Skip to content
Part 2 of 10 in the Series Sharri Kare Ne by Rukayya Ibrahim Lawal

YUBI

Icce Tun Yana Ɗanye Ake Tankwara Shi

Ina tafe ina saƙe-saƙe a raina, ‘To wane irin kasuwanci ne Umma take yi da take samun kuɗi haka? Me ya sa take ɓoye samunta? Lallai da walakin goro a miya.’

Da wannan na ƙarasa ɗakina tare da ɗaga katifata na tura maganin ciki sannan na mayar na yi kwanciyata, a lokacin ne kuma zazzaɓin da na gama yi wa ƙarya ya yi mini dirar mikiya.

Don haka na fara yunƙurin jingine duk wani tunani a gefe na rufe idanuna wai ko na samu bacci ɓarawo ya sace ni, amma hakan ya ci tura. Ranar a haka na wuni a kwance sallah kawai take tada ni sai wajajen ƙarfe 2:30 na dare baccin ya sure ni.

Washegari ta kama ranar Asabar don haka tun da sassafe Umma ta tada ni, bayan ta tambaye ni jiki na ce da sauƙi na fito na kama mata wasu ‘yan aikace-aikacen gidan da na saba yi.

Ni ɗaya tilo ce a wurin iyayena sauran duk sun rasu, kasancewar mahaifiyata wabi take yi (ma’ana da ta haifi yaro ba ya jimawa a duniya yake komawa).

Bayan mun kammala komai ta umurce ni da shiryawa don tafiya makarantar islamiyya tun da ta ga alamar sauƙi a tattare da ni.

Ba musu na yi wanka na shirya a cikin gogaggen uniform ɗina kalar fari da tsanwa, duk da sarai na san cewa yadda zan je haka zan dawo ba tare da na kama komai a cikin abin da ake koyar mana ba, amma hakan bai hana ni yin haramar tafiyar ba.

A hankali na leƙa waje na ga ba kowa a kusa da ɗakin nawa sai na koma ciki na buɗe akwatina na hankaɗe kayan sawana, sai ga babbar wayata ta shafawa da nake ɓoyewa a can ƙasan tufafina gudun kada wani ya san da ita. A hanzarce na ciro ta na jefa a ƙasan jakata na rufe da zif na fito.

A tsakar gida na sami Umma na yi mata sallama sa’annan na ƙarasa ɗakin Abbana na karɓi kuɗin makaranta naira ɗari na fito suna saka mini albarka tare da addu’ar neman kariyar ubangiji a kaina.

Koda na isa cikin makarantar ƙarfe 8:00 na safiya wannan kuma shi ne lokacin fara darasi don haka kai tsaye na shige ajinmu, kafin ma na zauna Malaminmu ya shigo, dalilin da ya sanya ɗalibai suka nutsu kenan. Kamar dai yadda na saba kullum a kujerar baya nake zama domin na fi jin daɗin cin karena babu babbaka ba tare da Malam ya yi saurin ankarewa ba.

A wannan ranar ma a bayan na zauna ni kaɗai tare da kifa kaina a kan tebur na janyo babbar wayata daga jaka na shiga manhajar adana littafai da ke kan wayar domin fara abin da na saba yi na karance-karancen littafan batsa.

Daidai lokacin da Malam ya fara biya wa ɗalibai karatun Alqur’ani a daidai lokacin na fara karanta wani sabon littafin batsa mai suna GIDAN DAƊI na wata marubuciya ɓoyayyiya mai suna Mrs Mahabeer.

Ƙwararriya ce a wurin rubuta alfasha, kamar yadda na ƙware a karanta alfashar duk da cewa ina sane da haramun ne amma kullum idan ban karanta ba ba na samun nutsuwar ruhi.

Wani abin mamaki duk da damuwar da nake ciki ta faru da ni ne silar irin wannan karatun amma hakan bai saka na daina ba, abin ya zame mini tamkar shan taba muddin ban yi ba ba na samun sukuni a zuciyata.

Ƙarin abin mamakin duk lokacin da na fara karatun komai girman damuwar da nake ciki nakan neme ta na rasa a lokacin nishaɗi ne zai maye gurbin ta sai bayan na kammala damuwar za ta samu damar dawowa a matsugunninta.

Na yi nisa a duniyar shauƙi kawai na ji ana girgiza kafaɗata, firgigit na yi tamkar wacce ta dawo daga duniyar mafarki. Asiya da take zaune a gabana ce ta girgiza kafaɗar tawa bayan na ɗago kai na kalle ta ta ce
“Malam ya ce ki matso ki karanta.”

Na yamutsa fuska kamar wacce ta ga kashi sannan na ce “Kawai ke ki je ya karanta mikin.”

“An fa kammalawa kowa karatunsa ke kaɗai kika rage.” Ta ba ni amsa.

Sanin halin naci irin na Malam ya saka na ɓoye wayata a muhallin da ta fito sannan na ɗauki Al qur’anina kamar da gaske na nufi wurin shi cikin nutsuwa na zauna tare da buɗe littafin.

“Ehem wace Sura ce?”

“Kahafi.” Na faɗa kamar wacce aka yi wa dole. Ya dube ni yana haɗe fuska tare da watso mini tambaya, “Noorhan wai me ya lalata miki ƙwaƙwalwa ne? Sama da wata ɗaya kenan ina maimaita miki wannan surar amma har yanzu ba ki iya ta ba.” Ban ce da shi komai ba sai birtsino leɓe da na yi kaɗan a raina na ce
“Da dai karatun novels ka tambaya nan na fi faɗi da yalwa.” Bai san me nake tattaunawa da zuciyata ba don haka da ya ji shiru alamun ba zan amsa masa ba sai ya ɗora zancensa da faɗar, “Bismillah karanta.” Yana tsare ni da ido kamar wanda aka cewa idan ya ɗauke idonsa a kaina zan gudu.

Nan na fara inda-inda na rasa inda zan kama don kuwa rabona da yin bitar karatuna har na manta. Ganin da gaske zan ɓata masa lokaci ya ba ni umurnin ci gaba da zama a gaban kujerar da nake sa’annan ya fara yi mana nasiha kamar yadda ya saba.

A ranar ya taɓo nasiharsa a kan manyan zunubai a addinance, kuma nasihar tasa kacokan ta tattara a kan haramcin zina, misalanta da illololinta. Bayan kowa ya nutsu ya ci gaba da bayani kamar haka: Allah maɗaukakin sarki yana cewa a cikin Alqur’ani mai girma,

Bismillahir-rahamanir rahim
“Wala taƙarabuz-zina innaha kana fahishatan wa saa’a sabila.” Ma’ana; “Kada ku kusance zina haƙiƙa ita zina alfasha ce kuma mummunar hanya ce.”

Idan mu ka yi la’akari da faɗar Allah maɗaukakin sarki, bai ce kada ku yi zina ba, sai ya ce kada ku kusance ta. Bi ma’ana kada ku aikata abin da zai iya saka ku aikata ta.

Mene ne waɗannan abubuwan da ke kusanta bawa da zina?”

Ya ɗan yi jim yana rarraba idanunsa a ajin tare da gyara zamansa sannan ya ci gaba da cewa, “Na farko daga cikin su akwai sakakkiyar magana ko na ce yasasshiyar magana mai nuna cewa mutum yana da ra’ayi da ita zinar. Misali hirar batsa a furuce ko a rubuce.”

Yana faɗar hakan sai jikina ya yi sanyi a ɗan gajeren lokacin da bai fi sakanni biyu ba na tuna ranar farko da na fara hilatar Amir da hirar banza a chart. Malam bai ba wa ƙwaƙwalwata damar linƙaya a duniyar tunani ba ya sake cewa,

“Abu na biyu shi ne miyagun wassani kamar wasar duka ko kuma wasar idanuwa irin su jan gira, kanne ido da sauran su. Sa’annan akwai hanyoyin sadarwa irin hirarraki (charts) waɗanda ake yi na zamani kamar yadda kowa ya sani a nan ma mutune da yawa sun kusantar da kansu da abubuwan da ke janyo zinace-zinace ta hanyar tura bidiyoyin batsa, sitiku, sautuna na banza da littafan batsa.”

Da ya zo kan wannan gaɓar sai da na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da sunkuyar da kaina ƙasa don sai na ji a raina kamar nasihar tashi da ni yake yi, ko kuma ya san abin da na aikata kuma nake kan aikatawa.

Ajin ya yi tsit ba ka jin komai sai motsin iskar fankar da ke kaɗawa, kamar ba wasu rayayyun halittu a cikin ɗakin karatun, da dukkan alama jikin kowa ya yi sanyi kuma nasihar tana ratsa su. Ina nan a sunkuye na sake cin karo da muryarsa yana faɗar
“Annabi ( s a w ) yana cewa duk wanda ya tsare abu biyu lallai zai shiga aljanna, waɗannan abubuwan guda biyu su ne baki da al’aura.

Akwai mai wata tambayar game da waɗannan bayanan kafin mu je ga bayanin nau’o’in Zina?” Shiru ba wanda ya tamka masa. Malam Hamisu ya yi murmurshi mai sauti kana ya ci gaba da cewa,

“Na ji duk kun yi shiru da alama kuna jin kunya ko? Na san kuma wasu daga cikin ku za su ji haushina a ransu har su ce me ya sa zan tara yara masu ƙarancin shekaru kamar ku ina yi musu wannan nasihar?” Bai jira an amsa masa ba da yake tambayar ma bai yi don a amsa ba don haka ya ci gaba da cewa,

“Amsar ita ce icce tun yana ɗanye ake tanƙwara shi, idan ya bushe ba ya tanƙwaruwa sai dai ya karye. A yau muna cikin wani irin rikitaccen zamani da waɗancan abubuwan da na lissafa suka halakar da da yawa cikin matasanmu masu tasowa ire-iren ku. Da yawa ƙananun matasa kamar ku sun faɗa damuwa, wata ma har ta yi ciki dalilin waɗancan matsololin da kuke yi wa kallon ƙananu. Kuma ma a mafi yawan lokuta ƙananun matsaloli ne suke rikiɗewa su zama manya ta yadda har za a rasa mafita wasu lokutan, shi ya sa na ke sanar da ku domin kare ku daga faɗawa kwazazzaɓon nadama.”

Zuwa lokacin na gama tsarguwa musamman da na ɗago kaina na ga idanuwansa ƙyam a kaina, sai nake ji kamar da biyu yake nasihar don haka na ɗaga hannu murya a sanyaye na ce “Ya mu’allim li haaja.”

Bai tamka mini ba sai alama da ya yi mini da hannu wacce ke nuni da ya ba ni dama. Damar da na samu kenan na gudu daga ajin na koma can wani lungu da yake bayan ajujuwan namu na zauna tare da haɗa kai da gwuiwa a take na ji kukan nadama yana zuwar mini. Ina kuka ina tunanin mafita a cikin wannan al’amari na tsaka mai wuya da na tsinci kaina.

‘Allah ga waɗannan marubutan da suka yi silar lalata tarbiyyata, Allah kai ne masanin ilimin gaibu kai ka san yadda za ka yi da bayinka ina neman adalcinka.’ Na faɗa a zuciyata ina mai ci gaba da rera kukana cikin wani irin sauti mai ba tausayi.

Ina tsaka da kukan na ji ƙarar ƙararrawa alamar an buga tara, na miƙe a sanyaye na goge fuskata da kyau sannan na wayance na shiga cikin ɗalibai kamar yadda aka saba gudun tuhuma.

Safiya ce ta zo kusa da ni tana tambaya ta me ya hana ni dawowa aji? Cikin yaƙe na samu wani yasasshen uzurin na ba ta tare da faɗar “Mu je ki raka ni na siyo awara yau haka na fito ban sakawa cikina komai ba garin sauri.”

Zahiri na yi hakan ne don na samu ta daina tuhuma ta a kan rashin komawa aji da nake da tabbacin ba zan iya faɗa mata dalilin ba. Ba ta yi mini musu ba muka rankaya zuwa cikin makarantar inda masu sana’a ke zama, na sayo mana awarar ɗari ita kuma ta saya mana fiyawota guda biyu muka koma bakin rumfar ajinmu muka zauna.

Ina fara ci na ji wani irin amai yana taso mini a take na dawo da wanda na haɗiye na shiga sheƙa amai a galabaice. Daliban da ke wurin suka yo cincirindo a kaina kowa na son sanin abin da ke faruwa da ni. Safiya da wasu biyu cikin ɗaliban ne suka taimaka mini da ruwa na wanke fuska ta da jikina na koma na zauna.

Ganin duk na yi laushi kamar sabon biredi ya saka Headmaster ya yi mini umurnin komawa gida tare da faɗar “Ki bari sai kin ji sauƙi sosai sannan ki dawo, Allah Ya ƙara afuwa.” Na amsa da amin ina noce kai ƙasa ganin irin kallon ƙurillar da yake bi na da shi kamar mai son gano wani abu a tattare da ni.

Safiyan ce dai ta miƙo mini jakata ko cikin ajin ban koma ba na fice daga makarantar ina saƙe-saƙe a raina.

‘Wannan matsalar fa sai daɗa girma take, Allah Ka yafe mini Allah ka tausaya mini.’ na faɗa a zuciyata.

A maimakon na durfafi cikin unguwa don zuwa gida kawai sai na nufi babban titi na tare abin hawa da nufin zuwa Abubakar Tafawa Ɓalewa Teaching Hospital da ke cikin ƙwaryar garin Bauchi. Na yanke a raina zan je na ga Dr Saif ko da Nuriyyah ba ta tare da ni, wannan karon ba wai don ya zubar da abin da ke cikina zani ba, zan je ne da wata manufar dabam.

Ummu Inteesar ce

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sharri Kare Ne 1Sharri Kare Ne 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×