Omar ta koma tsokanata ko ta ina, yana fadin, in je in ci gaba da shan soyayya kawai, shi ba yanzu zai je Najeriya ba, ya kawo matarsa asibiti ne a MEDICANIA tana da matsala ne tun kafin haihuwar first born dinsu.
“Ya Omar kana da Da ashe?” Na fada excitedly, wasu hawaye na son kara tsarto min, ya ce, “Aryan ba, yana nan a gida yanzu haka, a five year old charming boy, kin ce ba kya son jin yadda na hadu da Soulmate dita balle yadda muka samu Aryan da kyar da sidin ludayi ta hanyar artificial insemination. . .