Bayan ta shige banɗakin sanin halinta sarai ya sanya su tashuwa, figaggun kayansu suka saka, har za su fice a ɗakin ɗayar ta ce, "Baby kinsan babe ba mutunci ne da ita ba koh, better mu gyara mata bed ɗin kamun ta fito."
Tsaki ɗayar ta ja, "Mtsww! bea ke fa kin cika tsoronta wallahi, shegiya kawai ko duka ne ai bata isa ta mana ba, sai mu danne shegiya mu ƙwaƙwuleta ma, amma kina yin abu kaman wani kina storonta, ita uwar wace a cikinmu?"
Jin mostin Soffy ya sanya ɗayar rufe mata baki, tana rufe bakin. . .