YUBI
Icce Tun Yana Ɗanye Ake Tankwara Shi
Ina tafe ina saƙe-saƙe a raina, 'To wane irin kasuwanci ne Umma take yi da take samun kuɗi haka? Me ya sa take ɓoye samunta? Lallai da walakin goro a miya.'
Da wannan na ƙarasa ɗakina tare da ɗaga katifata na tura maganin ciki sannan na mayar na yi kwanciyata, a lokacin ne kuma zazzaɓin da na gama yi wa ƙarya ya yi mini dirar mikiya.
Don haka na fara yunƙurin jingine duk wani tunani a gefe na. . .