Hajjo kisto mai kyau ta yiwa Kuluwa, kiston su na fulani, cikin hannu babba sai bayan hannu ƙanana biyu, haka ta mata haɗaɗɗen cukunta, da kuma guda bibbiyu a ko wani ɓangare na goshinta dama da hagu, ba ƙaramin kyau kiston ya yi wa Kuluwa ba, dama mai kyau idan ya ƙara da wanka to ba’a magana.
Kuluwa surutu ta dinga yi, hira dai mara kai balle wajan zama, faɗi take, “Hajjo ai ni da Kawu za mu je Makka da Madina, kuma zan sayo miki baby staraba fa, ni kuma Kawu zai sayo mini miji na dinga masa abinci, ina masa wanka na lallashesa yayi bacci na goye sa, kin ga zan shiga aljanna tun da ina masa biyayya.”
Hajjo girgiza kai tayi ta ce, “Daɗina da ke watarana idan kika yi magana kaman a baki kyauta, watarana kuma kaman a rufe ki da duka, Kulu kin fa girma, sa’anninki kin sani duk yawanci sun yi aure, wasu har da yara, amma ke shirirtanki ba kaɗan ba musamman idan surutunki ya mosta.”
“To ai Hajjo shiyasa na ce nima Kawu zai sayo mini miji, kyakkyawa fari bana son baƙi kaman mijin bibalon baffa”, Kuluwa ta faɗa tana tura baki kaman za ta yi kuka.
Hajjo ta ce, “To Allah ya baki lafiya ya kuma baki miji nagari, ya nuna mana lokacin da rai da lafiya.”
“Ai lafiyata lau Hajjo, kuma kin ga idan Kawu ya sayo mini miji to nima har da gaɗa da wasanni (event’s na Fulani) sai anyi a aurena.”
“Allah ya nuna mana to.”
“Ummmmmmn na ma fasa ai Hajjo, sai nayi karatu na zama babba, har da kuɗi zan yi in dinga bawa kowa shayi irin nawa da safe a garin nan, in sayawa kowa kayan ƴan gayu irin wanda Kawu ke saya mini, kuma kullum idan na fita nima sai na kawo wa kowa staraba a garin nan, ai nayi kirki ko Hajjo?” Faɗin Kuluwa tana washe baki irin ta faɗi abin arziƙin nan.
Hajjo shiru ta yi wa Kuluwa bata kuma ce mata komai ba, har ta mayar mata da ɗan-kwalinta, amma sai Kulu ta zame wai ai zafi take ji a kanta idan ta saka ɗan-kwali, a bar kiston ma ya sha iska ya huce kada ya lalace ya ɓaci da zafin da ake yi, Hajjo idanuwanta ta mayar kan TV kawai, bata kuma tankawa shirmen Kulu ba, dan idan ba shirme ba kisto abinci ne da za’a ce zafi zai ɓata sa, a haka har bacci yayi gaba da Hajjo a kan kujeran.
Kuluwa ajiyan zuciya ta sauƙe tare da lumshe kyawawan idanuwanta, ta kuma buɗe su a hankali, sannan ta miƙe tana mai ambaton Allah, tsakar gidansu tayi ta shiga ayyuka cikin nistuwa, dan kamun ka ce me tuni ta ɗaura abinci ta gyara gida tsaf, sai dai duk abin nan da take yi fistari take ji, amma ta kasa shiga banɗaki sai kai kawo take kaman mai safa da Marwa, tana ta faman maste ƙafafuwanta, a haka har ta gama aikin amma Hajjo bata tashi ba, tana gama haɗa komai ta je ta zauna a gaban Hajjo kawai ta saka kuka.
Hajjo cikin bacci take jin muryan Kuluwa na sheshsheƙan kukanta, tuni ta buɗe ido a razane tana faɗin, “Me ya faru Kulu?”, Da muryan bacci.
Kuluwa kam kuka take bilhaƙƙi stakaninta da Allah, tana kan haɗe ƙafafuwanta, wan da lura da hakan da Hajjo tayi shi ya sanya ta gane abin da Kuluwan ke yi wa kuka, miƙewa tayi kawai ta rakata, basu komo ciki ba kuma sai da Kuluwa tayi wanka, suka yi alwala sannan ta wuce ɗakinta, Hajjo ma ta wuce nata ɗakin, tana addu’an shiriya wa Kulu, a ce fistari idan ta kamaka sai ka zama kaman wani ɗan goye.
Hajjo na yin sallah ta fito duba aiki, amma ta tarar Kuluwa ta gama komai, murmushi tayi tare da sanya mata albarka, da mata fatan samun lafiya, domin tana da tabbacin ko aurar da Kulu suka yi yanzu idan ta samu lafiya, to ba dai miji yayi kuka da ita akan aikin gida ba, sai dai wani abun daban.
Kuluwa tana idar da sallah ta shirya abinta, ta fito wai za ta anguwa amma Hajjo ta hanata, akan ta bari sai Kawunta ya dawo, haka Kulu ta zauna zaman jiran dawowan Kawunta har bacci yayi gaba da ita.
Kawun Kulu na yin sallama ta buɗe idonta, da sauri taje ta rungumesa suka shigo palourn nasu tare, tana masa sannu, shi kuma sai saka mata albarka yake.
Kulu ce ta kawo wa Kawunta abinci da ruwa da komai, ya ci tana ta kan masa surutunta dan har ta mance da batun zuwa anguwa, Kawu sai washe baki kawai yake na jin daɗin bakin Kulu ya buɗu, dan shi surutunta ba ya gimsarshi, da wannan shirun nata gwanda ta kwana tana masa surutunta, Hajjo kuwa tana daga gefe tana kallonsu ko ƙala bata ce ba, har Kawu ya gama.
Wannan rana haka suka cinyesa cikin annashuwa, da kuma surutun ƴar tasu, har Kawu suka fita bayan gari da Kulu da yamma, su ne ba su dawo ba sai wajan goshin Magrib, sai farinciki da stalle Kuluwa take yi, dan daman Kawu ya saba mata da hakan, ɗaukanta su fita yawo yake yi muddin yana gida, watarana har ma su bar cikin ƙauyen nasu, Kuluwa kuma wannan abu saka ta farinciki yake yi.
WACECE KULUWA?
Hauwa’u Ibrahim Modibbo Beti, shi ne asalin sunanta, mahaifinta Ibrahim Modibbo Beti wanda ake ƙira da Kawu, haifaffen wata ruga ce da ta faɗaɗa zuwa ƙauye da a ke ƙiranta da Hes-Beti.
Ibrahim Modibbo Beti (Kawu), shi ne ɗa na uku a wajan mahaifinsu Modibbo Beti, yana da yayye biyu mace da namiji, sai kuma ƙanne uku, mace ɗaya maza biyu, goggoji(babbar yayarsu), tana aure a cikin ƙauyen Hes-Beti, sai Baffajo shi ma yana can ƙauyen Hes-Beti da iyalansa, ƙanwar sa mace ƴar autansu kuma tana aure a Gurin (gwaggon Kulu da ta zo a farkon labari), sai ƙannensa biyu, ɗaya mai bin sa yana can Hes-Beti da iyalansa, ɗaya kuma yana ƙauyen Chi-gari da iyalansa.
Hes-Beti ƙauye ne cukuf sosai, domin asalinsa ruga ne, da aka hayayyafa shi ne ya koma ƙauye aka bar ƙaura a cikinsa, domin Chi-gari ya fi sa komai da komai na ci-gaba, a Hes-Beti ba boko ba asibiti, daga maganin gargajiya da suke yi sai karatun Allo, sai wata chemist guda ɗaya wacce dai za’a ce ta fi babu, domin sau da dama idan suna buƙatan abu a ƙauyen to Chi-gari suke shigowa, ko na ci ko magani duka, wasu yaransu ma suna shigowa Chi-gari yin karatun boko, sannan suna zuwa cin kasuwa duk ranan kasuwan Chi-gari.
Yayyun Kawu da ƙannensa duk ba wan da bai da manyan yara, mata da maza, dan Baffajo ma yaransa sun bai wa goma baya, goggoji ma sun kusa goma, haka ƙannensa duk yaransu suna da yawa, kuma da yawansu sun aurar da yaran nasu, saboda a Hes-Beti suna aurar da yara maza da mata da wuri, dan a can zallan Fulani ne ba abinda suke yi sai kiwo da kuma harkan nonon shanu.
Hajara Salisu Giɗaɗo, wacce ake ƙira da Hajjo, mahaifiyar Kuluwa, ita ma asalinsu ƴan ƙauyen Hes-Beti ne, dan suna dangantaka da su Kawu ta abota amma ba ta jini ba, mahaifin Kawu da mahaifin Hajjo abokanai ne na haƙiƙa aminan juna, auren ma asali auren haɗi aka musu, saboda Kawu ba ya kula mata balle zancen aure, ganin haka Modibbo Beti mahaifinsa ya roƙi alfarma aka bai wa Kawu auren Hajjo, sunan Kawu ya samu asali ne tun daga yaran goggoji da suke ƙiransa da hakan, ita kuwa Hajjo tun daga gidansu ake ƙiranta da haka.
Da yake Kawu ya taso mai zafin nama da zafin nema, to tun da Modibbo Beti mahaifinsu ya ware ma kowannensu dabbobinsa, shikkenan a hankali a sannu arziƙin Kawu ke bunƙasa, komai ya taɓa sai yayi albarka, a haka har aka yi aurensu da Hajjo, ba su shige wata guda a Hes-Beti ba suka ƙaura Chi-gari da zama, saboda Kawu ya ce yaransa ba za su tashi a Hes-Beti ba, yana son su yi ilimin zamani da kasuwanci da sauransu, kuma mahaifinsa Modibbo Beti bai hana shi ba illa ma albarka da ya sa masa akan hakan.
Kawu suna cika shekara guda da aure Hajjo ta santalo yaronta namiji, kyakkyawan gaske farin bafulatani, amma yaro ko suna ba’a yi ba ya koma, Hajjo bata wani koma wankan gida ba a gidanta tayi jego, tana gama arba’in wani cikin ya shiga, nan ma wata tara cif ta haifo ɗan ta namiji santalele da shi, wannan sun yi suna ya ci sunan Modibbo (Muhammadu), har sun yi wata uku shi ma ya koma, a lokacin da yaron ya koma a lokacin ta kuma samun wani cikin, a taƙaice sai da tayi haihuwa biyar masu kyau duka maza suna komawa, sannan a na shida ne ta haifo ƴa mace in da ranan suna, yarinya ta ci suna Hauwa’u, wannan yarinya na da wata shida ta koma, daman hajjo tana da wani cikinta maƙale a maranta mai matuƙar bata wahala, ciki yana kai haihuwa ta kuma haifo ƴa mace, kyakkyawa da ita baƙa ba kaman sauran da suke farare ba, ranan suna aka maida mata sunan Hauwa’u ana ƙiranta Kuluwa, cikin ikon Allah da kuma yardan Allah, Kuluwa ta fara girma sannu a hankali, sati ɗaya, wata ɗaya, wata biyu…har ta cika shekara guda lafiya lau, tun da wannan yarinya ta kai shekara guda nan Kawu ya ɗau son duniya ya ɗaura a kan Kuluwa.
Kulu na da shekara ɗaya da rabi, Hajjo ta kuma haifo wani yaron, aka saka masa suna Salisu takwaran baban Hajjo ana ƙiransa Ahijjo, har Hajjo ta kuma haihuwan wani yaro namiji yaranta suka zama uku, lokacin Kulu na da shekara uku da rabi da haihuwa, daga nan kuma Hajjo bata kuma samun wani cikin ba.
Yaron da Hajjo ta haifa daga baya bai wani jima ba ya koma, ya rage Ahijjo da kuma Kuluwa, yara masu hankali da nistuwa da kuma shiga zuciya, Ahijjo fari ne tass da shi kyakkyawa, sai dai shi daman tun haihuwansa bai da ishashshen lafiya, balle kuma da aka yi cikin yaron ƙarshe a kansa sai abun ya ƙaru, dan har yayi shekara biyu baya umn baya umn’umn, ita Kuluwa kuma lafiya take ba za’a ƙirata mai surutu ba, kuma ba za’a ƙirata shiru-shiru ba, sai dai bata da hayaniya kam sosai.
Kulu tana shekara Uku ta fara zuwa makarantan islamiyya, inda take ƙoƙari sosai wajan karatu, sannan idan ta dawo gida takan dinga yi wa ƙaninta Ahijjo karatun, kuma suna zuwa Hes-Beti gaishe da dangi, dan zuwa wannan lokacin ma iyayen Kawu duk babu su, Hajjo ce kawai mahaifinta ke raye, duk dangi ba wanda baya ƙaunar Kulu, har Gogogoji ta ce Kawu ya bata Kulu, amma ya shafa wa idanuwansa toka ba tare da yayi kunyan Fulani ba, ya ce a bar masa ƴar sa zai riƙe ta da kansa, saboda su yi karatun ilimin addini da na zamani ya bar Hes-Beti, dan haka Kuluwa ba za ta zauna a Hes-Beti ba.
Kulu na da shekara biyar a duniya, lokacin kuma Ahijjo na da shekaru huɗu, Kulu watarana daman takan bi Kawu jeji duk ranan da zai fita da dabbobinsa da kansa, ko kuwa wataran takan bi masu kiwon yamma idan ba za su jima ba, ko kuma ba za su yi nisa da gari sosai ba.
Kawu baya son zuwan Kulu jeji ko da shi ne, amma kuma son da yake mata bai sa ya hanata ba, yana dai iya ƙoƙarinsa wajan kula da ita in tare suka tafi, idan ba da shi ba kuma to sai dai idan ba’a sani ba ta fita ta bi su, amma ba’a bari ta bi su.
Rayuwa na tafiya sannu a hankali, watarana staustayin da ta zama silar abubuwa da yawa a rayuwan waɗannan bayin Allah ta fitar da Kulu, kuma da ikon Allah Kulu ta ja hannun Ahijjo suka tafi tare, wai sun bi bayan masu kiwo, kuma Hajjo bata san da fitar su ba.
Kulu da karambani wai su hau bishiyan mongoro da Ahijjo, yaron da tafiyan ma sai lokacin yayi ƙwari da yake da shekaru huɗu, haka ta ingiza shi saman bishiya ita ma ta kama ta ɗale kaman biriya, Ahijjo da ya gaji ya saka mata kuka, Kuluwa tayi banza da shi kaman bata san kuka yake ba, hankalinta na kan wani mongoro da take son stinkowa, Kulu ta dage sai miƙa hannu take za ta stinko mongoro, har da ɗaga ƙafa kaman ba’a kan bishiya take ba, tsautsayi da ba’a saka masa rana, garin ɗage ƙafa sai ƙafan Kulu ya goce, tun daga kan bishiyan kan ta ya fara garuwa da reshe-reshe, har ta samu ida isa ƙasa ta buga kan ta, Kulu ko mosti bata yi ba balle a kai ga ihu, domin kuwa tun daga kan bishiyan ta sume tun kamun ta ida isowa ƙasa.
Ahijjo yana ganin yacce Kulu ta faɗo ƙasa sai ya ɓare baki yana dariya, abinka da yaro da yaranta ba wayo ga ba isasshen lafiya, sai ya ɗauka wani abin gwaninta tayi, musamman da ya leƙo ya ganta kwance wanwar a ƙasa ko mostawa bata yi, sai ya ɗauki hakan a wasa ya kama washe baki yana dariya, cikin maganansa da ya fara koya yake ƙiran sunanta, “Uwuwa (Kuluwa), ci taci ci aukeni(ki tashi ki sauƙeni).”
Abin da Ahijjo ke ta maimaitawa kenan, ganin shiru sai ya saka kuka tare da sake jikinsa shi ma ya faɗo daga kan bishiyan har ƙasa, cikin rashin sa’a kuwa ya faɗi a kan wani dutse tuni kai ba ƙwari ya fashe.
Shiru-shiru Ahijjo da Kuluwa suna yashe a ƙasan bishiya, ba su ko mosti kaman waɗanda ma ba rai a tattare da su, sannan ba giftawan kowa balle a kallesu.
A gida ɓangaren Hajjo kuwa hankalinta idan yayi million’s to ya tashi, tasan ba tare da masu kiwo suka fita ba, to ina suka yi?
Tana cikin wannan staka mai wuya sai ga Kawu ya dawo, abu na farko da ya fara tambaya kuwa shi ne, “Ina Kuluwan Kawu?”
Hajjo da ta rasa abin faɗa nan ta zayyana masa gaskiya, ita ta fita maƙota ne ta dawo bata same su ba, da yake Kawu ya san halin Kuluwa da son bin masu kiwo sai ya ɗauka a hakan kawai, amma ya yi wa Hajjo ɗan faɗa ya wuce ciki.
Magriba na yi sai ga masu kiwo sun dawo, Kawu ya fito yana tambayansu Kuluwa da Ahijjo, amma suka ce basu tafi tare da su ba, nan fa hankalin Kawu da Hajjo ya kuma tashuwa, ai ba wani batun stayawa dogon zance Kawu yayi gaba, masu masa kiwo suka rufa masa baya wajan nemo yaransa, Hajjo kuwa an bar ta da sintiri a gida zuciyanta sai bugawa yake ta ma kasa yin sallar.
Kawu suna tafiya ba su yi nisa ba cikin ikon Allah kuwa sai ga su a gaban bishiyan mangoron, ganin yaransa a wannan halin sai da ya kusa haɗiyan zuciya dan firgici da tashin hankali, a haka suka jido yaran sai gida, an shafa musu ruwa anyi komai amma yara ko mostawa ba su yi ba, haka suka ɗauke su sai asibitin da suke da shi a wannan ƙauyen.
Kwana suka yi curr a asibiti ba farkawan yara ba labarinsu, sai cikin dare ne Ahijjo ya mosta, kamun safiya kuma ya ce ga garinku, haka aka dawo da gawansa gida aka masa sutura, a ranan mutanen Beti suka zo.
Kuluwa sai da ta kwashe sati guda a asibiti bata farfaɗo ba, ga shi sai ruwa ake ɗaura mata, da abin ya ishi su Baffajo sai suka ɗauketa suka koma Hes-Beti da ita, ba su yi wani tunanin kai ta babban asibiti a cikin gari ba, suka koma ƙauye da ita wai za su yi na gida.
Komawansu Hes-Beti da kwana biyu masu kyau Kulu ta fara mosti, amma idanuwanta ma bata buɗe ba balle baki, wasa gaske ana maganin gida sai da aka kwashe wata guda sannan fa Kulu ta iya buɗe idanuwanta, nan ma tana buɗewa za ta saka ihu ta kulle, tana kuka tana buge-buge, sai suka fara tunanin ko mutanen ɓoye ne, haka dai suka dage da magani har abun ya sauƙaƙa cikin ikon Allah, amma dai Kulu abinta ya zama kaman na mai hauka, kaman kuma na mai aljanu.
Ko da suka tattaro suka dawo Chi-gari, nan ma ba’a bar yin maganin ba iri da kala, amma abu sai a hankali dan sai da tayi shekara biyu kamun abun da take na kaman aljanu ya rabu da ita, lokacin kuma tana da shekaru bakwai a duniya, da abin ya ragu sai Kawu ya saka ta a makarantan Boko, ba’a wani jima ba sai fa wani abu mai ɗaure kai ya samu Kulu wan da ba’a gane masa ba, Kulu sai tayi kwana uku wani bin har huɗu ma tana nan kaman mutum-mutumi, ba ta umn ba ta umn-umn, komai sai an mata, idan aka bar ta a waje a zaune haka za ta zauna sai an ɗagata, idan ma a kwance ne to sai an ɗagata, wanka sai an mata komai sai an mata, abinci kuma ba ta ci sai dai Kawu ya bata wani abun mai ruwa-ruwa.
Sannan idan aka kwana biyu zuwa uku ko huɗu, to idan Kulu ta fara wani mahaukacin surutu, ko kai wayene sai ka ji haushinta, ga iya tambaya ga damun mutum ga ɗan banzan kukan shagwaɓa, idan ka ƙi kulata to muryanta sai ya karaɗe gari, abun dai sai a hankali.
Wannan batun shirun da take yi da kuma surutun stiya idan abin ya juya, an yi magani har an gaji, tun tana shekara bakwai har yanzu da take da shekaru goma sha bakwai a duniya, a cikin shekarun nan ba irin abin da ba’a yi ba akan cutanta, kuma a haka ta sauƙe Alqur’ani mai girma, sannan ta gama primary school, ta gama Jss, tana Sss 2, shekara mai zuwa za su zana WAEC.
Duk da rashin lafiyan Kuluwa hakan bai hana ta samun manema ba, farinjini ne da ita sosai, tun daga kan na dangi har da wasu bare, Goggoji tayi-tayi Kawu ya aurawa yaronta Kuluwa amma ya ƙi sam, ya ce ba da shi ba aurar da Kulu ga mai mata da yara, da ace tana da ishashshen lafiya to da sauƙi, amma bata da lafiya ba da shi ba, aje kishiyoyi su sako ta gaba, ko miji ya wulaƙanta ta, dan haka Goggoji sai take jin haushin Kulu da Kawu ta stane su, shi kuwa Baffajo daman Allah ya masa rasuwa, a taƙaice dai yaran dangi samari da masu auren duk sun nema auren Kulu Kawu ya hana, saboda ya ce ba zai aurar da Kulu ga wanda hankalinsa bai kwanta da shi ba, Kulu idan ciwonta ya tashi komai sai an mata, to a irin mazan yanzu ba ko wanne bane za’a samu wanda zai jure yi mata wannan hidima ba tare da ya wulaƙantata ba, dan haka shi bai isa ba, wannan furuci na Kawu shi ya saka dangi gaba ɗaya suka stani Kulu, kowa baya son magananta duk saboda Kawu ya hana yaransu auranta.
Haka a cikin garin Chi-gari duk waɗanda suka nema, Kawu ya hana su ya ce ba fa zai aurar da ƴar sa a kasa kula masa da ita ba, ko a mayar masa da ƴa ƙaramar bazawara tun da wuri, bai isa ba, shi dai muddin da ransa da lafiyansa to zai tsayawa Kulu su nemi magani, sannan tayi karatu kuma, duk lokacin da Allah ya kawo mata mijin da ya dace to zai aurar da ita, sosai Kawu ya toshe kunnensa daga duk wani maganganun dangi da mutan gari, na ƴar sa ta stufe a gida har shekaru sha bakwai ba aure.
A cikin ƴan uwan Kawu da ke raye mata da maza, duk babu mai son maganan sa shi da ƴar sa sai ƙanwarsa da ke aure a Gurin (Aminatu gwaggon Kulu), wacce ba’a jima da yin auren ƴar ta sa’ar Kulu ba, kuma cikin ikon Allah a lokacin Kulu tana halin surutu ne ba shiru-shiru ba, dan haka ta yi ƙawancen auren sannan ta tara go-slow na samarin Gurin, wan da abin ka da fulanin ƙauye idan ana hidimar aure, to fa yaransu ƙanana iskancinsu da yawa, sai su nemi yi wa yaran mutane fyaɗe a wajan biki, hakan ta kusa ristawa da Kulu Allah ya taimake ta, daganan Kawu ya ce ba inda za ta ƙara zuwa ba tare da shi ba, kuma ta daina zuwa wajan bikin aure balle ma tayi ƙawance.
Kawu yana ƙaunar Kulu sosai, sai abinda take so yake mata, yakan je cikin gari tare da ita idan tana halin surutu, su je su sayo kayakin sakawanta da komai na ƴan gayu, kuɗi sosai yake kashe mata, shiyasa a waye Kulu take, kawai rashin lafiya ne da sangarta suka maidata sai a hankali.
Kuluwa a shekarunta yanzu na sha bakwai, ba irin baiwa da Allah bai azurtata da shi ba na budurwaye, tana da komai Masha Allah, sai dai abu guda shi ne har zuwa yanzu Kulu bata taɓa yin jinin al’ada ba, amma kuma tana da wani irin ciwon ciki da yake damunta sosai duk wata, indai tana halin shiru wannan ciwon ya sameta to fa ba abinda za ka dinga gani sai hawayenta ɗaya na bin ɗaya, idan kuwa lokacin da take surutu ne to idan ta dinga ihu da kuka bacci ne kawai zai sa kunnen mutane ya huta, sun yi maganin gida har sun gaji akan mastalolin Kulu amma shiru, sai dai tun daga asibitin chi-gari ba su taɓa stallakawa zuwa wani asibiti a wajan garin ba, Allah bai basu basiran yin tunanin zuwa babban asibiti ba, kullum suna cikin yin maganin gida ne kawai, dan duk zatonsu aljanu ne, anyi maganin aljanu kuma amma ba abin da ya sauya sai wanda ba za’a rasa ba.
Kuluwa duk wannan ciwo nata, duk ranan da ta samu sauƙin cutan shiru ta fara cutan surutu, to idan tana aiki za ka ce ba ita kaɗai take yi ba mutanen ɓoye na taya ta, sannan tana da son stafta da gyara, kisto, ƙunshi, wanka, kwalliya, da ƙamshi, abin da bata so kuma bata iya ba shi ne wanki dan Hajjo ke mata, watarana ma Kawu ke mata da kansa, a barta dai da saka kaya a kai a kai da kuma gyara ɗaki, sannan Kuluwa bata taɓa yardan shiga banɗaki ita ɗaya, ko da rana sai an rakata, idan da dare ne kuma ko tare ta shiga da mutum, to bata wanke fiska a banɗaki sai ta fito stakar gida, dan da farko ma a waje take wankan, sai da ta zama budurwa sannan Hajjo ta hanata dole sai dai tayi a banɗaki ko a mata a banɗaki.
Wannan kenan dangane da Kulu da iyayenta, sauran abubuwan sai mun nusta cikin labari za mu san su, musamman ciwon da ke damun ta.
Ci-gaban Labari.
Washe-gari da sassafe Kulu ta riga kowa tashi, ta gama ayyuka komai da komai, Hajjo na fitowa ta rakata tayi wanka, sannan ta zo ta shirya cikin uniform nata na boko ta ɗau jakanta, bata wani karya ba kawai ta sha ruwan zafi Kawu ya bata kuɗin tara(kuɗin kashewa a makaranta), suka fita tare ya sauƙeta a makarantan da mashine nasa, duk da makarantan babu nisa amma da mashine yake kai ta kuma da mashine yake ɗauko ta saboda gata da soyayya.
Kuluwa tun da aka sauƙeta a mashine suka yi sallama da Kawu, sai ga wani irin nistuwa da kwarjini sun mata ƙawanya, kan ta a ƙasa take tafiya a hankali cikin nastuwa kaman bata son taka ƙasa, har ta shige ajin nasu, Allah ya taimaketa tukunna Malami bai shigo ba, dan haka kujeran da take zama ta nufa ta zauna.
Ƴan ajin nasu tun shigowanta suke ta washe baki, dan kuwa sun san tun da suka kalleta ita kaɗai to bakin a buɗe, da bakinta a kulle to tare da mahaifinta za ta shigo ko Malama, Kulu ba ta wani yin wasan banza a makaranta ko neman reni, amma kuma tana da daɗin sha’ani da kowa, tana fahimtan karatu sosai ba kamar ta a ajin nasu wajan ƙoƙari.
Wata mai suna Fadila ce ta shigo ajin, direct a wajan zaman Kuluwa ta kai idanuwanta, ganin Kuluwa sai ta washe baki, domin taji daɗin ganinta, rashin zuwanta kwana biyu ba ƙaramin kewanta tayi ba, ƙarasowa tayi ta zauna a gefenta tare da cewa, “Hauwa’u Ibrahim sai yau?”
Murmushi mai kyau Kuluwa ta sakar mata, tare da cewa, “Ummmn”, tana gyaɗa kai alaman eh.
Fadila ta ce, “Sannu da dawowa to, ga abubuwan da aka yi kwana biyu da baki zo ba, sannan darasin ranan na malam lissafi ina so ki ƙara mini haske a kai.”
Kuluwa cikin nistuwa ta karɓa ta shiga copynsa, tana gamawa malami ya shigo musu, a taƙaice sai da aka fita tara sannan suka zauna tan yi wa Fadila bayanin darasin su na ƙarshe akan lissafi, haka suka wuni a makarantan Kulu ita ce nan ita ce can, ba kowa take yi wa magana ba, amma idan wanda take yi wa magana take tare da shi to fa an shiga uku da surutu, dan in a aji ne sai an sa sunanta sau ba adadi a noise marker, ba ruwanta ko malami na aji surutunta take yi, don idan bakin Kuluwa ya buɗe to fa ba shi da full stop wato mastaya, sauƙin abun ma abin da aya shafi karatu take yi wa surutun, dan idan ta tashi sai ta iya fara kawo abin da aka musu daga farkon term har ƙarshensa, wai bayani take a haka Kuluwa mai craming za’a ce mata ko screenshot.
*****
A ɓangaren mutanen Arab emirates (Dubai), Shaameekh tun da suka yi wannan aiki ya baro asibiti ko leƙa wa bai sake yi ba, kawai ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan training nasa ne, wanda hakan ya sa Shaameekh ya ƙara wani ƙwanji, damastansa suka ƙara fitowa da Six-packs nasa ma Masha Allah, idan ka kallesa ba riga ba za ka so ɗauke idonka daga kallon surarsa ba.
Yau da take juma’a ranan da za su yi wasan ne, amma da yake sai zuwa dare za su yi to tun da asuba Shaameekh ya shige wajan mosta jikinsa, sanye da short-nicker kyakkyawan ƙirjinsa a waje, Punching bag ya ɓata lokaci sosai wajan bugunsa, sannan ya koma kan kan sauran, sai haɗa zufa kawai yake yi, domin lokaci ya ɗauka mai stayin gaske yana aiki guda, har sai azahar sannan ya sararawa kansa ya fice a wajan cikin takunsa na ƙasaita, kai ka ce ba gama wahalar da kansa yayi ba, haka ya wuce ya kwankwaɗa ruwa mai sanyi a fridge nasa sannan ya shige ɗakinsa.
Toilet ya shige a haka, tare da sakar wa kan sa ruwan sanyi yana lumshe ido, bai da damuwan da ya wuce anjima tayi su yi su gama su huta, ya gama packaging na kayansa da komai, yau ɗin nan yake son barin Dubai idan Allah ya amince.
Sai da ya ɓata lokaci mai stayin gaske wajan wanka, ya haɗa da na juma’a da alwala duka, sannan ya sanya rigan wankansa ya fito, hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana goge jikinsa, haka ya wuce gaban Haɗaɗɗen walldrop nasa ya nemo 3quater da t-shirt bodyhug ya saka(Shaameekh zuwa juma’a da guntun wando ya kuma feshe jikinsa da turare sannan ya ɗau key na motansa da wayoyinsa ya fice a gidan, ya nufi masallaci.
Nafilansa yayi raka’a biyu kamun aka shiga salla, sannan da aka idar ma yayi raka’a huɗu, domin sallahn juma’a duk da ita ma nafilance, amma ana haɗa ta da nafilfulun da ake yi wa sallahn azahar, sannan an fi son mutum yayi biyu a farko huɗu bayan sallahn juma’an, saboda yin biyu bayan sallahn juma’a kan saka wasu tunanin ko ka cike juma’a ta koma huɗu ne(wato azahar kenan ba juma’a ba), idan huɗu kayi farko ya fi kyautuwa biyun ka bar su ka yi a gida maimakon a masallacin.
Shaameeƙh ya ɗau tsawon lokaci yana addu’oinsa na neman alkairi da sa’a, game da wasan da za su yi anjima, saɓanin wasunmu da ko exam’s za su yi sai an haɗa da tsafi, ƙwallo tsafi, dambe stafi, aure tsafi, kasuwanci stafi etc, Allah kyauta mana wannan zamani.
Ganin har la’asar ta kusa, bai wani bar haraban masallacin ba, kawai ya zauna ya ci-gaba da addu’oinsa, har lokacin sallahn la’asar ɗin tayi, sannan yayi sallahn ya fito ya yi wa motansa key.
Wajan shaƙwata hakan nan mai kyau Shaameeƙh ya nufa, yana parking motansa ya fito tare da zura hannunsa a aljihu yana taku mai kyau, ta nufi wajan zaman nasu fiskan nan sam ba fara’a.
Su biyu ya samu zaune a haɗaɗɗen table nasu, Manseer na hango sa ya fara dariya kaman ba lau ba, ɗaya gayen da ke zaune a gefensa ne ya ɗan ja guntun staki ya ce, “Mai zaman banza kana da buƙatar a duba maka lafiyan kan ka akan wannan dariyan.”
Manseer sai da ya stagaita dariyan sannan ya ce, “Muhseen ba za ka fahimci me nake yi wa dariya ba, dubi fa wannan ƙaton gardin gauron sai ya wani ce ba ya buƙatan aure yanzu, bayan a yanzu haka da ba’a kan gajimare yake ba ma Batman nasa a murɗe yake stam, kai amma na tausayawa matayenku, ai duk mai auran ɗan dambe aiki ya ganta, dan wannan mosta jikin naku, ba iya damastanku ke ƙaruwa ba har da Batman naku, wayyo kukam kyawunta ku samu mata masu halittan zurfi da ɗan buɗaɗɗen Garage, kuka haɗu da mai matsatstsan Garage kam gaskiya spanner’s nata za su ji a jikinsu, dan engine’s na ƴan dambe daban ne”, Manseer ya ƙarisa maganan dai-dai shaameeƙh ya iso wajan nasu.
Shaameeƙh ciki-ciki ya musu sallama, sannan ya samu waje ya zauna, da yake ya ji ƙarishen maganan Manseer, hararansa yayi tare da cewa, “Ɗan iska dai bai ji daɗi ba a rayuwansa, a ce mutum bai da magana sai ta banza, ɗan iskan ma’aikacin asibiti kawai.”
Manseer yana dariya ya ce, “Ƴan iskan fa suna da yawa, tun da kai ɗin ma aikin asibitin kana yin sa.”
Muhseen hannu ya miƙa wa Shaameekh suka gaisa, sannan ya ce, “Man ka ƙyale wannan mai zaman banzan bai da aikin yi ne, mu da muke da wasa zuwa jimawa ai munsan da abu a gabanmu.”
Kamun Shaameeƙh ya buɗe baki tuni Manseer ya ce, “Ni kuma na gaban nawa kai ka sace su? Ko ka fara shafi-mulera ne bamu sani ba?(masu kwashewa mutane al’auransu).
Shaameeƙh dafe kai yayi ya ce, “Allah ya shiryaka.”
“Ko wani ɗan kutuma-nege na buƙatan shiriya, musamman dai kai wanda wai baya son zancen aure”, faɗin Manseer yana kai abin sha bakinsa.
Muhseen murmushi yayi ya ce, “Mai zaman banza ka je mun sallameka.”
“Ƙafata ƙafarku, sai za ku shiga da’ira(filin wasa), sannan nayi gefe dan ba ta wajan na biyo ba, Allah rufa mini asiri da yin dambe, na je wataran a bugar da ni a bar matata da heartbreak babu harkan hawa gajimare, dan na tabbata bugu guda aka mini a da’irar wasanku sai lahira ko dogon suma, abin da bakwa zama haka kawai, daga masu stafi sai asiri, sai dodonni ƙulle-ƙullenku.”
Muhseen murmushi yayi ya ce, “Mastalan masu zaman banza kenan, ka ga mu za mu iya jaa da masu stafin dan Allah muka kama kuma ya isar mana.”
Manseer da Muhseen sai surutunsu suke Shaameekh na jin su bai ce komai ba, sai ma ordern abu dai-dai buƙatansa da yayi, abinci da zai ƙara masa energy a jiki ba zai damesa zuwa anjima ba.
Sai da ya cika cikinsa sannan ya duba agogo, ganin lokaci ya ja ya miƙe tare da cewa, “Muhseen za mu yi maganan a can, yanzu lokaci ya ƙarato akwai abin da zan ɗauka, after isha’i sai mu haɗe.”
Manseer ya ce, “Ɗan ƙwaya tun yanzun za ka sha ƙwayar taka dan ta jiƙa, a dai dinga jin storon Allah za’a mutu.”
Shaameeƙh ko kallon Manseer bai yi ba ya bar wajan.
Muhseen murmushi yayi ya ce, “Kai fa ba ka da dama Manseer, dan kasan kai kuran ƙarfen Man ne shiyasa kake masa haka, anyway tare na gan ku, nima ka ga tafiya akwai abin da ban ƙarisa ba.”
“Ku dai dinga jin storon Allah wallahi, ban da shan ƙwaya ko tsaface-tsaface saboda abin duniya, abin da ma hanya ce mai sauƙi da za’a muku 1 blow 7 die sai dai ku ji walakiri na faɗin Man rabbuka?”
Dariya sosai Muhseen yayi ya ce, “To wa ya ce maka duka an taru an zama ɗaya ne? Dan wasu nayi dole wasu na yi ne, a komai a ko ina akwai na gari akwai na banza, mu Allah muka kama, kuma kai ma ka dinga faɗa wa kanka gaskiya ka rage harkan mata.”
Manseer ya ce, “Mu da mata ai mutu ka raba, Batman ba haƙuri dole sai an kai engine zuwa ga Garage.”
“Allah ya shiryeka mai zaman banza”, faɗin Muhseen yana murmushi.
Manseer yana dariya ya ce, “Ameen masu duka ɗaya mutuwa.”
Muhseen tare da Manseer suka miƙe, Manseer ne ya biya kuɗin komai har da abinda Shaameeƙh ya ci, sannan shi da Muhseen kowa ya shige motansa ya kama hanyarsa.
Shaameeƙh yana barin wajansu ya wuce gidansa direct, ya jawo system nasa yana ayyukansa, sai Magrib ya tashi yayi sallah, bai tashi a wajan ba sai isha’i, ya jima yana addu’a sosai, sannan ya miƙe ya shige wanka, yana fitowa cikin isa ya shirya hankali kwance, yanzun ma 3quater ya saka da armless dan sai ya je wajan wasan nasu, zai sanja kaya zuwa na shiga filin wasa.
Shaameeƙh sai wajan ƙarfe goma ya bar gidan, amma Manseer ne ya zo ya ɗauke sa dan ya haɗa kayansa na tafiya Nigeria, daga can Manseer zai kai sa airport ba zai komo gidan ba, ya gama sallama da mai gadinsa kmda mai aikinsa.
Manseer na driving yana faɗin, “Gaskiya Man kana son wahalar da kan ka sosai, daga ka gama wannan banzan wasan sai airport ba za ka bari ko hutawa ka yi zuwa gobe ba, sai ka ce abin barin duniya, ko a maste kake ayi maganan auren a kawo maka matar ce?”
Shaameeƙh guntun murmushi yayi wanda yayi matuƙar fito da kyawunsa, cikin muryansa mai daɗin sauraro ya ce, “A mugun hannu ma nake, kai ƙarshenta ma a ƙafa nake, kai baka ganin idan ba wasa za muyi ba bana son yawan mosta jiki sosai-sosai, saboda saka Manhood na yake ya dinga harbawa neman taimakon gaggawa.”
Wani irin dariya Manseer ya saka tare da dukan stairy, kaman zai yasar da su a hanya ya ce, “Haba Man ai ni nasan duk karya ce kake, ɗazu yanda na ganka nasan ai jiki ya mostu da kyau, to wallahi kamun ka fara tafiya kana ƙoƙarin danne abu a stakiyan ƙafa gwanda tun wuri ka yi aure.”
Guntun staki Shaameekh ya ja ya ce, “ban shirya aure ba yanzu, ban da lokacin mace”, dai-dai sun iso filin da za’a yi taron.
Manseer yana parking ya ce, “Ka kusa daina fita kenan, domin idan ka ƙuresa ya harba ba komawa sai ya ji sa a sararin gajimare.”
Shaameeƙh tattara komai da zai buƙata yayi ya fice a motan yana faɗin…
*****