Skip to content
Part 2 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir Takori

Dr. Amina Mas’ud tana (ward round ) ranar Litinin da safe aka aiko wata nos ta gaya mata Dr. Turaki na kiranta in ta gama abinda take yi. Ta amsa da “toh” a zuciyarta tana fadin ‘this is not his habit (wannan ba dabi’ar sa bace)  kebewa da mata, ko kiran likita yana tsakiyar aiki. It must be important. Kwana biyu basu zo aiki ba saboda ‘election’ (zabe), bayan zabe kuma taje kauye gaida Baffanninta  ta kwana biyu, don haka yau tanada aiki da yawa zai shiga lokacinta gaskiya.

Ta cigaba da zagaya marassa lafiyarta daya bayan daya tana rubutu a files dinsu bayan ta yi musu tambayoyi har ta gama. Sannan ta nufi ofishin consultant din nasu.

Da sallama ta bude kofar ya amsa sannan ta shiga,

“have a seat please Dr. Amina.”

Ta zauna, sannan ta gaisheshi. Ya amsa cikin sakin fuska sannan ya dora bayani.

“Nasan kinsan Engnr. Ma’arouf Ji-qas ko? Ba sai na gabatar dashi a gareki ba?”

“Na fara sanin shi a bakin Yayana Ilya,  na sanshi a kafafen yada labarai tun yana dan majalisa, na kara sanin shi shekaranjiya waccan as the elected governor (matsayin wanda ya lashe kujerar Gwamna). Ka ga kuwa na san shi da yawa. Har kuri’a saida Ilya ya tattagemu muka je muka sa masa nida Goggona.

An shaideshi da cewa mutumin kirki ne. That’s all I know about him. Bayan wannan bansan komai da ya dangance  shi ba.”

“Da kyau. Kin taba sanin yana da (paralysed daughter) mai shekaru biyar?”

“Gaskiya bansani ba. I know nothing concerning his personal life (bansan komai na kebantacciyar rayuwarsa ba. Maybe Ilya ya sani, sabida shige-shigensa da bin kwakkwafinsa a kansa.”

Usman Turaki yayi murmushi.

“To shine yake neman wani taimako daga gareki…. kodayake ta wani fannin baza’a kirashi taimako ba tunda aikinki ne ya gaji hakan, kuma abu ne da ba kyauta zaki yi shi ba. You are on your proffession. Yana so ki koma gidansa da zama ki cigaba da bawa yarinyar sa (treatment) da asibiti ke bata zuwa shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Kinsan dai yadda (paralysis) yake ba abu ne da za’a ce ga ranar tashi ba tunda bashi da kayyadadden lokaci. Yayi alkawarin ninka miki albashin da kike karba daga gwamnati sau hudu a kowanne wata. Duk (weekend) zaki tafi gida ki dawo Monday.

Na yarda da kwarewar ki akan aikinki da sadaukarwa. Shiyasa na zabo ki cikin dubu. A ganina wannan wata hanyar samun alkhairi ce mai dimbin yawa gareki da iyayen ki. Amma zamu baki gajeren lokaci kiyi tunani ki kuma nemi amincewar iyayenki daga yau zuwa gobe saboda  hakan ya bukata, yaya kika gani?”

Amina ta nisa. Tunda ya fara magana bata katse shi ba. Ba rayuwa a ‘government house’ ne abinda ya dadata da kasa ba a’ah, kudin nan da za’a ninninka a bata wadanda in a asibiti ne sai tayi shekaru tana Tarawa,  ba kuma amfanin kanta zatayi dasu ba, burin data dade dashi akan Goggonta zata cika dasu ta huta tarin data soma tun fara aikinta mai bata lokaci da cin rai,  har yau kuma bata tara kwatan abinda take son tarawa ba tunda ba wani dadewa tayi da fara aikin ba, gaskiya ilmi mai zurfi yayi a rayuwa don har abada bazaka daina cin moriyarsa ba. Allah yasa Goggon ta amince.

*****

Amina da Goggonta, tareda Inna Zulai Babar Ilya kuma aminiyar Goggon, da Goggo ta kirawo don ta taya ta jin wannan almara ko kuwa rashin kan-gado da Amina tazo mata da shi.

“In banda rashin kan-gado irin naki Amina, ina hankali na zai kwanta kina kwance wani muhalli daban da nawa, alhalin nasan ban yi miki aure ba?” Goggo ta fada cike da damuwa, muryarta a sanyaye.

Inna Zulai ta ce

“Dama ace aurenki zai yi ne don ki kula da diyar da ya fi armashin ji”.

Amina ta jefawa Inna Zulai harara ta gefen ido, ganin tana tufksa tana kara warware  mata. Amina ta gyara zama.

Goggo akan aikina nake. Mune proffessionals din da ake ‘hiring’  har gida mu kula da mai lalurar  shanyewar barin jiki ‘if a person can afford (idan mutum zai iya biya). Sannan ban bar aikina na gwamnati ba za’a bada aro na na shekara daya ne in daina karbar albashin gwamnati in karbi na wadanda suka haye ni. Ki kwantar da hankalinki Goggo duk karshen sati zan taho gida in koma Lahadi da yamma. Sannan fa akwai matar aure a gidan. Kuma Goggo gidan gwamnati ya wuce duk yadda kike tsammani. Girmansa da fadinsa in ba kai ka nemi mutum ba ba abinda zai hada ku. Albashina za’a ninka sau hudu Goggo bada jimawa ba Allah zai cika min burin dana ke dashi akan ki. Ki barni nayi aikina Goggo in har kin yarda akan-kanki cewa kin bani tarbiyyya yadda ya kamata. Duk inda na shiga zan iya kula da kaina Goggo, zan nuna tarbiyyar da kika yi min da yardar Ubangiji bazan baki kunya ba. Hakan bazai yiwu ba ba tareda na samu goyon baya, kwarin gwiwa da albarkar ki ba Goggo.

Shekaru bakwai ina karatu a Jami’a wbaki taba samun wani abin Allah wadai daga gareni ba, sai don zan je aiki na shekara daya duk karshen mako ina tare da ke? Da zanyi hidimar kasa Gombe na tafi, duk baki nuna damuwa ba goggo sai wannan da muke cikin gari daya?”

Goggo ta nisa, “Amina mutane da halayen su canzawa suke kamar wahainiya in suka samu daular duniya, ina tsoron ki da shiga daular nan Amina kada halayen ki da tarbiyyar ki su canza…”

Kafin Amina tace komai Ilya yayi sallama ya shigo. Amina ta gode Allah a zuciyar ta don ta tabbata mai taya ta wannan ‘battle (yakin) da wadannan dattijai masu tsoron duniya da abinda ke cikinta ya zo. Itama tana yarda da abinda suke hangowa kawai tana kare kanta ne don tana son yin aikin ko burin data ke dashi akan Goggo ya cika. Ba tana son yin aikin bane don taje taji dadin rayuwa ko makamancin hakan, zata cika alkawarin data taba yiwa Goggo ne tun tana kankanuwa.

Goggon da bata yi karatun zamani ba, amma ta tsaya (against all odds) ta samar dashi gareta, ta cika mata burin ta, har gashi yau al’umma na amfana da ita, ya zame mata hanyar samun abinci na har abada, ya zama silar samun hanyar dogaro da kai a gareta.

Kullum ta dauki albashi cikin asusun ta sai ta tuna babanta,

“Ina ma kana raye Baba? In rashin kudi ne yasa ka sha wahalhalun da ka sha a rayuwarka, yau ga kudin na samar maka bani da abinda zanyi dasu. Don haka zanyi komai da gumi na don Goggo taji dadi a karashen rayuwarta.

Ilya ya shigo ya zauna gefe “Wai me kuke tattaunawa ne ana gani na aka yi  wani gumm?”

Goggo bata tanka ba, don ta san shi sarai, muddin ya ji akan aikin wa ake wannan takaddamar Amina tayi nasara ta gama. Don kaifin bakinsa sai yafi na kowa. Inna Zulai da batasan hakan ba ta soma harhada masa dan abinda ta fahimta.

“wai Gwamna Ji-qas, ke son daukar Amina aiki ta kula da diyar sa mai shanyeyyen jiki, amma dole sai ta koma gidansa don ya rabo yarinyar daga gadon asibiti,  zai dinga ninka mata albashin ta na asibiti sau hudu duk wata. Goggo ta kasa amin……” Ilya ya kasa tsayawa yaji karshen zancen nan yayi tsalle ya dire yace “kan uban nan!  To shine kuka sa Dr. Amina a tsakiya kuna son yi mana sagegeduwa? To ke Amina yanzu wai me kike ce musu sun ki yarda? Goggo in wannan damar ta wuce Amina anya kin yiwa kanki adalci ganin irin wahalar da kika ci da jikinki, lafiyarki da aljihun ki  kamin Amina ta zama likita? In tambaye ku, ina ruwan Ji-kas da Amina don ya dauketa aiki cikin gidansa, ance muku bashi da mata ne ko manemin mata ne? To in silar hakan ne Allah zai baiwa Amina miji sai ku sa kafa ku shure alherin Allah? Kai ban taba jin Goggo kin bani takaici irin na yau ba, kin biyewa Inna Zulai kifin rijiya kuna ta bata yawun bakinku akan alherin da yazo har gida ya same ku.

Shin wai ance muku Amina itace kadai likitar kashi a jihar Bauchi? Don kun samu Allah ya zabo ta cikin dubu ya bata shine zaku tsaya kuna kasa ta akan faranti tana lallashin ku tana muku bayani kuna dojewa? Dr. Amina, adana yawun bakinki zai yi miki amfani a gaba, barni dasu. Ku gayamin duk abinda kuke gujewa na shigar Dr. Amina gidan gwamnati…”

Amina banda dariya ba abinda takeyi, Goggo da Inna sun kirne fuska sai jifansa suke da harara. Shi kuwa ya kai hannuwa ya harde a kirji ya mike kafafu a dole jira yake su bashi amsa. Goggo tace.

“Sannu uban mu.  Matse baku nan mu sai mu gaya maka abinda muke gujewa din na zuwan mace babu aure wani waje ta kwana”. Ilya ya gyara zama ya gyara murya.

“A inda babu Uba, komai kankantar namiji Uba ne. Don haka ni Ilya uban Amina, na amince diya ta Dr. Amina taje aiki gidan Engnr. Ji-kas.

Da take kwana a asibiti binta kuke? Kai ni ba don kar ace nayi rashin kunya ga Iyaye ba da sai ince ban taba ganin gidadawan mutane irinku ba. Ana kiranku gidan Gwamnati kuna cewa ba zakuje ba…”

Goggo ta dauki kwanon silva a gefenta  ta jefe shi da shi, Inna Zulai data fi kusa dashi ludayi ta kaiwa bakinsa ya kauce. Amina tace “haba Yaya Ilya, maimakon ka gyara ka tayani lallashin su duk ka kara damalmala al’amarin. Goggo kuyi hakuri, nidai na gaya muku akan aikina zan je gidan Gwamna don wani kebantaccen uzri dana ke dashi akan ki Goggo. Amma in baki amince ba na hakura Goggo, zan je na samu Dr. Turaki gobe in fada masa ban samu amincewar ki ba”

Jikin Goggo yayi sanyi. Ta san Aminan ta har ga Allah batada kwadayi, bata nemi komai ta rasa ba, Amina gudun maza take ba son kai kanta garesu ba. Amina na son aikinta fiyeda komai a rayuwarta. Ta sha gaya mata yana sanya mata nutsuwa, yana sa ta nishadi, yana sa ta farin – ciki yana rabata da damuwa.

Duk ta yarda da wannan, kawai dai burin ta a yanzu Amina tayi aure shine kwanciyar hankalinta, ba wai bata son ta da aikin ta bane. Kuma ta yarda yanzu Amina bata korar masu son ta sune suka dauke kafa.

Goggo Hauwa ta nisa ta dubi Amina, Zulai da Ilya masoyan su na gaskiya da duk suka zuba mata ido. Kowannensu ta bakinta yake son ji don a yanke maganar haka kowa ya huta.

“Amina, na yarda kije aikin ‘yar Gwamna amma a bisa alkawari guda daya”.

Amina ta dago da nutsuwa akan kyakkyawar fuskarta, “wane alkawari ne Goggo? Insha Allah zan cika miki shi muddin bai fi karfin na ba”.

Kije kiyi aikin na amince, amma idan kafin cikar wa’adin aikin ya cika Allah ya kawo miki mijin aure zaki bar aikin kiyi aurenki. In yaso idan mijin ya amince sai ki cigaba”

Amina tayi murmushi har gefen kumatunta biyu suka lotsa.

“Ai a bisa wannan alkawarin muke Goggo har gobe. Wallahi ba ni nake korar su ba, su suke korar kansu. Amma na kara yi miki wannan alkawarin. Ko yau na fara aikin gobe mijin ya zo, zan bar aikin nayi aure ko wanene shi.”

Da sauri Ilya yace “A’ah  Dr. Amina, daina cewa ko wanene, idan kuturu ko Gyartai  ya zo ba ruwan Goggo fa, ke zaki zauna dashi”.

Goggo Hauwa bata san sanda tayi dariya ba, duk zukatansu sukayi dadi, don basa son ganinta cikin damuwa ko yaya, walwalarta itace tasu. Inna Zulai ta mike tayi musu sallama tana fadin.

“kin bari sun kalallameki da dadin bakinsu. Ni nayi nan, tunda ko na sake cewa komai ma ba tasiri zaiyi ba.”

Ilya yace “haka ne Hajiya Inna, gara ki adana yawun bakinki zai yi miki amfani gobe. Sai Ji-kas! Wallahi sai Ji-kas!! Insha Allahu sai Ji-qas bamu fada a banza ba, bamu sha rana a banza ba!!! Gashi tun ba’a je ko’ina ba nida Amina mu zamu fara shan inuwar gwamnatin Ji-qas. Mune a cikin gidan gwamnati!”

Washegari Amina da kwarin gwiwar ta ta doshi ofishin consultant dinta Dr. Usman Turaki. Saidai kash! Ofishin Turaki a kulle. Wani masinja ke gaya mata ai Dr. Turaki an bashi appointment na kwamishinan lafiya. Ya bar asibiti sai nan da shekaru hudu.

Allah ya so tanada lambar wayarsa a lokacin waya ta fara a cika duniya. Duk wani babban ma’aikaci yanada ita.

Ta kira shi ya kwatatanta mata sabon ofishinsa, sai yace ta jira a office dinta zai turo direba ya kaita yanzun nan.

A wata sassanyar mota da Amina bata taba shiga irinta ba, aka kaita (ministry of health) inda ofis din kwamishina Turaki yake.

Amina bata bi dogon layin da ake bi wajen ganin kwamishinan ba, kai tsaye aka sada da ita gareshi.

Amina ta shiga da nutsuwar ta kamar yadda take ciki kullum, irin wadda zuzzurfan ilmin boko ke gadarwa mai shi.

Ta gaisheshi, ta kuma yi masa murnar sabuwar kujerarsa. Yayi godiya, sannan ya tambayeta ta yi shawarar? Iyayenta sun amince?

Amina ta ce “Goggo ta amince. Amma a bisa sharadin in miji ya zo kafin lokacin kwangila ya cika zan bar aikin in yi aure.”

Dr.  Turaki yayi murmushi mai kama da dariya. “That’s good”. Wani dan tunani ya darsu a zuciyar sa akan Ma’arouf da Amina. Amma daya tuna halin mutumin nasa sai yayi gaggawar goge tunanin daga zuciyarsa ya janyo na abinda ya tara su.

“kiyi parking yau. Duk da mai girma gwamna ya gayamin bakya bukatar zuwa da komai, amma mutum baya rasa abin amfanin sa. Kayan sanyawa ne bakya bukatarsu. Yau za’a maida takwararki gidan daga kauyen Ji-qas. Don Allah Amina ki kula da ita yadda ya kamata. As a doctor nasan bakya bukatar a tuna miki yadda zakiyi da patient dinki.  But wannan patient din need extra-more saboda marainiya ce, sannan lafiyarta (matters a lot to her Dad). Zai nutsu ne kadai wajen aikin al’ummar sa in ya tabbatar Amina tana a kyakkyawan hannu kuma tana cikin koshin lafiya koda bata taka kasa.

Daga yau zan bar zama jakada a tsakaninku, kai tsaye zaki dinga magana da His Excellency in kuna bukatar wani abu ko sanar dashi wani abu na cigaba  ko na ci baya da ya danganci lafiyar diyarsa. Be the best doctor and the best physiotherapist as we know. Kawo wayarki in sanya miki lambar tasa”

Amina ta mika masa, ya sanya tayi saving. A ranta ta san ta karba ne kawai amma bazata taba iya kiran MA’AROUF JI-KAS ba! Wani kwayan mutum guda daya da ko sunansa bata taba kwatanta fada ko da a zuciyarta ba, duk da zasu kasance gida daya, shi din dai (Turakin), zata cigaba da baiwa jakadancin ko yana so ko baya so.

Su wanene wadannan gwarazan Ma’arouf da Amina? Daga ina suke? Menene asalinsu? Ga dai kaddarar rayuwa ta hadasu bayan kowannensu alamu sun nuna duniyar sa daban ce data dan uwansa??? Mu waiwaya baya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 28

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sanadin Kenan 1Sanadin Kenan 3 >>

2 thoughts on “Sanadin Kenan 2”

  1. Barka takorinmu the best among the rest. Tabbas ke din ta daban ce, salonki ba irin nasu bane. His excellency jikas da Amina sun nishadantar damu. Iliya masoyin jikas ya nishadantar damu. Allah ya karo zakin hannu. Allah bada jinkiri mai albarka. I’m dai da Rai da lafiya, toh bazamu gajiya da bibiyarki ba

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×