Nan gefena ta zauna ta kwafar min aikin da aka yi duka tace in naje gida in tabbata na yi assignment din, wanda na darasin English ne akan darasin letterwriting (rubutun wasika).”
Tun daga ranar muka wani irin kulle ni da Ko’oje, tunda ta fahimci inada rauni take karfafani, idan na nemi sarewa ta ciccibe ni, tare da taimaka min kullum da rubutu har na fara sabawa da rubutun aji da kai na komin yawan sa da yin assignment.
Idan na koma gida kuma Ya Umar shi yake zama malami na, duk abinda aka koya min a. . .