni a zaune nake da ba shakka na fadi daga kan kafafu na.

Boddon sa ce da gaske, Azumin Ummati, Siyaman Abba. Amma yanayin da ya gan ta ba cikin sa ya yi ta mafarkin ganin ta ba. Boddo da ‘dream husband’ dinta ya yi zaton ganinta cikin kyakkyawan yanayi da madaukakin kwanciyar hankali wanda ya zarta yanayin da ya gan ta a ciki yanzu.

Boddon sa ta rame, duk da nauyin shekaru da ya karu a kan ta kyawunta yana nan. Duk da idanunta da suka yi zuru-zuru kyawun ta bai dushe ba, haskenta bai dakushe ba, tana nan tana sparkling like before, sai dai ba ta cikin nutsuwa da kuma alamun babu kwanciyar hankali a tare da ita.

Na mike na kama Ya Omar a bainar jama’a na kankame ina kuka. Na kasa magana na kasa cewa komai sai kuka mai sauti “yeeeee yeeeee yeeee”. Kowa da ke wajen ya maido hankalin sa a kan mu. Omar ya kalli gaban sa, ya kalli bayan sa ya ga yadda na janyo masa attention din ‘yan asibiti da ma’aikata, sai ya canza harshe ya ce “Boddo am, Boddo yofam ta a moftanam mi himbe tamma don ko mi wanni ma. Salu en dilla, salu nastu mota kin ji Boddo na”. (Boddo sake ni kada ki tara min mutane a dauka wani mugun abin na yi miki, wuce mu je mota mu yi magana kin ji Boddo na).”

Ya kama hannu na muka bar reception din muka fice zuwa parking lot, wata mulmulalliyar bakar mota “BUGATTI” Ya Omar ya bude min na shiga. Cikin azama ya shiga mazauninsa ya tada motar muka fita daga asibitin Medicania da gudun gaske.

Tunda ya hau titi nake kuka ina kururuwa, gabadaya na gigita shi, na firgita shi. A dole ya kashe motar a gefen titi yana fadin.

“Ya isa… ya isa Boddo kin ji… komai ya kare daga yanzu insha Allah tunda yau Allah ya nuna miki ni kin gan ni buya ya kare min kuma… lokacin komawar mu gida dukkan mu ya yi”.

Kuka nake wurjajan na ce, “Hamzah ba zai taba bari na in koma gida nan kusa ba, ka tafi da ni gidanka kawai Ya Omar mu gudu wajen Abba. Na gaji, wallahi na gaji da rayuwa babu ku”.

Dariya Omar ya hau yi, na bude jikakken ido na ina kallon handsome Ya Omar da ya koma wani babban mutun classy, gentle, handsome, ya ce, “Soyayyar kuma fa Boddo? Ina soyayya? Ina labarin soyayya? Ina Dream Husband din ki? Ina Hamzah Mawonmasen din ki kike cewa in gudu dake da auren ki?”

Wayar Omar ta yi kara da wani irin speacial tune, yayin da wani lafiyayyen suna da aka rubuta da harshen Larabci ya bayyana a kan screen din wayar, ‘HALEEB-QALBY (madarar raina) in harshen Hausa.

Omar Gambu, ya daga wayar ya kara a kunnensa yana magana da dukkan kulawa da soyayyar da miji zai iya bai wa matar sa a waya.

“Haleeby kin fito ne?”

“Na fito ban gan ka ba”.

“Har na zo kuma aka kira ni, na fita. Ki zauna a reception ki ba ni one-two hours. I’ll be there in a jiffy”.

Ta ce, “Alright Honey, please hurry and take care”.

“Take care too, much LOVE!”.

Sakin baki, ido da hanci na yi galala ina ji, kuma ina ganin ikon Allah wanda aka ce ba ya taba karewa a duniya. Na dubi Ya Omar, gabadaya ya canza ya zama ingarman mutum mai cikar zati da kamala, ya murje ya yi fresh da shi, fatar nan ta kara komawa jazir da ita kamar ta Balaraben Madina, ga wata ‘yar kwarya-kwaryar kiba da ya ajiye mai nuna zaunawar naira da hutu a jikin sa.

“Ya Omar kai ne kuwa?” Na fada unblievably tun daga karkashin zuciyata.

“Baka kyauta ba ko kankani Ya Omar, tafiyar ka ba ka san abin da ta janyo min wajen Abba ba da baka yi ta ba. Kana fita, ni ma ya kore ni sai Mambillah, na koma can ma na ci ubana a hannun Ummati har sai zuwa lokacin da Allah ya kawo Young Abba, sannan na samu sauyin rayuwa”.

Na ci gaba da kuka ina fadin, “Ya Omar ba ka kyauta wa kowa ba. Da kyar in hawan jini bai kama Abba ba a kan neman ka . Ni kuwa ka gan ni nan a kan korar da ya yi min nake rayuwar gararin zuci da gararin aure har yanzu, tafiyar ka maimakon ta gyara al’amura kamar yadda ka yi zaton itace solution to bata gyara komai ba, instead, damalmala su ta kara yi. Don kuwa kora ta Abba yayi yau kusan shekaru tara yace sai ranar dana nemoka ka dawo zasu yafe mini shi da Ummati.

Ashe kai kana nan hankalin ka a kwance ba abin da ya dame ka, kullum zullumin mu yana bisa halin da ka ke ciki ne. Ashe-ashe kai kana nan kana soyayya da wata madarar ranka???”

Na ci gaba da gunza kuka har da na bakin cikin wai yau a gabana wata banza ce Ya Omar ke kira madarar ransa, ba ni Boddon sa ba. Zuciyata ta yi saurin tambayata cewa, “Kada dai Boddo kin manta baya? Ko kuwa shi ke nan don ke kin ki shi sai duka matan duniya su ki shi as handsome and perfect gentleman as he’s? Wannan rashin adalci irin naki Boddo da me ya yi kama? Kada dai Boddo KISHIN OMAR KI KE? To a wace hujja?”

Da sauri na furta kalmar astagfirullah! Astagfirullah! Astagfirullah”. Har sau uku, zuciya mai kawace-kawace, zuciya mugun nama ta hau kawata min Ya Omar yau, ta shiga gaya min I’m the loser domin kuwa Omar ya fi Hamzah komai da komai yanzu musamman kwarjinin addinin musulunci, (a baya ban taba tsayawa na yi masa kallon nutsuwa ba iri wanda nayi masa yau yana waya da matar sa zan ce ko budurwar sa sabida hankali na da nutsuwa ta basa jiki na a baya suna can ga shirmen mafarkai na kadai). Zuciyar ta cigaba da fada min zan fi samun kwanciyar hankali,, tattali, soyayya da tausayi a tare da Ya Omar tunda shi yana da imani da tsoron Allah a zuciyar sa, yana tsayar da salloli biyar tabbas, yana kuma yin azumi yana bada zakkah sannan dan uwana ne mafi kusanci wanda ya san girman iyaye na. A suffa da zati ma ba za a taba hada su wuri guda ba, domin bafillacen Mambilah da dan kabilar Berom ba za ka taba hada su wajen tsarkin nasaba ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 58Sakacin Waye? 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×