Skip to content
Part 7 of 10 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

Bayan ta shige banɗakin sanin halinta sarai ya sanya su tashuwa, figaggun kayansu suka saka, har za su fice a ɗakin ɗayar ta ce, “Baby kinsan babe ba mutunci ne da ita ba koh, better mu gyara mata bed ɗin kamun ta fito.”

Tsaki ɗayar ta ja, “Mtsww! bea ke fa kin cika tsoronta wallahi, shegiya kawai ko duka ne ai bata isa ta mana ba, sai mu danne shegiya mu ƙwaƙwuleta ma, amma kina yin abu kaman wani kina storonta, ita uwar wace a cikinmu?”

Jin mostin Soffy ya sanya ɗayar rufe mata baki, tana rufe bakin kuwa sai ga Soffy ta fito daga toilet ɗin, ɗaure da guntun towel a jikinta, iya waist nata kawai ta ɗaura na fulaninta a buɗe( breast).

Ganinta ya sanya ɗayar saurin fara gyara gadon, ɗayar kuwa mai masifan gaba-daya na mujiyanta( idanuwanta), duka na kan ƙirjin Soffy.

Ankarewan da Soffy tayi da kallon da take yiwa breast nata, shi ya sanya ta mai da towel ɗin ƙirjinta ta juya tana tsaki, tare da cewa, “Shegiya jarababbiya mai mugun ido, in dai nice ƙwalelenku wallahi, sai gani sai hange daga nesa”, ta faɗa tare da wucewa gaban mirror tana shafa mai nata, amma a hakan ma gaba-daya mazaunanta kusan rabi a buɗe, waccan dai sai haɗiye yawu take, ga taƙaicin maganganun Soffy ga kuma kwaɗayinta.

Bayan ɗayar ta gama gyara gadon, jan hannun wacce ke stayen tayi suka nufi ƙofa tare da cewa, “baby zo mu wuce, ke kuma babe safe travel.”

Suna ƙoƙarin ficewa Soffy ta ce, “Ku jirani na gama ku yi dropping na a airport.”

“Okay Babe muna jiranki a palour”, suna gama faɗa suka fice, zuwa palourn.

Kallon ɗayar tayi ta ce, “baby please ki daina nuna jarabanki a fili akan Soffy, bata da kirki ko kaɗan infact ma bata son wannan abu ko kaɗan, and nima am getting jealous please ki bari.”

Ajiyan zuciya ɗayar ta sauƙe ta ce, “Shikkenan bea duk yacce kika ce haka za’a yi, kinsan ina son ki over”, rungume juna suka yi nan palourn suna jiran fitowan Soffyn.

Suna fita a ɗakin Soffy ta bi bayansu da mugun kallo, ta ja staki wai sha-shashshu wahalallu, sannan ta tashi ta cire towel ɗin jikinta, sharp-sharp ta shirya.

Legis ta sanya sai top long-sleeve da cap, side back nata ta rataya ta ja ƙofan ta rufe. A palourn ta same su zaune ko wacce na danna wayanta, cewa tayi, “Angelina, Leesha na fito mu wuce ko.”

Tashuwa suka yi dukansu ko ina na ɗakin nata sai da suka rufe, suka kashe komai na wuta, sannan Soffy ta ja ƙofan palourn ta kulle ta jefa key ɗin a jakanta, motorn su da suka parker a environment na gidan suka nufa, Angelina wacce suke cewa bea ita ce ta shiga mazaunin driver dan ta ja su. Kula da Soffy tayi tun fitowansu Leesha na ta haɗe fiska, hala har yanzu ranta a ɓace sai ta taɓe baki, ta shige gefen mazaunin driver, tana ciro chewing gum tare da jefawa a bakinta.

Leesha staki ta ja ganin Soffy ta shiga gaba, sai ta shige baya ita kuma amma bawai don ta so hakan ba.
Ta mirror Soffy take kallon duk abin da Leesha ke yi, murmushin gefen baki tayi tana faɗin wahalalliya kawai.

“Babe yanzu yaushe za ki dawo?” Faɗin wacce ke tuƙa motan.

“Bea dis time sai kun ganni kawai cuz i have a lot to do at home”, Soffy ta faɗa tana yastine fiska.

“Babe what about our exams? you know very soon za mu fara and it’s a dangerous semester.”

“Forget about exam’s zan san yacce zan yi handling nasa, cuz ba wani big deal bane, my biggest problem now yana gida sai na seta komai zan dawo.”

“Okay Allah ya dawo da ke lafiya, Allah sa komai yayi yacce kike so.”

“Woww! Ameen my bea shiyasa nake yin ki over”, Hiransu suke tsakaninsu su biyun ba Leesha ciki, har suka isa airport da ke garin Delhi a qasan India. Suna zuwa dai-dai lokacin tashin jirgin yayi kenan, Angelina na murmushi ta ce, “babe you’re born lucky, kinga ba wani ɓata lokaci sai kwanan Nigeria.”

Murmushi Soffy tayi ta ce, “yeah! Bea kwa iya tafiya yanzu sai mun yi call.”

Daman Soffy bata ɗau komai ba sai side back nata, haka ta shige jirgin seat da yake numbernsa a ticket nata shi ta wuce ta zauna. Bayan sun ga shiganta jirgin, jan motorn suka yi dan barin airport ɗin, bayan sun hau kan hanya gefen titi Angelina tayi parking, juyowa tayi ta ce “baby meyasa ba za ki dawo gaban ba tun da ta sauƙa.”

Tsaki Leesha ta ja ta juyar da kai, Angelina ta ce, “Please baby ki dawo gaba ni ba driving naki zan yi ba, in ma babe ce ta ɓata maki rai am sorry ai dai ba ni ba ce, kullum ina faɗa maki kiyi haƙuri da halinta, amma ba kya fahimta.”

“Look Angelina in baki ɗauka na ki sauƙe ni, kinsan dai nasan hanya ko?”

Angelina sauƙa tayi ta dawo gidan bayan ta kulle musu ƙofa, rungume Leesha tayi ta ce, “Please baby banson fushinki fa kin sani, ba yacce na iya da Soffy ne am so sorry.” “Bea gaskiya nikam idan zaman mu ba zai yiwu ba, better na sani idan yaso sai na fita harkanku, tun da daman tare na ganku zan barku taren shikkenan.” “Baby am sorry kin ji dan Allah ki daina fushi da ni, kema kina gani ai ba komi tsakaninmu tun kamun ma ki zo, ba yacce na iya da rashin mutuncinta ne kawai.”

Leesha ta buɗe baki za ta yi magana sai Angelina ta haɗe bakinsu( wa iya zubillah).

Leesha da Angelina kenan, ƙawayen Soffy na ƙut da ƙut, kuma abokanan faɗanta, dukkansu a nan Delhi suke karatu, course ɗaya class ɗaya komai ɗaya haka suke, Angelina ƴar India ce a nan suka haɗu da Soffy, sai Leesha da take ƴar Nigeria a babban birnin Abuja, mahaifinta babban hamshaƙin mai kuɗi ne, to daman ita already idanuwanta a buɗe suke saboda an sangarta ta da kuɗi, tana zuwa India ta haɗe da Angelina wacce daman ta jima tana bin Soffy da maganan lesbian ta ƙi, to Leesha na zuwa suka jone sai dai addu’an Allah ya shirya.

*****
Jirgin su Soffy yayi landing a babban filin jirgi dake cikin garin Yobe, da misalin ƙarfe 11pm da mintuna a agogon Nigeria. Ganin dare yayi kuma daman ba tayi waya da gida ba, hakan ya sa ta nemi taxi kawai, kwatance ta masa yace ya gane anguwan, shiga tayi suka kama hanya.

Big Dad da big Mom zaune suke a palourn nasu, kallo suke  suna hira su biyunsu.

“Assalamualaikum”, Sabeer ne yayi sallama yana mai shigowa palourn, bayan iyayen nasa sun amsa masa sallaman.

Ƙarasowa palourn yayi, ɗaya daga kujerun dake palourn ya samu ya zauna, cikin girmamawa ya ce, “Barka da dare Dad.” “Yauwa barkanmu son, sannunka da shigowa ko.”

Amsawa Sabeer yayi tare da gaishe da iyayen nasa duka, suka amsa sannan big Dad ya ce, “Sabeer ya labarin ƙanwarka ne kam, shiru fa har yanzu bata dawo ba kuma layukanta ba sa shiga, both na Nigeria da na Indian, mutum tun jiya yana hanya.”

Sabeer ya ce, “Dad inajin bata taso da wuri ba ne, but am sure yau za ta shigo komin dare.”

big Mom ta ce, “To Allah ya sa, Allah ya kawota lafiya, ni damuwana ma yanzu layukanta duka a kashe ba sa shiga, idan ta iso ya za’a yi ta sanar balle driver ya je ɗaukanta.”

“Mom ba ga taxi’s ba, tun da ta rufe wayoyin ta ai sai ta hau motorn haya kuma, driver ma ya huta fita da daren nan.”

Big Mom Hararan Sabeer tayi ta ce, “Lallai ma Sabeer ashe ba ka da imanin ƴar uwanka, ƙanwar ka ta biyo motan haya da daren nan, kana faɗa ko damuwa baka yi ba.”

“Mom ya za’a mata to? ra’ayinta ne fashigowa da daren a hakan ma wai dan an mata magana ne, dan haka ita ta jiyo ko ba haka ba Dad?”

Murmushi big Dad yayi ya ce, “Allah ya shirya ka son.”

Da “Ameen”, Sabeer ya amsa.

Big Mom ta ce, “Wai Alhaji har kana murmushi kana biye masa, ƙanwarsa na can hanya ga dare, ai wallahi da ace ta ƙira to Sabeer zai sha mamaki, dan shi zai je ya ɗauko ta.”

Murmusawa yayi dan yasan rikicin mahaifiyar tasa, da kuma son da take wa Soffy, kaman ita kaɗai ta haifa mace, cewa yayi, “Allah ya huci zuciyan Mom tamu, da ta ƙira kam Insha Allah zan je ɗaukota, ur wish is my command Hajiyar mu.”

Big Dad ya ce, “So kin ji ai ɗan ki mai jin magananki ne.”

“Allah ya muku albarka dukanku”, faɗin big Mom.

Sabeer ya amsa da Ameen, sannan ya ce, “kuma kasan me Dad? Allah ko ɗazu  da na je gidan Alhaji baba, sai da ya tambayeni ko ta iso, Hajiya mama tai ta surutu.”

Big Dad jinjina kai yayi ya ce, “Allah ya shiryaku ya iso da ita lafiya, ku na saka mini iyaye surutu da girmansu.”

“Dad na faɗa misu za ta dawo, za ta dawo, amma stofin nan sai surutu suke yi…”, Sabeer bai ida gama rufe baki ba sai ganin mutum suka yi ya shigo palourn kaman an jeho sa daga sama. “Ayoyoo Mom, Ayoyoo Dad”, da haka ta shigo palourn ba sallama.

Sabeer ne ya kalle ta, sannan ya ce, “Sis ina sallaman?”

Tura baki Soffy tayi tare da haɗe fiska ta wuce wajan Mom, tana faɗin, “Mom i miss you soo much wallahi, Dad sannunku da gida.”

Sabeer rai a ɓace ya ce, “Ba da ke nake magana ba?”

Mom ce tayi caraff ta amshe tare da cewa, “Haba Sabeer wani irin rashin imani ne haka? Yarinyarka ta dawo ko hutawa ba tayi ba kana mata tsawa haka, ni fa bana son takura.”

“Mom sallama ne fa bata yi ba, kuma gaskiyan ne masifa? To Allah ya baki haƙuri Hajiyarmu, amma dai dawowan ma ba don Shaameekh ya mata magana ba, to ba dawowa za ta yi ba.”

Big Dad ne ya ce, “Soffy bana son shirme daga yau kada na kuma ganin kin shiga waje ba sallama, Sabeer kai kuma bana son surutu daga dawowan ta ka rufe ta da faɗa, sannan mamanka na faɗa kana faɗa.”

Ƙwafa big Mom tayi ta ce, “A’a Alhaji ka ƙyale sa dai yayi surutun tun da shi ya haife ni ko ya haifa mini ita, a ce ba za’a bar yarinya ta huta ba daga dawowanta sai masifa, Sabeer kada ka fita a idona inma uban wa ya saka ta dawowa ba dai ta dawo ba, to bana son dogon magana.”

Soffy miƙewa tayi tana faɗin, “Mom and Dad nikam na shiga daga ciki dan na gaji”, ta faɗa tana nufan hanyan da zai sada ta da ɗakinta, ba tare da ta cewa yayan nata komai ba.

Big Mom ta ce, “Okay doter a huta lafiya.”

Ajiyan zuciya Sabeer ya sauƙe tare da miƙewa yana faɗin, “Hajiyanmu da Alhajinmj nima na gudu safiyar alkairi.”

Iyayen nasa haɗa baki suka yi wajan cewa, “To Allah ya tashe mu lafiya.”

Da Ameen ya amsa ya fice a palourn yayi part ɗin da yake nasu yaran mazan gidan.

*****

Ɓangaren Shaameekh da ya shige wanka, sai da ya ɗau lokaci sosai kaman ko yaushe sannan ya fito, sanye da rigan wankansa mai kalan bula(blue)

Gaban dressing mirrornsa yaje yana drying gashin kan sa, yana gamawa ya shafa man sa mai stadan gaske, sannan ya ƙara tajewa, ya shafawa gashin nasa turaren kai, sannan ya taje gemun sa ɗan dai-dai gwanin sha’awa, lokaci ya duba ganin lokacin sallahn magrib ya ƙarato kuma daman yana da alwalansa, dan haka sama-sama ya shafa mai ya sanya jallabiya da short, ya fesa turarukansa masu daɗin ƙamshi na gaske, ya ɗau keynsa motansa ya fice a ɗakin. Ruwa ya ɗauka a fridge ya sha kamun ya fice a palourn, Motor ya shige ya mata key sai masallaci.

Ko da suka idar da sallahn bai tafi ba, har sai da yayi isha’i, bayan ya idar da azkar nasa da komai fita yayi a masallacin ya shiga motor yayi gaba. Sai da yayi tafiya sosai, wanda da alama ya bar anguwan da yake ma gaba ɗaya.

A Gaban wani babban gida yayi parking bai shiga da motorn ba ya sauƙa, yayi knocking ƙofan jin shiru ya sanya shi turawa ya shiga cikin gidan.

Direct palourn gidan ya shiga da sallama ba kowa a palourn nan ma shiru, sai sautin TV da ke aiki.

Bedroom ya wuce kai staye, “Assalamualaikum”, shiru ba’a amsa masa ba nan ma, sai dai ya ji alaman mostin ruwa a banɗakin, hakan ya sanya shi gane cewa mai gidan yana banɗaki ne.

Wucewa yayi wajan makeken haɗaɗɗen gadon da ke cikin ɗakin, ya yiwa kan sa masauƙi a bakin gadon ya zauna, tare da fiddo wayansa yana danna.

Can ba jimawa Manseer da ke banɗakin ya fito ɗaure da towel mai ɗan girma a ƙugunsa, ganin mutum zaune a kan gadonsa ya sanya shi buɗe baki zai tsala ihu, shi kuwa Shaameekh da kan sa ke kan waya, to daman ya ji fitowansa dan haka cewa yayi, “Ka ga malam kar ka kashe mini dodon kunne da ƙaton muryanki.”

Ajiyan zuciya Manseer ya sauƙe ya ce, “Innalillahi ɗan air kai ne dama? Za ka sa na sume”, ya faɗa yana ƙarasawa gaban closet nasa tare da cigaba da magana, “Wallahi Man ka storitani mutum sai ka ce wani aljani.”

“Ka sani ko ni aljanin ne, ƙaramin ɗan iskan gauro kawai a ce wai duka wannan ƙaton gida, ba mata sai dai mutum yai ta bin matan banza”, faɗin Shaameekh.

“Man ba gauro za ka ce ba, gauro da yayan sa ƙaton gardin gauro mara lafiya, dan tabbas baka da lafiya.”

“Mtsww! wai mutum ace a zo gida ba mai gadi balle mai aiki, taklless of matan gida tsabar rashin gaskiya, Allah dai ya yaye maka, bari naje Nigeria tabbas sai na zuga Abba an maka aure.”

Dariya Manseer ya saka ya ce, “Au wai Man an faɗa maka hakan damuna zai yi? Kai dai da ba kada ishashshen lafiya ne zai dame ka, ni ai ka ga alaman ko mata huɗu zan zauna da su kuma na yiwa ko wacce ciki, ka ga abin da zan ce maka shi ne kawai Allah ya stare hanya, dama dai auren nake so je ka zuga Abban kawai.”

“Ɗan iska kai ne dai ba ka da lafiya ni garau nake, matan ba su gabana ne kuma ban shirya aure yanzu ba”, Shaameekh ya faɗa yana taɓe baki.

“Matsalarka Man ni dai auren ma kuwa shi ne a rai na, sannan in ban yi wannan shekaran ba to Insha Allah wani shekara zan shiga daga ciki.”

Shaameekh barin danna wayan yayi yana kallon Manseer ya ce, “Man wai ina za ka je kake kwalliya haka?”

“Yawon nemo chika(beb) zan je, ai abin da kake son ji kenan dama”, Manseer ya faɗa yana fesa turare.

Taɓe baki Shaameekh yayi ya ce, “Ka gama muyi magana please ni shi ne abin da ya kawo ni, ba shirme ba.”

Bayan Manseer ya gama shiryawa, palourn suka fito suka zauna, Manseer ya ɗauko musu abin sha a fridge da snack’s ya ajiye, sannan ya ce, “Man ko zaka ci abinci?”

“Allah ya sauwaƙa naci girkin namiji, kai fa bayan iskanci har da daudanci kake yi, idan ba haka ba me ya haɗa ka da dafa abinci? Girki ai sai mace kai kuma ka ƙi ɗaukan Maid staban maƙon kuɗi.”

Manseer ya ce “Ba ruwanka da kuɗi na tun da na iya”, ya faɗa yana wucewa kitchen.

Da plate ya fito cike da jolof na taliya da manja, wan da ya ji kifi da su green beans, sannan ya zauna yana cin abincin sa, yana faɗin, “kai dai tun da ba zaka ci girkin namiji ba sai mace ya rage maka, nikam ba na cika cikina daman ni na girka abu na ba wani ya girka mini ba.”

Shaameekh Yoghurt kawai ya ɗauka shi ma kurɓan yayi ya ajiye, sannan ya ci gaba da danna wayansa.

Manseer yana gama cin abinci ruwa ya kora, sannan ya tattara wajan ya kai kwanukan kitchen, ba jimawa ya dawo ya zauna gefen abokin nasa.

Shaameekh ya ce, “Yanzu dan Allah bayan girki har da wanke plate’s or me suke ƙiran sa da hausa duk kai kake yi Man?”

“Capital Yes ma kuwa ɗan renin wayo, wai wanke-wanken ne mai ake ƙiransa da hausa, kana nufin baka san sunan wanke-wanke ba, to har da shara da goge goge ni nake yi, ai dai kaga gidan clean.

Ikon Allah fan’s, abin mamaki gani Shaameekh da dariya, har da riƙe ciki dan dariya, sai da ya stagaita sannan ya ce, “Kai ɗan daudu, kai ɗan iska, kai ɗan aiki and the most funny thing about all this is that kai ne kuma mai gadin gidanka”, ya faɗa yana dariya har da riƙe ciki.

Manseer ya ce, “Shege mugu kayi ta dariya kaman mahaukaci, ai dai wallahi a cewa mace ga ni ga kai ta zaɓa ɗaya, to am telling you ba mai zaɓan ka, dan  ba abinda za ka mata idan ba ka tara mata gajiya ba, sannan ka bar ta da ayyukan gida duka ita ɗaya.”

Shaameekh guntun ya ja ya ce, “Daman da kake maganan nan what is she there for? Ai in ni zan yi wa mace aikin gidanta, to ta mutu ba’a mata aiki ba wallahi, tayi aikinta staff sannan ta zo na ƙara mata da nawa aikin.”

Manseer ɗaga hannu sama yayi, ya ce Allah kar ka kashe ni ka nuna mini ran da zan ga Shaameekh, yana yi wa mace aiki, ai kuwa ranan duniya duka sai ta ɗauka, har media sai sun ganka sun sheda sun tabbatar mace ta saka ka aiki.”

Taɓe baki Shaameekh yayi ya ce, “Mu magantu akan abin da ya kawo ni.”

Manseer hankulansa duka ya tattara ya miƙa wa Shaameekh yana sauraransa, ya ce, “Ina sauraranka aboki.”

Sai da Shaameekh ya numfasa, sannan ya ce, “Akwai mastala babba Manseer.”

Cikin yanayin kulawa Manseer ya ce, “Mastalan me haka Man?”

Shaameekh cewa yayi…

*****

<< Shameekh 6Shameekh 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×