Ba zan iya tantance how I reacted ga maganganun Abba na ba, bayan wucewar sa saman bene, abinda na sani kawai shine Abba da gaske yake yanzu kam, kan hada mu aure ni da Ya Umar, wanda ke garin Calabar a halin yanzu yana kammala hidimar kasa bayan kammala digirin sa da (first class result) kamar yadda Abba ke masa buri. Na tattara warning din Abba na jiye a gefe don ban dauke shi a matsayin abinda zai dame ni har ya hanani kwanciyar hankali ba, yadda nake da tabbacin Abba na so na kamar yadda yake son kan sa. . .