Skip to content
Part 9 of 11 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

A hankali drivern ke tuƙa su Ummiy, sakamakon Ummiy bata son ana gudu a kan hanya, baby da ke zaune a gidan baya a gefen Ummiy, dubanta ta ta kai kan Ummiy tana murmushi ta ce, “Ummiy gobe ai ba da wuri za mu tafi ba tun da flight za mu bi ko?”

Ummiy ta ce, “Idan kika tsaya baccinkin nan za ki tashi a ce miki na jima da isa Yobe, dan haka idan za ki gama komai da wuri ki gama.”

Baby shiru kawai tayi tare da kwanciya a jikin Ummiy har suka isa, driver na parking Ummiy ta fito, ita kuma baby ta ɗauka wa Ummiy jakanta da labcoat suka shige cikin gidan a tare, Ummiy tayi ɗakinta ita ma baby tana zuwa ta ajiye wa Ummiy labcoat nata ta wuce nata ɗakin, sai da ta wasta ruwa sannan ta shiga haɗa kayan da za ta tafi da su, a daren ranan duk suka gama kimstawa, kuma da wuri suka kwanta.

Washe-gari asabar da safe bayan sun karya sun yi komai da komai, zuwa ƙarfe takwas suka fito, sai da suka yi waya da Shaameekh da kuma Daddy sannan suka fice a gidan, baby sai washe baki take kaman wacce bata taɓa hawa jirgi ba, ko kuma bata taɓa zuwa Yoben ba.

Driver ne ya kai su airport, jirginsu ya ɗaga ƙarfe tara na safe sai Maiduguri, a can suka sauƙa, da yake Ummiy tayi magana da Daddy (yayanta baban Jidderh), to sun samu an turo musu driver daga gida, tun da wuri ma yake jiran isowan su, suna sauƙa ya saka kayakinsu a mota suka ɗauki hanyan Yobe.

Sun baro Yola ƙarfe tara sun iso Maiduguri ƙarfe goma sha ɗaya saura na safe, sun ɗau hanyan Yobe a cikin a wanni huɗu suka isa, da yake drivern gida ne to a sannu suke tafiya, zuwa ƙarfe huɗu na yamma da yardan Allah Ummiy suna cikin gidan alhaji baba.

Driver na gama parking baby ta ɓalle murfin mota ta fito, da gudunta tayi cikin gidan tana washe baki tana faɗin, “Yaya jidderh oyoyo ina kike ga babynki.”

Hajiya Mama da ke zaune a palourn ita da Alhaji baba, haɗe fiska tayi tana faɗin, “Fauziya sallaman da aka koya miki kenan?”

Tura baki baby tayi ya ce, “Stohuwa ina yaya Jidderh.”

“Ta tafi koyan sallama dan ƙaniyarki”, Ummiy da shigowarta kenan ta faɗa haka, tare da yin sallama.

Amsa sallaman Ummiy su Hajiya Mama suka yi, Alhaji baba na faɗin, “ƙyalesu amaryata ƴar Fulani, zo abinki na faɗa miki ina Hauwa’u take”, ya faɗa yana sakar wa baby murmushi.

Hajiya Mama taɓe baki tayi ta ce, “Da ka barta ai rashin sallaman nata ya kulata, Faɗimatu sannunku da hanya ko, sannu da gajiya.”

Ummiy na murmushi ta amsa tare da samun waje ta zauna tana faɗin, “Barka da hutawa Mama da Baba fatan mun same ku lafiya?”

“Lafiya alhamdulillah Faɗimatu, ki bari ku huta tukunna za mu gaisa ai, ga amaryata daga zuwa ta shiga sumbatun neman Hauwa’un da bata jima da barin gidan nan ba”, faɗin Alhaji baba yana murmushi.

Hajiya Mama ta ce, “Sai ta bi takwaran gidan ubanta ai tana can ita ma da rashin jin ta, halan Faɗimatu ke ce baki koya wa ƴar ki sallama ba.”

Ummiy tana murmushi ta ce, “Haram Mama, rashin ji ne kawai.”

“Ko kuma ɗaukin son ganin ƴan uwanta ba, ni ai nafi son haka Allah ya musu albarka ya ƙara haɗa kawunansu”, inji Alhaji baba ya faɗa da murmushi a fiskansa.

Duk amsawa suka yi da Ameen, sannan baby ta juya wai tayi fushi za ta fice a palourn, Hajiya Mama ta ce, “Idan kin fice dai kada ki kuma shigo mini gida.”

Alhaji baba ya ce, “A’a ba za’a yi haka ba, Amaryata ƴar Fulani zo abinki”, ya faɗa da stigan rarrashi.

Baby sai da Alhaji baba yayi rarrashi, Ummiy kuma ta aika mata da mugun kallo sannan ta dawo, direct wajan Alhaji baba tayi ta zauna ta maƙale sa tana faɗin, “Ni wajanka kawai na zo da yaya Jidderh, ba ruwana da matarka.”

Dariya Alhaji baba yayi ya ce, “Ƙyaleta kishi take, ta ga kyakkyawa bafulatanar Yola za ta ƙwace mata miji shiyasa.”

Murmushi baby tayi ta ce, “Kuma kaman tasan abin da nazo yi kenan, maza a bata red card a gyara mini gida na zo zama, kuma no kishiya in my house.”

Ba iya Alhaji baba ba, har Hajiya mama sai da tayi dariya tare da girgiza kai ta ce, “Ja’iran bafulatana.”

Ummiy ta ce, “baby tashi ki shigar mana da kayan ciki.”

“Duk ku shiga ku huta Faɗimatu, ga abinci ma duka yana jiranku”, faɗin Baba Alhaji cikin soyayya ne tilon ƴar sa mace.

Ummiy ta amsa wa mahaifin nata, tare da miƙewa tayi ɗakin da yake mallakinta a gida, baby ta shigo musu da kayakinsu sannan ta shiga wanka, tana fitowa Ummiy ma ta shiga ta wasta, duk suka sauya kaya sannan suka wuce cin abinci, Ummiy ta samu favorite nata haka ma baby, da yake Baabaa Larai tasan da zuwansu, ta shirya musu abinci irin wanda kowannensu ya fi so, suka gama ci suka yi sallolinsu.

Sai da suka idar sannan suka fito palourn wajan su Hajiya Mama, baby har ta zauna sai ta miƙe kaman an stikareta, wai za ta tafi gidan Daddy wajan yaya Jidderh, Hajiya Mama da Ummiy suka ce mata ta dawo lafiya, Alhaji baba kuma ya ce, “Amaryata ƴar Fulani zo kiyi zamanki ki huta, indai Hauwa’u ne za ta shigo anjima tun da tasan za ku zo yau, idan ma bata shigo anjima ba da sassafe za ki gan ta.”

“Ni fa sai na je Stoho, dan idan ban ga yaya Jidderhta ba babu kwanciyan hankali”, baby ta faɗa tana bubbuga ƙafa.

Hajiya Mama ta ce, “Allah ya raba mu da rashin kwanciyan hankali, wuce kada ki dame mu.”

Alhaji baba murmushi kawai yayi tare da faɗa mata to ta dawo lafiya, amma dai ta sa driver ya kai ta kar ta je a ƙafa ga gajiyan hanyan Yola bata warware ba.

Sai sannan baby ta fahimci yaren da ake mata, cikin farin ciki ta fice a palourn, tana zuwa haraban gidan ta fara yin karo da Kawunta Sale wan da suke ƙira da Uncle, tare da Yaya Ahmad yaron Kawunta Abdul-rahman wanda suke ƙiransa da Baba.

Uncle ne ya fara sakin murmushi yana faɗin, “Ina ganin babyn Uncle na tabbatar da Aunty Fatima tana gari.”

Ya Ahmad ya ce, “Ƴammata yaushe a gari?”

Baby na washe baki ta ce, “Oyoyo ga Uncle ga Ya Ahmad ni na fara ganinku, yanzun nan muka iso zan je gidan Daddy ne wajan yaya Jidderh.”

Uncle ya ce, “Baby tun baki huta ba?”

Murmushi tayi tare da cewa, “Uhmn! Uncle wajanta fa na zo.”

Ya Ahmad murmushi yayi ya ce, “Uncle kai ka shiga wajan stoffi ni bara na ajiye budurwata a gidan Daddy.”

Uncle murmushi yayi da yake yasan Ahmad neman maganan baby kawai yake, sai ya musu a dawo lafiya ya shige cikin gidan wajan Aunty Fatimansa shi ma.

Baby bubbuga ƙafa tayi ta ce, “Ka ga ba Ya Ahmad ka fara za ka kashe mini kasuwa ba.”

Dariya Ahmad ya saka har suka ƙarisa wajan motansa suka shiga, yana tada motan ya ce, “To ƙarya nayi ne babyna ko ni ba saurayinki bane?”

Tura baki baby tayi ta ce, “Gaskiya ni a sauya mini suna ma, na daina son babyn, haka kawai cousin’s za su kashe mini kasuwa, kuna cewa babynku ai sai a ɗauka duk samarinane ku, ƴar yarinya da ni.”

Ya Ahmad dai dariya ya dinga yi yana zolayanta, dan daman aikin kenan idan ya haɗu da ƙannen nasa, indai ba wacce yasan za ta renasa ba ne to sai ya zolayeta, sai ya ce shi dukkansu zai aure su, shi mata fiye da huɗu zai aura.

Yana driving suna dariyansu har suka isa gidan Daddy da yake ba nisa, dan gidan Daddy shi ne gida na uku a jerin gidajen nasu, yana horn mai gadi ya buɗe musu suka shiga, ko da yayi parking locking na ƙofan baby yayi, sai da ya fita sannan ya buɗe mata da kansa yana faɗin, “rankishidaɗe budurwata an iso.”

Baby dariya ta saka tare da fitowa tana faɗin, “Allah bai wa matar Ya Ahmad haƙuri, gaskiya sai ta daure da stokanan kan nan, idan bata sani ba zuciyanta zai buga ta ɗauka gaske ne.

“Ah haba ai ina yin mata kuma na fita harkanku na gama yaudareku.”

A tare suka jera suka shige cikin gidan baby na dariya wai ya gama yaudare su, baby ta wangale muryanta tare da yin sallama da ƙarfin gaske kaman za ta fasa musu dodon kunne, dan Ya Ahmad sai da ya toshe kunne yana dariya kawai ya ƙarasa cikin palourn ya zauna, ita kuma baby da ƙarfi take cewa, “Jama’an gida ina yaya Jidderhtaaaaa?”

Mummy da tun daga ɗakinta ta jiyo muryan baby, fitowa tayi tana faɗin, “Ai muddin aka ji ana yi wa jidderh ƙiran biyan bashi to ke ce baby, Allah shiryaki ya nuna mana ranan da za ki girma.”

Baby na ganin mummy da gudu ta je ta rungumeta tana dariya, tana faɗin, “Ameen Hajiya Mummy tamu ta Daddy.”

Jan kunnen baby Mummy tayi tare da cewa, “Sarkin zolaya kowa ya kakanki ko.”

Baby murmushi tayi, dai-dai lokacin Deeyah da Subby suka fito, tana ƙoƙarin musu oyoyo kuma sai ga Yusuf, wani irin ihu ta yi tare da yin stalle suka rungume juna da Yusuf, sannan suka tafa ta ce, “Ko ban ga yaya Jidderhta ba an biya ni, tun da ga my Yusee magana ta ƙare.”

Mummy waje ta samu ta zauna tana faɗin, “Kada a yaudara mini yaro a ci kuɗinsa a kyalesa a ce yayi ƙarami.”

Baby dariya tayi ta ce, “Ai ni da Yusee ana together Mummy, shi ne ma mijin bana kula kowa dan da shi za’a yi, ya ce na riƙe alƙawari, ko ba haka my Yusee?”

Yusuf yaro kyakkyawa mai kimanin shekaru goma sha biyar, murmushi ya saki tare da cewa, “Babyna sannu da zuwa.”

Deeyah da Subby ƙarisowa palourn suka yi suna faɗin, “Ai tun da kika ga maƙale matan ki dole ma ki mance da kowa, mu wa muka kashe miki ba oyoyo?”

Baby murmushi tayi ta ce, “Yaya Subby yaya Deeyah nayi missing naku Allah, amma fa tun da naga Yusee na to ko yaya Jidderh na yafe mata oyoyo.”

Jidderh da fitowanta daga ɗaki kenan, ta ji abin da baby ke faɗa sai ta murmusa tare da cewa, “yaya Jidderh ma ta yafe miki oyoyon babynmu.”

Jin muryan Jidderh kaman daga sama, tuni baby ta miƙe tayi wajanta, tana zuwa ta faɗa jikinta, Jidderh ƙin rumgeta tayi, sai da baby ta bada haƙuri wai ai da wasa ta faɗa, sannan Jidderh ta rungumeta tana musu sannu da hanya, duk palourn sai dariya suke yi har Yusuf.

baby ta ƙi barin jikin Jidderh tana maƙale da ita, har aka ƙira magrib kowa ya tashi dan gabatar da salla, Ya Ahmad ma ya yi wa Mummy sallama yayi tafiyansa, baby bin Jidderh tayi ɗakinta, suna idar da sallah suka fito suka yi wa Mummy sallama, suka wuce gidan Baba Alhaji wajan Ummiy.

Uncle Sale yana shiga cikin gidan direct yayi wajan Ummiy yana faɗin, “oyoyo barka da zuwa sannu da hanya Aunty Fatima.”

Murmushi Ummiy tayi ta amsa, waje ya samu ya zauna sannan ya gaishe da iyayen nasu suka amsa, ta gaisheta ita ma suka amsa, sai da suka taɓa hira sosai har magrib kamun nan, shi da Alhaji baba suka wuce masallaci, Ummiy tayi ɗakinta dan yin nata sallahn, Hajiya mama ma tayi ɗakinta.

Jidderh da baby da ƙafa suka taho, suna tafiya suna hira baby sai surutu take cika Jidderh da shi, tuni ta faɗa mata Ya Shaameekh zai duba wani mara lafiya, kuma zai yi wasa kamun ya taho, jidderh duk bata san da wannan ba sai a bakin baby, da yake ba wani waya suke yi ba, idan bata ƙira ba baya ƙiranta, sai dai idan ta damesa da misscall’s kamun nan zai ƙira, kuma ko sun yi wayanma baya wuce na minti biyar shikkenan an angaisa sai sallama, amma wani abu guda shi ne ita sam abin baya damunta, sai ma ƙara mata jin soyayyansa da yake yi, ita za ta iya zama da Ya Shaameekh ko ya yake.

A haka baby na surutunta, jidderh kuma na tunaninta har suka iso, sai da jidderh ta gaisa da baba mai gadi cikin fara’a, sannan suka wuce cikin gidan, sallama ɗauke a bakinsu duk suka shiga, ganin Uncle da small Uncle bai sanya jidderh mamaki ba, dan dama tasan muddin Ummiy ta zo kamun a ga kowa sai an gansu.

Cikin fara’a suka ƙarisa palourn, jidderh na sunne kai cikin kunya ta ƙarisa wajan Ummiy ta durƙusa har ƙasa tana faɗin, “Barka da hanya Ummiy, sannunku da zuwa.”

Ummiy hannunta ta kai ta ɗago jidderh ta zaunar da ita, sannan tana murmushi ta ce, “Yauwa Uwar masu gida, fatan mun same ku lafiya?”

“Lafiya alhamdulillah! Sai alkairi Ummiynmu.”

“Amaryata kunyan gwaggon taku kike yi haka?” Alhaji baba ya faɗa yana murmushi.

Hajiya Mama ta ce, “To gulma ya mosta ba dole tayi ta sunne kai ba, takwara da feleƙen stiya, yaushe tabar gidan nan amma har ta dawo.”

Uncle da small Uncle duk murmushi suka yi, tare da amsa gaisuwan jidderh da baby, dan sun san stokana ce kawai irin ta iyayensu, amma duk sun san abin da ya sa jidderh ke kunyan gwaggonta ai.

Ummiy murmushi tayi kawai ta ce, “baby tun da kin sako ta gaba ta zo, ai sai ku je ki mata hira, kin ga Hajiya na takurawa yarinyata.”

Hajiya Mama taɓe baki tayi ta ce, “Ku iyayenta ne ai shiyasa take muku kunya, da bakwa nan da takwara ta kasa mini halinta sarai na santa.”

Alhaji baba ya ce, “Amaryata je ku huta abinku ki ƙyale stohuwannan kishi take.”

Jidderh da duk kunyan Ummiy ya cika ta, a hankali ta miƙe bata ce komai ba suka yi ciki, baby ta rufa mata baya, sannan fa ta saki ajiyan zuciya ta fiddo wayanta, dan ƙiran Ya Shaameekh ta sanar da shi isowan su Ummiy, tun da baby ta faɗa mata basu yi waya da shi ba, amma jidderh ta ƙira ya fi sau uku bai ɗauka ba, haka ta haƙura kawai ta aje wayan, ta ci gaba da sauraran hiran baby.

Su jidderh na barin palourn, small Uncle ya ce, “Eh Aunty Fatima mun yi sa’ar surka, irin wannan ladabi da jin kunya, ai a matan yanzu ba’a samun irinsu, Allah dai ya nuna mana wannan biki da rai da lafiya.”

Uncle Sale ya ce, “Ameen ya Rabbi, ai Uwar masu gida ba laifi, ni duk yaran namu ma ban ga mai irin hankali da nistuwarta ba, mata da mazan duka ba irinti, Allah ya mata albarka ya tabbatar da alkairi.”

Ummiy na murmushi ta ce, “Sunan Hajiyarmu gare ta ai dole tayi hankali.”

Hajiya Mama taɓe baki tayi, ta ce, “Ku kuke ganin hankalinta tun da ƴar ku ce, ni ai Isma’il da Maryam sun renani da suka mini takwara da wannan ja’ira mai fitinan stiyan.”

Ummiy ta ce, “Mama kishi dai kawai kike yi.”

“Haba kishi da wannan mummunan ƴar taku, Allah sauwaƙa”, faɗin Hajiya Mama.

Duk sai abin ya basu dariya, har Alhaji baba sai da ya murmusa sannan ya ce, “Kishin kuwa kike yi, ga shi ya fito a filin Allah, ai duk jikokina mata a dai cikin waɗanda suka girma ba mai kyawun Hauwa’u, ɗan gwanda ita fauziyan ma da yake ita ruwa biyu ce ta haɗa jini da Fulani, amma duk da haka bata kai Hauwa’u ba.”

Duk murmushi suka yi har Hajiya Mama, domin kuwa gaskiyan Baba Alhaji, duk da dai dan jidderh sunan matarsa gare ta.

Haka suka sha hiransu, har isha’i tayi, su Uncle suka yi wa Ummiy sallama a huta gajiya sannan suka wuce masallaci, daga can kuma an yi sallah kowa ya wuce gidansa, Alhaji baba ya shigo tare da Ya Sabeer da Ya Faisal, dan da wuya ka raba gidan Alhaji baba da jama’a, ga ƴaƴa ga jikoki Masha Allah.

Su Sabeer duk sun yi wa Ummiy sannu da zuwa, sun gaisa sun sha hira sosai har sannan Sabeer ke sanar da su Baba Alhaji ai Soffy ta dawo, Ummiy murmushi tayi ta ce, “Masha Allah! Ƴar gidan gwaggo mutan India an samu dawowa kenan.”

Ƙwafa Hajiya Mama tayi ta ce, “Wato ma Safiya ta kwana biyu da dawowa, amma saboda iyayenku sun ɗaure mata wajan zama shi ne ko ta zo gaishe da mutane, ba mastala Allah ya kawo Sulaimanun lafiya, dan naga kaman shi yake son ya zama sallamammen miji, an saka mishi suna Sulaiman ai an yi laifi, bari shi kuma ya sallame.”

Ya Sabeer da Ya Faisal duk haɗa baki suka yi wajan bai wa Hajiya Mama haƙuri, Ummiy ma ta ce, “kiyi haƙuri Mama, wataƙila gajiyan hanya ne bai ƙyaleta ba.”

“Fatima ɗaure wa ƙarya wajan zama, tafiya a jirgin ne gajiya? Kuma a jirgin kuka zo ai amma bai hana fauziya zuwa wajan takwara ba” Hajiya Mama ta faɗa tana jefa wa Ummiy mugun kallon, da ya sanya ta jan baki tayi shiru.

Alhaji baba ya ce, “Magana ya ƙare, shi Sulaimanun zai shigo ai, kuma ranan taro dole duk za su zo.”

Hajiya Mama ta ce, “Amma Alhaji kasan Sulaiman yanzu ko shigowa gaisuwan ma yaushe rabon da a gansa.”

Alhaji baba ya ce, “Shikkenan magana dai ya kare Hajiya.”

Dan dole Hajiya Mama(masifatu ƙawar Baabaa mero) tayi shiru, daga nan kuma Sabeer da Faisal suka musu sallama suka fice.

Suna fita Faisal ya ce, “Soffy kuma ta shiga uku da Hajiya Mama dan ran ta ya ɓaci.”

“Dai-dai kenan wallahi, ai yarinyan nan samun wajanta yayi yawa, su Dad sun ɗaure mata gindi da yawa, sam bata ji ta rena kowa, daman Shaameekh ne kawai dai-dai ita kuma baya nan, ni Allah Allah nake wani Lahadi ya zagayo ya ji a jikinta”, faɗin Sabeer yana murmushin mugunta.

Faisal dai ajiyan zuciya ya sauƙe ya ce, “To Allah ya kyauta.”

“Ameen dai” faɗin Sabeer, sannan suka yi sallama kowa yayi gidansu.

Ummiy da ƙyar ta bai wa Hajiya Mama baki sannan ta haƙura, Alhaji baba daman da mitan Hajiya Mama ya ishe sa miƙewa yayi ya shige ɗakinsa ya bar su a palourn.

Su Ummiy ma shigewan suka yi dan su kwanta su huta, Ummiy na shiga ɗakinta ƙiran Daddy na shigowa, nan ta ɗauka suka gaisa ya musu sannu da hanya, da kuma ya ta samu su baba da mama, ta faɗa masa duk suna lafiya suna gaida shi, ko da ya tambayi baby ta faɗa masa suna tare da jidderh, murmushi kawai yayi suka ci-gaba da hiransu, sun ɗau lokaci kamun suka yi sallama, ba tare da Ummiy ta ƙira Shaameekh ba, tayi addu’a ta kwanta dan huta gajiya.

Baby da jidderh a ɗakin Hajiya Mama suka zauna, suna idar da sallahn isha’i baby na surutu har bacci yayi gaba da ita, jidderh kuma danna wayanta take har lokaci ya ɗan ja, sannan sai ga ƙiran Shaameekh, cikin farin ciki ta ɗauka, suka gaisa yana amsa mata kaman ko yaushe, da fara’a ta ce masa, “Su Ummiy ma sun iso da jimawa ai, ga babyma muna tare amma tayi bacci.”

Jinjina kai Shaameekh yayi a ɓangarensa ya ce, “Masha Allah, ki gaishe su sai zuwa gobe zan ƙira Ummiy yanzu ina ɗan wani aiki ne.”

“Allah ya taimaka abun ƙaunan Jidderh, Allah ya kuma ba da sa’a, Allah sa kuyi aikin da wasan duka cikin nasara.”

“Ameen Nagode”, Shaameekh ya faɗa a taƙaice, dan yasan tabbas baby ce ta faɗa mata.

Sallama suka yi ya kashe wayansa, Jidderh ma gaba ɗaya ta kulle wayanta, dan tasan halin Safwan yanzu sai ya ce zai ƙirata ya kasa bacci sai ya ji muryanta, tana kashewa ta aje ta ɗauro alwala sannan tayi addu’a, ita ma ta bi lafiyan gado sai bacci.

Washe-gari da wuri baby da Jidderh suka tashi, suka yi aikin gidan tare da baabaa larai, sai da suka gama sannan suka koma suka wasta ruwa, ba jimawa duk kowa ya fito suka karya, Ummiy ta gaishe da iyayenta, su Jidderh ma suka gaisheta.

Suna gama karyawa Ummiy ta koma ta kwanta dan ƙara hutawa,(Abinka da likita masu aikin da ba hutu kullum ana hanyan asibiti, Allah ya saka muku da mafificin alkairi likitocinmu maza da mata, masu ƙoƙari wajan ceto rayukan bayin Allah.), Su baby ma baccin suka koma.

Wannan rana Ummiy wuni tayi tana hutawa ba in da ta je, ko da ta tashi ma hira suke yi da iyayenta, su ci abinci su yi sallah shikkenan.

Yanzun ma Ummiy zaune suke da iyayen nata suna hira, Ummiy ce ta ce, “Yauwa Baba a yi wa aboki afuwa da uzuri, sai ranan asabar zai samu zuwa Insha Allah saboda wasu ayyukan da suka taso masa.”

Hajiya mama ce ta tari numfashin Baba Alhaji ta ce, “Wani irin ayyuka ne haka duk bai tashi yin su ba sai yanzu, shi wannan yaron ma fa baya ji sam amma shi ma za mu haɗu ne.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “Hajiyarmu ayi haƙuri, zai staya duba wani mara lafiya ne shiyasa, kuma a yanda ya faɗa mini, larabawan sun ce mara lafiyan na cikin mawuyacin hali ne, sannan ga wannan aikin nasa na dambe wai suna da shi.”

“Allah bai wa marassa lafiya gaba ɗaya lafiya, shi kuma da yake da lafiyan yake wasa da nashi Allah ya shirya sa, idan ba wasa da lafiya ba me wani abu wai shi dambe, kai amma wannan yaro ba sai a hankali”, faɗin Hajiya mama tana bata fiska.

Alhaji baba murmushi yayi ya ce, “To Allah Ubangiji ya taimaka, ya kuma ba da sa’a, Allah ya kawo shi lafiya, yau da asabar ai duk ɗaya ne a wajan Allah, muddin dai muna da nisan kwanan ganin ranan, dan dole a jira abokin takarana, wannan zaman dan su za’a yi.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “Ameen ya Hayyu ya Qayyum Baba.”

Sai da Ummiy ta diɓa kwana biyu mai kyau tana hutawa, sannan a na uku ta shirya dan zuwa gidan yayyunta ta gaishesu, gidan big Dad ta fara zuwa, amma cikin rashin sa’a ta samu baya nan da yake ba da sassafe ta je ba, bata samu Soffy a gida ba wai ta fita da sassafe, wannan ma mai aiki ce ta faɗa mata, domin big Mom kam ko kallon arziƙi Ummiy bata samu a wajanta ba, tun da ta fito ta kalli Ummiy ce ta zo sai ta juya ta koma ciki basu ko gaisa ba, kuma daman muddin big Mom ta amsa gaisuwan Ummiy, to a gaban Hajiya mama ne, domin duk iskancinsu suna shakkan Hajiya mama da Alhaji baba, duk da Alhaji baba ba ya masifa, amma muddin abu ya shafi na kawo rabuwan kan zuri’ansa ne to sai inda karfinsa ya ƙare a kan mutum.

Ummiy inda sabo ta saba, dan haka bata wani jima ba ta miƙe ta fice abin ta, driver ya ja mota suka yi gidan Daddy, da sallama ta shiga palourn, cikin sa’a kuwa ta samu Daddy na gida, dan yau ɗin bai je office ba, suna zaune da matarsa suna hiransu yana aikinsa a gida, duk yara sun tafi school, Jidderh ce daman kawai ta gama makaranta a yaransa, ita kuma sun tafi gidan small uncle da baby, dan matan small uncle wacce suke kira da Aunty Zee bata da damuwa sam.

Daddy da Mummy da murmushi suka amsa sallaman Ummiy, Mummy na faɗin, “lale maraba da mutanen Adamawa.”

Ummiy ta samu waje ta zauna tana faɗin, “Yauwa matarmu, yaya sannu da hutawa ashe yau da sa’a nake tafe, na ɗauka kai ma ka tafi office ai kaman yaya Sulaiman.”

Murmushi Daddy yayi ya ce, “sannu da zuwa Fatima, sannunku da hanya, kin yi sa’an samuna kam dan kwana biyu tun zuwanki bana nan shiyasa ma ba ki ga na leƙa gidan Baba ba, jiya cikin dare na dawo, kinsan abubuwan ba zama sai a hankali.”

“To dai Allah ya taimaka yaya, fatan mun same ku lafiya?”

“Lafiya alhamdulillah sai alkairi Fatima, ya mai gidanki ya labarin Mai sunan Baba, dan fauziyan kam na gansu tare da Uwar masu gida.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “Baban fauziya yana lafiya, aiki ne ya hanasa samun daman zuwa dan bai dawo ba, Shaameekh kuma yana can ƙasar mutane yaya.”

“Allah ya taimaka ya ba da sa’a, shi kuma mai sunan Baba yaushe zai shigo to? dan na samu labarin ita Safiya ta kwana biyu da dawowa ma, Kabeer kuma sai ƙarshen wannan satin za su shigo da sauran ƙannensa.”

Ummiy ta ce, “Ameen yaya, Insha Allah shi ma Shaameekh ƙarshen satin nan zai dawo, ko ranan Juma’a ko Asabar, yanzun ma duba wani mara lafiya ne ya riƙe sa da kuma wasan da za su yi.”

“To Allah taimaka ya basu sa’a, Allah musu albarka ya kawo su gida lafiya duka, ni bama waya da shi kwana biyu kinsan yaron naki sai a hankali, ga busy kaman iyayensa, ga kuma kunya kaman mace.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “Shaameekh kam haka yake sai addu’a, ko Baban fauziya fa sai idan ya ƙirasa, amma haka kawai ba ƙiransa yake ba sai a hankali.”

“Allah shirya mana shi ya masa albarka, kinsan wasu mutanen dama haka suke da kunya, akwai misalansu da yawa, ko cikin sahabban Annabi SAW, ana yaba irin kunyan sayyadina Uthman RTA”, Daddy ya faɗa yana murmushi.

Mummy da daman Ummiy na zama ta tafi kawo mata ruwa, dawowa tayi ɗauke da tire da abubuwa a kai, ta dire a gaban Ummiy tana faɗin, “Mutan Yola ga ruwa, kada a ce nabar miji da ishi.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “Daɗina da matar nan neman lada, ko masu aiki ta ƙi bari na kawo mata, wai komai za ta yi da kanta dan kawai tana storon kishiya”, faɗin Ummiy da take kai abin sha bakinta.

Daddy murmushi yayi ya ce, “kema dai kya ce haka Fatima, sam-sam Maryam bata barin wani ƙofa ma balle na samu daman ƙaro aure, komai yi take.”

Murmushi Mummy tayi ta ce, “Ni bana storon kishiya, idan Allah ya kawo muku ta gari ku auro.”

“A’a faɗa gaskiya fa matarmu”, Ummiy ta faɗa cikin zolaya.

Mummy ta ce, “Gaskiyan kenan Maryam bata storon kishiya, nasan na riga na gama samun tawa fadar ban da damuwa da kishiya.”

“Wannan haka yake, kin gama kanainaye mu matarmu”, faɗin Ummiy, sannan suka gaisa cikin fara’a da zolaya, Daddy yana jin su yana aikinsa sai murmushi yake yi abinsa.

Ummiy wuni tayi curr a gidan Mummy bata je ko ina ba, har yaran makaranta suka dawo suka sameta, duk da sun je gidan Alhaji baba sun mata oyoyo, amma yanzun ma cikin farinciki suka mata oyoyo suka gaisa, Yusuf mutumin baby yana maƙale da Ummiy.

Mummy ta ƙi barin Ummiy ta ɗaga ko cokali, duk aikinta ita take yi, ko me Ummiy ke so kamun ta mosta ta miƙo mata, ba ruwanta da Ummiy ƙanwar mijinta ne, saboda Ummiy ta girmi Mummy a shekaru, ba komai stakaninsu sai girmama juna da wasa da fara’a, Daddy ma tare da shi suka wuni har ya fita ya dawo, dare nayi Ummiy ta ce za ta koma gidan Alhaji baba, amma Mummy ta dage sam sai dai su kwana, haka Ummiy ta haƙura suka kwana, washe-gari da sassafe ta koma gidan Alhaji Baba, saboda sauran yayyun nata da suke nan, sun riga da sun haɗu da su a gidan Alhaji baba, Daddy da big Dad ne kawai daman tun zuwanta basu zo ba, shiyasa ta je gidajensu, yanzu sai anyi meeting, idan sauran yayyun nata sun dawo za ta ƙoƙarta duk ta je musu kamun su koma ita ma ta koma.

Jidderh ta cancarawa baby kistonta mai ɗan iskan kyau, tun da baby ta zo aiki ya same su, yau su je nan gobe su je can, su dai su Meelat gaba ta kai su wai gobaran titi a Jos.

*****
Ɓangaren Shaameekh mutanen Dubai kuwa, hankali kwance ya samu ya gama duk abin da ya kamata, ranan Litinin ya haɗu da likitocin da za su yi aiki tare, Dr. Naresh Trehan daga India, da kuma Dr Fouad M Abbas daga Europe, sai shi oga Shaameekh Dr Adam M Aliyu.

Sun yi arrangement na komai, kuma cikin ikon Allah ranan Laraba suka yi aiki, wan da babu ko shakka da yardan Allah sun yi nasara, dan dukkansu ƙwararrun likitoci ne akan mastalan wannan mutumin, sai dai farkawansa ne kawai za’a jira, daman normally wannan aikin idan aka yi wa mutum sai ya kai wata kamun ya farfaɗo saboda wasu condition’s, amma su suna stammanin in Allah ya yarda ba zai kai watan ba.

Bayan Shaameekh ya gama da issuen mara lafiya ya samu nistuwa, shikkenan kuma ya mayar da hankalinsa wajan ci-gaba da tarining na wasan da za su gabatar ranan juma’a da yardan Allah, daga nan kuma sai tahowa gida Nigeria.

*****
Kuluwa na sakin wannan ƙayataccen murmushin, a hankali ta mosta laɓɓanta, cikin sansanyar daddaɗan muryanta ta ce, “ALHAMDULILLAHIL LAZI AHYANA BA’ADA MA AMATANA WA ILAIN-NUSHUR….” Ta karanto da duk sauran adduo’in tashuwa a bacci, sannan ta miƙe tsaye tare da yin miƙa, Uhmn Masha Allah santaleliyar haɗaɗɗiyar budurwa.

Cikin nistuwa take tafiya kaman wacce ke tambayan ƙasa kamun ta taka, har ta fito a ɗakin nata, jin ba alaman mostin iyayenta hakan ya tabbatar mata basu tashi ba, tura ƙaramin bakinta tayi tare da zuwa bakin ƙofan ɗakin tayi sallama.

Kawu cikin baccinsa da bai yi nauyi ba ya jiyo mostin buɗe kofa, tashuwa yayi ya zauna yana sakin murmushi dan yasan ba ko shakka zai yiwu Kulu ce, tana yin sallama kuwa ko gama rufe baki bata yi ba ya amsa, da sauri ya tashi Hajjo yana faɗin, “Hajjo tashi Kulu na sallama.”

Hajjo a ɗan firkice ta tashi, kusan rige-rigen isa bakin ƙofan suka yi, haka suke a duk lokacin da maganan Kulu ya dawo, to farinciki suke ji kaman ranan ta fara magana a duniya, fitowa suka yi Kawu ne ya fara mata magana cikin ƙauna, da fillanci ya tambayi ya aka yi me take buƙata?

Kuluwa cikin shagwaɓa ta ce, “Banɗaki Hajjo za ta raka ni.”

Ba musu Hajjo ta yi gaba ta bi bayanta suka fice, rakata tayi har cikin banɗakin dan ko ta tsaya a waje to ba za ta yarda ta shiga ita kaɗai ba wai storo take, sai da ta gama buƙatar ta sannan suka fito, Kawu ma ya shiga ya kama ruwa ya fito, duk su ukun tare suka yi alwala, Kawu ya ja su suka yi nafila a tare, har sai da aka ƙira sallah sannan ya tafi masallaci, Kulu da Hajjo suka yi nasu sallahn su ma.

Suna idar da addu’a da komai, Kawu na shigowa Kulu ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa da fara’a yana saka mata albarka, yana mai ƙara hamdala a zuciyansa, yana addu’an Allah ya raba Kulu da wannan cuta da aka rasa gane masa, Allah ya bata lafiya na har abada.

Hajjo ma amsa gaisuwan Kulu tayi, sannan Kulu ta miƙe Hajjo ta raka ta banɗaki, Kulu yau da kan ta tayi wanka sannan suka fito, ta wuce ɗakinta, sharp-sharp ta shirya cikin riga da wandonta masu taushi, sannan ta fito ta wuce kitchen, ta hura wuta ta ɗaura ɗumame, ta fito ta share stakar gida, kamun ta shigo ciki kuma Hajjo ta gyara palourn da ɗakunan nasu, amma Kulu sai da ta ƙara gyarawa ta cika ko ina da ƙamshi, tuni gida yayi fes-fes sai ƙyalli kawai yake yi da ƙamshi.

Kuluwa aiki ta sha kaman wata mai aiki da inji, kuma sam-sam babu sanyin jiki a ayyukanta, sai dai in tafiya take to ka rantse ƙwai ne ya fashe mata a ciki.

Ita ta haɗa komai na karyawa, suka karya da iyayenta, sannan Kawu ya miƙe zai fice, ta tashi ta rakasa tana faɗin ya kawo mata staraba.

Kulu na dawowa ta gyara wajan, ta yi wanke-wanke da komai, ta je wajan dabbobin Kawu ta duba su tana murmushi har mai kiwonsu ya zo ya fice da su, sannan ta gyara wajan ta koma cikin gida, sai da Hajjo ta kuma rakata banɗaki tayi wanka, amma yanzu a waje Hajjo ta staya da yake gari yayi haske storon nata ya ragu, sannan suka koma ciki ta kuma saka wani dogon riganta mai kyau ta kanti, ta zo ta kunna musu kallo, Hajjo da ita ma tayi wanka ta shirya zama tayi tana faɗin, “Kulu yau ba za ki makarantan ba ne?”

“Hajjo sai gobe zan je yau kisto za ki mini”, ta faɗa da ƴar muryanta cikin shagwaɓa.

Hajjo bata ce komai ba kuma, tun da tasan idan Kulu bata yi niyan yin abu ba babu mai saka ta dole musamman makaranta, idan kuma tayi niya to ba sai an saka ta tayi ba, watarana tana son bokon watarana kuma bata so haka take, hakan kuma baya hanata ƙoƙari a makaranta dan a ta Allo har ta sauƙe, littatafai take yi da hadda.

Kulu zama tayi a ƙasan palourn akan pillow, Hajjo kuma na kan kujera suna fiskantan TV, Hajjo ta fara taje kan Kulu ta fara raki tana faɗin, “Wayyoo kai na Hajjo, Wayyoo zafi, nikam na fasa.”

Hajjo ta ce, “Ai nasan halinki Kulu, ina sake wa za ki ce a miki, abu mai sauƙi ne ma ki saka kuka, dan haka sai mun yi, ni halina da ke kenan idan bakinki ya buɗe Shikkenan duka duniya sai sun sani, ki addabi mutane da abu kaɗan ihu kaman jare.”

Tura baki Kuluwa tayi ta ce, “Yauwa Hajjo kinsan me?”

“Uhmn ko banyi niyan yin hira ba sai kin mini ai Kulu, shiyasa idan bakin ya kullu duk sai ki sa gidan yayi ba daɗi, ni bar damuna da surutu muyi kallon.”

Hajjo na kitso Kulu na raki, tana kuma kan surutu kaman cakwai-kwai-wa, ga murya zaƙi kaman sikari, dan dole Hajjo ke amsawa bata yi niya ba, idan kuma abin ya ishe ta sai ta yi shiru ta ƙyaleta, gaba-daya surutun Kulu ya hana Hajjo fahimtan mai ma ake a TV, Allah Allah kawai take Kawun Kulu ya dawo ko za ta huta, dan wannan suturun sai shi, daman shi ke biye mata.

<< Shameekh 8Shameekh 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.